05/06/2024
YANA DAGA SHARUDDAN DA IMAM HASAN (AS) YA SHARDANTAWA MU'AWIYYA CEWA A DENA ZAGIN IMAM ALI (AS).
-Sheikh Ibraheem Zakzaky (H)
To, akwai kuma yanzu wadanda s**a dauka ma kansu zagi na fitan arziki. To, ina kira ga ‘yan uwa da kar a mai da zagi da zagi, in mutum ya zage ka ka kyale shi. Yanzu da yake zamanin social media ana ta zage-zage a social media, to ina kira ga ‘yan uwa a dena zagi a social media, har sai ya zama in mun ga wani ya yi zagi mun san cewa ba a cikinmu yake ba. Ya zama mu ba dabi’armu ce mu yi zagi ba. Ba a zagi, an fahimta ai. Ba a zagi.
Akwai (Umayyawa), sun sabbaba, sun mai she da zagin Amirulmuminin (AS) sunnah tun yana da rai. Yana daga sharuddan da Imam Hasan (AS) ya shardantawa Mu’awiyya cewa a dena zagin Imam Ali (AS), kuma ya yarda, amma kuma daga baya aka dawo aka cigaba da zagin. Aka mai da zagin k**ar addini. Amma duk da haka (Shi’ar Ahlulbait) ba mai da martani s**a yi da zagin ba.
Ance ma Amirulmuminin (AS) da kansa lokacin da ya shiga birnin Basra, wata mata ta zazzage shi a gabansa, sai aka ji karan takobi ya fito cikin takobi, Malikul Ashtar ya zaro takobi shar, sai Amirulmuminin yace masa me za ka yi? Sai yace Ya Amirulmuminina baka ji abin da take fada bane? Sai yace ai zagina ta yi, shi kuma zagi ana ramawa da zagi ne ko a yafe, to na yafe mata. Sai dole Ashtar ya mai da takobin a kube.
Kuma Imam Zainul Abidin (AS) ya taba cewa wani daga cikin mabiyansa, in ka ga mai zagin Imam Ali (AS) me za ka yi? Yace, in zan iya zan kwakwale masa idanu ne. Sai Imam yace masa kar ka yi haka. Ni na kan ga mai zagin Imam Ali (AS) na yi masa sallama, na mika masa hannu mu gaisa. Haka s**a koyar da mu.
Kuma Amirulumininin (AS) ya ji wasu daga cikin mabiyansa suna zagin Mu’awiyya da mutanensa, yace A’a, ba zaginsu za ku yi ba, ku bayyana abubuwan da s**a yi ne wanda suke ba daidai ba, sai a fahimce su, amma ba zagi ba.
Zagi ba dabi’ar mumini bane. An fahimta ai. Saboda haka muna so ya zama in mun ga mutum ya yi zagi, to mu san cewa ba a cikinmu yake ba.
Na ga wani zagi da wani ya yi, lokacin da ‘Jurha’, wadanda aka ji ma rauni s**a zo, sai na bude musu hannuna ina nuna musu kun ga nima inda aka harbeni. To sai aka dauki hoton wajen, sai mutane suna ta ‘comment’, to sai wani ya dauki wannan hoton ya saka a wani wuri, da yake sun dauki ma’aikata, sai ya fara ‘comment’ da zagi, yace ai ku Shi’a jakuna ne!
To, me ya kawo batun jaki a nan? A baya su kan ce ai wane ma jaki ne, sai su saka hoton jaki. Ya zo a hadisi cewa duk wanda yacewa wani mutum jaki, to ranar Alkiyama Allah zai zo da mutumin yace to ni na halicce shi mutum ne, maishe shi jaki din. Ko zagi ake yi ba a ce da mutum jaki.
Saboda haka irin kalmomi irin wadannan mu fahimce su cewa in mun gansu ma na makiya ne. Ina so ya zama ‘yan uwa sun dauki wannan. Kar wani ya sake zagi! Da mun ga zagi mu san cewa wannan makiyi ne yake yi, ba a cikinmu bane, don ba dabi’armu bane, wani ya yi zagi amma ba mu ba, sai mu gane bambanci tsakaninmu da saura.
To, sai mu ce muku ruwanku mahassada, ko ku gane ko kar ku gane, ko ku yi bakin ciki ko kar ku yi, sai mu ce ma ‘mutu bi gaizikum!’, ku mutu da bakin cikinku ma. Ko me za ku yi ku yi, iyakanku dai zage-zage ne sai ku yi ta ta yi, da zagi yana kari da ya mana, da kuma yana canza fuskarmu da ya canza mana fuska, amma bai canza mana komai ba. Saboda haka ku ba da kokari in zagin zai fissheku.
Yankin Jawabin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) da yayi a Abuja. Ranar Yaumus Shuhada a Shekarar 1443/2022.
Daga Zauren Tafsir Da Jawaban Jagora