Mohiddeen Online

  • Home
  • Mohiddeen Online

Mohiddeen Online Sci, Biz & Tech fancier, Digital Marketer, Writer and CEO of Alphamega Digital Services

Dear Mohiddeen Online Users,I am deeply sorry to inform you that my app and website, Mohiddeen Online, may probably stop...
05/10/2023

Dear Mohiddeen Online Users,

I am deeply sorry to inform you that my app and website, Mohiddeen Online, may probably stop working very soon.

Over the past year, many people have benefited from this platform, where I've shared useful insights from various fields, and uploaded essential docs, eBooks and videos.

Unfortunately, due to certain challenges, I find myself in a position of shutting it down. I really apologize for any inconvenience this hard decision may cause, and deeply appreciate your support throughout this journey.

Thank you!

—Muhammad Auwal Ahmad ( )

Idan ba ka samu garaɓasar 60% discount na shiga private forum ɗina da kyautar littatafaina ba, ka hanzarta gobe sai ƙare...
02/10/2023

Idan ba ka samu garaɓasar 60% discount na shiga private forum ɗina da kyautar littatafaina ba, ka hanzarta gobe sai ƙare. Wannan ce babbar dama ga waɗanda ke son kasancewa members.

✔Over 200 lectures...
✔Over 60 eBooks...
✔2 Premium eBooks...
✔Unlimited access...
✔60% discount...

Mafi yawan lectures da ke ciki game da online business, marketing, web mastering, business strategies and management, ecommerce da sauransu

Tuntuɓe ni ta WhatsApp 👇

https://wa.me/2348162374764

GARAƁASAR KWANA UKU!Ina masu son shiga private forum ɗina M-O Forum? Ga dama ta samu.....tare da mallakar littatafaina i...
30/09/2023

GARAƁASAR KWANA UKU!

Ina masu son shiga private forum ɗina M-O Forum?

Ga dama ta samu...
..tare da mallakar littatafaina irin su Zo Mu Gina Kamfani, Sirrukan Sana'o'i 99, eBillions Mastery, Kasuwancin Yanar Gizo, da sauransu.

Daga yau 30th September zuwa 3rd October, kana da damar samun garaɓasar 60% discount a wannan lokacin don shiga forum ɗin tare da kyautar duk waɗannan littatafai.

Wow!

A forum ɗin akwai 200+ lectures da 60 eBooks, yawanci a kan online business, marketing, ecommerce, blogging, webmastering da sauransu.

Ba wani dogon bayani ka tuntuɓe ni ta WhatsApp daga yanzu zuwa 3rd October 👇

https://wa.me/2348162374764

—Muhammad Auwal Ahmad ( )

RABE-RABEN MASANA NA'URA..matakan zama ƙwararren masanin na'uraSaboda yawan kuskure ma'anonin matakan ƙwarewa a fannin n...
11/09/2023

RABE-RABEN MASANA NA'URA
..matakan zama ƙwararren masanin na'ura

Saboda yawan kuskure ma'anonin matakan ƙwarewa a fannin na'ura ya sa na ɗauki ƙudirin yin wannan taƙaitaccen rubutun don fayyace rabe-raben masana na'ura k**ar haka:

1. COMPUTER LITERACY
Mataki na farko a duniyar na'ura shi ne saninta; wato dole mutum ya san mece ce ita, yaya ake amfani da ita, da kuma yadda ake sarrafa ta. Duk wanda ya iya wannan shi ake ƙira Computer Literate. Irin waɗannan su s**a fi yawa a cikin al'umma, misalin irinsu akwai masu tura waƙa da sauran al'ummar gari masu amfani da na'ura.

2. COMPUTER GEEKINESS
Idan mutum ya san na'ura da yadda ake amfani da ita da yadda zai warware matsalolinta, to yana wannan matakin, ana ƙiran shi Computer Guru ko Computer Geek. Irin su ne masu gyaran na'ura da warware matsalolinta.

3. COMPUTER SPECIALISM
Mataki na uku shi ne ƙwarewa a wani ɓangaren zamani na na'ura. A nan mutum zai ƙware a wani fanni, misali a programming, ko software development, ko häcking, ko graphics, ko embedded systems, ko robotics, da sauransu. Duk wani wanda ya ƙware a fanni guda na na'ura a wannan matakin yake, ana ƙiran shi IT Guy ko Computer Specialist.

4. COMPUTER PIONEERING
Mataki na ƙarshe kuma shi ne zama Computer Pioneer, wato wanda ya tumbatsa a duniyar na'ura har ya ƙirƙiro wani sabon abu. Misalin irinsu akwai Tim-Berner Lee, Steve Jobs, Alan Turing, Charles Babbage, James Gosling da sauransu.

A wannan bayanin za mu fahimci cewa, a misalance k**ar haka abun yake:

—Computer Literate shi ne ɗan primary zuwa secondary

—Computer Guru shi ne mai digiri (BSc)

—Computer Specialist shi ne mai MSc

—Computer Pioneer shi ne mai PhD har ya zama Professor Emeritus

Wannan misali ne yadda za mu ga abun a zahiri. Don haka yana da kyau mu fahimci waɗannan matakan, don mu ma mu san matakin da muke sai mu ƙara dagewa.

