Zamani Writers Association

  • Home
  • Zamani Writers Association

Zamani Writers Association BARKA DA SHIGOWA WANNAN PAGE MAI ALBARKA. MUNA MAKA/KI FATAN ALKHAIRI, MUN GODE DA ZIYARTAR MU

🧟‍♀️🧟‍♀️                        🧟‍♀️🧟‍♀️*ALJANAR FATIMA BOOK 2*🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️By *Kingboy Isah* °°°°°°°°...
26/04/2023

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••

_$$ Free book but support us read in our site $$_
http://www.bonitomi.com/2023/04/aljanar-fatima-book-2-part-2-hausa.html

*^ Part 2 ^*

Talatu ta ce "Wallahi mama tana kwada min ta ruga a guje kuma kinsanta da gudu..." "Ke ni yi mun shiru ina Mairon take inje in ci ubanta ba zan iya bari har sai ta dawo gida ba yanda zuciyata ke tafasa". Talatu tace "Ba zai wuce taje gidan Inna Ma'u ba don can take guduwa in tayi laifi ta san ko Baba ba zai bita can ya daketa a gaban Inna ba". Cikin fushi Kubura ta nufi hanyar fita daga ita sai daurin kirji ko riga babu jikinta b***e ayi maganar mayafi, a irin jahilinci na kauye hakan ba wani abu bane don matar aure ta fita a haka bama batun neman izinin mijinta ake ba tukun.

Laure tace "Yaya ina zaki kuma", "Gidan Inna Ma'un can zan bita in mata dan banzan duka ko a gaban Inna ne". Kafin Laure ta daga baki tuni Kubura tayi waje Talatu da Wasila s**a rufa mata baya. Da fitarsu sai ga Salame da kaninta s**a kaiwa Fatsuma ciyawar Mairo, Fatsuma ta amsa taje ta juyewa awakinta guda biyu suma yunwa suke ji dan tun jiya da rana basu ci komai ba. Laure kuwa tsaki tayi ta koma wajen dakan furarta ita kuwa Fatsuma ta koma daki cike da fargabar abinda zaije ya zo ko kadan bata son tashin hankali.

Bagazan-bagazan ta fado gidan ko sallama babu Mairo na ganinta tayi sauri ta zagaya ta boye bayan Inna Ma'u dake zaune bisa tabarmar kaba, "Fito dan ubanki munafuka yau sai na kakkaryaki" Kubura ke fadar haka yayin da ta nufi Mairo gadan-gadan "To marar kunya ai sai ki fara kakkaryani kafin ki karyata". Curus ta tsaya tana huci tare da aikawa Mairo sakonnin harara ta bayan Inna Ita sam shigowarta bata ma lura da Inna Ma'u ba don tsabar masifar dake cinta. Inna tace "Ya kikayi tsaye kuma ki aikata abida kika zo aikatawa mana don da ganin shigowarki ba sallama b***e gaisuwa na san da shirin dukana kika zo". Inna Ma'u ta fada a hassale, yatsine baki Kubura tayi hade da cewa "Inna Ma'u ina kwana" "Da ban kwana ba zaki ganni ne? Marar kunya gaisuwar ma sai na roka me ya kawo ki gidan nan".

Kubura ta kamo kan Talatu "Inna dubi kan Talatu yarinyar nan Mairo ce ta dauki murgujejen dutse ta maka mata a kai. Ga hannun Wasila har jini ya kwanta inda ta cijeta sannan Asabe ma bata kyaleta ba haka ta lakada mata dan banzan duka don haka na zo in ci ubanta la'ada waje". Inna Ma'u ta k**a baki "Iyee yanzu ke Kubura ko kunyar fadi bakiji ba dubi gandara-gandaran yaran nan naki tubarakallah ace basu isa su tare fadan ga wannan yar yarinya ba har sai kin shigar musu babba dake ki shiga fadan yara kuma dangin juna to ga Mairon a bayana sai ki zo ki daketa a gabana in gani".

Duk yadda ta zo a firgice tana shakkar yin hauka a gaban Inna Ma'u tasan halin Inna Ma'u in ta mata hauka tana iya daukar ice ta buga mata don haka ta juya a fusace hade da fadin "Zaki fito wallahi yau sai kin gane shayi ruwane ina gida zaki tarar dani". Fuu! Ta fice Inna Ma'u na masifa Mairo ta fito daga bayanta tace Inna ta tafi ba. Dakuwa ta mata da hannu "Ungo nan dan gidanku me ya hadaki da 'Ya'yan wannan jarababbiyar matar kin sani sarai irin zaman da kuke a gidan ba ma sai kun taba su ba". Mairo ta kwashe duk abinda ya faru ta fadawa Inna, Inna Ma'u ta girgiza kai tace, "To ai ga irinta nan yanzu Allah kadai ya san irin masifar da kika jawowa kanki da mahaifiyarki na sha fada miki ki guji abinda zai hadaki da mutanen nan ba kaunarku suke ba ke da mahaifiyarki". Ita kan Mairo ta san abinda Inna Ma'u take fada gaskiya ne yau kam sai ta kwashi kashinta a hannu fatanta dai kar a taba mata ummanta wanda shima tasan abu ne mai wuya.

