Three Pens Foundation

  • Home
  • Three Pens Foundation

Three Pens Foundation Tallafa wa masu neman taimako, wannan itace manufar mu. Ubangiji mu ke roka da yayi mana jagora. Aamin

23/10/2024
AN YANKE KAFAR YARINYARNAN 😭Ina jin damuwa da tashin hankali duk lokacin da zan fadi sakon an yanke kafa ko an cire ido ...
06/09/2024

AN YANKE KAFAR YARINYARNAN 😭
Ina jin damuwa da tashin hankali duk lokacin da zan fadi sakon an yanke kafa ko an cire ido ko an cire wani sashin jikin mutum, tabbas abun akwai tashin hankali, amma Allah ya fimu son bayinsa, muna adduar Allah ya basu lafiya da juriya, wanda za su iya taimakawa yarinyarnan da siya mata kafar roba kofarmu a bude ta ke, domin tun kafin a yanke kafar ta ke cewa a gayawa Anty Fauziyya ta siya mun kafar roba idan an yanke mun tawa😭.
Allah ya sakawa wadanda s**a taimaka da alkairi amin ya Allah.

DON ALLAH KU TAIMAKAWA YARINYARNAN ZA A YANKE KAFARTA😭.

Duk lokacin da zaa cire wani abu daga jikin mutum ko kafa ko ido ko hannu Ina shiga tashin hankali, ace mutum roko ya ke ma a taimaka masa a cire masa Sashin jikinsa ba karamin tashin hankali ba ne.
An kwana biyu da turo yarinyarnan na saka ta a layi ko kudin da zaa kaita asibiti babu, yanzu ake kirana ana sansr da wani ya taimaka musu an samu kaita asibiti an ce yanke kafar zaa yi kuma ba su da halin da za su biya kudin, gashi an ce ciwon na ci gaba da cin jikinta don haka aikin gaggawa zaa yi mata, don Allah ku taimaka musu, a kalla zaa nemi kusan Dubu Dari Uku (300) na aiki da magani da sauransu, ku taimaka mata🙏

Ga wanda za su taimaka za su iya tura taimakonsu ta account dinmu.
Account Number: 0109299375.
Bank name: Access
Account name: Creative Helping Needy Foundation.
Ko
Account Number: 0127121207
Account name: Fauziyya Danladi Sulaiman
Bank name: Gt.

Ga masu neman Karin bayani za su iya tuntubarmu ta WhatsApp ko message ko kiranmu ta wannan lambar waya, 07037147070, Allah ya baku ikon taimakawa ko da tayamu yadawa ne.

CreaCreative helping needy foundationaAlhassan Mai LafiasHafsat Bashir YunusazFauziyya D. SulaimaneThree Pens Foundationafsat3pens


MUN TARAWA YARONNAN MAI JINYAR MAHAIFIYARSA 600KAlhamdulillah mun samu tarawa yaronnan mai jinyar mahaifiyarsa Dubu Dari...
25/08/2024

MUN TARAWA YARONNAN MAI JINYAR MAHAIFIYARSA 600K
Alhamdulillah mun samu tarawa yaronnan mai jinyar mahaifiyarsa Dubu Dari shida (600k), mun ba su Dubu dari Hudu (400k) a hannunsu zaa gyara wani daki a gidansu a fitar da shi waje a mayar da shi shago mu zuba masa gawayi a ciki na kudin ya zama dealer din gawayi, mun siya masa kayan abinci na 100k, mun ajiye 100k da za mu dinga kaita asibiti, na san dai ba isa za ta yi ba, amma Insha Allah za mu ci gaba da kula da ita karkashin kungiyarmu, idan an kammala gyaran Sharon za mu nuna muku.
Muna adduar Allah ubangiji ya farantawa dukkan wadanda s**a taimakawa wannan baiwar Allah da
yaranta, mungode.

MATASHIN DA YA SADAUKAR DA RAYUWARSA SABODA MAHAIFIYARSA😭

Rayuwa matashinnan cike take da abun tausayi, shekaru bakwai mahaifiyarsa tana jinya barin jikinta daya ya shanye, shi yake kula da ita ya mata wanka ya dafa mata abinci ya kuma fita ya samo mata kudin magani, rayuwa ta masa wahala yanzu yana neman al'umma su taimaka masa, idan ya fita mema baya samu gashi ya barta a gida babu msi kula da ita.
Baya karatu sai jinyar mahaifiyarsa, ko bahaya za ta yi shi yake dorata a foo, idan kuma ya fita ya dawo ya tarar ta bata jikinta ya gyarata, tabbas wannan yaro Dan Albarka yana bukatar taimakonku al'umma 🙏😭.

