Zafafan Kalaman Soyayya

  • Home
  • Zafafan Kalaman Soyayya

Zafafan Kalaman Soyayya Zafafan kalaman soyayya domin nishadin masoya
(2)

Slm Duk Kanni Yabo Da Aminci Suntabba Ga Tauraruwa Xuciyana Kasan Cewarki Cikin Farin Ciki Shine Abinda Xuciyana Take Bukata ? Ya sahibana Namallaka Miki Xcyt Naki Kawai Nake Jira Dan Syyyrk Ta Xamo Jinin Jikina Aduk Duniyanna Kece Kika Sace Mun Xcyt Idan Nakalli Idanuwanki Ko Naga Fuskanki Jina Nake Tamkar Namallakeki Ina zunzurutun SONKI

29/12/2024

Big shout out to my new rising fans! Rabi U Abdullahi

24/08/2024

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Jibril Adamu Aliyu, Baba Black Sa'a, Fahad Kabir Abdullahi, Salisu Salis, Moubarak Mannirou, Mous'ab Abdoulkadir, Nana Khadeejarh, Itz Matazu, Laouali Baba, Aisha Saifullahi, Khazeem Alhassan, Aleeyou Aleeyou, Abu Adam Gurawa, Real Ibrahim Ashiru, Khalil Muhammad, Abdullahi Umar, Mutari Dan Malan, Deejart Aleeyu, Zaharabinne Saidu

A kowane lokaci ina wani fata, fatan Allah Ya bar mu tare har abada, ina ji a jikina hakan zai kasance, saboda kin kasan...
28/03/2024

A kowane lokaci ina wani fata, fatan Allah Ya bar mu tare har abada, ina ji a jikina hakan zai kasance, saboda kin kasance a cikin zuciyata na tsawon rayuwata tun kafin haduwarmu. Ina sonki.

• Son da nake yi miki ya zarce adadin taurarin da ke mamaye sararin samaniya a cikin kowane dare. Ko da a ce za mu yi fada a kowace rana, son ki ba zai taba raguwa ba a cikin zuciyata. Son ki nake masoyiyata, irin son da bai da farko b***e karshe.

• Ni da ke tamkar ruhi ne da gangar jiki, idan babu daya, dayan ba zai samu ba. Ina son ki.

• Idan da a ce zan zamo ruwan hawaye a cikin idanuwanki zan kasance cikin zubowa a saman kumatunki na gangaro izuwa labbanki, amma da a ce za ki zamo hawaye a cikin idanuwana ba zan bari ki zubo ba daidai da dugo daya, domin gudun kar na rasa ki. Ina son ki.

• Ba zan iya yi miki alkawarin wadata ki da dukkan wani abu da yake a duniyar nan ba, amma na yi miki alkawarin ba ki dukkan wani abu da ya kasance mallakin zuciyata ne saboda kin mallake ta, ta zama taki har abada.

Ramadhan Kareem hubbina fatan kasancewa cikin farin ciki 🕊️🕊️🕊️ 🌙🌙🌙

Murmushin ruhi daya baya iya Gina ruhi biyu matukar biyun ruhin za su kasance daya ke iya Murmushi daya baya iya Murmush...
23/03/2024

Murmushin ruhi daya baya iya Gina ruhi biyu

matukar biyun ruhin za su kasance daya ke iya Murmushi daya baya iya Murmushi

SO bazi ginu a cikin gangar biyunan junan ba

Ita fa aikan sakon SO daka ZUCIYA ne izuwa wata ZUCIYAR

mai zai hana muradi ya zamo daya kaga gangar jiki zata zo a biyu Murmushi a biyu

Shakuwa a biyu mazaunin tadin rai a biyu ita kau ruhin zata cure ta zo a mazauni a gudan daya

Kaga harafi biyu na kalmar SO ya cure ya zamo a daya haka masoya ya kamata su kasance

SO DUNIYAR HALITTAR

""ANWAR""(Untold Story) Fitowa Ta Ashirin Da Shida (26)Mubarak El SharawyBayan Mahaifin tina ya sanar da ita cewa ya sam...
04/03/2024

