06/09/2021
KIRA ZUWA GA ADDINI
Jawabin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a Mu’utamar a garin Gusau, shekarar 2012
MAQASUDIN ZUWANMU GARIN GUSAU
Bismillahir Rahmanir Raheem.
Kamar yadda masu gabatarwa s**a yi bayani cewa makasudin zuwana Gusau don rufe wani taro ne wanda ake ce ma ‘conference’ ko ‘mu’utamar’, ko taron karawa juna sani, wanda sashin ‘yan uwa da suke manyan makarantun gaba da sakandire s**a shirya.
Dama akwai dandalin da ake cewa ‘Academic Forum’ wacce ke kula da daliban manyan makarantu da malamai masu karantarwa a irin wadannan makarantun. To su ne s**a shirya wannan taron wanda s**a fara tun shekaran jiya Alhamis, kuma za su kare gobe (Lahadi). Su ne s**a gayyaceni don na zo na yi jawabin rufe taron nasu.
To, dama irin wannan taron nasu su kan kira shi a garuruwa daban-daban, duk lokacin da muka je kowane gari sai su yi amfani da wannan damar a sadu da mutanen gari (al’ummar musulmi) gaba daya, a gaggaisa da wasu kalmomi ko yaya ne. Wannan shine ya sa ‘yan uwa na Gusau s**a bidi a zo a yi jawabi ga kowa da kowa, kuma aka amsa musu a kan haka nan.
To, gashi lokaci ya yi nisa, ya kamata ya zama muna gab da tashi ne, amma yanzu za mu fara. Saboda haka a gurguje ba tare da daukan dogon lokacinku ba, zan jaddada mana cewa gaskiyar magana ita ce ba wani abu ne sabo zan fada ba. Duk da kamar yadda shi Malam Shu’aibu ya fada cewa rabona da nan garin shekaru 18 ne cur in bai manta ba. Ina jin bai manta ba dama, rabona da nan garin shekara goma sha takwas din ne cur, akalla wanda aka yi wa’azi ga mutane.
YINMU A MUSULMI BABBAR FALALA CE
To, amma abin da zan fada yanzu ba zai bambanta da wanda na fada wancan lokacin ba, da ma wasu lokuta kafin lokacin, kuma haka ma ba zai bambanta ba har nan gaba.
Kalma ce sassauka. Alhamdulillah, muna godiya ga Allah da ya mana baiwar zama musulmi, wanda wannan baiwa ita ce ta fi a kan dukkan baiwowin da Allah Ta’ala ke wa mutum. Na farko, halittar mutum daga rashi baiwa ne, domin da ba a haliccemu ba ma da babu mu. Saboda haka samar da mu daga rashi babban baiwa ce da Allah Ta’ala ya yi mana.
To, akwai baiwan da ya fi wannan. Bayan an samar da kai din, sai Allah Ta’ala ya fifita mu ya yi mu mutane, wanda su ya fifita birbishin sauran halitta (har da mala’iku da Aljannu, ballanta ma tsintsaye, kwari, dabbobi, kifaye a ruwa da sauransu), duk halittun da mutum zai gani, zai ga cewa mutum shine Allah Ta’ala ya fifita birbishin duk halitta.
Hatta a kyawun halitta da Allah ya wa mutum, ya fi kowace halitta kyau, don Dan Adam ba zai ga wata halitta a cikin halittu ya yi burin da ace shine wannan halittar ba komai kyawunsa kuwa. A kan ce Mariri yana da kyau, ko Barewa, amma Dan Adam ba zai ga Mariri yana da kyau yace ina ma shine Mariri ba. Ko kurciya, wacce ita ma aka ce tana da kyau, ko ma Dawisu, wanda yake da ado, Dan Adam ba zai ga Dawisu yace ina ma shine ba. Allah Ta’ala ya fifita Bi’adama birbishin duk sauran halittu. To, wannan babban baiwa ce; aka samar da kai daga rashi, sannan kuma aka yi ka mutum.
To, haka nan kuma wata falala da ta wuce a yi ka mutum shine a yi ka musulmi. Yinka musulmi ya fi a yi ka mutum. Domin kuwa in har ka kasance kai mutum ne amma ba musulmi ba, to gara ma a yi ka ba mutum ba. Gara a yi ka Akuya ka rika Mee, ko da kuwa wani zai sace ka. Akalla dai in ka je gobe kiyama ba wuta ba Aljanna ga akuya, amma shi kuwa mutum, an yi gida biyu dominsa; imma wuta ko Aljanna. To ba wanda zai shiga Aljanna sai musulmi. In ka shafa Aljanna kakakaf kowa da kowa musulmi ne, ba yadda za a yi kafiri ya shiga Aljanna.
Duk wanda ka ganshi a Aljanna musulmi ne, saboda haka a yi ka a musulmi ya fi a yi ka a mutum. Domin in an zo hisabi gobe kiyama, aka wa dabbobi hisabi ana cewa su zama turbaya. Wanda kuma Allah Ta’ala ya bamu labari a cikin Alkur’ani cewa: “Kuma kafiri zai ce ya kaiconsa, inama na zama turbaya.” Wato yana burin makomar dabba. To ka ga ashe shi yinsa mutum bai amfane shi ba, saboda yinka a musulmi ya fi a yi ka mutum. Saboda haka wannan babbar ni’ima ce yin mutum musulmi.
Dalilin da yasa nake cewa yinka musulmi, saboda mun ga kanmu ne a musulmi. Mun ga kanmu ne Alhamdulillahi iyayenmu musulmi ne, kakanninmu musulmi ne, kakannin kakanninmu iyakan saninmu dai mun girma a cikin musulmi ne. wannan baiwa ce da Allah Ta’ala ya mana, ba bisa hadari bane, ba kuma zabinmu bane, baiwa ce ta Allah Ta’ala.
Za mu cigaba
- Cibiyar Wallafa