Ga wanda za su taimaka za su iya tura taimakonsu ta account dinmu.
Account Number: 0109299375.
Bank name: Access
Account name: Creative Helping Needy Foundation.
Ko
Account Number: 0127121207
Account name: Fauziyya Danladi Sulaiman
Bank name: Gt.

Ga masu neman Karin bayani za su iya tuntubarmu ta WhatsApp ko message ko kiranmu ta wannan lambar waya, 07037147070, Allah ya baku ikon taimakawa ko da tayamu yadawa ne.

NB: DON ALLAH KU TAIMAKAWA KO DA TAYAMU YADAWA NE 🙏😭

CreatCreative helping needy foundationaHafsat B YunusatSenator Uba SanisAlhassan Mai LafiaiFauziyya D. SulaimanaLaylah Ali Othmanfsat3pens


ASIBITI SUN BIYO IYAYAN YARINYARNAN BASHI GASHI KO AIKI BAA YI BAWallahi iyayan yarinyarnan suna cikin tashin hankali na...
20/12/2023

ASIBITI SUN BIYO IYAYAN YARINYARNAN BASHI GASHI KO AIKI BAA YI BA
Wallahi iyayan yarinyarnan suna cikin tashin hankali na bashi da asibiti s**a biyo su kusan Dubu Dari Biyu da Hamsin (250k), Kwanaki mun aika musu abun da muka tara musu 438k, wanda a hoto kawai sai da aka kashe 300k, kafin a samu ayi hotonma an je ya fi sau uku ga ambulance da ake daukar haya ga sauran dawainiya don haka abun da muka tara tuni ya kare, kowa yasan yadda zaman Asibitin musamman National Hospital kuma a garin Abuja ya ke da cin kudui gashi yarinyar tana ICU.

A yanzu haka mahaifinta ya daina zuwa asibitin saboda babu sai kakarta ke kula da ita, da ya ke yan biyu ne su dayar lafiyarta kalau ita kuma wannan aka haifeta da Tumor, don haka mahaifiyarsu tana gida tana kula da dayar, kakar ta zauna anan, yanzu haka sai ta yi bara sannan ta ke samun abincin da za ta ci b***e ace su iya biyan bashi, kuma idqn sun biya sai sun ci gaba da kula da itai, don ance dole sai yarinyar ta kara kwari kafin ayi aikin.
Yanzu haka kakar ta kira tana kukan a taimaka musu a sallamesu don ba za su iya ba, kuma an ce idan aka yi sallamar yarinyar za ta iya rasuwa.don Allah jamaa ku taimakawa bayin Allah nan karo na biyu.

Ga wanda za su taimaka, za su iya saka taimakonsu ta account dinmu.

Account no; 0109299375
Account name: Creative Helping Needy Foundation.
Bank name: Access.
Ko
Account name: 0127121207
Account name; Fauziyya Danladi Sulaiman.
Bank name: Gt bank.

Ga masu neman Karin bayani za su iya tuntubarmu ta WhatsApp ko message ko kiranmu ta wannan lambar waya. 07037147070.

Don Allah Al'umma ku taimakawa jaririyarman da duk abun da Allah ya h**e muku, ko ku tayamu da yadawa har a samu a taimaka mata.



Real Hafsat 3pens
Fauziyya D. Sulaiman
Creative helping needy foundation
Fk Abdul Foundation
Senator Uba Sani
Umar Shehu Zaria

Wannan ita ce FATIMA MUSA, matar aure mai yaya 3 da Allah ya jarraba da hatsarin mota.Ta samu rauni (kashin Bayan Ta Ne ...
17/12/2023

Wannan ita ce FATIMA MUSA, matar aure mai yaya 3 da Allah ya jarraba da hatsarin mota.

Ta samu rauni (kashin Bayan Ta Ne ya Karye) kuma abun ya taba lakkar jikinta.

Assibiti an nemi kudi har N2,500,000 domin yin aikin, kuma mahaifinta talaka ne sosai.

Hakan yasa yarinyar ta share har shekara daya da wata shida ba’ayi aikin ba, kuma kudin da mahaifin ya nemo bayan ya sayarda gonarsa kudin bazai kai 200k ba.

Saboda bayin Allah fisabilillah ku taimaka da wani abu domin ceto rayuwar wannan boyar Allah.

N20 N50 N100 N200 N500 N1000 N5000 N10,000 N20,000 N50,000 N100,000 ko nawa Allah ya h**e a taimaka.

