25/08/2022
*BAYANIN YADDA AKE YIN ISTIKHARA IRIN WACCE ANNABI YA KOYAR:*👇
Istikhara wata sallah ce da akeyi domin neman za'bin Allah madaukakin sarki game da wasu al'amura guda biyu da bawa yake neman zabin Allah a cikin ďaya daga cikinsu, misali kamar a harkar neman aure dadai sauran wasu al'amuran. Anan zamu fahimci cewa ashe ita istikhara ibadace kuma Annabi muhammadu ﷺ shine ya koyar da yadda ake yin ta, sabida haka duk wanda yayi wata istikhara ba irin wacce manzon Allah ﷺ ya koyar ba, to ya sani ba istikhara tabbatacciya yayi ba koda ma yayi babu wani tasiri da zatayi domin Allah madaukakin sarki baya karbar duk wata ibada har sai anyi yita a bisa koyarwar Annabi muhammadu ﷺ. Sahabi jabir (ra) yana cewa: *MANZON ALLAH ﷺ YA KASANCE YANA KOYA MASU ISTIKHARA A CIKIN DUKKAN AL'AMURANSU KAMAR YADDA YAKE KOYA MUSU SURA DAGA CIKIN AL'KURANI.* hadisin yana cikin *Sahihul Bukhari* kunga wannan yake nuna mana ashe ita itikhara annabi ne ya koyar da ita bawai kowa gaban kansa zeyi kawai yaje ya aikata abinda yaga dama a matsayin istkhara ba. Hal ila yau dai sahabi jabir yana cewa: Annabi yace: *IDAN 'DAYANKU YAYI NUFIN YIN WANI AL'AMARI TO YAYI SALLAH RAKA'A BIYU BA SALLAR FARILLAH BA SANNAN YACE* 👇
*اللهم إني أستخيرك بعلمك، وأستقدرك بقدرتك، وأسألك من فضلك العظيم فإنك تقدر ولا أقدر، وتعلم ولا أعلم، وأنت علام الغيوب، اللهم إن كنت تعلم أن هذا الامر _(ويسمي حاجته)_ خير لي في ديني ومعاشي وعاقبة أمري فاقدره لي ويسره لي ثم بارك لي فيه، وإن كنت تعلم أن هذا الامر شرلي في ديني ومعاشي وعاقبة أمري فاصرفه عني واصرفني عنه واقدرلي الخير حيث كان ثم رضني به.*
MA'ANARYA ADDU'ARALLAHSHINE: *YA ALLAH ALLAH INA NEMAN ZA'BINKA DA ILIMINKA KUMA INA NEMAN KA BA NI IKO DOMIN IKONKA, KUMA INA ROKONKA DAGA FALALARKA MAI GIRMA, DOMIN KAI NE MAI IKO, NI KUWA BA NI DA IKO, KUMA KAI NE MASANI, NI KUWA BAN SANI BA, KUMA KAI NE MASANIN ABUBUWAN FAKE(GAIBU). YA ALLAH! IDAN KA SAN CEWA WANNAN AL'AMARI* ( TO ADAI DAI NAN WAJEN SAI MUTUM YA AMBACI BUKATAR TASA MISALI YA ALLAH IDAN KASAN CEWA WANNAN SAURAYIN NAWA ALHERI NE GARENI... ) *ALHERI NE GARE NI A CIKIN ADDININA, DA RAYUWATA, DA KUMA KARSHEN AL'AMARINA, KA KADDARA MINI SHI, KUMA KA SAUKAKE MINI SHI, SANNAN KA ALBARKANCE NI A CIKIN SA. KUMA IDAN KA SAN WANNAN AL'AMARI SHARRI NE GARE NI A CIKIN ADDININA, DA RAYUWATA, DA KARSHEN AL'AMARINA, KA KAWAR DA SHI DAGA GARE NI, KUMA KA KAWAR DA NI DAGA GARE SHI, KUMA KA KADDARA MINI ALHERIN A DUK INDA YAKE, KUMA KA SANYA NI IN YARDA DA SHI* Yaku bayin Allah Wannan itace fa addu'ar istikhara wacce Annabi ﷺ ya koyar yanzu kuma za muyi bayaninta daki daki in sha Allahu.
