Madubi TV

Madubi TV MADUBI TV zamuci gaba da kawo maku kaya tattun shirye shirye a harshen Hausa.

MUHIMMIYAR SANARWAR GARGAƊI ZUWA GA MASU ANFANI DA SUNAN KATSINA POST A DANDALIN FACEBOOKMuna yi ma ɗaukacin al'umma mus...
03/07/2023

MUHIMMIYAR SANARWAR GARGAƊI ZUWA GA MASU ANFANI DA SUNAN KATSINA POST A DANDALIN FACEBOOK

Muna yi ma ɗaukacin al'umma musamman masu bibiyar KATSINA POST gaisuwa irin ta addinin Musulunci.

Bayan haka, mu a KATSINA POST, muna matuƙar nuna rashin jin daɗin mu kan yadda ake cigaba da samun wasu marassa ƙima da mutunci da ke cigaba da anfani da suna da alamar kamfanin mu suna gudanar da ayyukan su na rashin kyautawa a wannan kafar ta FACEBOOK.

Misali, akwai wani mai suna Anas Suleiman (https://www.facebook.com/anas.sulaiman.9615566) da ya buɗe wani dandali (Group) mai suna Katsina Post Group 2 (https://www.facebook.com/groups/1064637617835697/?ref=share&mibextid=NSMWBT) kuma suke anfani da sunan mu da alamar kamfanin mu (logo) suna gudanar da shi ta hanyar da ba ta dace ba wadda ba mu da alaka ta kusa ko ta nesa da shi.

Haka zalika akwai wani mutum da muke kyautata zaton ɗan ƙaramar hukumar Kankia ne ta jihar Katsina da ya buɗe turaka (account) da sunan Katsina Post (https://www.facebook.com/profile.php?id=100086452748284&mibextid=ZbWKwL) yana yin rubuce rubucen da ba su dace da aikin jarida ba.

A dukkan wannan, ayyukan mutanen da muka lissafa a sama su na sa kamfanin mu a cikin tsaka-mai-wuya ta yadda wasu ke tunanin mu ne ke yin su.

Da wannan ne muke kira gare su da su gaggauta rufe dandalin da kuma shafin na su domin kaucewa jefa kan su cikin matsala da kuma fushin hukuma.

Domin kaucewa duk wani shakku, shafin KATSINA POST na Facebook guda ɗaya (1) ne (https://www.facebook.com/katsinapost?mibextid=ZbWKwL) kuma muna da dandali mai suna Katsina Post Group (https://m.facebook.com/groups/1972924576330045/?ref=share&mibextid=NSMWBT).

Baya ga waɗannan, duk wani shafi ko dandalin da kuka gani, to ba namu bane kuma ba mu da alaƙa ta kusa ko ta nesa da su.

Mun gode kwarai da gaske.

Mustapha Saddiq,
Shugaban kamfanin jaridar KATSINA POST.
08067205524.

HAJJ 2023: GOVERNOR RADDA GIFTS 4,634 KATSINA PILGRIMS N278M
02/07/2023

HAJJ 2023: GOVERNOR RADDA GIFTS 4,634 KATSINA PILGRIMS N278M

Katsina State Governor, Malam Dikko Umaru Radda, has donated N278 million to the State Pilgrims in Saudi Arabia.

Why we increased PoS fees - Mobile money agents
30/06/2023

Why we increased PoS fees - Mobile money agents

Point of Sale (PoS) operators have explained why their transaction fees have been raised. Stephen Adeoye, Public Relations Officer of the Lagos Chapter of the Association of Mobile Money and Banks …

Rikicin Yan TikTok – Suddenly Da Aisha Zakee.https://awa24.com.ng/2021/12/30/1262/
30/12/2021

Rikicin Yan TikTok – Suddenly Da Aisha Zakee.

https://awa24.com.ng/2021/12/30/1262/

Lamarin tiktok nada matukar ban mamaki duba da yadda mafi akasarin masu amfani da shi ke zama tamkar

Martani Episode 7 Hausa Novel 2022https://youtu.be/iO1C8rlF5kI
07/12/2021

Martani Episode 7 Hausa Novel 2022

https://youtu.be/iO1C8rlF5kI

Barka da zuwa Tashar MADUBI TV muna godiya da ziyartar Wannan Channel namu Mai Albarka, dafatan kun amfanu da abinda kuka kalla... Mungode! Mungode!! Mungode...

