Hijrah Tv

Hijrah Tv Hijrah Media LTD
(2)

'๐—ฌ๐—ฎ๐—ป ๐˜€๐—ฎ๐—ป๐—ฑ๐—ฎ ๐˜€๐˜‚๐—ป ๐—ฐ๐—ฒ ๐˜€๐˜‚๐—ป ๐—ธ๐—ฎ๐—บ๐—ฎ ๐˜„๐—ฎ๐—ฑ๐—ฑ๐—ฎ ๐—ฎ๐—ธ๐—ฒ ๐˜‡๐—ฎ๐—ฟ๐—ด๐—ถ ษ“๐—ฎ๐—ฟ๐—ฎ๐˜‚๐—ป๐—ถ๐˜†๐—ฎ๐—ฟ ๐˜„๐—ฎ๐˜†๐—ฎ ๐—ฐ๐—ฒ ๐—ฎ ๐—•๐—ผ๐—ฟ๐—ป๐—ผRundunar ฦดan sandan Najeriya reshen Borno ta ce ta ...
05/01/2024

'๐—ฌ๐—ฎ๐—ป ๐˜€๐—ฎ๐—ป๐—ฑ๐—ฎ ๐˜€๐˜‚๐—ป ๐—ฐ๐—ฒ ๐˜€๐˜‚๐—ป ๐—ธ๐—ฎ๐—บ๐—ฎ ๐˜„๐—ฎ๐—ฑ๐—ฑ๐—ฎ ๐—ฎ๐—ธ๐—ฒ ๐˜‡๐—ฎ๐—ฟ๐—ด๐—ถ ษ“๐—ฎ๐—ฟ๐—ฎ๐˜‚๐—ป๐—ถ๐˜†๐—ฎ๐—ฟ ๐˜„๐—ฎ๐˜†๐—ฎ ๐—ฐ๐—ฒ ๐—ฎ ๐—•๐—ผ๐—ฟ๐—ป๐—ผ
Rundunar ฦดan sandan Najeriya reshen Borno ta ce ta k**a wata mata da ake zargin ta shahara wajen sace-sacen waya da wasu mutum 84 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar.

Laifukan da ake zargin mutanen sun aikata ฦ™unshi haษ—in baki da fyaษ—e da kisan kai da fashi da makami da sata da mallamar muggan mak**ai da kuma shan tabar wiwi.

Da ake holen mutanen a Maiduguri ranar Alhamis, Kakakin rundunar ฦดan sandan ta Borno, ASP Daso Nahum.

Ya ce rundunar ta samu rahoton laifuffuka 49 sun kuma samu waษ—anda ake zargi 27 da laifi. Ya ฦ™ara da cewa rundunar tana bincike kan wasu laifuffuka 14 sai wasu 31 da aka gurfanar da su a kotu.

Kakakin ya ce an k**a matar ranar 28 ga watan Disamban da ya gabata bayan ayyana ta a matsayin wadda ake neman ruwa a jallo sak**akon sace-sacen wayoyin jama'a.

"Yayin bincike, ta faษ—i wanda suke satar tare, suna zuwa gidajen mutane a matsayin ฦดan aiki inda suke kwashe wayoyin mutanen da suke yi wa aiki."

"An gano waya kirar Techno LC6 yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin k**a mutanen da wayar ke hannunsu daga bisani kuma a gurfanar da su a kotu," k**ar yadda kakakin ฦดan sandan ya bayyana.