A can gida kuwa Yaya Kubura gaba daya ta hautsuna gidan da masifa takanas take zuwa har kofar dakin Fatsuma tana ta balbalin bala'i zagi da ashariya ba irin wanda baya fitowa a bakinta, Laure na tayata jefi-jefi. Har misalin karfe biyar Kubura na zaune a tsakar gida tana masifa a wannan karon harda jin haushin rashin zuwan Bukar gida da wuri. Zuwa can ta kalli Fatsuma dake kulkula daddawa a dan karamin turminta dake kofar daki dogon tsaki "Matsww Shima wannan tsinannen yaron ko ina ya shiga ko abincin raina bai dawo ci ba yanzu haka yana can tare da shegun abokanansa sun tafi daji yawon shiririta. Ke Talatu maza bi Wasila duk inda yayanku yake ki nemo min shi". "To" Talatu tace hade da mikewa ta nufi waje.

Fitarta yayi dai-dai da shigowarsa tafe yake yana shan rake cikin zumbula-zumbulan kayansa wanda sun masa yawa gasu sunyi datti ba wanki, Fari ne ba laifi amma baya da jiki ya tara wani dan iskan gashin baki kansa ya sha iski kwalkwali. Da ganinsa Kubura ta dora hannaye biyu a kai ta fashe da kukan munafurci sai kace wacce uwarta ta mutu. Shi kuwa da ganin haka baki daya ya gigice hankalinsa ya tashi baisan lokacin da yayi wulli da raken da yake hannunsa ba ya ruga gareta, "Innalillahi uwar gida- uwar gida me ya faru wa ya taba mun ke me kikewa kuka share hawayen daina kuka dan Allah fada min me ya faru".

Ita kuwa tamkar yarinya kara kware baki baki tayi hade da fadin "Bukar wallahi ba zan iya ba na gaji kawai ka sakeni na tafi gidanmu ba zan tsaya gidanka a kashe min yara ba kuma a bini da zagi ta wuta ta uba". Hankalin Bukar in yayi dubu ya tashi domin duk lokacin da Kubura ta ambaci kalmar saki a tsakaninsu ji yake zai iya aikata komai domin magance damuwar da ta sa ta fadin haka. "Dan Allah dan annabi Kubura ki daina ambatar saki a tsakaninmu ni Bukar ina zan iya rayuwa ba tare dake ba haba uwar gidana sarautar mata daina kuka ki fada min waye ya taba miki yara a garin nan nasha aradu ko mai gari ne sai inda karfina ya kare".

Fatsuma tunda ta ga Bukar jikinta ke karkarwa musamman da ta ga yadda Kubura ke kuka domin hatta Laure idan makircin Kubura ya sauka a kanta Bukar baya jiya mata dadi, b***e ita kuma da ya tsaneta a zaman da take a gidan ita da yarta ko baiwa ta fita gata. Kubura ta nuna Fatsuma da hannu "Wane irin mai gari kuma ga mayyar da ta hade baki da yarta nan suke son kashe min yara to wallahi ba zan yarda ba dole ka dau mataki in ba haka ba sakina kawai zakayi saboda na lura bani da yanci a gidan nan domin a kan hakan babu irin zagin da Inna Ma'u bata mun ba don naje in daki Mairo".

Baki daya ran Bukar dake tsugune gaban Kubura ya baci don haka ya mike tsaye hade da fadin "Me s**awa yaran naki fada mun yanzun nan in dau mataki a kanta munafuka daina kallona da idonki k**ar na bera". Ya dallawa Fatsuma harara "Mairo ce kana ganinta tamkar karama ashe tayo gadon bakin hali da mugunta wajen uwarta ta lakadawa Asabe dan banzan duka, ta ciji Wasila a hannu sai da jini ya fito bata tsaya iya nan ba ta dauki dargwajejen dutse ta kwalawa Talatu a kai ba don Allah ya kiyaye ba aradu da sai dai a kwaso kwakwalwarta a kwarya".

Da jin haka Bukar ya dora hannu a kai hade da fadin "Innalillahi na shiga uku ita Mairon ce ta aikata haka yanzu yarinyar nan duk dukan da nake mata da wanda Zubairu yake mata wato ba ji take ba shine take neman kashe mun yara" Ya watsawa Fatsuma wulakantaccen kallo, "Ko dake ba laifinta bane tarbiyar da shegiyar uwar nan tata take koya mata kenan, zo nan dan ubanki yau sai na kakkaryaki a gidan nan".

Fatsuma da tunda ya fara maganar dama tuni ta daina dakan daddawar ta sunkuyar da kai jikinta na rawa a hankali ta taso don bata isa tayi masa gardama ba ta kara laifi. A gabanshi ta durkusa ta daga baki "Gan.." Bata karasa ba ya ware karfinsa ya wanka mata mari wanda sai da ta fadi kwance daga durkushen da take ta dafe bangaren da ya mara a gigice domin sai da ta ga taurarin wahala. "Ke dan ubanki irin tarbiyar da kikewa yar tawa kenan wato bakin cikin hali irin naki har kin fara goga mata gashi ta fara tayaki kishi tana son kashe yan uwanta wato..." "Don Allah don annabi kayi hakuri ba zata kara ba zan mata fada".

Da fadar haka a fusace ya rufeta da duka tamkar wanda ya k**a barawo naushi da harbi ta ko'ina ita kuma Fatsuma banda kuka da ihu ba abinda take yi. Inda saboda ta saba da wannan dukan laifi kadan zatayi a cikin gidan ya lalasata saboda rashin gata. Ana cikin haka sai ga Mairo ta shigo gidan a guje tana kuka tana sosa baya. Da ganinta Bukar ya bar kan Fatsuma yayi caraf ya cafketa "Zo nan Allah ya kawo ki azzalamu". Hannu ya ware ya dankara mata duka a baya tamkar ba karamar yarinya ba nan take Mairo ta fara tari tuni lumfashinta ya fara kokarin daukewa.