Martani Episode 2 || Hausa Novel 2021https://youtu.be/IM5jELPOgVE
01/12/2021

Martani Episode 2 || Hausa Novel 2021

https://youtu.be/IM5jELPOgVE

Barka da zuwa Tashar MADUBI TV muna godiya da ziyartar Wannan Channel namu Mai Albarka, dafatan kun amfanu da abinda kuka kalla... Mungode! Mungode!! Mungode...

BREAKING NEWSRundunar Hisba ta jahar katsina ta Samu nasarar K**a wasu matasa da mota bankare da giya, ta maka su kotu, ...
01/12/2021

BREAKING NEWS

Rundunar Hisba ta jahar katsina ta Samu nasarar K**a wasu matasa da mota bankare da giya, ta maka su kotu, inda kotu ta tura su gidan yari har na tsawon wata shida.

Wannan ba karamar nasara bace hukumar ta samu, Kwanakin baya majalisar zartarwar Jahar katsina ta aminche da kaddamar da ayyukan hukumar.

Follow us 👉 Madubi TV

Yadda aka ritsa ’yan bindigar da s**a kai hari a cikin gidan kurkukun birnin Jos na Jihar Filato ranar Lahadi.
29/11/2021

Yadda aka ritsa ’yan bindigar da s**a kai hari a cikin gidan kurkukun birnin Jos na Jihar Filato ranar Lahadi.

Alhaji Aliko DangoteFollow us 👉 Madubi TV
29/11/2021

Alhaji Aliko Dangote

Follow us 👉 Madubi TV

DA ƊUMI ƊUMINSA | Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Bude Hanyoyin Sadarwa A Fadin Jihar.Daga Comr Nura Siniya.Gwamnatin jihar Ka...
26/11/2021

DA ƊUMI ƊUMINSA | Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Bude Hanyoyin Sadarwa A Fadin Jihar.

Daga Comr Nura Siniya.

Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Nasiru El-rufa'i, ta janye matakin da ta dauka akan dokar rufe hanyoyin sadarwa a wasu yankunan jihar, Daga yau Juma'a 26- ga watan Nuwanba 2021.

Majiyar Katsina Online ta samu rahoton cewa Gwamnatin tace sauran matakan da ta dauka suna nan, kamar yadda aka sani wanda ya kunshi, hana zirga-zirgan babura da sayar da mai a jarka a wasu kananan hukumomi dake jihar da cin kasuwannin mako mako da kuma sayar da dabbobi.

Dukkan wadannan sauran dokokin zasu cigaba da aiki, kamar yadda Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shi.

Haka zalika Gwamnan jihar Nasiru El-Rufai, ya baiwa jama’a hakuri bisa wannan mataki wanda yace daukarsa ya zama wajibi saboda tsaron dukiya da rayukan jama’a.

Gwamnatin jihar tace daga lokacin da aka kafa dokokin zuwa yanzu an samu gagarumar nasara a lokacin bayan toshe hanyoyin sadarwar.

Earn up to N3000 for inviting your friends to PalmPay!Simply go to the Refer & Earn section on the app to get started.ht...
26/11/2021

Earn up to N3000 for inviting your friends to PalmPay!

Simply go to the Refer & Earn section on the app to get started.

https://palmpay8.page.link/dRDRU

Share your special invitation link with your friends to invite them to the app. Your friends should fill in their phone number and then download the app, register and start transacting. You’ll be getting rewarded for each new referral as they complete their onboarding journey.

How to use it;
- Open your PalmPay app
- Click on the Refer and Earn Feature
- Click on “Invite new users to get cash”
- Click on a contact and send your link

N/B: Each earning task is valid for 7 Days.

I use the PalmPay app for free bank transfers and to get discounts on airtime and more. Use my link to join and get N100 airtime for Free. https://palmpay8.page.link/dRDRU

Help me claim my PalmPay cash reward and you can get yours too. Follow my link to Sign Up and help out.

Jarumar Kannywood Halima Yusuf Atete. An haifi  a ranar 26 ga watan Nuwambar 1988, a garin Maiduguri, jihar Borno. A she...
26/11/2021

Jarumar Kannywood Halima Yusuf Atete.

An haifi a ranar 26 ga watan Nuwambar 1988, a garin Maiduguri, jihar Borno.

A shekarar 2012 ta fara fitowa a cikin fina finan Hausa, kuma tayi fina-finai da yawa, amma fim ɗin Ƙona Gari, Asalina da Dakin Amarya su ne s**a sa Atete ta shahara.