๐—ก๐—ฎ๐—ท๐—ฒ๐—ฟ๐—ถ๐˜†๐—ฎ ๐˜๐—ฎ ๐—ฟ๐˜‚๐—ณ๐—ฒ ๐—ท๐—ฎ๐—บ๐—ถ'๐—ผ'๐—ถ๐—ป ฦ™๐—ฎ๐˜€๐—ฎ๐˜€๐—ต๐—ฒ๐—ป ๐˜„๐—ฎ๐—ท๐—ฒ ๐Ÿญ๐Ÿด ๐—ฏ๐—ฎ๐˜†๐—ฎ๐—ป ๐—ฟ๐—ฎ๐—ต๐—ผ๐˜๐—ผ๐—ป '๐—ฑ๐—ถ๐—ด๐—ถ๐—ฟ๐—ถ ษ—๐—ฎ๐—ป ๐—ž๐˜„๐—ฎ๐˜๐—ฎ๐—ป๐—ผ'Gwamnatin Najeriya ta haramtawa wasu jami'...
03/01/2024

๐—ก๐—ฎ๐—ท๐—ฒ๐—ฟ๐—ถ๐˜†๐—ฎ ๐˜๐—ฎ ๐—ฟ๐˜‚๐—ณ๐—ฒ ๐—ท๐—ฎ๐—บ๐—ถ'๐—ผ'๐—ถ๐—ป ฦ™๐—ฎ๐˜€๐—ฎ๐˜€๐—ต๐—ฒ๐—ป ๐˜„๐—ฎ๐—ท๐—ฒ ๐Ÿญ๐Ÿด ๐—ฏ๐—ฎ๐˜†๐—ฎ๐—ป ๐—ฟ๐—ฎ๐—ต๐—ผ๐˜๐—ผ๐—ป '๐—ฑ๐—ถ๐—ด๐—ถ๐—ฟ๐—ถ ษ—๐—ฎ๐—ป ๐—ž๐˜„๐—ฎ๐˜๐—ฎ๐—ป๐—ผ'
Gwamnatin Najeriya ta haramtawa wasu jami'oin ฦ™asashen waje 18 tafiyar da harkokinsu a ฦ™asar inda ta bayyana su da masana'antun haษ—a digiri.

Gwamnatin ta kuma gargaษ—i ฦดan Najeriya su guji shiga jami'oin.

Matakin ya shafi jami'oi biyar daga Amurka sai guda shida daga Birtaniya, uku kuma daga Ghana.

Da take sanar da matakin dakatarwar cikin wata sanarwa, hukumar kula da jami'oin Najeriya, NUC ta yi bayani cewa jami'oin 18 ba su da sahhalewar gwamnati don tafiyar da harkokinsu a don haka ta rufe su.

Ta ce "Hukumar NUC na sanar da jama'a musamman iyaye da ษ—alibai cewa waษ—annan jami'oin ba su da lasisin gwamnatin tarayya don haka an rufe su saboda take dokar ilimi ta Najeriya ta 2004.

Daga cikin jami'oin da wannan matakin ya shafa akwai jami'ar Applied Sciences & Management da ke Jamhuriyar Benin da jami'ar Volta University College da ke Ghana sai International University da ke Missouri a Amurka da sauran cibiyoyinta da ke Kano da Legas, akwai kuma jami'ar Collumbus da ke Birtaniya.

A jiya Talata ne ma'aikatar ilimi ta ce ta dakatar da tantance shaidar digiri daga jami'oin Benin da Togo, a wani yunฦ™uri na tsaftace ษ“angaren ilimin, har zuwa lokacin da za ta kammala bincike a kan ingancin makarantun.

Matakin dai ya zo ne bayan wani bincike da jaridar Daily Nigerian ta gudanar kan yadda ma'aikacinta ya samu shaidar kammala digiri daga wata jami'a a Cotonou cikin ฦ™asa da wata biyu.

