12/12/2025
Attajirin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, Aliko Dangote ya bai wa gidauniyar Aliko Dangote kwata na dukiyarsa.
Dangote ya bayyana hakan ne a Legas ranar Alhamis a wajen kaddamar da shirin ilimi na Aliko Dangote Foundation.
Ya ce tuni ya bai wa mahaifiyarsa da ‘ya’yansa uku wasiyar hakan saboda halin mutuwa.
Ya sanar da kaddamar da zuba jarin N100bn a shekarar 2026 don tallafawa almajirai 155,009
Zai ba wa makarantar marayun yan mata N590m kowace shekara a Maiduguri muddin makarantar ta ci gaba da wanzuwa.
Majiya Daga : Business Day