Allah Ya taimaka Ya sa mu dace, amin

—Muhammad Auwal Ahmad ( )
Scientist, technologist, Cofounder/CEO of Flowdiary

25th June 2022

06/08/2023

A cikin littafin Malcolm Gladwell mai suna Outliers: The Story of Success, ya kawo wani tsarin koyon skill wanda ya yi wa laƙabi da The 10,000-Hour Rule, wanda kai-tsaye yake nuna cewa matuƙar ka tsaya tsayin-daka a duk wani skill da kake son koya kuma ka ba shi 10,000 hours to haƙiƙa sai ka ƙware a kai kuma ka zama gwani.

Wannan yana nuna cewa akwai buƙatar ka rinƙa shafe sa'o'i biyu a kullum kana koyon wannan skill ɗin, wanda daga ƙarshe hakan zai sa ka shafe har tsawon shekaru 13 da watanni 7, wato ka cika 10,000 hours ke nan.

Idan ka tuna daman an ce ka kwantar da ranka, yana ɗaukar tsawon shekaru 10 kafin ka gina career a kowanne field.

A WANNE MATAKI KAKE A "THE SIX WEALTH ARCHETYPES"? Shahararren masani Dan Lok ya nuna ɓangarorin da neman arziƙin mutum ...
30/07/2023

A WANNE MATAKI KAKE A "THE SIX WEALTH ARCHETYPES"?

Shahararren masani Dan Lok ya nuna ɓangarorin da neman arziƙin mutum yake tafiya wanda ya yi wa laƙabi da "The Six Wealth Archetypes" a cikin littafinsa mai suna Unlock It.

Ga su k**ar haka:

1. THE CAGED LION
Kana da ƙarfi, ilimi da basira, amma sai aka kulle ka a wani yanki ana bautar da kai tare da ba ka ɗan wani abu da ake ƙira albashi wanda kwata-kwata ba ya isarka, amma saboda kana tsoro ka bar aikin ka nemi na kanka, sai ka zauna don dole aka ci gaba da bautar da kai.

Wannan shi ne abun da aka yi wa zaki. An kamo shi daga daji an kulle shi a wani keji ana ba shi nama kaɗan-kaɗan duk da cewa yana da ƙarfi da izza. A maimakon ya yi kukan kura ya fita ya nemi na kansa wanda zai ishe shi, amma sai yake tsoro idan ya fita a nan bai san inda zai je ba. Ya bari an kulle shi a keji ana amfani da shi ana samun kuɗi.

2. THE CHAINED MAGICIAN
Kana da basira da fiƙira sosai, amma sai ake daƙile duk wani ƙoƙarin da kake yi don ganin ka ƙirƙiri abubuwan zamani. Mutanen garinku suna cewa ka fiye nuna cewa kai me basira ne, ta yaya za ka ce za ka iya ƙera jirgin sama, ko wayar hannu, ko manhajar na'ura da sauransu. Ai kawai ka daina nuna cewa kana da basira, ka manta da mafarkin da kake yi na zama wani abu a rayuwa.

Haka ake yi wa matasa masu fiƙira. Ana sare musu gwiwa cewa ba za su iya komai ba tunda su ba Turawa ba ne. Ana ƙaryata fiƙirar da Allah Ya ba su ana sare musu gwiwa tare da daƙile duk wani bincike na ilimi da za su yi. Sai ka ji an ce, "Kai har ka isa ka ce za ka iya ƙirƙira abun da Turawa suke ƙerawa?" Idan kuma ka yi sai a ce, "Ai wahalar banza kake sha, wannan ɓata lokaci ne kawai, ka bari ka koma aikinmu na gargajiya." Suna ci gaba da sare maka gwiwa cewa ba za ka iya kawo wani canji a yankinku ko duniya ba.

3. THE HUSTLING TREASURE HUNTER
Kai ne ka kutsa cikin duniya neman kuɗi, neman abun da za ka rufa wa kanka asiri. Duk da ka ƙira kanka ɗan fafutuka, amma kana yawan sarewa da zaran ka ji ƴar wahala ko kuma ka ga k**ar ba za ka iya yin wani abu ba. Kana yawan sarewa da zaran ka fara nema, kana yawan kawo ƙorafe-ƙorafe da excuses a matsayin dalilan da ya sa kake faduwa.

Idan aka ba ka wata idea sai ka ce ai ba ka da lokaci ko kuɗi. Idan aka ce ka nemi ilimin wani abu sai ka fake da cewa ya yi tsauri ko kuma babu lokaci. Kana yawan ƙorafi amma ba ka amfani da wata dama don kai ma dama, kai dai kullum kana ikirarin cewa fafutuka kake amma ba da gaske kake ba.

4. THE INNOCENT PRISONER
Ka gama karatu ka samu aiki a lokacin da kake matashi, amma bayan shekaru sun ja kuma nauyi ya ƙaru, sai abubuwa s**a fara tafiya a baibai. Ga shi nan dai kana samu ba laifi amma ba ya isar ka, kuma ba ka iya wata sana'a ba da albashi kawai ka dogara. Shi ke nan, sai ka fara ganin abubuwa suna tafiya a baibai.