""ANWAR""
(Untold Story)

Fitowa Ta Ashirin Da Shida (26)
Mubarak El Sharawy

Bayan Mahaifin tina ya sanar da ita cewa ya samu labarin tana soyayya da dan bahaushe musulmi, tina bata boye masa ba ta tabbatar masa, inda yake tambayarta meyasa ta antaya chakwakiyar soyayya da dan bahaushe musulmi

Tina tace dashi naji ina sonsa ne sbd kyawawan dabi'unsa wanda addininsa musulunci ya koyar dashi, da kuma wanda al'adunsa na bahaushe ya koyar dashi

Babanta yace menene cikin addinin musulunci banda kazanta, ta'addanci dacin zarafin diya mace da tauye mata yanci?

Tina tace aikam baba babu addini mai tsafta kamar musulunci, babu addinin dayazo da zaman lafiya kamar musulunci, hakama babu addinin daya bawa mata yanci kamar musulunci. Meyasa nace haka baba?

Saboda musuluncine yake banbance maka fari da baki, abu maikyau da mara kyau, duk abunda musulunci ya haneka dayinsa zai fada maka illolinsa, idan kuma ya umurceka dayinsa sai fada maka amfaninsa,

Kamar misaline, musulunci yace kayi sallah, domin ita sallah tana hana mutum yin abubuwa marasa kyau, musulunci yace kayi azumi, domin azumi yana kara lafiya da karfin imani, kana azumi zaka dingajin yunwa, hakan zaisa ka dinga tunawa da yadda marasa damar cin abinci sukeji idan s**a rasa abinci, kaga zaka taimakesu, musulunci yace kayi zakkah, zakkar tanasa Allah ya yafe maka kura kuranka da laifukanka.

Batun wata mata yanci, abinda musulunci ya fara korewa kenan a dabi'un jahiliyya, a jahiliyya idan an haifi mata ana biznesu da ransu, zuwan musulunci ya hana, a jahiliyya mata basu da gado, zuwan musulunci yace a basu gado da kaso daya cikin kaso biyu da namiji zai samu, musulunci yace mu killace mata, budurwace ko matar aure, shiyasa suke suturta jikinsu da hijabi, baba ko abune kaje siya kaga an lullubeshi da wani abu kasan abun nan yana da daraja, meyasa ake saka biscuits ko sweet a leda? Sbd kimarsa

Mu Hadu A Kashi Na 27
Ina Godiya Masoya

15/02/2024
Zafafan Kalaman soyayya na ranar masoya 1Kasancewar ki a tare da ni, ya sa ni jinkaina a matsayin wani mutum mai daraja ...
15/02/2024

Zafafan Kalaman soyayya na ranar masoya 1

Kasancewar ki a tare da ni, ya sa ni jin
kaina a matsayin wani mutum mai daraja ta musamman. Ina son ki, so irin wanda kalmomi ba zasu iya bayyanawa ba. Kece kyakkyawar Macce da na taba gani a cikin rayuwata. Hakika babu kalarki A duniyata .

Barka da zagayowar ranar masoya ta Duniya.

Kome Rahama Sadau Take Kokarin Nunawa? Mubarak El Sharawy
23/01/2024

Kome Rahama Sadau Take Kokarin Nunawa?
Mubarak El Sharawy

Alhamdulillah!  Alhamdulillah!!  Alhamdulillah!!! A Hukumance An Sanya Rana/Watan Daurin Aurena (October 2024)Kodai Ya K...
12/01/2024

Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!

A Hukumance An Sanya Rana/Watan Daurin Aurena (October 2024)

Kodai Ya Kasance 5/Oct Ko 12/Oct Ko 19/Oct Ko 26/Oct. Sai Abunda Hali Ya Bada

Babu Abin Farin Ciki DaTaya Murna Daya Taba Faruwa Dani Kamar Wannan.

Indai Kayi Farin Ciki Kuma Kinji Dadin Wannan Labarin Kuyi Min Posting Na Musamman Da Wannan Hoton Dan Ku Tayani Murna Da Fatan Alkhairi

He We Go!




