30/09/2023
Computer Skills guda 5 da yanzu duniya take yayi, waɗanda karka bari ace bakada guda ɗaya a ciki..
Duk da kasancewar akwai Computer skills kala-kala a duniya amma akwai waɗanda s**afi samun kasuwa a duniyar Technology, wato waɗanda ake yayi kuma ake nema a duniya. Ga guda 5 da nasani waɗanda ya kamata ko basics na guda ɗaya a ciki ka koya saboda rayuwa.
1. Coding and Programming: Yadda technology yake bunƙasa yanzu a duniya yanada ƙyau ace kanada Skills na Programming, koyon programming Languages irinsu: Python, Java, JavaScript, da C++ zai taimaka maka wurin ƙirƙirar softwares, websites, automate tasks, da ƙirƙirar duk wani innovative solutions. Wanda zaka iya dogaro da kanka, ka gina kanka.
2. Data Analysis: Yana da ƙyau ka koyi wannan skills ɗin musamman ma'aikatan dake aiki a ma'aikatu, hukumomi da bankuna, ƙwarewa a wannan ɓangaren yana kawo Promotion a wurin aiki cikin sauri, anaso kasamu ƙwarewa sosai da wasu tools ko softwares da ake aiki dasu wurin Data Analysis, kamar irinsu Excel, SQL (Structured Query Language), da kuma Data Visualization platforms irinsu Tableau ko Power BI. Ƙwarewa a waɗannan abubuwan zasu taimaka maka wurin ƙwarewa a aikinka, sannan zaka iya sa'ar samun Promotion a wurin aiki idan aka fahimci ƙwarewarka.
3. Cybersecurity: Kamar yadda aikata laifuka da kuma samun yawan Vulnerabilities a kafofin sadarwa da manhajoji da sauran fasahohi yaketa ya yawaita a kullun a Internet da kuma cikin duniyar fasaha, hakan ya zama dole ayi amfani da ilimin Cybersecurity domin samar da tsaro a waɗannan sabbin fasahohin da ake samarwa, dan haka sanin cybersecurity fundamentals yanada matiƙar muhimmanci da kuma sanin ɓangarorin da s**a shafi network security, secure coding practices, vulnerability assessment da incident response. Sanin waɗannan ɓangarorin a Cybersecurity zai taimaka maka kasan yadda zaka iya kare muhimman bayanai da ba'a buƙatar su fita wato sensitive informations, duk wani kamfani ko wata fasaha ta duniya tana buƙatar Cybersecurity.
4. Cloud Computing: Duk wani babban business da kasani akan Internet sai an haɗashi da wannan Skills ɗin yake samun kafuwa mai ƙarfi har ya zama ana Competition dashi a duniyar kamfanonin sadarwa a internet.
Kamar yadda kaga irinsu: Amazon Web Services (AWS), Microsoft Azure, da Google Cloud Platform (GCP), abun ya zama ruwan dare wannan Skills ɗin yana canza tsarin businesses sosai. Dan haka yakeda ƙyau ka koyi wasu ɓangarori na wannan skills ɗin kamar irinsu: Virtualization, Scalability, da Cloud Deployment Models karantar waɗannan ɓangarorin zaisa ka fahimci Cloud Technologies sosai.
5. Digital Literacy: Yanzu duniya ta koma Digital, kamfani zai iya ɗaukarka aiki batareda sai kaje an baka Office kullun da safe ka tashi ka shirya kaje ba, kana gidanku kanayi ma kamfani aiki, kamfaninka yana Lagos kana Katsina zaka iya aiki dasu batareda kaje Lagos ba, wannan shine ake kira da Remote Work And Digital Communication, dan haka ya zama wajibi ka ƙware a ɓangaren sanin Digital Skills sosai domin sanin yadda zaka dinga amfani da Digital Technologies, yanada ƙyau ka mayar da hankali ɓangaren koyon: Microsoft Office Suite, Google Workspace (formerly G Suite), project management software, da online collaboration platforms irinsu Slack ko Trello.
Allah Yataimaka..🙏
Salisu Abdurrazak Saheel