5. THE SUCCESSFUL CASTAWAY
Kana ji a ranka duniya ta yi watsi da kai don ba ka da wani "value", amma duk da haka kana gwagwarmayar neman na kai wa bakin salati. Zaman kaɗaici ya dame ka domin kullum a cikinsa kake. Ba ka da wani farin ciki saboda keɓanta da ka yi daga cikin mutane, ko kuma dai rashin "value" ɗin ne ya janyo maka keɓanta daga mutane, ƴan'uwa da sauran abokai.

6. THE UNFULFILLED KING
Duk da kasancewarka sarki wanda ya mallaki tarin dukiya da kayan alatun duniya, amma har yanzu kana ji ba ka ƙoshi ba. Kullum kana cikin tunanin yadda za ka ƙara yawan mamaye wasu yankuna, ninka yawan arziƙinka, da faɗaɗa hanyar da za ka ƙara tara dukiyoyi. Duk da cewa ba ka rasa komai ba, amma kullum kana jin ƙishi.

——————————————————
Idan ka nutsu ka karanta wannan abun da kyau kuma ka nazarce shi da kyau tare da faɗaɗa tunaninka, za ka gano cewa haƙiƙa kai ma ka taɓa faɗawa cikin ɗaya daga cikin waɗannan matakan ko kuma yanzu kana kai.

Idan duk ba haka ba ne, ka tsaya ka yi nazarin amfani da rashin amfanin kasancewa a cikinsu, sannan ka yi wa kanka karatun-ta-nutsu don gujewa faɗawa.

Allah Ya fishshe mu, amin.

✍ Muhammad Auwal Ahmad ( )
CEO, Flowdiary
30th July, 2023

WANI HATSABIBIN MADATSI YA ƘIRƘIRO WATA FASAHAR AI DON GUDANAR DA AYYUKAN ƁARNAƊaya daga cikin abun da ake gudu a duniya...
18/07/2023

WANI HATSABIBIN MADATSI YA ƘIRƘIRO WATA FASAHAR AI DON GUDANAR DA AYYUKAN ƁARNA

Ɗaya daga cikin abun da ake gudu a duniyar tech yana shirin faruwa, a yanzu haka wani hatsabibin madatsi ya ƙirƙiro wani AI chatbot kawai saboda gudanar da ayyukan kutse.

Saɓanin ChatGPT wanda aka yi masa training da ɗabi'u kyawawa da gujewa ayyukan ɓarna, shi wannan sabon aikin shaiɗancin mai suna WormGPT an samar da shi specifically don gudanar da ayyukan ɓarna.

An sanya wa WormGPT zunzurutin mugunta da miyagun halaye, don babban dalilin da ya sa aka ƙirƙire shi shi ne taimaka wa mugaye wajen gudanar da ayyukansu na ɓarnace-ɓarnace, ta'addanci da sauran miyagun ayyuka a duniyar fasaha.

Wannan aikin wani hatsabibin madatsi ne wanda har yanzu duniya ba ta gane ko wane ne ba.

AI ya fara shiga hannun mugaye, lamarin akwai matsala.

—Muhammad Auwal Ahmad ( )

GOOGLE YA FUSATA, YANA ƘOƘARIN TAƁO TSÙLIYAR DODOGoogle yana ɗaya daga cikin tech giants da s**a fara leveraging fasahar...
15/07/2023

GOOGLE YA FUSATA, YANA ƘOƘARIN TAƁO TSÙLIYAR DODO

Google yana ɗaya daga cikin tech giants da s**a fara leveraging fasahar AI a tech industry. Sun jima suna fama. Ba AI kaɗai wanda ya kasance 5th generation of computer ba, Google da IBM har sun kutsa cikin 6th generation wato quantum computers.

Amma cikin ƴan shekarun nan sai aka samu wasu kamfanoni masu tasowa suna ƙoƙarin yi musu fintinkau a duniyar fasahar AI, misali irin su OpenAI. Duk da cewa a zahiri ba haka ba ne, amma duniya tana ɗauka kusan haka ne.

Tun da jimawa Google yana da AI chatbot ɗinsa mai suna Google Assistant k**ar dai yadda Apple yake da Siri, to amma bayyanar ChatGPT ya ƙara nuna cewa har yanzu chatbots suna da kasuwa sosai, musamman yadda aka yi revolutionizing industry ɗin da fasahar AI.

Bayan ganin nasarar ChatGPT, sai nan take Google ya rikice, ya fara neman yadda zai yi ya ture ChatGPT cikin gaggawa. A garin yin gaggawa kuma a fusace sai Google yake ƙoƙarin tsokano inda masana suke hani a kai, inda suke gargaɗi cewa kar a taɓa.

Masana suna gargaɗi cewa idan aka matsa da improving ɗin fasahar AI to haƙiƙa za ta haifar da matsala ga wannan duniyar. Suna ganin cewa maƙeta za su iya amfani da wannan fasahar su sanya mata mugun hali yadda za ta cutar da al'umma.

