The Independent Hausa Times

  • Home
  • The Independent Hausa Times

The Independent Hausa Times The Independent Hausa Times is a Publication that answers the facts where ever they lead.

Rahotanni sun bayyana cewa cigaba da karyewar  darajar Naira a Najeriya na kara ta’azzara bashin da ake bin kasar, inda ...
06/11/2023

Rahotanni sun bayyana cewa cigaba da karyewar darajar Naira a Najeriya na kara ta’azzara bashin da ake bin kasar, inda rahoton ya bayyna cewa bashin da ake bin kasar ya zarta naira tiriliyan 20 a cikin watanni biyar.

Jaridar Dailytrust ta rawaito cewa sabon tsarin matakan ciyo bashi da gwamnatin tarayya ke shirin aiwatarwa zai kara ta’azzara bashi da sama da naira tiriliyan 89 kafin karshen shekarar da muke ciki.

Kazalika a wani rahoto da ofishin dake kula da bas**a a najeriya ya wallafa a shafinsa na intanet na nuni da cewa bashin da ake bin Najeriya a ciki da wajen kasar tun a watan yunin day a gabata ya zarta naira tiriliyan 87.

01/11/2023
A yayin da wa’adin da aka sanya domin kawo karshen ta’amali da cigaba da wanzuwar kudade na zahiri da s**a hada da Naira...
01/11/2023

A yayin da wa’adin da aka sanya domin kawo karshen ta’amali da cigaba da wanzuwar kudade na zahiri da s**a hada da Naira 200, 500 da 1000, ke kara karatowa, rahottani sunyi nuni da cewa an soma samun karancin kudade na zahiri a Jihohi Borno da Kano.

Idan za’a iya tunawa, Babban Bankin Najeriya CBN ya fidda sanarwa dake cewa biyo bayan umarnin Kotun Koli a watan Marsi na bana, zaa a cigaba da anfani Naira 200, 500 da 1000 har zuwa 31 ga watan Disambar bana.

Matakin Hukuncin Kotun Kolin Najeriyar na zuwane bayan da wasu Yan Najeriy s**a garzaya gabanta domin yanke hukuncin kan halin da al’umar kasar s**a samu kansu biyo bayan matakin Bankin CBN karkashin Mista Godwin Emefeile na yanukurin kawo karshen ta’amali da kudade na zahiri.

A yayin da Kasashen Duniya s**a gudanar da bikin ranar cimaka ta duniya, Najeriya ta bi sahunsu, an jiyo ‘yan Najeriyar ...
17/10/2023

A yayin da Kasashen Duniya s**a gudanar da bikin ranar cimaka ta duniya, Najeriya ta bi sahunsu, an jiyo ‘yan Najeriyar na kokawa kan yadda cimakar ke zama barazana garesu sakamakon tsadarsa.

Majalisar Dinkin Duniya kan gudanar da bikin ranar tunawa da abinci ta duniya a duk ranar 16 ga watan Okotaban kowwace shekara, inda ranar tayi dai-dai da ranar da aka samar da hukumar abinci ta duniya domin dakile kamfar cimakar.

Al’umar Najeriyar sun kuma nuna halin dimuwa kan yuwar mutane dayawa ka iya rasa abinci a kasar muddin ba’a dauki matakin kawar da matsalolin dake yiwa manoma barazana a halin yanzu ba.

Sai dai, a dai-dai lokacin da Alumar kasar ke bikin ne, Hukumar dake kula da harkokin kiddidiga NBS ta wallafa wani rahoto dake nuni da cewa an samu tashin farashin kayyayakin cimaka da kaso sama da 26 a watan Satumban bana, tashin da ba’a samu ba cikin shekaru 18 da s**a gabata.

Karamin Kwamitin  binciken harkokin makamashi da Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinibu ya kafa ya bankado cewa Najeriya na...
12/06/2023

Karamin Kwamitin binciken harkokin makamashi da Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinibu ya kafa ya bankado cewa Najeriya na asarar Dalar Amurka biliyan 46 sakamakon satar Danyen Man Fetur a kasar, inda a hannu guda kasar ke asarar sama da Dalar Amurka biliyan 10 sakamakon tallafin man fetur da gwamnatin tace ba zata cigaba da biya ba.
Kazalika, alkalluman sun yi nuni da cewa Najeriyar na asarar sama da Dalar Amurka biliyan 56 a cewar kwamitin, inda kwamitin ya kuma kara da cewa Najeriyar na asarar sama da Biliyan 70 Dalar Amurka na masu zuba a hannun jari daga kasashen ketare musanman a fanin harkokin man fetur.
Kwamitin ya kara da cewa hakan na faruwa ne duk da gyaran dokar harkokin makamashi da Najeriyar ta yi a shekarar 2011.

