19/01/2024
Gwamnatin Tarayya ta bayyana sauƙaƙe wa ‘yan Najeriya tsadar kuɗin wutar lantarki har Naira tiriliyan 1.6 a shekarar 2024.
Shugaban Hukumar Raba Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC), Sanusi Garba ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai, a Abuja ranar Laraba.
NERC dai ta fito da sabon farashin kuɗin wutar lantarki ga dukkan masu amfani da ita a ƙasar nan.
Garba ya ce sabon tsarin ya samar da farashin da masu amfani da wuta za su biya, domin masu zuba jari a harkar su amshi kuɗaɗen gudanar da harkokin wutar.
Ya ce sabon tsarin ya nuna cewa saboda raɗaɗin tsadar rayuwar da ke addabar jama’a, to masu amfani da wuta ba za su biya fiye da yadda su ke biya a baya ba.
Ya ce sabon tsarin farashin shi ne kamfanonin sayar da wuta wato Discos za su riƙa caji domin su samu damar ci gaba da kasancewa su na tafiyar da aikin su.
“Wasu za su riƙa biyan N110 duk kWh ɗaya, wasu N120 duk kWh ɗaya, wasu ma N230 duk kWh ɗaya.
“Saboda kowane kamfanin wuta wato Disco aikin sa ya sha bamban da na kowa, bida nagarta da sauran su, shi ya sa muka yanka farashin kowace adadin wuta, bisa tsare-tsaren da gwamnati ta gudanar.
“Saboda gwamnatin ta ce bari daga yanzu saboda matsalar tsadar rayuwa, ba da daɗewa ba za a fara biyan kuɗin tallafi na wutar lantarki.
“Idan aka fara aiki da biyan tallafin na wutar lantarki, ana sa ran gwamnati za ta biya Naira Tiriliyan 1.6 matsayin kuɗin tallafin fetur a cikin shekarar 2024. Aƙalla dai duk wata Gwamnantin Tarayya za ta biya wa masu amfani da wutar lantarki har Naira biliyan 120 duk wata.