Fatsuma bata san lokacin da karfi ya zo mata ba da gudu ta yunkura ta fizge Mairo daga hannun Bukar a gigice tana fadin "Mairo! Mairo! Innalilahi wa'inna illahir raji'un Mairo dan Allah karki mutu bani da kowa sai ke kece dan sauran farin cikin rayuwata da ya rage in kika mutu ya zanyi". Ta fashe da kuka tana girgiza Mairo da lumfashinta ke sama-sama Kubura da Lauren da s**a zuba ido suna kallo ta dora hannu a kai "Bukar ka kasheta" Bukar ya ja tsaki "Tama mutu mana a wajena da mutuwarta da rayuwarta duk daya". Kamar hadin baki Laure da Kubura s**a tuntsire da dariya yayin da Bukar ya juya ya fice a gidan

Fatsuma kuwa k**ar tayi hauka Halimatu da ta shigo gidan tana ganin abinda ke faruwa da gudu ta nufi randar ruwa ta debo zata kaiwa Fatsuma wata gigitaciyar tsawa Laure ta daka mata "Intuwa ku..ubanki wa zaki kaiwa ruwa". Cikin firgici tace "Mama Mairo karta mutu". A fusace Laure tace "Kan ubanki idan ta mutu ita din kanwar uwarki ce? Nace ita din kanwar uwarki ce?". Jiki a sanyaye ta koma gefe tana kallon Fatsuma dake rungume da Mairo tana kuka. "Yau na ga iyayi ko miye ruwanta a ciki idan ta mutu harda kokarin dukko ruwa, ke da ma zakiyi fatan ta mutu yaushe rabon mu da cin gumbar sadaka". Cewar Kubura ai kuwa s**a sake bushewa da dariya ita da Laure......

25/04/2023

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••

http://www.bonitomi.com/2023/04/aljanar-fatima-book-2-part-1-hausa.html

*^ Part 1 ^*

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammadu S.A.W da iyalansa da sahabbansa da bayin Allah na kwarai.

*GABATARWA*
Godiya ga Allah da ya sake bani damar sake dawowa gareku dauke da cigaban wannan hakaitaccen labarin mai dauke da tarin darussa na rayuwa. Duk da kasancewar ba labarin da ya faru a gaske bane ina fatan za'a samu darussan da kan iya zamowa izina ga rayuwarmu ta gaske musamman ga masu wasu daga cikin halayyar dake bayyane a cikin labarin na farko da ma wannan na biyun.

*TUNATARWA*
Ina fatan wadanda s**a dauri aniyar bibiyar wannan labarin nawa zasu kasance masu yi mun uzuri a wasu lokutan da labarin bai samu a kan lokaci ba, kasancewar yanzu abubuwa sunyi yawa. Haka zalika idan anga wani kuskure a cikin labarin ko kuma typing error za'ayi mun uzuri, tare da ankarar dani idan da bukatar hakan a game da tafiyar labarin na gode.


Tafe take cikin rana sai zufa take, nauyin ciyawar awakin da ta dauko bai hanata gudu-gudu sauri-sauri ba, da alamu dai a hanzarce take. Yarinya ce karama da ba zata haura shekara 8 zuwa 9 ba, dattin da ke jikinta da na kayanta ba zasu hanaka sata sahun farko cikin kyauwawan mutane ba, kasan cewarta fara da ka ganta kaga yarinyar fulani. Ba takalmi a kafarta zanin kuwa dake jikinta duk ya tattare saboda tsabar datti da kuma tsufa da yayi. Rigar kuwa har ta soma cirewa daga wajen wuya. A hanzarce ta karaso garesu yayin da ta cillar da ciyawar da ta daukko ta shaki kwalar rigar wata yar bakar yarinya. Marin da ta wanka mata ne yasa ta saki ciyawar dake kanta hade da fasa kuka

kukan ne ya janyo hankalin dayar yarinyar da suke tare ta juyo da sauri tana kallon abinda ke faruwa. "Dole kiyi kuka barauniya kin dauka cewa bansan ciyawata hannu biyu kika kwashe ba" "Yau za'ayi bur..uba, Mairo Asabe kika mara" Cewar yarinyar da suke tare da Asabe wanda itama dauke take da tsanwar ciyawar dabobbi a kai. A fusace Mairo ta saki Asabe wacce ta fadi a wajen tana birgima da ihu irin na batatun yara k**ar wacce aka cire mata wani sashi na jikinta. "An mareta din Lantana ko zaki rama mata ne" Mairo ta fada tana mai fuskantar Lantana cikin masifa, Murguda baki Lantana tayi hade da cewa "Ba zan rama mata ba amma wallahi sai na fada ma mamarta". Da fadar haka tayi hanyar gida da gudu, itama kuwa Asabe ta tashi ta bita baya a guje tana kuka k**ar wacce ake cire mata rai. Tsaki Mairo tayi ta tattara ciyawar Asabe da tata ta hade waje guda ta daure ta dora a kai ta nufi gida gabanta na faduwa.