Ta fi fitowa a matsayin mace mai zafin kishi, marar mutunci ko yar bariki (a cikin fina finai.)

Ta fito a fina finai sama da 160, amma ga wasu kaɗan daga cikin fina finan da Atete ta fito a cikin su:

- Wata Hudu, Yaudarar Zuciya
- Asalina, Kona Gari , Ba'asi
- Dakin Amarya, Matar Jami’a
- Wata Rayuwa, Ashabul Kahfi
- Maidalilin Aure , Mu’amalat
- Soyayya Da Shakuwa , Igiyar Zato
- Alkalin Kauye, Bani Bake
- Kurman Kallo, Uwar Gulma
- Bikin ƴar gata, Alƙalin ƙauye

Tattara bayanai:

Wane fata zaku yi mata?

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari Tare Da Kwamishinan Kananan Hukumomin Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule G...
26/11/2021

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari Tare Da Kwamishinan Kananan Hukumomin Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo

INNALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJI'UNBabban Mai Hidimtawa Kuma Ladanin Masallacin Kandahar Dake Katsina Ya RasuAllah Ya Yi W...
26/11/2021

INNALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJI'UN

Babban Mai Hidimtawa Kuma Ladanin Masallacin Kandahar Dake Katsina Ya Rasu

Allah Ya Yi Wa Malam Abdullahi Ladan Na Masallacin Kandahar Dake Cikin Garin Rasuwa A Daren Laraba

Allah Ya Jikansa Da Rahama!

Matar Sufeto Janar Din Ƴan Sandan Najeriya Ta Kawo Wa Masari ZiyaraUwargidan Shugaban Ƴan Sandan Najeriya, Hajia Hajara ...
25/11/2021

Matar Sufeto Janar Din Ƴan Sandan Najeriya Ta Kawo Wa Masari Ziyara

Uwargidan Shugaban Ƴan Sandan Najeriya, Hajia Hajara Usman Alkali A Lokacin Da Ta Kaiwa Gwamna Alhaji Aminu Bello Masari Ziyarar Ban Girma A Gidan Gwamnatin Jihar Katsina Yau Alhamis

Wata Babbar Kotu A Jihar Lagos Ta Yankewa Gawurtaccen Mai Garkuwa Da Mutane "Evans Hukuncin Kisa.Daga Comr Nura Siniya. ...
25/11/2021

Wata Babbar Kotu A Jihar Lagos Ta Yankewa Gawurtaccen Mai Garkuwa Da Mutane "Evans Hukuncin Kisa.

Daga Comr Nura Siniya.

Wata babbar kotun Legard a jihar Lagos ta yankewa Mista Chukudimeme Onwuamaduke wanda akafi sani da Evans hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun shi da laifukan satar mutane da fashi da makami da sauran miyagun laifuka da ya aikata ga al'ummar Najeriya.

A farkon Shekarar 2017 ne jami'in dan sanda DCP Abba kyari ya samu nasarar kamo kasurgumin mai garkuwa da mutanen Mr Evans wanda ya gawurta wajen aikata Kidnapping da ayyukan fashi da makami da satar dukiyar jama'a a yanar gizo.

Yanzu dai kotu ta yakewa Evans hukuncin kisa ta hanyar rataya.

True Love:💖 The 14th Emir of Kano Khalifa Muhammad Sanusi II and his lovely wife.💚💎💙
25/11/2021

True Love:💖 The 14th Emir of Kano Khalifa Muhammad Sanusi II and his lovely wife.
💚💎💙

Da Ɗumi-Ɗumi!Gwamna Masari ya ƙaddamar da aikin gadojin ƙasa 2 wanda za a yi a ƙofar Ƙaura da Ƙofar Ƙwaya a kan kuɗi nai...
25/11/2021

Da Ɗumi-Ɗumi!

Gwamna Masari ya ƙaddamar da aikin gadojin ƙasa 2 wanda za a yi a ƙofar Ƙaura da Ƙofar Ƙwaya a kan kuɗi naira bilyan 5 da milyan ɗari 8 kamar yadda Kwamishinan ma'aikatar ayyuka, gidaje da sufuri, Tasi'u Ɗanɗagoro ya bayyana.