Duk da cewa ilimin psychology ya nuna cewa ana haifar kowanne mutum da zunzurutun mugunta, to amma shi kuma wannan AI ɗin za a iya sanya masa a kundin jawabansa, yadda zai kasance mugu da amfani da duk wani nau'i na mugunta.

Ɗan dakata, ba cewa na yi Google yana ƙoƙarin ƙirƙirar mugun AI ba, amma sun kusa taɓo wajen. Suna amfani da tsarin Napoleon Bonaparte cewa idan ka sa maƙiyi a gaba kar ka juya baya, amma shi kuma a haka aka kashe ki a yaƙin The Battle of Waterloo bayan ya yi watsi da shawarar manyan dakarunsa.

A nan, Google ya sa kai straight a kan cimma ƙudirin ƙirƙirar AI ba tare da la'akari da kuskuren da hakan zai haifar ba. Suna ƙirƙirar wani mahaukacin AI wanda yake iya yin fushi irin na Ɗan Adam da sauran wasu ɗabi'u na mutane waɗanda s**an wuce misali.

Saboda tsabar yadda ɗaya daga cikin engineers ɗin Google ya tsorata da wannan aikin, sai ya fito fili ya ce ga abun da suke shirin fito da shi, amma nan take Google s**a kore shi saboda ya tona musu asiri.

A yanzu haka, Google sun fitar da sanarwa cewa suna kan ƙirƙirar wani mataki a fasahar AI wanda duniya ba ta taɓa ganin irinta ba. Bayan wannan, a yanzu haka sun cimma wani babban mataki a duniyar quantum computing wanda masana s**a ce tabbas shi ne 6th generation of computer.

Quantum computers suna da matuƙar sauri waɗanda s**a ninka waɗannan computers ɗin namu (classical computers) sau dubunnai a sauri da komai da komai. Aikin da za a shafe a tsawon shekaru 47, quantum computer na kamfanin Google ta yi su cikin ƴan daƙiƙu.

Da zaran Google sun ɗaura AI ɗinsu a kan quantum computers ɗinsu tare da 5G technology, duniya za ta koma sabuwa. Daga nan Google zai zama abun tsoro k**ar yadda Elon ya ce yana tsoronsu.

Abun da Google suke shi ne, ba sa ruɗu, they tend to go slowly. Amma wannan AI competition ɗin da aka fara daga 2022 zuwa yau ya fusata su. Don haka s**a duƙufa wajen samar da manyan fasahohin da za su ba wa duniya mamaki cikin ƙanƙanin lokaci.

—Muhammad Auwal Ahmad ( )

15th July 2023

KA SO ABUN DA KAKE YIAkwai wani guy da ake ƙira Ola of Lagos a social media, ya yi ƙaurin suna wajen ɗaura bidiyon motoc...
11/07/2023

KA SO ABUN DA KAKE YI

Akwai wani guy da ake ƙira Ola of Lagos a social media, ya yi ƙaurin suna wajen ɗaura bidiyon motoci da gidaje yana tallata su ko yana nuna yadda s**a kasance na alfarma.

Asalinsa aikin goge-goge da share-share yake yi a wani kamfani inda ake biyansa N17k duk wata. Bayan ya fara wannan aikin sai ya yi tunanin cewa shi fa neman kuɗi ya fito, don haka bari ya nemi wani aikin ya haɗa biyu yadda zai samu kuɗi da yawa, don haka sai ya ƙara neman wani cleaning job ɗin kuma ya samu, amma irin wannan na tashi-biya ne.

Kasancewarsa mai son motoci da gidaje na alfarma, sai yake ɗaukar bidiyonsu a waya yana ɗaurawa a shafukansa na sada zumunta duk da ba shi da mabiya.

Akwai wani blogger da ake ƙira Tunde Ednut shi ya fara sharing videos ɗinsa wanda duniya ta yi noticing ɗinsa, tun ana masa dariya har abun ya fara girma. Da ya ga haka, sai ya ƙara ƙaimi kan abun da yake yi har ya zama content creator.

Wata rana Tunde Ednut ya sa wata gasa ta N2m. Allah Ya taimaki Ola ya ci wannan gasa, kuma aka ba shi N2m k**ar yadda aka yi alƙawari. Ba iya nan ba, Davido da kansa ya ɗauki nauyin Ola zuwa Dubai wajen wani bikin motoci da ake yi mai suna Dubai Car Festival. Daga nan Allah Ya ɗaga darajar Ola rayuwarsa ta canja.

A yau, ana biyan Ola sama da N1m don ya yi bidiyon talla guda ɗaya kacal.

Na san zuwa yanzu kowa zai ɗauki darrusa kala-kala daga labarin Ola, amma ni manyan abubuwan da nake son nuna mana a nan su ne k**ar haka:

1. KA SO ABUN DA KAKE YI, k**ar yadda Jeff Bezos ya ce, "Love what you do", shi ma Jack Ma ya ce, "Follow your passion." Yanzu shi wannan daga son motoci da gidajen alfarma Allah Ya taimake shi ya samu hanya.