Ba komai take tsoro ba sai Yaya Kubura mamansu Asabe tasan halin jarabar matar nan. To amma dole ne ta kare mutuncin kanta da na uwarta, ba zata lamunci irin cin kashin da ake musu a gidan ba dan anga hakurin uwarta yayi yawa. Allah-Allah take karfinta ya kawo domin ta rika daukarwa uwarta fansa a kan su Yaya Kubura ko da cizo ne. Tafe take cikin sauri tana sake-saken zuci ga yunwa na kwakwalarta don haka ta fito ciyawar ko karyawa batayi ba. Tun daga nesa ta fara hango Wasila Talatu da Lantana sun yo hanyar da take. A zuciya tace ku kam ba tsoranku nake ji ba gwara ma da kuka biyo ni dajin. Tun kafin sun hade suke aiko mata zagi da ashar tana jinsu bata tanka ba ta zo zata gitta ta gefensu. Wasila ta jawota ta baya hakan yasa ciyawar dake kanta ta fadi kasa, "Gidan uwar wa zaki munafuka yau sai kin gane shayi ruwane sai munyi kasa-kasa dake a dajin nan tunda kika daki Asabe".

Bata tanka ba sunkuyawa tayi da niyar daukar ciyawarta ta kara gaba, cikin fushi Talatu ta hangizata tayi tangal-tangal saura kadan ta kife a kasa. Talatu tace "Magana muke muke kinyi banza damu uban wa yace ki daki kanwata" Mairo tace "Ciyawata ta daukar min dole na daketa dan gobema kar ta kara". Talatu tace "Ciyawar Banza ciyawar wufi". Wasila tasa kafa tayi kwallo da ciyawar, cikin fusata Mairo tace "Wasila! Ki daina, Wasila ki daina". "Idan naki fa? Ko dukana zakiyi". Cewar Wasila dake rike da kugu tana zarowa Mairo ido, tabbas da niyar dukan Mairo s**a zo amma suna shakka duk da kuwa sun girmeta, sun san halinta k**ar mage take daga kun fara fada zata cijeka. Talatu wacce itace yayar Wasila ita kuma Wasila yayar Asabe tace.....

Karanta full page a site dinmu

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

http://www.bonitomi.com/2023/04/aljanar-fatima-book-2-part-1-hausa.html

👆🏻👆🏻

30/10/2021

Hey

14/08/2021

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_1_

*Thanks to Almighty Allah for giving me ability and power to start the other part of the book _SHARIK~HAYATI_, many thanks to my follwers, fans and Family i luv u all❣️*

