Hisnul muslims

  • Home
  • Hisnul muslims

Hisnul muslims Wannan page din munbudeshine don taimakama kanmu wajen koyan addu'o'i cikin sauki, daga Qur'ani da su

May Almighty Allah forgive us and Grant us jannah, Ameen.
06/04/2024

May Almighty Allah forgive us and Grant us jannah, Ameen.

06/04/2024

Allahumma,lnnaka afuwun tuhibbul afwa, faafu annaa.

Manzon Allah (s.a.w.) yana cewa: duk wanda ya sallaci sallar dare wato tarawihi na watan ramadan, kuma yana mai imani da...
25/03/2024

Manzon Allah (s.a.w.) yana cewa: duk wanda ya sallaci sallar dare wato tarawihi na watan ramadan, kuma yana mai imani da kwadayin lada Allah zai gafarta masa zunubansa wadanda s**a wuce. Yan uwa munji garabasa daga bakin da baya karya s.a.w. kar muyi sake da wannan garabasa har yawuce bamuyi abin da ya dace ba awannan wata mai albarka, Allah muke roko ya amsa mana ibadunmu ya sanya mana a mizani.

Annabi (s.a.w) yace duk Wanda yamin salati kwara daya tak  Allah zai masa guda goma. To yan uwa munji garabasa daga  bsk...
26/02/2024

Annabi (s.a.w) yace duk Wanda yamin salati kwara daya tak Allah zai masa guda goma. To yan uwa munji garabasa daga bskin da bays karya. Allah yasa Annabi s.a.w. ya CeCe mu

29/12/2023

🌴 FALALAR TUBA DA ISTIGFARI🌴

📜 Manzon Allah ﷺ yace "Yaku mutane ku tuba zuwa ga Allah, domin lallai ni ina tuba a wuni sau ɗari".
📚 صحيح مسلم ٢٧٠٢

📜 Manzon Allah ﷺ yace "Madalla ga wanda aka samu Istigfari mai yawa acikin takardarsa".
📚 صحيح ابن ماجه ٣٠٩٣

📜 Manzon Allah ﷺ yace "Babu wani mutum da zai aikata wani zunubi, sannan ya tashi yayi tsarki (Alwala), sannan yayi sallah raka'a biyu, ya nemi gafarar Allah, face Allah ya gafarta masa".
📚 حديث حسن ، رواه الترمذي ٤٠٦

▪️Malamai s**a ce
"Idan mutum ya nemi gafarar Allah ya tuba gareshi, tuba ingantatta, kuma ya ciratu zuwa ga zunubi, Allah zai karɓi tubansa, kuma zai gafarta masa. Idan ya sake komawa zuwa ga zunubi sannan ya nemi gafarar Allah kuma ya tuba, tuba ingantatta kuma ya ciratu zuwa ga zunubi, Allah zai karɓi tubansa, kuma ya gafarta masa. Kamar haka, laifin zunubin da yawuce ba zai dawo ba, tare da tuba ingantatta. Allah maɗaukaki yace
(وَإِنِّي لَغَفَّارٌ لِّمَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَالِحًا ثُمَّ ٱهۡتَدَىٰ) طه ٨٢ ، وقال : (إِنَّ رَبَّكَ وَاسِعُ ٱلۡمَغۡفِرَةِ) النجم"
📓 فتاوى اللجنة الدائمة ٣١٩/٢٤

▪️Ibnul Qayyum رحمه الله yace
"Abubuwa huɗu suna jawo arziƙi: (i) Tsayuwar dare (ii) Yawaita istigfari lokacin safiya (iii) Yawaita sadaka (iv) Ambaton Allah a farkon yini da ƙarshensa".
📘زاد المعاد ٣٧٨/٤

▪️Ibn Kathir رحمه الله yace
"Duk wanda ya siffanta da siffar Istigfari Allah zai sauƙaƙa masa arziƙinsa, zai sauwaƙa masa al'amarinsa, zai kiyaye sha'aninsa da ƙarfinsa".
📙تفسير ابن كثير ٣٢٩/٤

▪️ Ibnul Qayyum رحمه الله yace
Wanda ya dauwama yana Tasbihi sirrikansa zasu warware (buƙatunsa zasu biya). Wanda ya dauwama yana Tahamidi (Godiya ga Allah) alkhairai zasu bibiyeshi. Wanda ya dauwama yana Istigfari za'a buɗe masa abubuwan da s**a kulle mashi".
📕الداء والدواء ١٨٨

▪️Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai

Yakai Ɗan-uwa mai Albarka ka yaɗa wannan saƙo, zaka samu lada. Domin lallai duk wanda yayi nuni kan aikin alkhairi kamar ya aikata ne

Allah Ka bamu ikon tuba ingataciya..🤲

23/11/2023

Kowacce Cuta Tana Da Magani.
Maganin Zunubi Shine Istigfari.
Ya Ubangiji Allah Ka Amshi Tubanmu Kasa Aljannah Ta Zamo Makomarmu🤲.