๐—ฌ๐—ฎ๐˜„๐—ฎ๐—ป ๐—บ๐˜‚๐˜๐—ฎ๐—ป๐—ฒ๐—ป ๐—ฑ๐—ฎ ๐˜€๐˜‚๐—ธ๐—ฎ ๐—บ๐˜‚๐˜๐˜‚ ๐—ฎ ๐—ด๐—ถ๐—ฟ๐—ด๐—ถ๐˜‡๐—ฎ๐—ฟ ฦ™๐—ฎ๐˜€๐—ฎ๐—ฟ ๐—๐—ฎ๐—ฝ๐—ฎ๐—ป ๐˜†๐—ฎ ๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ๐˜‚ ๐˜‡๐˜‚๐˜„๐—ฎ ๐Ÿฐ๐ŸดHukumomi a Japan sun ce adadin mutanen da s**a mutu sak...
02/01/2024

๐—ฌ๐—ฎ๐˜„๐—ฎ๐—ป ๐—บ๐˜‚๐˜๐—ฎ๐—ป๐—ฒ๐—ป ๐—ฑ๐—ฎ ๐˜€๐˜‚๐—ธ๐—ฎ ๐—บ๐˜‚๐˜๐˜‚ ๐—ฎ ๐—ด๐—ถ๐—ฟ๐—ด๐—ถ๐˜‡๐—ฎ๐—ฟ ฦ™๐—ฎ๐˜€๐—ฎ๐—ฟ ๐—๐—ฎ๐—ฝ๐—ฎ๐—ป ๐˜†๐—ฎ ๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ๐˜‚ ๐˜‡๐˜‚๐˜„๐—ฎ ๐Ÿฐ๐Ÿด
Hukumomi a Japan sun ce adadin mutanen da s**a mutu sak**akon girgizar ฦ™asa mai ฦ™arfin gaske a Japan ya ฦ™aru zuwa 48.

A cewar hukumomin girgizar ฦ™asar ta kai ฦ™arfin maki 7.6 kuma mutane da dama sun jikkata sak**akon ibtila'in.

Jami'ai sun ce akwai yiwuwar adadin ya ฦ™aru yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Masu aikin ceton na ta faษ—i tashin zaฦ™ulo masu sauran numfashi daga ษ“uraguzon gine-ginen da s**a rushe sai dai masu kai ษ—aukin na fuskantar cikas sak**akon toshe titunan da s**a lalace.

Firaministan Japan, Fumio Kishida ya ce "muna ฦ™oฦ™arin lalubo mutanen da girgizar ta shafa kafin lokaci ya ฦ™ure mana."

Ya ฦ™ara da cewa wasu masu aikin agajin na fuskantar ฦ™alubale wajen kai wa zuwa yankin Noto Peninsula.

Al'ummar yankin sun yi fama da matsanancin sanyi cikin dare saboda rashin wutar lantarki.

Akasarin birane suna cikin matsalar rashin wuta.

01/01/2024

DAGA FILIN WASANNI EPISODE 1
Host: Ahmed Sanusi Abbas

๐—œ๐˜€๐—ฟ๐—ฎ'๐—ถ๐—น๐—ฎ ๐˜๐—ฎ ๐—ฐ๐—ฒ ๐—ฎ๐—ธ๐˜„๐—ฎ๐—ถ ๐˜†๐—ถ๐˜„๐˜‚๐˜„๐—ฎ๐—ฟ ๐˜†๐—ฎฦ™๐—ถ๐—ป ๐—š๐—ฎ๐˜‡๐—ฎ ๐˜‡๐—ฎ๐—ถ ๐—ฐ๐—ถ ๐—ด๐—ฎ๐—ฏ๐—ฎ ๐˜๐˜€๐—ฎ๐˜„๐—ผ๐—ป ๐˜€๐—ต๐—ฒ๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ๐—ฎ ๐˜๐—ฎ ๐Ÿฎ๐Ÿฌ๐Ÿฎ๐ŸฐRundunar sojin Isra'ila ta ce tana tsammanin r...
01/01/2024