Kwance Ummi ta sameta ta rufo da blanket, jin motsi yasa tayi saurin goge hawayen idanta ta tashi ta zauna, Ummi ta zauna gefenta cike da damuwa ta ce "U haven't eat dear" dan turo baki tayi ta ce "Na koshi Ummi" shiru Ummi tayi tana kallanta ganin yadda ta kara mungun rama akan da, ta sauke ajiyar zuciya ta ce "To me zakici?" Tayi saurin girgiza kai ta ce "Banasan abinci kuma" Ummi ta ce "Me zakici to idan ba abinci ba, or do u need tea?" Ta girgiza kai, Ummi ta ce "Conflask?" Ta kara girgiza kai ta ce "Awara nakeso" Ummi ta ce "To bari na bawa Saudatu ta samo maki, tashi muje kasa" dan noke kafada tayi k**ar zatai kuka ta ce "Ummi bacci nakesan yi" Ummi ta kamo hannunta ta ce "Sai kiyi a kasan ai, zakuyi sallama da Mummy ne, beside that ma banasan kina zama ke kadai" dan kwalinta Ummi ta daura mata sannan ta k**a hannunta s**a fito a dakin. Very slowly ta dinga bin Umminta har s**a sauko a steps din, Mummy dake kallansu ta ce "Lafiya dai?" Ummi ta ce "Wai Awara zata ci" gefen Mummy Rafi'ah ta zauna ta ce "Mummy tafiya zakiyi?" Mummy ta kamo hannunta ta ce "Insha Allah, ina jiran driver ne, but kullum zan dinga zuwa kallanki harki samu sauki sosai, abinda nakeso dake shine ki daina kukan nan, idan Allah ya rubuta abu zai faru babu mahalukin daya isa canzashi, shi kuma Yusuf ki watsar da kashin sa, ki saki jikinki ki daina damuwa dashi, banda hauka irin naki ma mutum yaci amanarki haka amma ki zauna kina kuka akansa" share hawayen idanta tayi tana kallan Mummy ta ce "Ni bana san shi kuma, i hate seeing him, ko mai k**arsa banasan na gani, what is making me to cry is..." Fashewa tayi da kuka ta kasa karasawa, Mummy ta bata side hug ta ce "Dan ya barki da ciki a kanki aka fara? Ke dai ki kula da kanki ki haife abinda yake jikinkin ki kawai, ina guje masa ran da zai zo yana blaming abinda kika haifa dan dansa ne, wallahi babu me rabani dashi duk duniyar nan, saina wulakantashi k**ar yadda yayi mana, sai na sa shi kuka da kunci na har abada, kuma d'a ba nasa bane, kece uwarsa kece ubansa" ita dai Rafi'ah sai share hawayen idanta take, bayan haka ta zame akan sofa ta kwanta akan carpet ta rufe idanta tana addu'a, wani zafi da takaici take ji deep down her, ba dan ba dan ba da tayi addu'a Allah yasa cikin ya bare itama ta hutawa rayuwarta. Bayan 10 minutes Saudatu ta shigo da warmer a hannunta, Ummi dake zaune suna hira da Mummy ta ce "Kin samu?" Saudatu ta ce "Ehh na samu" Ummi ta daga Rafi'ah ta ce "Dear, ga Awaran an kawo maki" a hankali ta bude idanuwanta tana kallan Ummi ta ce "I'm sleepy" Ummi ta ce "I know, try and eat ko kadan ma, tin safe bakici komai ba" gyara zama tayi ta jingina da jikin kujera sannan ta bude warmer din, fork Saudatu ta mike mata ta fara cin Awaran, daga Ummi har Mummy kallanta suke, kai kace tayi sati bataci komai ba, na bakinta baya karewa take saka wani, su kam hakan yayi musu dadi, indai zataci ai komai zaizo da sauki, kusan rabin warmer din ta cinye sannan ta rufe ta ajiye a gefenta ta ce "Anjima zanci wannan" Ummi ta danyi murmushi tana kallanta ta ce "Ba wanda zai ta6a" daga haka ta kwanta ta limshe ido, nan da nan bacci me nauyi ya dauketa. Ba jimawa driver yazo daukar Mummy, a hanyarsu zuwa gida yake fada mata Jawad ya dawo, with surprise Mummy ta ce "Har sunyi landing?" ya ce "Wallahi Hajiya, kafin naje daukoshi wani abokinshi ya kawo shi gida" Mummy ta ce "Inaga dai sanda ya kirani yayi rabin tafiyar".
Anty Amina ce zaune a parlorn Ummanta tana shan exotic, lokaci~lokaci takan kalli Anty Rahama dake ta trying number Anty Khadija amma yaki shiga, Anty Amina tayi murmushi ta ce "Maman Leemah wai menene damuwarki akan Khadija ne? Naga randa abin ya faru munyi magana da ita tace sun bar kasar" Anty Rahama ta juyo tana kallanta ta ce "Duk tasu?" Anty Amina ta ce "Ehh mana, ni lokacin kaina ya dau caji ban gaya miki ba, ga zaman dole na asibiti" Anty Rahama ta ce "Amma tace tayi aure a Kaduna da mijin ta wuce kenan?" Anty Amina tayi dariya ta ce "Kema kinsan ba zata harshi ba ai, mijin da aka zautarwa hankali ya bar matarsa da manyan 'ya'yansa ya aureta ta ina zata barshi, ai suna caan ko wacce kasa Allah masani, amma dai ni banga abin tada hankali dan baki sameta a waya ba, ina dai burinmu ya cika, shikenan sai mu barta ta sha iska" Anty Rahama ta juyo tana kallanta ta ce "Hakane kuma, Allah ya raka taki gona" daga haka s**a tafa Anty Amina ta ce "Atooh, haushinama yarinyar da tai ciki, koba komai zasu danganta d'an da Yusuf" Anty Rahama ta mata wani kallo ta ce "Taab ai kuwa wannan yayar uwartan ba yarda zatai ba, lokacinfa da mukaje da Yah Muhammad gidan Yusuf wuka ta dauka tana nemansa daki daki wai saita kashe shi, nasan dai ko zafin haushine ya sata haka baxa dai ta bari ya kar6i abinda Rafi'ah zata haifa ba, ke nifa mamaki abin ya bani, banyi tinanin wannan figigiyar zata daukar ciki da wuri ba, gaki nan zabgegiya dake shekara kusan 5 ba labari" nan da nan Anty Amina ta hade fuska ta ce "Dan Allah kimin cikin nan idan zaki iya, ba dai Allah ke bayar ba, nayi maganin harna gaji babu labari, kema naga a shekaru 22 da kikai gidan mijinki 'ya dya kawai kika haifa" Anty Rahama ta ce "Amma dai na haifi dayar ko, to dan Allah kema kiyi zuciya ki haifo ko nakashashshe ne" Anty Amina ta mike ta ce "Sai dai ke ki haifo, gashi mun fara gani kin haifo mai cuta" cushion Anty Rahama ta cilla mata cikin 6acin rai ta ce "Ki shiga hankalinki Amina, karki kara kiramin Ikleemah da mai cuta" fitowa Umma tayi a daki taja Anty Rahama tana bata hakuri s**a shiga ciki, bayan nan ta fito ta rarrashi Anty Amina ma, wai ai sai ace basu da hadin kai, kuma abin kunya ne suyi fada a junansu, ita dai Anty Amina baki kawai ta ta6e taci gaba da shan exotic dinta.
Fuskarsa dauke da murmushi ya shigo parlorn, Mummy ta juyo tana kallansa ta ce "Mutanen Cyprus" ya dan shafa tulin gashin dake kansa ya ce "Ina yini Mummy" ta ce "Lafiya kalau, have a seat, ashe harka dawo?" ya ce "Ehh kusan awana 1 ma, fatan na sameku lafiya?" Ta ce "Alhamdulilah" mikewa yayi yana kallanta ya ce "Zan answer call ne" ta ce "Alright no problem" daga haka ya fita a parlorn, part din Maminsa ya shige hade da sallama, Abi na zaune a gefen Mami sai Ikram dake kan carpet a zaune, Jawad ya danyi kasa da kansa ya ce "Ashe ka dawo, na dauka zaka kirani na dauko ka" Abi ya ce "U don't have to worry son, kai da ka dawo a tafiya, Sadeeq ya daukoni" kan kujera Jawad ya zauna yana kallan TV, Abi ya kalli Mami data dan hade fuska ya ce "To meyasa bakije yau ba?" Ta juyo tana kallansa ta ce "Naga dai an sallameta har sun koma gida, gidanma kullum zan dinga zuwa kenan?" Abi ya sauke ajiyar zuciya ya ce "U have to go, asibiti da ban gida da ban, don't make me repeat my self kije kawai ki duba