2. Davido ya ce, "We rise by lifting others." A nan kam babu buƙatar explanation.

3. Kada ka raina abun da kake yi ko kuma ka karaya saboda mutane suna s**arka ko suna yi maka dariya.

4. Ka kwantar da hankalinka, idan Allah Ya tashi ɗaga darajarka babu wanda ya isa ya dakatar da Shi

Allah Ya albarkaci gwagwarmayarmu, amin

—Muhammad Auwal Ahmad ( )

11th July 2023

11/07/2023

Idan ka biye wa trends zalla ba za ka ƙaru da komai a social media ba sai ɓata data, amma waɗanda s**a gane tuni suna samun ilimi da kuɗi da kuma sada zumunci cikin sauƙi.

Don haka ka yi ƙoƙarin kasancewa cikin masu infinite gain!

Sunansa Jon Oringer, shi ne founder/CEO na Shutterstock, wannan website ɗin da ya ƙunshi miliyoyin hotuna.Kasancewar Ori...
10/07/2023

Sunansa Jon Oringer, shi ne founder/CEO na Shutterstock, wannan website ɗin da ya ƙunshi miliyoyin hotuna.

Kasancewar Oringer photographer kuma programmer, sai ya yi tunanin cewa bari ya samar da wani website wanda zai rinƙa ɗaura hotunan da yake ɗauka.

Ya yi creating wannan website wanda ya zama Shutterstock, sannan ya ɗaura hotunan da ya ɗauka sama da 30,000, daga nan ya ba wa sauran mutane dama su ma su ɗaura nasu.

Daga nan aka yi implementing subscription-based model, wato duk wanda yake son hotuna zai biya $49. A yau akwai hotuna sama da 444 million a Shutterstock.

Photographer ya yi amfani da damarsa, kai fa?

Akwai wasu muhimman darussan rayuwa da dole sai mutum ya koya, walau ta hanya mai sauƙi ko akasin haka. Shi ne abun da M...
07/07/2023

Akwai wasu muhimman darussan rayuwa da dole sai mutum ya koya, walau ta hanya mai sauƙi ko akasin haka. Shi ne abun da Malam Bahaushe yake cewa, "Idan mutum bai yi sharar masallaci ba to zai yi ta kasuwa." Haka nan dai shi ne abun da ake ƙira, "Learn it the Hard Way."

Akwai lokutan da ƴan'uwanka za su ba ka shawara a kan wani muhimmin abu saboda wani hatsari da suke hangowa a tattare da shi, amma sai ka ce ba ka so, kai ga abun da kake so nan shi za ka yi. Ba za ka gane abun da suke nuna maka ba sai lokaci ya ƙure ka zo kana nadama.

Dattijai waɗanda s**a shafe sama da shekaru 50 suna rayuwa a wannan duniyar sun koyi darussa kala-kala game da rayuwa, sun yi gwagwarmaya da faɗi-tashi. A duk waɗannan shekarun da s**a shafe darussa suke koya, amma idan s**a so ba wa matasa waɗannan darussa a kyauta a matsayin shawara sai ka ga ana watsi da su.

Babbar matsalar ita ce, idan ba ka ɗauki waɗannan shawarwarin a matsayin darussa ba, sai nan gaba za ka koya da kanka cikin wahala, wato "The Hard Way." Daman dole ne, ko cikin sauƙi ko kuma a wahale. Amma waɗanda s**a yi wa kansu karatun-ta-nutsu tuntuni sun farga sun san me suke yi.

Masana s**a ce waɗanda s**a fi faɗawa irin wannan halin su ne matasa. A wajen karatu, soyayya/aure, gina kai, da sauran al'amuran rayuwa.

Don haka tun yanzu ka horar da kanka yin sharar masallaci kafin ka yi ta kasuwa, domin wallahi ta kasuwar nan ba daɗi gare ta ba, kana yi kana kuka kana nadama.

Allah Ya tsare mu Ya sa mu dace, amin

—Muhammad Auwal Ahmad ( )

Daman na ce yanzu lokacin smart investors ne, don haka NNPC ma ta ce ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba, ta ce za ta zuba hannu...
04/07/2023

Daman na ce yanzu lokacin smart investors ne, don haka NNPC ma ta ce ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba, ta ce za ta zuba hannun jari a electric vehicles saboda faɗaɗa su a wannan yanayin da aka shiga na tsadar fetir.

Matuƙar NNPC za ta yi investing a electric vehicles saboda tsadar fetir, ranka ya daɗe wanne irin massive booming kake ganin za a samu?

A yanzu haka s**a ce suna discussing da Maiduguri-based electric vehicle startup (na Mustapha Gajibo), kuma suna son haɗa hannu don faɗaɗa abun yadda zai shiga wurare da dama cikin sauƙi.

Ɗazu da safe maigidanmu Oga Deen Yashe Dabai ya tura min wannan labarin.

A post ɗina na kwanaki na bayar da shawarwari guda uku waɗanda za ka ɗauki ɗaya daga ciki idan kana son zama smart investor a wannan lokacin don ka yi pondering ɗinsu.

Daga cire tallafin fetir da aka yi, cikin wata guda kacal NNPC ta samu N400b. To a hasashena, tabbas idan NNPC ta yi investing a wannan harkar da gaske nan da shekaru 2 kacal za a samu kaso mai tsoka na electric vehicles a biranen Nigeria.

