23/03/2024
Yadda namiji ke bayyana so da ƙaunar sa ya sha banban da yadda mace take nuna nata.
Shi namji yafi nuna nasa a aikace fiye da a kalamai, a inda ita kuma mace tafi nuna nata a kalamai da kuma a aikace.
Sai dai shi namiji yakan bayyana nasa a kalamai da aikace a inda ya samu kyakkyawan shimfida a rayuwar mace, matuqar mu'amalar su ko zamantakeqar su akwai girmamawa, mutuntawa, jan sa a jiki, sakewa, ba tsangwama, kushiya, kawaici akan raunin sa, ya samu yabo da jinjina, ga kulawa, ga shimfidaddun kalamai masu k**a zuciya da jan hankali, ga kiyaye umurni da kiyaye buqatar sa.
Matuqar yana son ki, tabbas kin masa shimfidar da zai nuna miki ƙauna a aikace wani lokacin har a kalamai, sai dai in baki da lura da sa hankali ba lallai ki gane yanayin yadda yake nuna miki soyayya ba tunda a tunanin mace yadda take nuna soyayya haka take son a nuna mata soyayya alhali shi namiji ba haka ya dauki so da har zai bayyanata yadda mace ke bayyana nata ba.
Ke dai sa hankali a abunda yake miki, ke da kanki zaki gane namijin dake son kine kadai zai miki abunda yake miki. Wannan abunda yakeyin ya wadatar sai ki cigaba da masa shimfidin da zai cigaba da baje miki kolin irin tashi soyayyar.
Da irin haka ake moran zama da miji.
Ubangiji ALLAH yayi mana Jagora Amin