Wakar Ranar Tunawa da #Hausa ta duniya daga bakin Dr Aliyu U. Tilde, Kwamishinan Ilimin Jihar Bauchi.
Yau 26/8/22 Duniya ke tunawa da Harshen #Hausa
Harshen Hausa yazama daya daga cikin manyan harsukan da Duniya ke tinkaho dasu, manyan kafafen yada labarai na Duniya sai sake bude sashen yada labarai suke da harshen #Hausa, fassarar manyan littafai, labarai, rahotanni duk da yaren #Hausa.
Lalle abin alfaharine ace harshen #Hausa ya kai ga wannan daraja kuma acikin karamin lokaci. Wannan bazai rasa nasaba da fikirar da Allah yayiwa #Bahaushe ba.
Allah ya kara daukaka harshen #Hausa da #Hausawa a duk yadda suke a duniya, amin.
AMINCI NEWS
26/8/22
Jawaban Sanata Kashim Shatima akan taron NBA daya gudana a Jihar Legas
SIYASA: Ina sane na sanya takalman sau ciki na sinikas domin inji sukar da 'yan adawa mahalarta taron Kungiyar Lawyoyin Najeriya NBA, Inji Dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na Jam'iyyar APC Sanata Kashim Shatima.
Sanata Shatiman ya sanar da hakan ne a wani hoton bidiyo daya kara'de kafar sada zumunta aranar Alhamis 25/8/22.
Ataron da da'aka gudanar ranar Litinin data gabata a Jihar Legas, Sanata Kashim ya wakilci ubangidan nasa Mr Bola Tinibu, shigarsa ta dauki hankalin masu adawa da shi sosai, yadda ya sanya rigar kot, jan lakatayin sannan da takalman sau ciki na sinika mai makon sau ciki na koba shu.
Tsohon gobnan Jihar Bornon yace, shifa tsohon ma'aikacin bankine kuma wayayye, yayi hakan ne kawai domin jan hankalin 'yan adawa duk da cewar, wani dan takarar Shugancin kasa ne ya dauki dawainiyar yada farfaganda akan shigar tasa.
(Ga Hoton bidiyon makale da wannan labarin, amman yaren turanci ne).
____________________________
Zaku iya tuntubarmu ta wadannan hanyoyi:
Whatzapp: +2348082069359
Imel: [email protected]
page: http://surl.li/ciagi
Facebook Group: http://surl.li/ciagn
Whatzapp Group: http://surl.li/ciaqc
Twitter: https://3c5.com/GNYsD