ta" tashi yayi ya fita a parlorn Mami ta bishi da wani irin kallo. Jawad dake kallanta ya ce "What's going on Mami?" Dan karamin tsaki taja ta ce "Ina kana da labarin auran Rafi'ah wanda akayi bayan kwana biyu da tafiyarka" ba karamin bugawa zuciyarsa tayi ba, ya daga mata kai yana kallanta, Mami ta ta6e baki sannan ta ce "She's divorced" with shock ya juyo yana kallanta ya ce "Divorced" ta ce "Saki ba, ya saketa saki daya" innalillahi Jawad ya dinga furtawa yana kallan mahaifiyarsa, Mami ta ta6e baki ta ce "Wallahi sakin wulakanci, daya bata takardar ya bar gidan shida matarsa, har yau ba'a san inda yake ba, ya tafi ya barta da karamin ciki, inka ganta k**ar ka hureta ta fadi, ni cewa nayi ma da zubar da cikin s**ai, yarinyar dako 18 bata cuka ba, sanda naje sunanta Ikram dina tafi shekara 1" kasa daina kallan Mami yayi, lokaci daya yaji komai nasa ya tsaya musamman data ambaci ciki, Mami ta gyara zamanta ta ce "Ni gani nake saboda cutarta ya gujeta, yanzu a zamanin nan yaushe zaka auri mata mai ciwan zuciya, duk wata fa sai sun kar6i magani ga uban tsada, shi kuwa inaga yayi na Allah yace ya gaji, ba dan ubanta nada dukiya ba inaga gidan da zasu zauna ma sai ya gagaresu" Tashi Jawad yayi ya shige daki, yana rufo kofar idanuwansa s**a cika da hawaye, bai bari sun zuba ba saima murmushi da yayi ya dauki key din motarsa dake kan mirror din dakin, jin an bude dakin yayi saurin juyawa, Mami ta ce "Ya muna magana zaka tashi ka barni ba excuse" ya ce "Na tina akwai inda zanje ne" ta ce "Ina?" Ya dan shafa kansa yana kallanta ya ce "Wajen aiki, akwai papers din da zan kai musu wanda na taho dasu" Mami ta ta6e baki ta zauna bakin gado ta ce "Haka dai kullum aiki aiki, idan dai kayi aure barin wannan kotun zakayi ka nemi wata" a hankali ya ce "Ohk, saina dawo" daga haka ya fita a dakin.
Driving kawai yake amma gaba daya tinaninsa ya tafi wajen Rafi'ah, minti 10 ya kaishi kofar gidan, yayi parking a waje sannan ya fito walking gently ya tura gate din, ganinsa yasa Mustapha ya kara bude kofar yana masa sannu da zuwa, daga masa hannu yayi ya nufi entrance din gidan, yana murda handle din yaji kofar a bude, ya shiga parlorn da sallama, Saudatu dake jera dinner akan dinning ta ce "Ina wuni" ya ce "Lafiya kalau, Ummi na nan?" Ta ce "Ehh bari in mata magana" upstairs ta nufa ta kwankwasa dakin Ummi, bayan an bata izini ta bude dakin ta shiga da sallama, Rafi'ah na kwance akan gado Ummi na rarrashinta, dan wani saban kuka ta kafa musu tinda ta tashi a bacci, Ummi ta kalli Saudatu dake tsaye gefe ta ce "Kin gama abincin ne?" Ta ce "Ehh na gama, kinyi bako ne a kasa" Ummi ta ce "Bako kuma at this time? Babbane?" Saudatu ta girgiza kai ta ce "Ehh babbane, dogo dan fari haka, yana da gashi me yawa a kansa" sosai zuciyar Rafi'ah ya buga, dan tinaninta ko Yusuf ne, ta ruko hannun Ummi k**ar zatai kuka ta ce "Dan Allah karkije Ummi" Ummi ta ce "Why Rafi'ah, bari na gani ko waye" daga haka ta zame hannunta ta nufi kofa ta fita, saukowa akan gadon Rafi'ah tayi tana kallan Saudatu ta ce "Fari ne?" Saudatu dake tsaye tana kallanta ta ce "A'a amma dai ba za'a ce masa baki ba" ajiyar zuciya ta sauke ta koma ta kwanta, dan tasan Yusuf yana daya daga cikin mutanen da za'a kira su asalin farare, a hankali Saudatu ta ce "Allah ya baki lafiya" daga haka ta fice a dakin. Tana saukowa ta sami Jawad da Ummi suna gaisawa yana mata jajen abinda ya faru, Ummi ta danyi murmushi ta ce "Toya zamuyi, haka Allah ya tsara mana, da munsan haka zai faru ko auran baza ai ba, to amma Allah shi yake tsara komai a duk lokacin daya so" Jawad da kansa ke kasa ya ce "Hakane" Ummi ta ce "Bari na turo ta ku gaisa" daga haka ta mike ta wuce upstairs, kwance ta sameta tayi shiru ta kurawa window ido, Ummi ta kamo hannunta ta ce "Daughter" kifta idanta ta danyi sannan ta kalli Ummi ta ce "Who was d visitor Mum?" Ummi ta ce "Ahmad ne, kije ku gaisa" tsayawa tayi tana kallanta bata dai ce komai ba, Ummi ta ce "I mean Jawad" a hankali ta ce "Ohh" daga haka ta mike, hijab Ummi ta dauko mata tasa sannan ta ce "U wash ur face, duk idanki ya kumbura" a hankali ta shiga toilet ta wanke fuskarta ta goge idanta with clean towel sannan ta fito, daga haka ta fita a dakin ta wuce downstairs, tin tana sakkowa yake kallanta ko kiftawa babu, ita dai kanta na kasa ta karaso parlorn da sallama, zama tayi akan carpet ta ce "Ina yini" ya ce "Fine, how are u then?" Silently ta ce "Same" Jawad yayi shiru yana kallanta, d**o kanta tayi s**a hada ido tayi saurin dauke kanta, a hankali taji muryarshi ya ce "Ya karfin jiki?" Ta goge hawayen idanta ta ce "Alhamdulilah" tinda ta rife bakinta hawaye s**a dinga sakko mata tana sharewa da hijab dinta, Jawad ya danyi kasa da murya ya ce "Destiny, kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwarsa, so u don't have to cry, one day one time u will laugh" fashewa tayi da kuka ta ce "I will never laugh again Ya Jawad, to laugh for what? Kasan zafin da nake ji deep down me, ni kadai nasan abinda nake ji, so nobody should tell me i will laugh one day" daga haka ta kifa kanta akan gwiwowinta, kallanta ya dinga yi daga inda yake zaune, jiin ta sausauta kukan da take ya ce "May be shi din ba alkhairi bane a tattare dake, Allah ya raba ku ne saboda ki samu wanda ya fishi alkhairi, just erase all ur bond together with him, ki manta dashi a rayuwanki, so don't cry for him pls" ta share idanta ba tare data kalleshi ba ta ce "I have to cry Yayah, he divorced me without any reason, ya azabtar dani a gidanshi ban gayawa kowa ba, after all ya tafi ya barni da cikinshi..." sarkewa muryarta tayi, hakan yasa tayi shiru tana kuka kasa kasa, Jawad ya ce "No, u don't have to, ai shi d'a na kowa ne, i can take care of the unborn child and still after his birth, so u forget about that man i beg u" a hankali kawai ta daga masa kai, ya ce "Promise u won't cry again" ta ce "Yes" ya ce "Yes what?" Ta ce "I can't make a promise to u, nasan sai nayi, saboda yin kukan kadai zai yi preventing dina from heart attack, inajin dadi idan nayi" Jawad ya limshe idanuwansa ya ce "To kiyi kadan" d**owa tayi tana kallansa, yana bude idanuwansa tayi saurin sunkuyar da kanta, ya ce "I think i have to go, kiyiwa Ummi sallama, Allah ya kara maki lafiya" silently ta ce "Ameen, nagode" daga haka ya mike ya fita a parlorn ta bishi da kallo, yana fita compound aka bude gate, motar Sadeeq ta shigo compound din, sosai Mami ta hade rai tana dalla masa harara, yayi karfin halin ya karasa parking lot din yana kallanta ya ce "Dama na gama abinda nake ne shine..." Wucewa tayi ta barshi nan wajen a tsaye, ya juyo yana kallan Sadeeq da fitowanshi a motar kenan ya ce "Till u come back" daga haka ya nufi hanyar gate Sadeeq ya bishi da kallo.