Daga nan kuma za a fara juya wa fetir baya, sai dai manyan masana'antu ne kawai za su neme shi. Home devices ɗinmu duk za su koma suna amfani da solar, sai me ya rage kuma?

Shawarata ga kowa a nan ita ce: mu tafi da zamani. Idan kana da kuɗi ka yi investing, idan kai matashi ne ka shiga harkar solar ka koye ta sosai, za ka zama "hot cake."

04/07/2023

GA PROGRAMME ƊIN DA NA YI ALƘAWARIN YI

Idan kana da business kuma kana son buɗe mata corporate bank account ka shiga wannan class ɗin, insha Allah zan taimaka maka ka samu cikin sauƙi ba tare da ka kashe ko sisi ba.

Ga requirement ɗin:
1. CAC certificate
2. NEPA/water bill
3. ID card
4. TIN
5. BVN

WhatsApp Class👇

https://chat.whatsapp.com/BdDRcieiJio0EIApAanZFN

: Amma don Allah kada ka shiga idan ka san ba za ka yi ba ko kuma ba za ka ba da attention ba, ko mutane 20 na samu waɗanda za su yi da gaske ya isa. Don haka idan ka san ba ka buƙata ko kuma ba ka cika requirement ba don Allah kar ka shiga 🙏

: Ko sisi ba zan karɓa a wajenka ba, kawai zan nuna maka yadda za ka buɗe ne, kuma free ne buɗewar. Sannan ba ni za ka turawa details dinka ba, a'a kai za ka buɗe da kanka, kawai ina so in nuna mana yadda za mu yi ne.

Gobe da daddare za mu yi idan Allah Ya kai mu 🙏

Ɗaya daga cikin IT guys na Kudu da ke matuƙar burge ni kenan, Hanu Fejiro, shi ne co-founder na Patricia.Ya ce ya yi try...
04/07/2023

Ɗaya daga cikin IT guys na Kudu da ke matuƙar burge ni kenan, Hanu Fejiro, shi ne co-founder na Patricia.

Ya ce ya yi trying aƙalla 27 business duk ya yi failing, amma bai bar su empty ba sai da ya koyi darussa daga cikinsu.

Wani abun koyi daga gare shi shi ne, duk wata idea da ya samu to ba ya barinta haka sai ya rubuta ta a wani littafi da ya sanya wa suna Ideas Book.

Wata rana suna zaune shi da brother ɗinsa a Lagos sai ya yi tunani cewa yadda rayuwa take tsada yanzu, nan da kwanaki kaɗan zai koma broke saboda babu wata sana'a ko aiki da yake yi, kawai savings ɗinsa yake cinyewa.

A take sai ya ɗauko Ideas Book ɗinsa ya fara laluɓo wacce idea zai yi implementing wacce za ta samar masa da N30k kacal a lokacin, sai ya samu idea a duniyar Crypto (ba ciki sosai ba, kawai ɗan transactions ne kaɗan-kaɗan), sai ya gayyato wasu s**a fara aiki a kai.

Cikin ikon Allah s**a samu massive growth a lokacin, sannan s**a ci gaba da gyara MVP ɗinsu da standardizing ɗin startup ɗin har ya zama complete Crypto startup.

A lokacin da na ka kalli interview ɗinsa a Techpoint Africa a shekarae 2021, startup ɗin ya girma har ya kai $50m valuation.

Da wasa, da trying, da faɗuwa, da kuka, da rashin bacci, da jajircewa s**a yi wannan aiki.

Amma abun mamakin shi ne, mu yanzu a nan idan muka zo yin register da wani app/website kawai don ya ƙi yi sai mu yi giving up mu rufe. A haka za mu yi creating startups?

Saurin sarewa da muke yi a abubuwa yana janyo mana matsaloli kala-kala. Don Allah mu daina.

Hanu ya ce a lokacin ba ya zuwa gida, gabaɗaya ya tare a office. Ya sa abokansa s**a yi taking risk na barin ayyukansu (jobs) don su yi building wannan abun. Ya ce shi a lokacin ko wanka ba sosai yake samun damar yi ba. Sleep late, wake up early....

Wannan fa ba Bature ba ne, kar ka ce ai Bature ya fiye naci rabu da shi. Wannan baƙar fata ne ɗan Nigeria, kuma akwai su da dama.

Jama'a mu dage mu daina giving up!

If you want to build yourself, you just sacrifice a lot of things — time, energy, money, and knowledge.

However, Aristotle says, "The root of education is bitter, but the fruit is sweet."

Allah Ya shige mana gaba, amin

—Muhammad Auwal Ahmad ( )

Boom!Kamfanin Meta zai ƙaddamar da sabon app ɗinsa mai suna Threads wanda zai yi goyayya da Twitter ranar 6th July.Sabod...
04/07/2023

Boom!

Kamfanin Meta zai ƙaddamar da sabon app ɗinsa mai suna Threads wanda zai yi goyayya da Twitter ranar 6th July.

Saboda irin yadda Twitter yake shan takura a hannun Elon, shi ya sa Meta s**a ce za su share wa mutane hawaye. Oops!

