Fityanu MEDIA HOUSE

Fityanu MEDIA HOUSE News and report

30/07/2024

Albishirinku yan uwa!
FASSARAN LITTAFIN TAFSIRIN MAULANA SHEIKH ANA KAN FASSARANSA CIKIN HARSHEN HAUSA

30/07/2024

Ba Gazawar Gwamnati Kan Lamarin Yau Da Kullum Yasa Zanga Zanga Ba,

Tsawwalawan Yan Kasuwa Da Boye Abinci a Rumbun Su Shine Ya Fusata Mutane Yin Zanga Zanga, Domin Gwamnati Tana Iyayinta

Fatan Allah Yakarawa Kasata Nigeria Albarka

Muhammad Yaa Sayyidy

30/07/2024

JAN GWARZO

Shi din ya kasance wani irin mutum wanda bai da wata manufa da ta fice gina al'ummar MANZON ALLAH (S.A.W), farin cikinsa farin cikin al'umma, bakin cikinsa shine ganin al'umma cikin damuwa.

Babu shakka samuwar wannan jami'a a irin wannan lokaci wani sinadarin magani ne, da zai zamo silar samar da magani ga dimbin damuwowi da ke addabar harkar ilmi, musamman bangaren 'ya'ya mata.

ALLAH YA KARA KULAWA DA SHA'ANINSA, YA BASHI KARIYA DAGA DUKKANIN ABIN KI, YA TSARE SHI SHARRIN HASSADA DA MAKIRKIN MAKIYA.

29/07/2024

ABINDA MUKE ZATON ZA SU AIKATA KENAN, SHI SUKAJE SUNA YI.

KA TSOKALE MUSU IDANU, KUMA BA ZASU TABA YIN NASARA AKANKA BA IMAM!

Abin ya kasance abin mamaki matuka, ace a yau Malamai ne suke bibiyar guraben jagorori yan Siyasa da nufin su taimakesu wajen shirya manakisa da makirci dan kawar da wani jagora cikin jagorori kawai dan ya kasance mai fadin gaskiya komai dacinta a kan kowa.

Wani labari na riskarmu ta karkashin kasa, tuni wasu daga Malamai sun soma kiraye-kiraye tare da bibiyar wasu manyan jagorori da nufin kulla makirci ga Imam suna masu juya ma'anar zancensa game da zanga-zanga da kuma son ganin dayansu ya kasance a bigiren da yake, domin fadada harkokinsu na kulla alaka da masu mulki da yan siyasa dan neman abin Duniya.

Ku kwana da sanin cewa: Shifa Imam tuni ya gama bayani cikin zancensa cewa : Ko rayuwarsa zai iya bayarwa a kan nemawa talaka mafita, kuma ku sani, lallai tuni ya gama bayani cewa : WADANDA YAKE SON KOYI DA SU A RAYUWA, BABU GUDA CIKINSU DA LIMANCI SHI NE YA ZAME MASA SILAR KAIWA ZUWA GA INDA YA JE SHI, saboda haka idan kuka ga yabar limanci a wannan Masallaci, to lallai inda zai je shine mafi alkairi da inda ya baro.

MUNA ROKON ALLAH YA CI GABA DA KULAWA DA MUTUMCINSA, KIMARSA YA KIYAYE MASA ALFARMARSA ALBARKACIN MANZON ALLAH (S.A.W).

ALHAMDULILLAH.

29/07/2024
29/07/2024
20/07/2024

Lafiya Danisan Kwana Maulana

20/07/2024

SHIN YA KUKE GANIN WANNAN KASA ZATA KASANCE, DA ACE AKASARIN MALUMA SUN KASANCE TAMKARSA CIKIN FADAWA SHUGABANNI GASKIYA A KOMAI...?

20/07/2024
ALLAH JIKAN MAZAN FAMAINNAL'ILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN.Allah Yayiwa Ɗaya Daga Cikin Jagororin Agajin Fityanul Islam (...
25/06/2024

ALLAH JIKAN MAZAN FAMA

INNAL'ILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN.

Allah Yayiwa Ɗaya Daga Cikin Jagororin Agajin Fityanul Islam (Initiative) Na Ƙasa, Umar Ibrahim Lagos Rasuwa, Allah Yajiƙanshi Yayi Mishi Rahama..

Sanarwa:

25/05/2024
14/05/2024

KU KOYAWA YARANKU HALAYE UKU.
1. Yawan gaishe da na gaba dasu.
2. Nutsuwa da barin wasa ahanya.
3. Futa cikin kyakykyawar shiga.

KU HANA YARANKU HALAYEN NAN.
1. Yawan yawace-yawace.
2. Yawan Abokai/kawaye barkatai.
3. Rashin kunya da fadace-faface.

KU RIKA GWABE BAKIN YARANKU
1. Idan suna sa baki a maganar manya
2. Idan suna kawo tsegumi da gulma.
3. Idan suna zagi ko karyata manya.

KUYI MUSU HORO ME TSANANI
1. Idan suna wasa da Sallah.
2. Idan s**a fara kwadayi da roko
3. Idan s**a fara karya da lalaci.

KU KARA JAWO YARANKU JIKI
1. Idan s**a balaga.
2. Idan basu da lafiya.
3. Idan kuna gida a zaune.