_08103810398_

BARKA DA SHIGOWA WANNAN PAGE MAI ALBARKA. MUNA MAKA/KI FATAN ALKHAIRI, MUN GODE DA ZIYARTAR MU

07/04/2021

👹 *TSIGITSILA* 👹

*Shaidaniya Uwar Shaidanu*
~~~~~~~~~~~~~~~~~
Short story
~~~~~~~~~~~~~~~~~

{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}

👨🏻‍💻 KING BOY ISAH ✍🏼

Part 9
°°°°°°°°°°

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

~*NOTE* Labarin Nan Bai Faru A Zahiri Ba, Jan Kunne Ne Ga Masu Mugun Hali~

*Aslm Kuyi hakuri bisa samun page daya kadai kwana biyun nan, ni kaina ina burin kammala littafin nan kafin azumi amma yanayin yau da kullum ba ko da yaushe nake samun dama ba.*

Fitowarta daga daki yayi dai-dai da sako kafar ido, ko da ganinshi Kubura ta sa shewa hade da nufar shi tana lale maraba. Jakar hannunshi da ledar ta karba ta nufi dakinta a nufinta ya bi bayanta. Sai gani tayi ya nufin hanyar kewayan Rakiya a hanzarce ta juyo tace, "Ina kuma zakaje ai ya k**ata ka dan shigo daki ka huta kafin ka shiga nan ko? Tunda ni na fara ganinka". Juyowa yayi ya dube ta baiyi mamaki ba domin yasan halin kishinta duk kuwa da kokarin boyewa da take. "Haba Kubura kinsan fa wannan zuwan ba zuwan lafiya bane. Zuwan lalura ne kinga kuwa ba bukatar hutawa dama saboda marar lafiya na zo to kinga kuwa dole na fara zuwa naga yanayin jikin nata kafin mu fara neman magani".

Yana gama fadin haka yayi gaba, Kubura ta bishi da kallo tare da murmushin mugunta, hade da cewa "Ayi mu gani idan tusa zata hura wuta". Da fadar haka ta kwashe da dariya yana jinta bai kulata ba yayi gaba. A dai-dai lokacin da ya taka kofar dakin Rakiya wani mugun wari ya daki hancinsa wanda bai taba jin kalarshi ba tunda yake a rayuwarshi. Hannu yasa ya rufe hanci kana ya daure ya karasa cikin daki. Yana shiga s**a hada ido da Rakiya nan take yaji kanshi na juyawa hade da wani masifafen ciwon kai na lokaci guda. Da faruwar haka yaji ya tsani Rakiya baya so ya kara ganinta a rayuwa.