10/01/2024

Assalamualaikum Jama'a Nine Naku Mahmoud A Yusuf Ina Tafe Maku Da Wani Tsrabane Bayan Jina Da Kukayi Kwana Biyu Shiru

Wannan Tsaraba Dai Shine Wani Labarina Ne Nakeso So Na Baku Kuma Labarina Soyayyane Don Idan Kuna Shielrya Kowa Ya Karkade Kunnensa Ya Saura Gobe Idan Allah Ya Kaimu Zan Fara Sakin Maku Shi Amman Sai Idan Naji Daga Gareku

Kunaso ....?
Eh ko Aa

Insha Allah Gobe

Banida Director dayafimin Wannan Bawan ALLAH a Kannyword Wato SARKI ALI NUHU Ga kadan daga cikin fina finai sa1 MANSOOR2...
08/01/2024

Banida Director dayafimin Wannan Bawan ALLAH a Kannyword Wato SARKI ALI NUHU
Ga kadan daga cikin fina finai sa

1 MANSOOR

2 GAMU NAN DAI

3 SARKI GOMA ZAMANI GOMA

4 MARIYA

5 BANA BAKWAI

6 ZAINABU ABU

7 MADUBIN DUBAWA

8 ADAMSY

9 HAFEEZ

10 MUJADALA

11 SAREENA

12 KAMANNI

13 FATI

14 HAUWA KULU

15 NIDAKE MUNDACE

WANNE FILM DINSA YAFI BURGEKA
©Mubarak El Sharawy

Yareeman Zango (Prince Zango) Mubarak El SharawyBana Tsammanin Tarihin Masana'antar Shirya Finafinan Hausa Zai Cika Bata...
05/01/2024

Yareeman Zango (Prince Zango)
Mubarak El Sharawy

Bana Tsammanin Tarihin Masana'antar Shirya Finafinan Hausa Zai Cika Batare Da Ambatan Sunan Adam A Zango Ba, Adamu Suna Daga Cikin Wadanda S**a Daukaka Darajar Wannan Masana'antar

Duk Da Yake Bai Samu Yabon Daya Kamata Ba Wajan Hukumomi Saidai Allah Ya Jefashi A Zukatan Al'umma

Duk Shekarun Dana Kwashe Ina Kallan Finafinansa Na Kiyaye Wasu Roles Guda Uku Da Dole Saidaishi Ne Zai Hau Yayi Kyau

(1)Zallar Nuna Biyayya Ga Iyaye Koda Kuwa Zai Cutu
(2)Isar Da Wani Sakon Addini A Shirin
(3)Soyayya Da Sadaukarwa

Duk Shirin Da Ake Bukata Masu Kallo Su Amsa Da Hannu Bibbiyu Wajibine Ya Nemo Adamu,

Shine Jarumi Na Farko Daya Hada Komai, Yana Fitowa A Film, Yana Shirya Film, Yana Bada Umurni, Yana Rubuta Film, Yana Tsara Bilm, Yana Kidan Taushi, Yana Waka, Yana Rubuta Waka, Yana Koya Rawa, Yanayin Komai

Bansan Kowanne Shiri Nashi Bane Zan Ambata Wanda Yafi Burgeni Amma Kadan Daga Cikinsu Akwai

Raga
Sai Wata Rana
Ga Duhu Ga Haske
Namamajo
Ga Zara Ga Wata
Ahlul Kitab
Zurfin Ciki
Maya

Shin Ya Kake Kallan Tasirin Adamu A Kannywood?
Shin Atare Da Adamu Meyafi Burgeka?
Wanne Shiri Nasa Yafi Burgeka?

""Sirrin Ga Duhu Ga Haske""Bana Tsammanin An Tabayin Shiri A Masana'antar Kannywood Kamar Wannan Shirin.. Shirine Wanda ...
29/12/2023

""Sirrin Ga Duhu Ga Haske""

Bana Tsammanin An Tabayin Shiri A Masana'antar Kannywood Kamar Wannan Shirin..

Shirine Wanda Ya Tabo Bangarori Guda Hudu Na Rayuwarmu..