31/05/2023

Asusun kula da yara na majalisar dinkin duniya zai kawo wata sabuwar hanyar kawo karshen yaran da basa zuwa makaranta a Najeriya nan da shekarar 2027.
A wani bincike da jaridar punch tayi na cewa ba za a iya tantance adadin yaran da basa zuwa makaranta ba, sai dai a wani rahoto da hukumar raya aladu ta majalisar dinkin duniya ta fitar a shekarar 2022 yayi nuni da cewa yara miliyan 20 ne basa zuwa makaranta a nahiyar Afirka.
Hukumar majalisar dinkin duniyar ta sha alwashin kawo karshen matsalar ta hanyar samar da matakai masu dore wa.

Kotun sasanta ma’aikata a jihar kano ta bayar da umarnin mayar da Muhuyi Magaji Rimingado a matsayin shugaban hukumar ka...
31/05/2023

Kotun sasanta ma’aikata a jihar kano ta bayar da umarnin mayar da Muhuyi Magaji Rimingado a matsayin shugaban hukumar karbar korafe korafe da cin hanci, inda kotun ta ce a aiwatar da umarnin nan take.

Matakin hukincin na zuwa ne karkashin jagorancin mai Sharia Ebeye David, inda y ace an hana muhyi kare kanshi ne a gaban kotu.

Mai Sharia David ya kuma kara da cewa majalisar jihar kano bat a da ikon sauke wani daga mukami ba tare da anji ta bakinsa ba ,inda ya kara da cewa an sauke Muhyi daga mukaminsa ba tare da bin kaida ba.

Jaridar daily trust ta rawaito cewa Gwamnatin Ganduje c eta dakatar Muhyi Magaji daga aiki inda daga bisani ta cire shi daga kan mukaminsa, bayan wani bincike da gwamnatin tace tayi a kansa.

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya cewa ya gaji kwanton kwangilar ayyukan da ba a karasa ba daga tsohon shugaban kasa Mu...
31/05/2023

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya cewa ya gaji kwanton kwangilar ayyukan da ba a karasa ba daga tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari da kudin su ya kai sama da tiriliyan 16.
An gano ayyukan ne ta hanyar manhajar bincike da kididdiga da ake yiwa lakabi da EYEMARK da shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar a karshen shekarar bara.
A can baya dai shugaba Muhammadu Buhari ya koka kan karancin maaikata da ke sanya ido kan harkokin gwamnati la’akari da cewa kwangilar gwamnati na da yawa a fadin gwamnati.

Hukumar Kula da Magunguna da Cimaka ta Najeriya NAFDAC ta yi hani da shigo da taliyar yara mai lakabin Indomie noodles d...
02/05/2023

Hukumar Kula da Magunguna da Cimaka ta Najeriya NAFDAC ta yi hani da shigo da taliyar yara mai lakabin Indomie noodles daga kasashen ketare zuwa Najeriyar.

Jaridar Dailytrust ta rawaito cewa Shugaban Hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye ta tabbatar da matakin a yayin wani taron manema labarai.
Hukumar ta dauki matakin hani ne biyo bayan bincike da Kasar Taiwan da Malasia s**a gudanar kan nau’in taliyar yaran, inda kuma bincikensu ya tabbatar da sinadarin ethylene oxide wanda guda ne cikin abinda ke sa kamuwa da cutar Kansa a cewar Jaridar Dailytrust.

Shugaban Hukumar ta kuma bayyana cewa samun sinadarin Ethylene Oxide ya sanya Shugaban sashin dakunan gwaje-gwajen cimaka na hukumar soma aikin sake duba matakin da aka dauka wajen gano kunshin sinadarin dake sabbaba kamuwa da Kansa.