Saude dake zaune tana damawa Sale Fura da sauri ta taso ta nufi mahaifin nata tana mishi sannu da zuwa. Tun kafin ta karasa ya daka mata tsawa hade da fadin "Bace mun da gani". Tsaye tayi kikam tana kallon baban nata cike da mamaki. Yau duka ba'ayi wata uku da tafiyarshi birni ba. In zata iya tunawa a tarihin rayuwarta bai taba yi mata tsawa ba. Sale ne ya taso da sauri ya nufin baban nashi da nufin ya dauke shi k**ar yadda ya saba. Ai kuwa yana karasawa Iro ta hankade shi nan take ya fadi kasa yana kuka. Saude da abun ya bara bata tsoro duk da kasancewarta yarinya, cikin sanyi tace, "Sannu da zuwa babu ina wuni". "Ban wuni ba dan uwarki, kiyi mun shiru ko in fafasa miki baki yanzun nan. Kun zo kun cika min gida da wari ke da uwarki". Iro ne ya fadi haka hannunshi rike da hancinshi

Rakiya ba karamin kaduwa tayi ba domin tana jin abunda ke faruwa, zuciyarta cike da kunci hawaye s**a gangaro daga idanunta domin tasan cewa ba Ironta bane mijinta ba haka yake ba aikin sihiri ne. Tana so tayi magana ba damar yi. Iro ya dube ta tana kwance cikin mawuyacin hali hade da cewa "Rakiya kin ban mamaki wannan wane irin hauka ne haka zaku cika min gida da wari ke da 'yayanki? Ko ance miki rashin lafiya hauka ne? Saboda baki da lafiya shikenan kuma sai akace miki ki zama kazama? To tunda haka kika zaba ki Rakiya na tsane ki, na tsani yayanki bana son ganinki haka zalika bana son ganin yayanki, da ace kina iya tafiya da yanzu zan kore ki ku fita ku bar min gidana". Gabanta ne ya fadi rass da jin kalamanshi, innalillahi kawai ta fara mai-maitawa a zuciya cike da tsoro da fargabar kar Iro ya saketa a cikin wannan hali na asiri domin tasan cewa ba yin kanshi bane.

Nan dai Iro yaita zazaga musu masifa ta inda yake hawa ba ta nan yake sauka ba. Daga jin zancen kai kasan ba na hankali bane. Kubura dake labe a bakin kofa tana jin abinda ke faruwa nan take farin ciki ya kumeta. Tabbas lokaci yayi da Rakiya zata dandani irin dacin bakin cikin da ta shiga a baya a sanadinta. Jahilci yasa Kubura ta manta da Allah, tunda ta mallaki aljana Tsigitsila ji take tamkar ran kowa na hannunta zata iya kashe duk wanda ta so a duk lokacin da taga dama. Sai dai kashe ta manta cewa bokaye da shedanun aljannu makaryata su kan kai mutu su baro shi a yayin da s**a gama amfanarshi.

Rakiya ce kwance tana bacci Sale na kwance shima a gefanta suna sharar bacci. A hankali Kubura ta bude dakin ta shigo, a dai-dai saitin Sale ta tsaya yayin da ta fiddo wata filleliyar wuka mai kaifi sai walkiya take. Nan take ta caka wa Sale wukar a ciki, ya kwalla kara yayin da jini yayi Feshi nan take ya mutu. Karar shi ne ya tayar da Rakiya. Kubura tayi saurin tsallakawa kan gado tasa igiya ta shake wuyan Rakiya da karfi. Nan take Rakiya ta fara mimikewa ranta zai fita bayan ta kasa kwacewa.

Firgigit ta farka tare da dafe kirji tana karanto Innalillahi wa'inna Illahir raji'un, neman tsari a wajen Allah tayi daga sharrin mummunan mafarkin da tayi, kallo daya zakayi mata ka gane cewa a matukar kidime take tabbas hankalinta ya tashi. Kuka ta fashe da shi ba dan komai sai dan sanin cewa bata yin mafarki duk kuwa mafarkin da tayi sai ya zama gaske. Tana ganin abubuwa da yawa a mafarki wanda kuma s**an zo su zama gaske. Ta fada a gida idan tayi mafarki yana zama gaske amma ba'a yarda ba. Daga karshe ta daina fadawa kowa saboda taji ance duk wanda yake mafarki kuma mafarkin ya zama gaske to maye ne. Dadin dadawama bata kwanciya sai tayi alwala, kuma ta karanta falaqi da nasi hade da surori uku na karshen suratul baqara domin haka malamansu s**a umarce su da yi a duk lokacin da zasu kwanta.

Shiyasa hankalinta ya tashi tabbas tasan cewa abinda ta gani a mafarki zai zama gaske. "Me yasa Mama Kubura? Taya ma hakan zai faru, kai aa gaskiya hakan ba zai taba faruwa ba. Babu ta yadda za'ayi mama Kubura ta kashe mamanmu, matar da take son cigabanmu fiye da nata. Sharrrin mafarki ne kawai. Gabanta ya fadi da ta tuna cewa tayi mafarkai ba adadi a baya kuma sun tabbata gaskiya. A kan nuna mata abu ko da ta hanyar misali ko kwatance ne a mafarki kuma ya zo ya zama gaske a zahiri. Saboda haka ta kuduri niyar tafiya kauye goben nan. Domin ba zata taba samun natsuwa ba.....................

BARKA DA SHIGOWA WANNAN PAGE MAI ALBARKA. MUNA MAKA/KI FATAN ALKHAIRI, MUN GODE DA ZIYARTAR MU

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zamani Writers Association posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Zamani Writers Association:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share