16/11/2023

Indai kanason ka gamu da Allah lafiya kuma tafiya lahira tayi maka sauki, To wajibinka ne yazamanto manzon Allah (s.a.w.) shine jagoranka, jagabanka kuma shine fitilarka. Ya Allah kasa annabi yazamanto fitilarmu mai haska mana hanya tagaskiya duniya da lahira. Ameen.

14/11/2023

Ga wata addu'a mai muhimmanci.

Abin da wanda ya ji tsoron wasu mutane zai fada:

اَللَّهُمَّ اكْفِنِيهِمْ بِمَا شِئْتَ.
Allahummak finihim bima shi'ita.
Ya Allah! Ka isar mini su da abin da Ka so.
Insha Allah inhar kalazimci wannan addu'a Allah zai kareka daga duk wani mai nufinka da sharri. Ya Allah muna rokonka ka tsaremu ka tsare gaban mu ka tsare bayanmu Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum.

Wannan kuma shine group link din.
09/11/2023

Wannan kuma shine group link din.

WhatsApp Group Invite

09/11/2023

Yan uwa haryanzu muna kara sanar daku cewa ga mai son shiga wannan group namu mai albarka na whatsapp to ya ajiye numbersa zamu yi addin dinsa insha Allah.

Surorin da zaka fara dasu kenan alokacin yin azkar na safiya da maraice, ayatul kursiyyu kafa 1, ikhlas falaqi da nasi k...
09/11/2023

Surorin da zaka fara dasu kenan alokacin yin azkar na safiya da maraice, ayatul kursiyyu kafa 1, ikhlas falaqi da nasi kafa 3 3.

Ya kai/ke! 'Yar uwa ina dukiyarki?ina ikon da ka/ki ke dashi?ina karfinka?To lallai muji tsoron Allah, muji tsoron muji ...
02/11/2023

Ya kai/ke! 'Yar uwa ina dukiyarki?
ina ikon da ka/ki ke dashi?
ina karfinka?
To lallai muji tsoron Allah, muji tsoron muji tsoron watarana da za'a sanyamu acikin kabarinmu muka kadai.
Ya! Allah ka gafarta mana ka yafemana.

30/10/2023

Cikakkiyar natsuwar ruhi ta tabbata ga mutumin da tunanin laifuffukansa ya hanashi hangen laifin wani.

Ya Allah ka kara jaddada imani a cikin zukatanmu.

23/10/2023

Don kana Fama da Qalubalen rayuwa, baya Nufin Watarana komai ba zai chanja ba.

Akwai juyin da zatayi, kai da kake neman taimako yanzu, kai zaka taimakawa wani gobe.

Wanda s**a Qi taimakonka Yau, ta yiyu gobe Sai sun biyo ta Qasan takalmanka. Babu wani baqon al'amari wajen Ubangijin da kake yiwa sallah.

Misalai sun wanzu masu tarin yawa, Wasu mun gani da idanunmu, Wasu mun ji a kunnuwanmu Wasu ma Sai dai mu hakaito da tunaninmu.

Kai dai kayi bakin kokarinka wajen kiyaye duk dokokin ALLAH. Kayi aiki tuquru iya iyawarka, kayi addu'a tuquru fiye da yadda zaka iya.

ALLAH ka taimakemu ka bamu iko da juriyar kowace irin jarawa da zata zo mana, kayiwa kowa budi na alkhairi don alfarmar annabi (s.a.w).

Allah ya yafe mana kura kuran mu baki daya.
22/10/2023

Allah ya yafe mana kura kuran mu baki daya.

21/10/2023

MASU RABAUTA A DUNIYA MUTANE UKU NE:

1. Wanda ya ƙyale duniya tun kafin ta ƙyale shi.

2. Wanda ya yi ma iyayen shi biyayya kafin su rabu da shi.

3. Sai wanda ya yi ƙoƙari har Allah ya yarda da shi kafin ya hadu da shi.
Allah muke roko ya bamu dacewarsa.

11/10/2023

IDAN KAƘI ABUBUWA 5 ALLAH
ZAI BAKA ABUBAUWA GUDA 10

1) Idan kaƙi haram
Allah zai baka halal
Kuma da farin ciki

2) Idan kaƙi ƙarya
Allah zai baka faɗin
gaskiya kuma da nitsuwa

3) Idan kaƙi Zina Allah
zai Aurar dakai da kuma
wadata na zahiri

4) Idan kaƙi aboki mara
gaskiya, Allah zai haɗaka
da mai gaskiya kuma wanda
zai ɗauraka a daidai

5) Idan kaƙi kallon haramun
da idanunka, kaƙi karɓan haramun
da hanunka, kuma kaƙi furta haramun
da bakinka, to Allah zai kare maka su
kuma zai kiyaye maka su cikin Aminci.