Za a Ƙaddamar Da Wutar Lantarki Ta Lambar Rimi A Cikin Wata Mai K**awa, Watan Disemba.Ministan wutar lantarki ya bayyana...
25/11/2021

Za a Ƙaddamar Da Wutar Lantarki Ta Lambar Rimi A Cikin Wata Mai K**awa, Watan Disemba.

Ministan wutar lantarki ya bayyana cewa za'a ƙaddamar da wutar lantarki ta lambar Rimi a watan December Goma Sha Takwas ga wata, hakan dai ya biyo bayan ziyarar da Dattijan Jihar Katsina s**a kai a Offishin Ministan.

Ministan yace Matsalar rashin tsaro ne yasanya aka samu tsaiko wajen ƙaddamar da wutar ta Lambar Rimi da kuma wasu kayan Wutar da aka sace.

Tsohuwar Jarumar fina-finan Hausa Fati Muhammad.Ko ba mutuwa akwai tsufa.
25/11/2021

Tsohuwar Jarumar fina-finan Hausa Fati Muhammad.

Ko ba mutuwa akwai tsufa.

Aikin gini a shatale-talen sabuwar tasha Katsina ya fara nisa.Shin minene fatanku a wannan aikin?
25/11/2021

Aikin gini a shatale-talen sabuwar tasha Katsina ya fara nisa.

Shin minene fatanku a wannan aikin?

WANI BAYANI NA CIRE TALLAFIN MAI CIKIN HARSHEN TURANCI ZAMU MAYAR DA SHI DA HAUSADaga Sani BelloBatureGwanatin tarayyar ...
25/11/2021

WANI BAYANI NA CIRE TALLAFIN MAI CIKIN HARSHEN TURANCI ZAMU MAYAR DA SHI DA HAUSA

Daga Sani BelloBature

Gwanatin tarayyar Najeriya ta ce, ta na so ta bada tallafin kudi dubu biyar-biyar 5,000 domin rage kudin sufuri ga talaka a matsayin cire tallafin mai gabaki daya da zasu yi.

Yanzu bari mu lissafa:

Idan za a baiwa yan Najeriya mutum miliyan arba'in 40m naira dubu biyar-biyar a Najeriya a wata guda za a kashe naira biliyan dari biyu 200b

Idan ka lissafa naira biliyan dari biyu sau sha biyu zai baka a shekara za a kashe naira tiriliyan biyu da digo hudu = N2.4Tr

A shekarar 2021 gwamnatin tarayya ta kashe naira tiriliyan daya da digo takwas akan tallafin man fetur= N1.8Tr

Shin ya lamarin nan yake?

Inama dai Ace Kyan Hali Mu Ke Duba Ba Kyan Fuska Ba.Sunanta Mary Ann Bevan wacce aka fi sani da "macen da ta fi sauran m...
25/11/2021

Inama dai Ace Kyan Hali Mu Ke Duba Ba Kyan Fuska Ba.

Sunanta Mary Ann Bevan wacce aka fi sani da "macen da ta fi sauran mata muni a Duniya," amma wadanda s**a zauna da ita sun mata shaida da cewa basu taba ganin mace mai kyan hali irinta ba.

Wannan mata ta samu matsala a yanayin girmanta, da kuma yanda fuskarta take cikin wani irin yanayi kamar yanda kuke gani a hotunanta.

Bayan rasuwar mijinta, ta Shiga matsanancin hali, ga matsalar bashi, ga yara 4 da s**a haifa ba mai taimakonta a kansu, sai ta yanke shawarar shiga gasa mafi kaskanci kuma ta samu nasarar cin wannan kambu mafi kasknci na " macen da ta fi muni a Duniya". Daga nan sai wata kungiya ta dauki hayarta, tana zagayawa da ita garuruwa, mutane suna zuwa suna kallonta suna dariya suna wulakantata suna bada kudi, in sun gama sai a bata lada.

Ta jure wulakanci da cin mutunci duk saboda ta kula da yaranta, ta basu rayuwa mai inganci har zuwa randa ta mutu a shekarar 1933.

Irin Rayuwar da muke ciki kenan yanzu, mutane suna maka hukunci ne da suffarka ta zahiri ( kyaun jiki da kyaun sutura).

Da ace mutane suna duba kyaun zuciya ba kyaun fuska ba, da Mary Ann Bevan da ire-irenta sun rayu a matsayin mata mafi kyau a Duniya.