(1) Addininmu (2) Al'adarmu (3) Soyayyarmu (4) Zamani

Anyi Shirin Birni, Anyi Shirin A Karkara, An Taba Bangaren Addini, An Taba Bangaren Al'ada

Wannan Shirin Ya Matukar Daukaka Darajar Addinin Musulunci Musamman Ga Wanda Basuyi Imani Da Addinin Ba,

Indai Kai Ba Musulmi Bane Ka Kalli Shirin Ga Duhu Ga Haske Saika Sassauta Kiyayyar Da Kakewa Musulunci

Haka Indai Kai Musulmi Ne Ka Kalli Shirin Nan Sai Ka Karajin Musulunci Ya Kara Kwanta Maka A Rai

Da Bukatar Kaje Ka Sabunta Kallan Wannan Shirin Domin Zai Kara Kayatar Dakai Sosai.

Jinjina Ga Malam Aminu Saira. Allah Ya Kara Basira

♥ Babban Sakamakon Dazan samu a wannan ranar shine ganin murmushi da annuri a fuskarki alokacin da muka hadu. Ba ina nuf...
29/12/2023

♥ Babban Sakamakon Dazan samu a wannan ranar shine ganin murmushi da annuri a fuskarki alokacin da muka hadu. Ba ina nufin hakan ne babban sakamako ba, ina nufin shine sakamako mafi muhimmanci a wannan ranar, saboda kin bayyana min kina sona, nima na bayyana miki ina sonki.

GA LAKANIN DAINA JIN SANYI😂Karda ki so ɗaya, kuma karda ki so biyu, amma dai ki ci-gaba da son ɗaya wadda ta mace a kan ...
26/12/2023

GA LAKANIN DAINA JIN SANYI😂

Karda ki so ɗaya, kuma karda ki so biyu, amma dai ki ci-gaba da son ɗaya wadda ta mace a kan son ki. Tauraruwar boye kece abun alfaharina.

Kalmomi na kasancewa ma'abota sauƙi wajen furtawa a dukkan lokacin da SO ya kasance shi ne harshen furtawar.

Zuciyata na yin haske a dukkan lokacin da muke tare, na kan shiga damuwa idan kika nesanta da ni. Duk da ka zamo mallakina amma zan so ki kasance mai kare min kanki daga harin da sauran maza zasu ke kawo miki a duk inda k**e. Fatan kina lafiya tauraruwar boye

Dandalin daukar shirin MADUBIN DUBAWA Shekaru 11 das**a wuce 2012👈 Shin meya birgeku game da wannan Shirin?
20/12/2023

Dandalin daukar shirin MADUBIN DUBAWA Shekaru 11 das**a wuce 2012👈 Shin meya birgeku game da wannan Shirin?

Rabuwar da baza'a kara haduwa ba har abada. Rabuwa tsakanin ma'abocin masararfi da Jaggu wato Pk. daya daga cikin dauka ...
19/12/2023

Rabuwar da baza'a kara haduwa ba har abada. Rabuwa tsakanin ma'abocin masararfi da Jaggu wato Pk. daya daga cikin dauka mafi Jan hankali da taba zuciya a cikin finafinan India.

Film din da yafi kowane film kawo kudi a lokacin sa. INDIA, OVERSEAS, WORLDWIDE.

Film din da ya fara kai 300cr a box office.

Film din da Aamir khan ya gwammace mutuwa ko kuma barin India sabida tsantsar nuna tsana da qiyayya da ya dinga samu daga mutanen Hindi.

RAJKUMAR HIRANI DA BADA UMARNIN YIN FILM DIN, ABIJIT JOSHI DA RAJ KUMAR HIRANI DA RUBUTAWA SANNAN VV CHOPRA DA SHIRYA FILM DIN 👀AMMA AAMIR KHAN DA KARBAR HUKUNCI.



kun fahimta ko sai an fahimtar daku©Mubarak El Sharawy
18/12/2023

kun fahimta ko sai an fahimtar daku

©Mubarak El Sharawy

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zafafan Kalaman Soyayya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Zafafan Kalaman Soyayya:

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share