11/11/2024
Ɓatagari sun sake lalata wutar lantarki a Arewacin Najeriya - TCN
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ƙasa, TCN, ya baiyana cewa ɓatagari sun lalata layin wuta mai karfin 33KV daga Lokoja zuwa Gwagwalada.
A wata sanarwa da Manajan yaɗa labarai na kamfanin, Ndidi Mbah, ta fitar a juya Lahadi, ɓatagarin sun lalata rumbun raba wutar lantarki na T306, T307 da kuma T308 a ranar Asabar.
Ta ce sun kuma sace wayoyin alminiyon har dauri biyu.
A cewar Ndidi, an gano hakan ne bayan da TCN ya tashi ma'aikatan sa don gano musabbabin katsewar wutar lantarki da safiyar Asabar.
Sai dai ta ce an fara kokarin gyaran matsalar, inda ta baiwa al'ummar yankin da ma sauran da ke kan layin wutar hakuri.
~ Daily Nigerian Hausa