Idan Allah bai h**ema kudi ba, don Allah kayi sharing ko Allah zaisa acikin friends dinka ko followers dinka asamu wanda zai taimaka.

Kuyi addu’a da fatan alkhairi 🙏

Allah yabada ikon taimakawa ameen.

Ga account details kamar haka:

3197851019
Alhassan Musa
First Bank



RReal Hafsat 3pensFFauziyya D. SulaimanCCreative helping needy foundationFFk Abdul FoundationSSenator Uba SaniUUba Sani

*THREE PENS FOUNDATION* (Helping Needy) Wa ni bawan Allah ya ba da ta shi gudumuwar ga Foundation. Jazakallahu khairNair...
17/12/2023

*THREE PENS FOUNDATION* (Helping Needy)

Wa ni bawan Allah ya ba da ta shi gudumuwar ga Foundation.
Jazakallahu khair

Naira 100, 200, 500, 1000 ba ya sa kaɗan ga samun lada.
_________________
Tallafa wa masu neman taimako, Marayu da Mabuƙata Wannan itace manufar mu.

Idan kuka taimaka wa waɗanda basu da shi, suke neman taimako, sai Ubangiji ya taimake ku kuma. Sai a gobe alqiyama sannan zaka san amfanin haka.

Ubangiji mu ke roka da yayi ma jagora.



Real Hafsat 3pens
Creative helping needy foundation
Senator Uba Sani
Fk Abdul Foundation
Uba Sani

TABBAS BAWAN ALLAH NAN YA HADU DA JARABAWOWI😭😭Wannan bawan Allah, ya hadu da rajjabawa kala-kala a rayuwarsa, da farko g...
16/12/2023

TABBAS BAWAN ALLAH NAN YA HADU DA JARABAWOWI😭😭

Wannan bawan Allah, ya hadu da rajjabawa kala-kala a rayuwarsa, da farko ga shi mai larura ta musamman (Gurgu) sannan Allah ya dora masa ciwon koda da takai har an fara yi masa dialysis, ga babu ga kuma tarin iyali, abun gwanin ban tausayi.
An kwana biyu da tura mun vedio dinsa muka saka shi akan layi, to an kara kirana yau, domin ya je wankin kodar yau babu kudi yana ta kuka gashi gobe zaa kara yin wani.
Nasa. Bayin Allah suna kokarinsu, amma wannan bawan Allah ma yana bukatar taimakonku, don Allah kar ku gajiya ku taimaka masa da dukkan abun da Allah ya h**e muku.

Ga wanda za su taimakawa bawan Allah nan, za su iya saka taimakonsu ta account dinmu.

Account no; 0109299375
Account name: Creative Helping Needy Foundation.
Bank name: Access.
Ko
Account name: 0127121207
Account name; Fauziyya Danladi Sulaiman.
Bank name: Gt bank.

Ga masu neman Karin bayani za su iya tuntubarmu ta WhatsApp ko message ko kiranmu ta wannan lambar waya, 07037147070.

Allah ya baku ikon taimaka masa da duk abun da Allah ya h**e muku, ko ku tayamu da yadawa har a samu a taimaka maasa.



Real Hafsat 3pens
Creative helping needy foundation
Fk Abdul Foundationn

Update: Alhamdulillah mun kaiwa matashiyarnan kudin da aka tara mata Dubu Dari uku da Ashirin (320k), har likitoci sun s...
14/12/2023

Update: Alhamdulillah mun kaiwa matashiyarnan kudin da aka tara mata Dubu Dari uku da Ashirin (320k), har likitoci sun saka lokacin da za su yi mata aikin, muna godiya ga bayin Allah da s**a taimaka, Allah ya saka muku da alkairi amin.

KU TAIMAKAWA BUDURWAR DA KE SHIRIN RASA KAFUFUNTA AL'UMMA😭

Wannan matashiya daman gurguwace kafarta daya ce, da kafarta guda daya take rayuwa da taimakon sanda tana zuwa har makaranta, rannan suna kan babur za su makaranta wasu masu mota s**a buge su ta samu karaya uku a kafarta mai lafiyar da ta ke lallaba rayuwarta da ita

Wadanda s**a kadesy din suma ba su da shi don tsohuwar motar haya ce, don haka Dubu Goma s**a iya bayarwa aka yi mata dorin gida, sai dai dorin yazo da tangarda domin ya lalace har kafar ta fara rubewa, gashi karayar har uku ce a kafa daya, ganin tana shirin rasa kafar me lafiya wanda idan hakan ta kasance sai dai ta koma jan-gindi, ga ta yarinya mai kokari ita ke daukar ta daya a makarantarsu, bayan an kaita asibiti, sai dai likitoci sun ce sai an ajiye kusan 300k kafin ayi mata aiki, kuma iyayanta ba su da halin biyan wannan kudin.
Don Allah al'umma ku taimaka mu ceci rayuwar matashiyar kar ta rasa kafar da take rayuwa da ita guda daya.
Ga wanda za su taimaka domin ceto rayuwar wannan matashiya za su iya saka taimakonsu ta account dinmu.