01/05/2023

Kungiyoyin Ma’aikata a Najeriya suna ci gaba da kokawa kan yadda rayuwar ma’aikata ke kara shiga halin matsi.
Matakin kokawar na zuwa ne dai-dai lokacin da Gwamnati da al’umar Najeriya ke bikin ranar Ma’aikatan.
An ware ranar 1 ga watan Mayun kowwace shekara a matsayin ranar Ma’aikata.
Sai dai, matakin na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta yi karin kaso 40 na albashin ma’aikatan, sun koka kan cewa karin bashi da alfanu.
Kazalika, rahoton Hukumar Kula da Kiddidiga a Najeriya na bayyana cewa an samu karin sama da kaso 22 na hawa-hawan farashin kayayyakin amfanin yau da kullum

Rahottanin dake fitowa daga fadar Shugabncin Najeriya na nuni da cewa Ma’aikatar Kudi, Kasafi da Tsare-tsaren Kasar ta a...
01/05/2023

Rahottanin dake fitowa daga fadar Shugabncin Najeriya na nuni da cewa Ma’aikatar Kudi, Kasafi da Tsare-tsaren Kasar ta ayyana manya ababen raya kasa uku dake fadar shugabancin kasar ciki har da Asibitin Fadar shugabancin kasar a matsayin wani bangare na ci gaba da cefarnar da kadarorin kasar.

Babban Sakataren fadar Shugabn Najeriyar, Tijjani Umar shi ya tabbatar da matakin a birnin tarayya Abuja a yayin wani taron zangon farko na matakin hadin guiwa da gwamnatin tarayya ke yi da kanfanoni masu zaman kansu.

An Sanya Sunan Tsohon Kwamishinan 'Yan sandan Jihar Kano CP Muhammad Wakili Cikin jerin sunayen Yan kwamitin karbar mulk...
07/04/2023

An Sanya Sunan Tsohon Kwamishinan 'Yan sandan Jihar Kano CP Muhammad Wakili Cikin jerin sunayen Yan kwamitin karbar mulkin gwamnan jihar Kano.

CP Muhammad Wakili dai yayi aiki a matsayin kwamishinan Yan sandan Jihar Kano Kuma yayi ritaya a ranar 24 ga watan Mayun 2019.

Mikiya Hausa Times ta Gano cewa Bayan Yin Ritaya da yayi a matsayin kwamishinan Yan sandan jihar Kano ya zama mai baiwa gwamnan jihar Gombe shawara a fannin tsaro.

Yanzu dai yana daga cikin yan kwamitin karbar mulki wanda Abba Kabir Yusuf ya amince da hakan ta cikin wata sanarwa da AB Baffa Bichi ya fitar.

Jam`iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta ce tana jin takaicin rashin nasarar da tayi a jihar Kano a zaben gwamnan da ya ga...
05/04/2023

Jam`iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta ce tana jin takaicin rashin nasarar da tayi a jihar Kano a zaben gwamnan da ya gabata.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, shine ya Bayyana hakan ga manema labarai Yana Mai nuna bakin cikin sun rasa jihar Kano.

Sai Dai shugaban na APC, ya ce sunyi duk abinda ya kamata suyi domin ganin sun samu nasarar lashe zaben, amma wasu ne basu yi abinda ya kamata ba wanda hakan ya jefa 'ya'yan jamiyyar a cikin wani hali.

Sanata Abdullahi Adamu, ya ce Kano tana cikin jihohin da suke bugun kirji cewa ta APC ce domin duk abin da za su yi jihar Kano na kan gaba a lissafinsu a cewar shugaban jam'iyyar ta APC

Ya kuma kara da cewa bayan komai ya lafa za su dauki matakin hukunta wadanda ba suyi wa jamiyyar abinda ya kamata ba domin samun nasara.

Kazalika yace suna da kwarin gwiwar cewa jamiyyarsu ta APC ce za ta lashe zaben jihohin Adamawa da Kebbi da ake jira a kammala.

Gwamnatin tarayya ta amince da kashe Kudi kimanin naira Biliyan 24.2 Domin Sanya na'urorin da al'umma zasu Yi amfani da ...
29/03/2023

Gwamnatin tarayya ta amince da kashe Kudi kimanin naira Biliyan 24.2 Domin Sanya na'urorin da al'umma zasu Yi amfani da yanar Gizo kyauta awasu muhimman wurare 75 afadin kasar Nan

Ministan sadarwa da Bunkasa Tattalin arziki Farfesa Isa Ali pantami shine ya Bayyana hakan yayin zantawar da manema labarai Dake Fadar shugaban kasa.

Yace Majalisar zartarwa ta amince da sakin Kudaden bayan Gabatar da Yadda aikin zai Kasance Ga majalisar zartarwa karkashin jagirancin shugaban kasa muhammadu Buhari

Yace Akwai Filayen sauka da tashi da guda 20 da zasu amfana da shirin amfani da yanar Gizo kyauta

Daga Cikin su akwai Lagos, Ondo. Imo, Anambra, Enugu. Port Harcourt, Akwa Ibom. Abuja Ilorin.

