20/09/2020
LABARAB MUJALLAR VISION
yau lahadi 20 ga watan satumbar 2020
20/09/2020 EDO/ELECTION
Har yanzu dai ana ci gaba da jiran sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da ya gudana a jiya asabar, wanda jami’ai ke cigaba da kidayar kuri’un da aka kada.
‘Yan takara 14 ne dai s**a fafata a zaben na jiya, sai dai hammaya tsakanin gwamna mai ci Godwin Obaseki na Jam’iyyar PDP da kuma Fasto Ize-Iyamu na APC ce tafi daukar hankali, wadanda sakamakon farko da ya fita ya nuna cewa dukkaninsu sun lashe mazabunsu.
Bayan kada kuri’arsa gwamna Godwin Obaseki, ya bayyana mamaki gami da kaduwa kan bata lokacin da ake yi kafin na’urar tantance mai kuri’a ta Card Reader tayi aikinta duk da ikirarin hukumar zabe na daukar matakan inganta ayyukanta, abinda yace ba shakkah zai takaita adadin mutanen da za su kada kuri’unsu.
Sai dai a nasa bangaren dan takarar APC Ize-Iyamu yace bashi da wani korafi kan yadda zaben ya gudana.
Zaben gwamnan jihar ta Edo dai, shi ne babban zabe na farko da ya gudana a kasar nan tun bayan barkewar annobar cutar sarkewar numfashi ta coronavirus.
20/09/2020 KATSINA
A wani yunkuri da take yi na kokarin magance matsalar ‘yan bindiga da s**a addabi sassan jihar, gwamnatin Katsina, ta ce ta bullo da wani sabon tsarin yaki da wannan matsala ta tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa.
Gwamnatin jihar , ta ce tana shirin fara aiwatar da wani sabon tsari da zai taimaka wajen yaki da matsalar 'yan bindiga da ke kai hare-hare a wasu sassan Katsina.
Yayin da yake ganawa da manema labarai, shugaban kwamitin tsaro a jihar Dr. Mustapha Inuwa, ya ce za a raya dajin da ya zama mabuya ga ‘yan bindigar.
A cewar Dr Mustapha Inuwa, daukan wannan mataki zai ta da dajin daga mafakar wadanda suke amfani da hanyar suna shiga garuruwan Babban Duhu, Lamma, Kurfi da sauran su.
An yake “shawarar cewa, dajin za’a maida shi gonaki, kuma wadanda suke bukata a yanka masu su yi gidaje a wurin, daga karshe kuma gwamnatin ta fara yin makaranta da asibiti.
20/09/2020 ZAMFARA
Wasu 'yan bindiga sun kai hari tare da sace mutane fiye da arba'in a garin Gobirawan Cali, da wasu mutum hudu a Magami dake yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
'Yan bindigar sun kai harin ne a jiya Asabar da misalin karfe uku da rabi da rana.
Wani da ya tsallake rijiya da baya a yayin harin ya shaida cewa, 'yan bindigar sun fara kokarin sace wani mutum ne inda s**a yi kokawa da shi daga bisani mutumin ya samu nasara a kan dan bindigar da yake shi ma yana tare da makami a jikinsa.
Nan da nan sai dan bindigar ya kwace makamin mutumin ya cilla cikin wata gona ya kuma gudu.
Jim kadan sai ayarin 'yan bindigar s**a shiga garin s**a bude wuta suna kuma korar jama'a.
Akalla an sace mutum sama da arba'in a yayin wannan hari amma kuma wasu daga cikinsu sun kubuta.
Al’ummar yankin dai basu samu damar sanar da jami'an tsaro faruwar wannan al’amarin ba saboda duk layukan sadarwar da ake da su basa aiki a garin.
20/09/2020 NIGER
Gwamnatin jihar Neja ta yi barazanar dakatar da samar da ruwan sha a Barikin Sojoji da ke Minna kan wasu kudade da ba a biya ba da yawansu ya haura Naira miliyan dari bakwai.
Bashi ne gaba daya na samar da ruwa ga sojoji, ‘yan sanda, DSS da sauran hukumomi ke bin su.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa na jihar, Yusuf Suleiman ne ya fadi haka a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Minna yayin da ya karbi bayanai kan bashin da suke bin hukumomin tsaro.