*BAYANIN YADDA AKE YIN ISTIKHARA* Da farko dai Ita sallar istikhara bata da wani ke'bantaccen lokaci da akace dole sai a lokacin mutum zeyi a'a duk lokacin da wani al'mari ya bijirowa mutum da safe ne ko da rana da yamma ne ko da daddare dukkan wadannan lokutan ya halatta mutum yayi sallar neman zabin Allah a cikinsu, misali koda a lokudan da aka hana sallah ne indai sai kuma wani al'amari ya bijirowa muttm kuna yana bu'katar ya nemi zabin Allah a cikin lamarin to ya halatta yayi sallar istikharar domin neman zabin Allah ko da a lokutan da aka haramta yin sallah ne kamar yadda malamai s**a ce.
:- *NIYYA* kamar yadda muka sani a cikin shahararren hadisin Amirul muminin Sayyadin umar dan khad'd'ab cewa manzon Allah yace dukkan ayyuka basa yiwuwa/tabbatuwa sai da niyyoyinsu. To kamar hakane itama sallah istikhara bata tabbatuwa sai da niyya. Bayan mutum yayi niyyar sallar istikhara sai yaje yayi al'awala kamar yadda yake sallah bata ingantuwa sai da al'wala, Amma idan mutum yana da al'wala a lokacin da yake son yin istikharar kawai zeyi sallar ne babu bu'katar sai ya sake sabuwar al'wala.
:- *SALLAH* Mutum zeyi Sallah Raka'a biyu.
:- *SURORIN DA AKE KARANTAWA A CIKIN SALLAR ISTIKHARA Dangane da surorin da mutum zai karanta a cikin raka'o'in, Wani bangare na malamai s**ace a raka'a ta farko mutum ze karanta fatiha da suratul fatiha da suratul kafirun *(Qulya Ayyuhal Kafirun)* a raka'a ta biyu kuma mutum ze karanta suratul fatiha da suratul ikhalas *(Qul-Huwallahu Ahad).* Wani bangare na malamai kuma s**ace a raka'a ta farko mutum ze karanta fatiha da wadannan ayoyin
*(وَرَبُّكَ یَخۡلُقُ مَا یَشَاۤءُ وَیَخۡتَارُۗ مَا كَانَ لَهُمُ ٱلۡخِیَرَةُۚ سُبۡحَـٰنَ ٱللَّهِ وَتَعَـٰلَىٰ عَمَّا یُشۡرِكُونَ وَرَبُّكَ یَعۡلَمُ مَا تُكِنُّ صُدُورُهُمۡ وَمَا یُعۡلِنُونَ وَهُوَ ٱللَّهُ لَاۤ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَۖ لَهُ ٱلۡحَمۡدُ فِی ٱلۡأُولَىٰ وَٱلۡـَٔاخِرَةِۖ وَلَهُ ٱلۡحُكۡمُ وَإِلَیۡهِ تُرۡجَعُونَ)*
[Surat Al-Qasas 68 - 70]
A raka'a ta biyu mutum ze karanta fatiha da wannan ayar:
*(وَمَا كَانَ لِمُؤۡمِنࣲ وَلَا مُؤۡمِنَةٍ إِذَا قَضَى ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥۤ أَمۡرًا أَن یَكُونَ لَهُمُ ٱلۡخِیَرَةُ مِنۡ أَمۡرِهِمۡۗ وَمَن یَعۡصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَقَدۡ ضَلَّ ضَلَـٰلࣰا مُّبِینࣰا)*
[Surat Al-Ahzab 36]
:- *LOKACIN DA AKE YIN ADDU'AR:* Ana karanta addu'ar istikharan Bayan an idar da sallah, sannan kuma mutum ze iya karanta addu'ar istikharar bayan ya gama karatun tahiya lokacin daya kammala salatul ibrahim kafin ya yiya sallama.