๐—œ๐˜€๐—ฟ๐—ฎ'๐—ถ๐—น๐—ฎ ๐˜๐—ฎ ๐—ฐ๐—ฒ ๐—ฎ๐—ธ๐˜„๐—ฎ๐—ถ ๐˜†๐—ถ๐˜„๐˜‚๐˜„๐—ฎ๐—ฟ ๐˜†๐—ฎฦ™๐—ถ๐—ป ๐—š๐—ฎ๐˜‡๐—ฎ ๐˜‡๐—ฎ๐—ถ ๐—ฐ๐—ถ ๐—ด๐—ฎ๐—ฏ๐—ฎ ๐˜๐˜€๐—ฎ๐˜„๐—ผ๐—ป ๐˜€๐—ต๐—ฒ๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ๐—ฎ ๐˜๐—ฎ ๐Ÿฎ๐Ÿฌ๐Ÿฎ๐Ÿฐ
Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana tsammanin rikici a Gaza zai ci gaba da gudana a tsawon shekara ta 2024.

A wani saฦ™on sabuwar shekara, mai magana da yawun rundunar tsaron Isra'ila Daniel Hagari ya ce an daidaita harkar tura dakarun soji don shirin tunkarar "faษ—a na tsawon lokaci".

Ya ce za a janye wasu dakaru - musamman ma sojojin wucin gadi - don ba su damar sake tattaruwa.

"Waษ—annan gyare-gyare ana yin su ne don tabbatar da ganin an yi tsare-tsare da shirye-shirye da nufin ci gaba da yaฦ™i a shekara ta 2024," in ji shi.

Ya ce wasu sojoji masu wucin gadi za bar Gaza "tun a wannan mako" don ba su damar "sake kintsawa gabanin wasu ayyuka da ke tafe".

Mutum 21,978 - akasari mata da ฦ™ananan yara ne - aka kashe a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar ma'aikatar lafiya da ke ฦ™arฦ™ashin ikon Hamas. Ta kuma an jikkata mutum 56,697 a Gaza a tsawon wannan lokaci.

Adadin ya haษ—ar da na mutum 156 da aka kashe da 246 da aka ji wa raunuka a tsawon sa'a 24 da ta wuce, ma'aikatar ta ฦ™ra da cewa.

๐—ฌ๐—ฎ๐—ฑ๐—ฑ๐—ฎ ๐—น๐—ฎ๐—บ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐—ป ๐˜๐˜€๐—ฎ๐—ฟ๐—ผ ๐—ธ๐—ฒ ฦ™๐—ฎ๐—ฟ๐—ฎ ๐˜๐—ฎษ“๐—ฎ๐—ฟษ“๐—ฎ๐—ฟ๐—ฒ๐˜„๐—ฎ ๐—ฎ ๐—ท๐—ถ๐—ต๐—ฎ๐—ฟ ๐—ญ๐—ฎ๐—บ๐—ณ๐—ฎ๐—ฟ๐—ฎKimanin al'ummomin garuruwa goma ne da ke yankin ฦ™aramar hukumar ...
30/12/2023

๐—ฌ๐—ฎ๐—ฑ๐—ฑ๐—ฎ ๐—น๐—ฎ๐—บ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐—ป ๐˜๐˜€๐—ฎ๐—ฟ๐—ผ ๐—ธ๐—ฒ ฦ™๐—ฎ๐—ฟ๐—ฎ ๐˜๐—ฎษ“๐—ฎ๐—ฟษ“๐—ฎ๐—ฟ๐—ฒ๐˜„๐—ฎ ๐—ฎ ๐—ท๐—ถ๐—ต๐—ฎ๐—ฟ ๐—ญ๐—ฎ๐—บ๐—ณ๐—ฎ๐—ฟ๐—ฎ
Kimanin al'ummomin garuruwa goma ne da ke yankin ฦ™aramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, suke gudun hijira zuwa wasu wurare sak**akon kwazzabar da 'yan bindiga da ke yi masu ta hanyar hare-hare, da aikata kisan gilla, da kuma sace mutane don neman kudin fansa da sauran miyagun laifuka.