Mataimakin Babban Manajan, na Kasuwancin Hukumar samar da ruwa na Jihar Neja, Aliyu Danladi Umar ya fadawa Kwamishinan cewa hukumar na bin Sojojin Nijeriya, ‘Yan Sanda, DSS da sauran Hukumomi bashin sama da Naira miliyan 700,000,000.
Ya bayyana cewa ‘yan sanda na ta kokarin ganin sun biya ta duk da cewa har yanzu ba su gama biyan bashin ba.
20/09/2020 IRAQ/SULEIMANI
Kwamandan Zaratan sojin iran Hossein Salami ya sha alwashin kai hari kan duk wadanda su ke da hannu wajen hallaka Janar Qasem Soleimani da Amurka ta kashe a harin da ta kai Iraqi a watan Janairu.
Shugaba Donald Trump a cikin wannan mako ya yi gargadin cewar Amurka za ta mayar da gagarumin martani kan duk wani mataki na Iran da ya shafi yunkurin daukar fansa kan kisan da aka yiwa Janar Qassem Soleimani, inda ya ke cewa idan sun kai mana hari ta kowanne fanni, mun bada umurni a rubuce akai musu irin sa har sau dubu.
Gargadin Trump na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta yi zargin cewar Iran na kokarin kashe Jakadiyar kasar da ke Afirka ta kudu Lana Marks zargin da hukumomin Afirka ta kudu s**a ce babu gaskiya a cikin sa.
Janar Salami ya ce ba za su kai wa Jakadiyar mace hari ba, sai dai za su kaiwa duk wadanda su ke da hannu wajen kashe Janar Qasem Soleimani, kuma duk wanda ya ke da hannu a ciki ya saurari hari.
20/09/2020 WHO
Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince a fara gwada magungunan yaki da cutar korona na gargajiya da aka samar a Afirka.
Cikin wata sanarwa, ofishin hukumar na Afrika dake a Brazzaville ya ce ya amince da yarjejeniyar gwada magungunan dai-dai da sauran gwaje-gwajen da ake yi wa rigakafin cutar da ake samarwa a kasashen duniya.
Hukumar ta ce duk wani maganin gargajiya da aka yanke hukuncin na da inganci to kuwa za a iya fara amfani da shi a fadin duniya.
Hukumar ta ce tantance magungunan ta ingantacciyar hanyar kimiyya ce za ta fayyace ingancin magungunan gargajiya da za su taimaka wajen yaki da cutar ta korona.
ASALIN HOTON,AFP
Matakin ya zo ne watanni bayan da shugaban Madagaska ya shelantawa duniya wani maganin gargajiya da ba a gwada ba, da yace zai taimaka wajen dakile cutar ta korona.
Suma wasu kasashe kamar Tanzania, da Comoros, Guinea-Bissau da Congo duk sun samar da nasu magungunan gargajiyan da ba a gwada ba.
20/09/2020 MDD/IRAN
Amurka ta mayar da dukkan takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan kasar Iran, ciki har da takunkumin makamai kamar yadda wata sanarwa da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya fitar ranar Asabar.
Sanarwar ta kira Iran a matsayin babbar kasa a duniya dake taimakawa ta’addanci da nuna wariya ga Yahudawa, haka kuma sanarwar ta ce takunkumin za su fara aiki daga jiya Asabar.
Amurka ta dauki wannan matakin ne saboda Iran ta kasa cika alkawuran da ta dauka karkashin yarjejeniyar JCPOA, kuma kwamitin tsaro na MDD ya ki daukar matakin tabbatar da ci gaban takunkumin makamai kan Iran wanda aka samar shekaru 13 da s**a gabata, a cewar sanarwar.
Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif, ya amsa ranar Asabar ‘yan sa’o’i kafin Amurka ta sanar da shirinta na sake maido da takunkumin kan Iran.
Tun farkon mako, Pompeo ya gana da ministan harkokin wajen Birtaniya Dominic Raab a Washington. A wani taron manema labarai da s**a gudanar ranar Laraba, Pompeo ya ce “Zasu koma MDD ta mayar da takunkumin saboda dokar makamai ta zamto ta dindindin a mako mai zuwa.”