Sauran akwai Kano, Sokoto Kebbi,Yola, Maiduguri ,Gombe.”

Baya ga filayen sauka da tashi akwai wasu makarantun Kasar Nan da zasu amfana suma da Shirin Domin Kara Bunkasa Tattalin arziki na Kasar Nan a cewar pantami.

Gwamnatin tarayya ta amince da kashe Kudi kimanin naira Biliyan 24.2 Domin Sanya na'urorin da al'umma zasu Yi amfani da yanar Gizo kyauta awasu muhimman wurare 75 afadin kasar Nan

Ministan sadarwa da Bunkasa Tattalin arziki Farfesa Isa Ali pantami shine ya Bayyana hakan yayin zantawar da manema labarai Dake Fadar shugaban kasa.

Yace Majalisar zartarwa ta amince da sakin Kudaden bayan Gabatar da Yadda aikin zai Kasance Ga majalisar zartarwa karkashin jagirancin shugaban kasa muhammadu Buhari

Yace Akwai Filayen sauka da tashi da guda 20 da zasu amfana da shirin amfani da yanar Gizo kyauta

Daga Cikin su akwai Lagos, Ondo. Imo, Anambra, Enugu. Port Harcourt, Akwa Ibom. Abuja Ilorin.

Sauran akwai Kano, Sokoto Kebbi. Yola, Maiduguri Gombe.”

Baya ga filayen sauka da tashi akwai wasu makarantu Kasar Nan da zasu amfana suma da Shirin Domin Kara Bunkasa Tattalin arziki na Kasar Nan Acewar pantami

Hukumar Zabe Mai zaman kanta ta kasa INEC ta Bayyana cewa zata Gudanar da zaben cike Gurbi Na Gwamna da Yan majalisar ta...
27/03/2023

Hukumar Zabe Mai zaman kanta ta kasa INEC ta Bayyana cewa zata Gudanar da zaben cike Gurbi Na Gwamna da Yan majalisar tarayya da na jihohi a Ranar Asabar 15 ga Watan April.

Cikin wata Sanarwa da Hukumar ta Fitar tace ta Dauki wannan Mataki ne Biyo bayan Wani taro da Hukumar tayi a Ofishin ta Dake Birnin tarayya Abuja.

Wasu Daga Cikin Zaben Da za a Gudanar sun Hada Dana adamawa tsakanin Gwamnan Jihar Mai ci Ahmad Fintiri na Jam'iyyar PDP da Kuma Sanata Aisha Binani Yar Takarar Gwamnan Jihar karkashin jam'iyyar APC

A Jihar Kano kuwa akwai Na Dan Majalisar tarayya na karamar Hukumar Fagge da Kuma na Kananan Hukumomin Tudun wada da Doguwa wadanda suna daga Cikin wanda za'a Gudanar.
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089533158225

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargadin yiwuwar canjin yanayin zafi a wasu jihohin kasar nan. Mai maga...
26/03/2023

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargadin yiwuwar canjin yanayin zafi a wasu jihohin kasar nan.

Mai magana da yawun hukumar Muntari Ibrahim ne ya bayyana hakan a Abuja,inda ya ce za a samu yanayin zafi sama da digiri 40 a ma’aunin celcius cikin sa’o’i 48 masu zuwa.

Ya kuma fadi jihohin da abin zai iya shafa kamar jihar Kebbi, Sokoto, Zamfara, Taraba, da Adamawa inda yanayin zafi zai iya tashi sama da digiri 40.

Ya kuma kara da cewa yawancin jihohin Arewa da wani yankin jihohin Oyo, Kwara, FCT, Nasarawa da Benue ana sa ran samun yanayin zafi tsakanin ma'aunin Celsius 35 zuwa ma'aunin Celsius 40.

Jihohin Bauchi, Gombe, Borno, da Yola zasu fuskanci barazanar fuskantar matsanancin zafi.

Ya kuma shawarci Mutanen da ke zaune a wadannan yankunan da su yawaita sha ruwa a wannan lokacin.

Ibrahim ya ba da tabbacin cewa hukumar ta NiMet za ta ci gaba sanar da 'yan Najeriya yanayin da kasar ke ciki. (NAN)

Address


Telephone

+2348034734796

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when The Independent Hausa Times posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to The Independent Hausa Times:

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share