Account no; 0109299375
Account name: Creative Helping Needy Foundation.
Bank name: Access.
Ko
Account name: 0127121207
Account name; Fauziyya Danladi Sulaiman.
Bank name: Gt bank.

Ga masu neman Karin bayani za su iya tuntubarmu ta WhatsApp ko message ko kiranmu ta wannan lambar waya. 07037147070.

Don Allah Al'umma ku taimakawa matashiyarnan da duk abun da Allah ya h**e muku, ko ku tayamu da yadawa har a samu a taimaka mata.


Na Jima Banyi Farinciki Ba Kamar Wannan Ranar:Wannan yaron MARAYA daga yau rayuwarsa ta canja IN SHA ALLAH, kuma ina muk...
13/12/2023

Na Jima Banyi Farinciki Ba Kamar Wannan Ranar:

Wannan yaron MARAYA daga yau rayuwarsa ta canja IN SHA ALLAH, kuma ina muku alkawali za’a kula sosai domin tabbatarda ingancin karatunsa, da daukar nauyin karatunsa har jami’a IN SHA ALLAH.

Mutane dayawa sun nemi abasu account number domin kara taimaka masa, saboda haka duk wanda yaji zai iya kara bada nashi gudun mawa to BISMILLAH:

Ko yanzu akwai aikin nema masa sana’a da zai dauke nauyin kansa da dogaro da kansa.

Amma mafi muhimmanci shine karatu, kuma Alhamdulillah anzo karshen maganar karatunsa na BOKO da ADDINI.

Saboda haka sadaka bata yawa, idan har da wanda yakeso ya kara taimakonsa to hanya a bude take, Allah ya saka da alkhairi, Abdulrazzak na godiya.

3197851019
Alhassan Musa
First Bank


KU TAIMAKAWA BUDURWAR DA KE SHIRIN RASA KAFUFUNTA AL'UMMA😭 Wannan matashiya daman gurguwace kafarta daya ce, da kafarta ...
13/12/2023

KU TAIMAKAWA BUDURWAR DA KE SHIRIN RASA KAFUFUNTA AL'UMMA😭

Wannan matashiya daman gurguwace kafarta daya ce, da kafarta guda daya take rayuwa da taimakon sanda tana zuwa har makaranta, rannan suna kan babur za su makaranta wasu masu mota s**a buge su ta samu karaya uku a kafarta mai lafiyar da ta ke lallaba rayuwarta da ita

Wadanda s**a kadesy din suma ba su da shi don tsohuwar motar haya ce, don haka Dubu Goma s**a iya bayarwa aka yi mata dorin gida, sai dai dorin yazo da tangarda domin ya lalace har kafar ta fara rubewa, gashi karayar har uku ce a kafa daya, ganin tana shirin rasa kafar me lafiya wanda idan hakan ta kasance sai dai ta koma jan-gindi, ga ta yarinya mai kokari ita ke daukar ta daya a makarantarsu, bayan an kaita asibiti, sai dai likitoci sun ce sai an ajiye kusan 300k kafin ayi mata aiki, kuma iyayanta ba su da halin biyan wannan kudin.
Don Allah al'umma ku taimaka mu ceci rayuwar matashiyar kar ta rasa kafar da take rayuwa da ita guda daya.
Ga wanda za su taimaka domin ceto rayuwar wannan matashiya za su iya saka taimakonsu ta account dinmu.

Account no; 0109299375
Account name: Creative Helping Needy Foundation.
Bank name: Access.
Ko
Account name: 0127121207
Account name; Fauziyya Danladi Sulaiman.
Bank name: Gt bank.

Ga masu neman Karin bayani za su iya tuntubarmu ta WhatsApp ko message ko kiranmu ta wannan lambar waya. 07037147070.

Don Allah Al'umma ku taimakawa matashiyarnan da duk abun da Allah ya h**e muku, ko ku tayamu da yadawa har a samu a taimaka mata.


Address


Telephone

+2347014993003

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Three Pens Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share