13/04/2023
Yadda Laulayin Ciki Yake Jawowa Mace Macen Aure Da Wuri Ko Kuma Babbar Matsala Da A Gaba Zata Kawo Mutuwar Auren
Dayawa Daga Cikin Yan'uwana Matasa Sunayin Aure Batare Da Sunsan Irin Sauye Sauyen Da Zasu Iya Kunno Kai A Lokacin Da Matansu S**a Samu Juna Ba Duk Da Ba Duka Ne Ake Samun Matsalar Ba, Wassu Kuma Sunsani Amman Sunbarshi A Matsayin Karamin Lamari Kawai A Iya Fatar Baki Ake Fada Don Nishadi Ko Hira.
Kafin Mutum Yayi Aure Yakamata Yasani
* Laulayin Ciki Yana Iya Mayarda Mace Kazama Duk Son Tsaftanta, Dole Idan Matarka Tazo Da Ire Iren Wannan Yanayi Ka Nemi Hanyar Da Zaka Iya Taimaka Mata Da Kuma Mata Uzuri La'akari Da Abaya Bahaka Kasantaba
* Laulayi Kan Iya Saka Mata Ganda Da Son Jiki Wanda A Wannan Lokacin Wassu Matan Kan Iya Zama Gwanaye Wajen Barnar Bata Abubuwa, Irin Abu Yafadi A Hannunsu Ko Kuma Suna Gani Abu Zai Baci Bazasu Iya Tashi Su Gyara Ba Ko Yana Kusa Dasu, Dole A Koyi Controlling Bacin Rai Tare Da Tuna Yadda Suke A Baya A Matsayin Hujjar Yimusu Uzuri
* Wassu Yana Zuwa Musu Da Bacin Rai, A Lokacin Da Mata Suke Laulayi Musamman A Stages Na Farko Farko Wahalar Ciki Wani Lokacin Saisu Rasa Abu Daya Dayake Musu Dadi S**anji Komai Baya Musu Dadi, Wannan Lokacin Komai Zasu Iya Fada Maka Wassu Ko Magana Mai Kyau Kayi Musu Bazasu Baka Amsa Mai Kyau Ba, A Wannan Lokacin Suna Bukatar Doguwar Uzuri Da Lallami Tare Da Mayarda Komai A Maslahance
* Yakamata A Koyi Yin Uzuri Akan Duk Wani Sauyi Da Aka Gani A Wannan Lokacin Tare Da Daukarsa A Matsayin Abu Mai Lokaci.
Zahiri Aure Ba Karamin Lamarine Wanda Kusan Musuluncine Ya Assasashi, Kuma Barazana Da Barnace Yadda Ake Wasa Yanzu Da Babban Al'amari Sunnar Manzonmu (S.A.W), Allah Ya Gyara Mana Ya Shiryemu
Jinjina gareku iyaye mata Allah ka bawa Aliyu Haeedar damar kulawa matarsa kamar yanda zai Kula da kansa komai fiye da haka
Tare da sauran Maza Baki Daya
Naku har kullum Aliyu Haeedar