To yanzu za mu zuba ido mu ga iya ƙarfin da Elon Musk da Mark Zuckerberg suke da shi a tech industry.

Haka nan a ɗaya ɓangaren shi ma Jack Dorsey yana ƙoƙarin sakin nashi app ɗin mai suna Bluesky wanda zai yi goyayya da Twitter

Yanzu za a fara wasan...

In our early 20s, let's value building connections. It's a big asset. Our ancestors used to say, "sabo da maza jari."If ...
04/07/2023

In our early 20s, let's value building connections. It's a big asset. Our ancestors used to say, "sabo da maza jari."

If your business collapses, your connections will help you recover it. If you need any help, the connections you have built will support you. So, the connections you have built with men will help you seize big opportunities.

However, your connections with those girls you call friends (ƙawaye) or girlfriends ('yan matanka) will not benefit you in any way.

It is said, "sabo da maza..." NOT "sabo da mata."

In university, they call you academic donkey.

If you gift them Happy Sallah, they silently call you "gara."

If you give them money, data, or airtime, they say you are just an ATM machine or "wawa."

They benefit from you, and that's why they hold you back. And note that they will surely discard you once they are done with you.

But if you gift men, they won't forget. However, ladies tend to forget.

Don't exhaust yourself trying to show off or impress ladies or your friends.

One of my best teachers, whom I am still proud of, says, "Your life is in your hands, if you like keep it otherwise throw it away."

P.S: Note that this post is not gender-biased! I'm just revealing the hidden bitter truths that our ears don't want to hear, our eyes don't want to see, and our hands don't want to touch.

Thank you!

A yanzu haka $Catly sun sayar da 16.97% na pre-sale ɗinsu, amma target ɗin shi ne sai ya kai 70% za a yi listing ɗinsa a...
03/07/2023

A yanzu haka $Catly sun sayar da 16.97% na pre-sale ɗinsu, amma target ɗin shi ne sai ya kai 70% za a yi listing ɗinsa a exchangers. Sannan yadda suke sayar da shi a yanzu a kan $0.004 kowanne guda ɗaya, idan ya hau exchanger zai koma 0.0066.

Bayan $2 Airdrop da suke bayarwa idan ka yi register, kullum za su ba ka 3% na total abun da ka mallaka har tsawon 15 days. Misali, idan ka sayi na $100 to kullum za ka samu $3, kenan za ka samu $45 a kwana 15, haka nan dai $90 a wata dɗaya.

Za ka iya yin register yanzu ta nan 👇

https://www.catly.io/mobile/ #/pages/cat?rid=880340

Sannan ka shiga sabon group ɗin da na bude don ƙarin bayani da updates👇

https://chat.whatsapp.com/JhpdY7MFEoo7merOrPXe94

Shiga ka dama idan kana da interest

03/07/2023

Insha Allahu a wannan satin zan yi programmes guda biyu: (i) ga waɗanda suke yin online business, (ii) ga waɗanda suke son fara online business da koyon digital skills

Gobe zan fara ɗaya.

Keep in touch!

01/07/2023

Game da post ɗina na Prof. Ndubuisi...

Maganar gaskiya ba zan iya yi maka suggesting inda za ka yi investing ba, saboda ina taka-tsantsan da yadda nake mu'amalantar jama'a da risks ɗin da nake taking.

Dalilina guda ɗaya shi ne, ba na so idan ka samu matsala ka zarge ni. Babu kasuwar da babu riba da faɗuwa, k**ar yadda ake cewa duk hannun da yake ƙirga riba wata rana zai ƙirga faɗuwa.

A karan kaina ba na tsoron kashe abun da na mallaka don taking risks, na san abubuwa biyu za su biyo baya: idan na yi nasara abun da nake so kenan, idan kuma na faɗi to zan koyi darasi.

Amma ni kam ba zan ce maka ga inda za ka sa kuɗinka ba, saboda kar a samu matsala ka ce "ai Mohiddeen ne ya ce in sa kuɗina a nan..."

Amma ni kam ko na faɗi babu wanda yake sani ballantana in zargi wani.

Allah Ya shige mana gaba, amin

Prof. Ndubuisi Ekekwe ya ba da labarin cewa a lokacin da team ɗin Kudabank s**a same shi a Lagos don ya zuba hannun jari...
30/06/2023

Prof. Ndubuisi Ekekwe ya ba da labarin cewa a lokacin da team ɗin Kudabank s**a same shi a Lagos don ya zuba hannun jari a bankinsu bayan ƙaddamar da shi, sai ya nuna rashin interest.

Ya ce a lokacin $100k ya so ba su, wanda tabbas ya fi ƙarfin abun, amma kawai ya share. Su ma s**a k**a gabansu.

Bayan shekaru biyu kacal, darajar kamfanin Kudabank ya kai $500m, kuma da a ce ya yi investing a wancen lokacin zuwa yanzu, da yanzu kuɗinsa ya kai $7.5m, amma rashin rabo ya hana shi taɓuka komai, duk da kasancewarsa ƙwararre a harkar investment da startups, amma ya yi missing wannan big opportunity ɗin.