:- *KAFIN MUTUM YA FARA ADDU'A* Zai fara da yabo da kirari ga Allah madaukakin sarki, Sannan sai yayi salatul ibrahim daga nan sai yayi addu'ar istikharar bayan ya kammala addu'ar sai ya rufe addu'ar da Salati ga Manzon Allah ﷺ Salatul ibrahim mutum zeyi.
:- *IDAN MUTUM YANA HALIN TSARKI* to ya jira har sai ya samu tsarki kamar me haila,jinin haihuwa d.s.s. baya halatta ayi sallar sai ana da cikakken tsarki. Amma idan ana tsoron Abinda za'ayi istikharar akan sa zai ku'bucewa kuma ana halin rashin tsarki to adaidai lokacin sai a nemi zabin Allah ta hanyar yin Addu'ar kawai ba tare da anyi sallar ba.
:- *IDAN MUTUM BE HADDACE ADDU'AR BA* Babu laifi ya rubuta a wani abin yana Kallon addu'ar yana karantawa Amma a haddace addu'ar shine yafi.
:- *IDAN MUTUM BE IYA KARANTA RUBUTUN LARABCIN BA* Babu laifi ya karanta addu'ar da hausa Amma a karanta da larabcin shine yafi.
:- *KASKANTAR DA KAI WAJEN NEMAN ZABIN ALLAH* ana so mutum ya dukufar da kansa wajen neman zabin ubangijinsa ya ajiye zabin zuciyarsa kada ya rinjayar da abinda yafi so yayin istikharar.
:- *SANYA YAQINI* ana so mutum ya sanya yaqini cewa lallai ubangiji zai datar dashi akan abinda shine mafi alkhairi a gare shi.
:- *TATTARA ZUCIYARSA YAYIN ADDU'AR* ana so mutum ya tattara zuciyarsa a lokacin fara addu'ar tare da tadabburin(hakaito ma'anonin) abin da addu'ar ta 'kumsa.
:- *HANYAR DA MUTUM ZAI GANE ZABIN ALLAH* mutum zaiji daya daga cikin al'amuran da yayi istikharar yafi kwanta masa a cikin ransa kuma za'a iya daukan dan lokaci kafin yaji hakan, sabida haka Ba mafarki mutum zeyi a nuna masa zabin nasa ba Kamar yadda wasu suke faďa, a'a kawai abin da yake shine mafi alkhairi mutum zaiji yafi kwanta masa a ransa zaiji yafi nutsuwa da daga daga cikin abubuwan daya nemi zabin, misali idan yaji abin ya fice a ransa bayan yayi addu'ar to kawai sai abar al'amarin, idan kuma yaji abin yayi matukar kwanta masa a cikin ransa shikenan sai ya rinjarayar da abin. idan kuma beji ya karkata a daya daga cikin abubuwan biyu ba Sai ya sake istikharar haka zai tayi har zuwa lokcin da zabin mahaliccinsa ya bayyana agareshi.
:- *BABU LAIFI MUTUM YAYI ISTIKHARA SAMA DA SAU DAYA* Babu laifi a maimaita istikhara fiye da sau daya idan yayi istikharar kuma be samu tabbaci a cikin zuciyar tasa ba, babu wani adadi da shari'a ta iyakance da ake yin istikhara.
Wallahu A'alam
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ
idan Anga Gyara A Sanar Damu 👏
=
=
Na So Kun San Tarin Lada Da Albarka Da Ake Samu Ta Hanyar Yada Ilimi Ko Wani Alkhairi
=
=
*ALLAH TA'ALA YASA MUDACE*