KU KWADAITAR DA YARANKU
1. Nacin karatu da rubutu.
2. Dagewa wajen cimma buri.
3. Lada da nasara in anbi hanyar Allah.

KU NUNAWA YARA MUHIMMANCIN
1. Riko da Addinin musulunchi.
2. Zumunchi da ziyarar dangi.
3. Lafiya, Lokachi da chance/kuruciya.

KU DAINA WADANNAN AGABANSU
1. Bayyana tsiraici/mu'amalar aure
2. Wasan banza na kuruciya, kallo.
3. Bayyana rashin jituwa atsakaninku.

KU YAWAITA AGABAN YARANKU
1. Karatun Alqur'ani da salloli.
2. Aikata gaskiya da Rukon Amana.
3. Wadatar zuci da godiyar Allah.

SUKE JIN TSORON KU TA HANYAR
1. Tsawatar musu in sunzo da wargi.
2. Rashin barinsu babu abinyi.
3. Taqaita nuna musu so kuru-kuru.

KU DAGE KU CIREWA YARANKU
1. Tsoron mutuwa.
2. Tsoron talauchi.
3. Tsoron wanda baya tsoron Allah.

KU GOYI BAYAN YARANKU INHAR
1. sune ke da gaskiya.
2. Ba sa6o s**a aikata ba.
3. sunyi abu domin kare mutuncinku.

KUKE TSORATAR DA YARANKU
1. Illar Hadama.
2. Futinar rigima.
3. Hadarin taqama da girman kai.

KU RIKA SANARDA YARANKU
1. Asali da Tarihi.
2. Mutuwa da kabari.
3. Dadi da rashin sa.

KU BAWA YARANKU HORO NA
1. Taqaita cin abinchi.
2. Karancin Barchi da zaman hira.
3. Watsarda dogon buri da sharholiya.

Allah yasa idan munji muyi aiki da abinda muka saurara ameen ya hayyu ya qayyum..

21/10/2023

FIRST AID GROUP FITYANUL ISLAM NA NAJERIYA BABI NA JAHAR BORNO.FAG_FIN_BORNO_MEDIA."SAKON GODIYA ZUWA GA MAMALLAKIN TASK...
21/10/2023

FIRST AID GROUP FITYANUL ISLAM NA NAJERIYA BABI NA JAHAR BORNO.

FAG_FIN_BORNO_MEDIA.

"SAKON GODIYA ZUWA GA MAMALLAKIN TASKIYA ALFAIDA MEDIA"

Assalamu Alaikum !!!

Shuwagabannin Tawagar FAG/FIN Borno Media, Musamman YAKUBU MUSTAPHA GREMA Borno Media Admin Da RABIU BABAYO Borno Media Edita Muna Godewa Allah Tare da Miqa Sakon Godiya Ta Musamman Zuwa ga Mamallakin (TASKIYA ALFAIDA MEDIA) Daya Zabemu Daga Cikin Wayanda Zamu Dinga Wallafa Rubututtuka da Karatuttuka Ta Fannin Addinin Musulunci acikin Wanna Kafa (Page) Mai albarka na (TASKIYA ALFAIDA MEDIA) Mungode Da'irin Wannan Kauna Da Taskiya Alfaida Media Kuka Nunamana Ubangijin Allah Yabar Zumunci.

Shugaban Tawagar FAG/FIN Borno Media Co-ordinator Muhammad Alhaji Muhammad Yana Matukar godiya Ga Allah bisa Wannan Dama da Mamallakin Wannan Shafi Mai albarka (TASKIYA ALFAIDA MEDIA) Ya bawa Wasu Daga Cikin Shuwagabanni na Tawagar FAG/FIN Borno Media Fatan alkhairi agaremu Baki Daya.

"Muna Rokon Allah" Yabawa Yakubu Mustapha Grema da Rabiu Babayo IKon Sauke Nauyin da aka Doramana "Ubangijin Allah" Ya Ɗaukaka Darajar FITYANUL ISLAM Of Nigeria, "Ubangijin Allah" Ya Ɗaukaka Darajar Mamallakin Taskiya Alfaida Media Page, Alfarmar Sayyidul Wujudi Bijahi Annabi Muhammad (S.a.w)

"Ameen Ya Allah"

Write✍️
Rabiu Babayo
Borno Media Edita.

SIGN 📝
YAKUBU MUSTAFA GREMA
FAG/FIN/BORNO/MEDIA/TEAM

"Duk wanda kaga yasan kai Musulmi ne tare da hakan  ya iya furta kalmar bid'a, ko shirka akanka. To babu abun daya rage ...
20/10/2023

"Duk wanda kaga yasan kai Musulmi ne tare da hakan ya iya furta kalmar bid'a, ko shirka akanka. To babu abun daya rage masa gare ka illa ya jiraci Alkiyama domin ya dannaka cikin wuta. Idan ma dawani amfani daza kayi masa bai wuce yai amfani dakai lokutan zabe ba".

SHEIKH DR.HALLIRU MARAYA.

Address

Galadima Street Yelwa Shendam
Yelwa
940101

Telephone

+2347043059424

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fityanu MEDIA HOUSE posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share


Other Media/News Companies in Yelwa

Show All