05/12/2023
Ƙungiyar Arewa Media Writer's Tayi Kakkausar S**a Kan Kashe Mutane Fiye Da 100 Da Jirgin Sojojin Najeriya Yayi.
Daga Kungiyar Arewa Media Writer's
Haɗaɗɗiyar ƙungiyar Marubutan Arewacin Najeriya tayi Allah wadai da kisan masu Mauludi da rundunar sojojin Najeriya tayi a Tudun-Biri dake ƙaramar hukumar Igaba a jihar Kaduna bisa kuskure.
Kimanin karfe goma na daren ranar Lahadi 03/12/2023 al'ummar garin Tudun-Biri dake ƙaramar hukumar Igabi s**a fuskanci mummunan tashin hankalin da yayi sanadin rasa rayukan mutane kimanin 126 a wani harin sama da jami'an sojoji s**a yi kan wasu gungun mutane da suke tsaka da bikin Maulidi, a rahotannin da muke samu, jami'an sojojij sun jefa abun fashewar ne inda yayi sanadin halaka kimanin mutum 126 ciki har da maza, mata da yara da tsofaffi, sai dai hukumar sojojin ta ɗauki alhakin kisan gillar, inda tace harin ya afku ne bisa kuskure.
Wannan irin mummunan kisan gillar ne ya janyo hankalin kungiyar Arewa Media Writers baki ɗaya tun daga matakin kasa, jihohi 19 tare da babban birnin tarayyar Abuja har zuwa ƙananan hukumomin Arewa, muna kira da kakkausar murya ga gwamnatocin Najeriya da su gaggauta yin cikakken bincike kan lamarin, tare da ɗaukar matakin biyan diyyar rayukan da s**a salwanta a sanadin wannan harin.
Irin wannan mummunan hari kan talakawan da ba suji ba basu gani ba ya taba faruwa a jihar Borno kwanakin baya, inda gwamman mutane s**a halaka, a lokacin ma hukumar soji tace bisa kuskure ne harin ya faru, shikenan rayukan bayin Allah ya salwanta ba gaira babu dalili?
Kungiyar Arewa Media Writers tayi kira ga biyan diyyar rayukan da s**a halaka ne a garin Tudun-Biri don kaucewa faruwar irin haka a nan gaba, ta yadda kodan tunanin biyan diyya zai sa hukumomi su tsaurara bincike gabanin jefa abun da zai halaka mutane da yawa irin haka.