To yanzu tashi ta wuce, saura ni da kai. Zuwa yanzu opportunities nawa ka yi missing? Sau nawa kana gani ana tallata abubuwa amma ka share? Sau nawa ka yi yunƙurin tallafawa wani kamfani don ku mora tare?

Haƙiƙa rabo ba ya wuce mai shi, amma lallai kada ka bari kana missing duk wata opportunity da ta zo gare ka, tabbas a cikinsu za ka samu wacce za ka dama k**ar yadda ni ma na dama.

Allah Ya ba mu sa'a, amin.

—Muhammad Auwal Ahmad ( )

30/06/2023

DO YOU KNOW WHAT HAPPENS WHEN YOU ARE SERIOUS ABOUT YOUR GOALS?

—Your friends will say you don't usually spend time with them or engage in their activities

—Your spouse or partner (if you have one) will complain that you don't give them time and attention

—Your relatives and close family members may think that you are distancing yourself from them

—Some people may label you as crazy or accuse you of being overly focused on materialistic desires

—Your capacity for critical thinking will evolve and gradually reach a higher level of maturity

—You will find yourself avoiding unnecessary arguments and conflicts

—You will stop spending on luxury items and prioritize investments that align with your objectives

—You will gain a deeper understanding of different perspectives on life

—Your mind will constantly be engaged to solving problems

—Your dedication will slowly inspire others, and you may become a source of motivation to those around you

—You will be facing many challenges from unexpected places

However, if you endure all these and keep focusing on your goal, you will definitely succeed and become an exemplary figure. Your persistence and focus will lead to tangible results and a sense of accomplishment that will fuel your drive.

—Muhammad Auwal Ahmad ( )

CEO, Flowdiary

Kasancewata a duniyar fasaha na fiye da shekaru goma, a kullum ina sha'awar samar da damammaki ga ƴan'uwana matasa musam...
25/06/2023

Kasancewata a duniyar fasaha na fiye da shekaru goma, a kullum ina sha'awar samar da damammaki ga ƴan'uwana matasa musamman da nufin samun abun dogaro-da-kai da gina ƙasarmu.

A matsayina na ma'abocin fasaha, na fara ƙaddamar da ayyukana daga shekarar 2014 har zuwa yau. Na rubuta dubunnan maƙaloli a cikin harsunan Hausa da Turanci, na gudanar da scientific research da dama, sannan da rubuta littattafai aƙalla goma-sha-biyu.

—A shekarar 2016 na samar da kamfanina ma farko mai suna Skyvillo, wanda yake a matsayin dandalin sada zumunta na yanar gizo musamman ga ƴan kasuwa

—A watan October na shekarar 2019 na saki littafina na farko a kan kasuwanci mai suna eBillions Mastery, wanda ya fito da wasu halastattun hanyoyi goma-sha-biyu da ake samun kuɗi a yanar gizo

—A shekarar 2019 na kafa wata gidauniya mai suna Yobe Youths Empowerment Programme da nufin koya wa ƴan'uwana matasan Yobe wasu muhimman skills don dogaro-da-kai

—A watan August na shekarar 2020 na ƙaddamar da wani motivational movement a dandalin sada zumunta mai suna " " don ƙarfafa gwiwar matasa don gina internet businesses don samun abun dogaro-da-kai

—A 2021 muka canja Zo Mu Gina Kamfani zuwa wani initiative da aka sadaukar don taimakawa matasa su samar da profitable biz ideas, da samun training, da mentorship da kuma investment

—A watan August na shekarar na fitar da littafina na biyu a kan kasuwanci mai suna Zo Mu Gina Kamfani, wanda ya jaddada muhimmancin gina kamfani da hanyoyin da ake bi wajen yi

—A farkon shekarar 2021 na samar da kamfanin Stackplaza, wata kasuwar yanar gizo da ke ba wa ƴan kasuwa damar tallata hajojinsu cikin sauƙi

—A watan April na shekarar 2022 muka samar da makarantar yanar gizo wacce muka yi wa laƙabi da Flowdiary, wacce ke koyar da digital skills da harshen Hausa don amfani da su wajen dogaro-da-kai

—A kusa da ƙarshen shekarar 2022 na saki littafina na huɗu a kan kasuwanci mai suna Sirrukan Sana'o'i 99, wanda ya zayyano wasu sana'o'i har guda 99 da dabarunsu

Kawai ina da ƙudirin bayar da gudummawata ko kaɗan ce don gina ƙasarmu, wanda nake amfani da damar hakan don sake ƙarfafa wa wasu ƙwarin gwiwwar yin abun da ya dace.

Ƴan'uwana matasa a kodayaushe su ne kan gaba a tunanina, kuma da Yardar Allah za mu ci gaba da fafutukar ganin an samu kyakkyawar makoma da ɗan abun da za mu iya yi, don an ce ɗan guntun gatarinka ya fi sari-ka-ba-ni.

Matuƙar za mu haɗa kai mu haɗa hannu haƙiƙa za mu samu nasarar gina gobenmu wacce muke fatan ta kasance a kan kyakkyawan tsari, in Allah Ya yarda.

—Muhammad Auwal Ahmad ( )

24th June 2023

Address

Baiomari, Baiomari

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mohiddeen Online posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Mohiddeen Online:

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share