Allah ya tsaremu
aikata laifi komin ƙanƙantar sa, Ameen.

09/10/2023

Ga wata Addu'a mai muhimmancin gaske.
Zakaga mutum yana yawan aikata fasikanci amma zuciyarsa bata son abun misali
Kamar yawan taba mace wacce ba muharrama ba ko maganganu na batsa
Kai wallahi ko ZINA kakeyi indai kana yawan karanta wannan addu,ar
To idan har acikin zuciyarka kana da burin dainawa to wannan addu,ar zata taimaka maka, kuma Allah ya shiryar dakai bakasan lokacin da zaka dainaba
Ga addu'ar Kamar haka:-
أللهم إنى أعوذ بك من شر قلبى ومن شر بصرى ومن شر لسانى ومن شر منيى
Allahumma inni a uzu bika minsharri Qalbee wamin sharri basaree wamin sharri Lisa,nee wamin sharri maniyyee

muna rokon Allah ya tsaremu daga fadawa munanan ayyuka.

Kuma muna rokon Allah ya shiryar damu akan hanyar muslunci.

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKAATUHU. _Zamanin da hanyoyin shagaltarwa su ka yawaita,a cikin sa.Ya zama dole ga...
08/10/2023

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKAATUHU.
_Zamanin da hanyoyin shagaltarwa su ka yawaita,a cikin sa.Ya zama dole ga mai neman tsira,ya ware wani lokaci na musamman da zai dinga ganawa ta musamman da Mahaliccin sa, domin shine Wanda ya halittashi Kuma yasanya masa dokoki da zaibi,
Allah muke roko ya bamu ikon Yi masa bauta Kamar yadda ya umurcemu.

06/10/2023

Allah madaukaki sarki yasa muwanye lafiya

03/10/2023
01/10/2023

Ku rika Yin Azkar kafin fita wajan aiki ko kasuwa. domin neman tsari da kariya daga musifun wannan zamani,Allah ya Karemu.

26/09/2023

Alhamdulillah da iznin Allah mundawo insha Allah zamu cigaba da kawo muku addu'oi kamar yadda muka saba bisa koyarwar annabinmu(s.a.w).

Muna rokon Allah madaukakin sarki yayi mana jagora. Ameen

10/04/2022

Wannan addu’ar an tsagota ne daga shahararriyar addu’ar nan wacce Manzon Allah (saww) ya yi ma Sayyidina Anas bn Malik (ra) a lokacin da Mahaifiyarsa ta kawo shi gare shi.

Ga addu’ar nan kamar haka :

Bismillahi rahmanir Rahim

ALLAHUMMA AKTHIR MALIY WA WALADIY, WA BARIK LIY FEEMA A’ATAITANEE.
FASSARA : “Ya Allah ka yawaita dukiyata da ‘ya’yana. Kuma ka albarkaceni a cikin abinda ka bani”.
Albarkacin wannan addu’ar da Manzon Allah (saw) ya yi wa Sayyidina Anas bn Malik (ra), Sai da Sayyidina Anas ya rayu kusan shekaru ?ari (100) a duniya. Kuma da idonsa sai da ya ga fiye da ?a?a ?ari daga cikin zuriyarsa.
Haka nan sai da ya zamanto dukiyarsa ta yi albarka ta yawaita sosai. Har ma bishiyoyin dabinon gonarsa sau biyu suke haihuwa duk shekara.

10/04/2022

An samo daga Manzon Rahama cewa, wanda ke son Allah ya buda masa kwakwalwa domin neman ilmi, sai ya lizimci karanta wannan Adduar. Bayan sallah asubah.

Ya man huwa fi Uluwi hi kainun, wa ya man huwa fi izihi ladifun, wa ya man huwa fi fiilihi muhidun, wa ya man huwa fi ilmi hi muhidun, wa ya man huwa fi majdihi munirun, bi rahmatika ya arrahma rahimin.

Assalamu alaikum jama'ar wannan gida mai albarka wannan shine sabon group whatsapp dinmu na hisnul muslom gama sha'awar ...
27/02/2022

Assalamu alaikum jama'ar wannan gida mai albarka wannan shine sabon group whatsapp dinmu na hisnul muslom gama sha'awar shiga sai ya shiga wannan link din a kasa
https://chat.whatsapp.com/FlPG8zO9yQnA3mPZeC6q38

WhatsApp Group Invite

09/04/2021

Aslm jama'a muna muku barka da wannan lokaci, kuma muna rokon Allah yasa muna daga cikin wadanda zasu azumci wannan wata mai albarka dake karatomu Allah yasada da alkhairinsa Ameen.

Yan uwa muyawaita fadin wannan addu'ar
01/02/2021

Yan uwa muyawaita fadin wannan addu'ar

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hisnul muslims posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share