Fassarar Imam Auwal Warure

Masari Zai Kaddamar Da Fara Aikin Gadar Kasa Gobe AlhamisIdan Allah Ya Kaimu Gobe Alhamis, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji...
24/11/2021

Masari Zai Kaddamar Da Fara Aikin Gadar Kasa Gobe Alhamis

Idan Allah Ya Kaimu Gobe Alhamis, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari Zai Kaddamar Da Aikin Gadoji Kasa Guda Biyu A Kofar Kaura Da Kuma Kofar Kwaya A Cikin Garin Katsina.

Za'a Kaddamar Da Aikin Da Misalin Karfe 2:00 Na Rana A Shatale-talen Kofar Kaura.

Ƴan-sanda sun cafke saurayin da ya ke yaudarar ƴan-mata ya gudu da wayar su ta salulaRundunar Ƴan sanda ta Jihar Kano ta...
18/11/2021

Ƴan-sanda sun cafke saurayin da ya ke yaudarar ƴan-mata ya gudu da wayar su ta salula

Rundunar Ƴan sanda ta Jihar Kano ta cafke wani saurayi mai suna Muhammad, wanda ya ƙware wajen yaudarar ƴan mata ya ce ya na son su, inda daga budurwa ta saba da shi, sai ya yaudare ta ya gudar mata da wayarta ta salula.

A wata sanarwa da Kakakin Rundunar Ƴan sandan, Abdullahi Kiyawa ya fitar a yau Laraba, dubun matashin ta cika ne bayan da wata budurwa da ke zaune a Sharaɗa ta kai ƙarar Muhammad Saifullahi ofishin ƴan sanda na yankinsu cewa ya yaudare ta ya gudar mata da wayarta.

Ta ce matashin ya zo gidansu ne ya kuma nuna ya na son ta ita kuma ta amince da shi, amma da ga bisani sai ya karɓe mata waya da ta ƙaninta ya ranta a na kare.

Budurwar ta yiwa ofishin ƙarin bayani da cewa lokacin da ya karɓe musu wayoyin, sai ya wayance cewa ya yar da mukullin babur ɗin sa, inda bayan sun taya shi nema, kuma suna tsaka da neman ne sai ya arce ya kuma kashe wayoyin.

Kiyawa ya ƙara da cewa jin haka, sai Kwamishinan Ƴan sanda, Sama'ila Shu'aibu ya umarci dakarun Kan-ka-ce-kwabo, wato Puff Ada, ƙarƙashin SP Abulrahim Adamu da su shiga farautar matashin.

Kwamishinan ya kuma umarci kakakin rundunar da ya kwarmata neman matashin a gidajen rediyo da talabijin.

Da ga nan ne ƴan sanda su ka shiga farautar sa har sai da su ka cafke shi a titin gidan zoo.

Matashin ya amsa laifin sa, inda kakakin ya ce ana ci gaba da bincike kuma za a gurfanar da shi a gaban ƙuliya.

- Daily Nigerian Hausa

Fitaccen mawaƙi Nura M. Inuwa ya samu ƙaruwar jaririya. Allah ya raya ta bisa tafarkin Manzon Allah (s.a.w.), amin.
08/10/2021

Fitaccen mawaƙi Nura M. Inuwa ya samu ƙaruwar jaririya. Allah ya raya ta bisa tafarkin Manzon Allah (s.a.w.), amin.

Zabiya Magajiya Dambatta ta rasu Mawakiyar Hausa da ta shahara, Magajiya Dambatta, ta rasu.Ta rasu a daren yau Juma’a a ...
08/10/2021

Zabiya Magajiya Dambatta ta rasu

Mawakiyar Hausa da ta shahara, Magajiya Dambatta, ta rasu.

Ta rasu a daren yau Juma’a a garin Dambatta bayan gajeruwar jinya.

Wasu Sabbin Hotunan Maryam Yahaya Da S**a Bayyana A Kafafen Sadarwa.
08/10/2021

Wasu Sabbin Hotunan Maryam Yahaya Da S**a Bayyana A Kafafen Sadarwa.

Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir ya rasuAn bayar da sanarwar rasuwar Sarkin Gaya Ibrahim Abdulkadir. Gaya daya ce ...
22/09/2021

Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir ya rasu

An bayar da sanarwar rasuwar Sarkin Gaya Ibrahim Abdulkadir. Gaya daya ce daga cikin sabbin masarautun da Gwamnatin jihar Kano ta kirkiro.

©Daily Nigerian Hausa

Address


Telephone

+2347061658047

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Madubi TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share