Jama'ar da matsalar ta addaba a yankin yammcin yankin tsafe sun shiga tsaka mai-wuya inda lamarin yake ta ฦ™ara tsananta.

Wani mazaunin yankin da ya buฦ™aci a sakaya sunansa ya yi wa BBC bayanin cewa lamarin ya shafi kusan garuruwa goma a yankin inda ya ce a baya bayan nan 'yan bindiga sun kai hari a ฦ™auyen Rakyabu a yankin inda s**a fatattaki al'ummar ฦ™auyen baki ษ—aya wanda haka ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu.

'A yanzu haka babu ko kaza a garin, kowa ya gudun sun dawo cikin garin Tsafe suna kwana cikin tasha da bakin t**i. Duk sun zama 'yan gudun hijira'. in ji shi

๐— ๐˜‚๐—ป๐—ฎ๐—ฎ ๐—ฎ๐—ถ๐—ธ๐—ถ ๐˜๐˜‚ฦ™๐˜‚๐—ฟ๐˜‚ ๐—ฑ๐—ผ๐—บ๐—ถ๐—ป ๐˜€๐—ฎ๐—ธ๐—ฒ ๐—ณ๐—ฎ๐˜€๐—ฎ๐—น๐—ถ๐—ป ๐˜๐—ฎ๐˜๐˜๐—ฎ๐—น๐—ถ๐—ป ๐—ฎ๐—ฟ๐˜‡๐—ถ๐—ธ๐—ถ๐—ป ๐—ก๐—ฎ๐—ท๐—ฒ๐—ฟ๐—ถ๐˜†๐—ฎ โ€“ ๐—ง๐—ถ๐—ป๐˜‚๐—ฏ๐˜‚Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ...
29/12/2023

๐— ๐˜‚๐—ป๐—ฎ๐—ฎ ๐—ฎ๐—ถ๐—ธ๐—ถ ๐˜๐˜‚ฦ™๐˜‚๐—ฟ๐˜‚ ๐—ฑ๐—ผ๐—บ๐—ถ๐—ป ๐˜€๐—ฎ๐—ธ๐—ฒ ๐—ณ๐—ฎ๐˜€๐—ฎ๐—น๐—ถ๐—ป ๐˜๐—ฎ๐˜๐˜๐—ฎ๐—น๐—ถ๐—ป ๐—ฎ๐—ฟ๐˜‡๐—ถ๐—ธ๐—ถ๐—ป ๐—ก๐—ฎ๐—ท๐—ฒ๐—ฟ๐—ถ๐˜†๐—ฎ โ€“ ๐—ง๐—ถ๐—ป๐˜‚๐—ฏ๐˜‚
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa tana aiki tuฦ™uru domin sake gyara tattalin arzikin ฦ™asar ta yadda za a mayar da hankali kan samar da manyan ayyuka tare da sabunta ayyukan more rayuwa.

Shugaba Tinubu ya bayyana haka jiya Alhamis lokacin da ya karษ“i baฦ™uncin mambobin kwamitin gudanarwar jam'iyyar APC a jihar Legas.

A cewarsa, "ina sa ran za a fitarda kasafin kuษ—i kowane lokaci daga yanzu, za ku ga yadda aka karkata kan manyan ayyuka, dole ne sabunta lalacewar ayyukan more rayuwa, mu kuma gyara hakan tare."

Ya kuma bayyana damuwa game da yawan yaran da basa zuwa makaranta a ฦ™asar bayan rahoton baya-bayan nan da aka fitar.

"Ya zama dole mu magance wannan matsala ta hanyar samar da ฦ™arin makarantu da ษ—iban malamai aiki da samar da tsarin ciyar da ษ—alibai." k**ar yadda Tinubu ya bayyana.

Shugaba Tinubu ya ce dole ne dimokraษ—iyya ta ci gaba kuma ta tafi da kowa da zummar magance talauci ta hanyar samar da damarmaki na aiki ga matasa da kuma inganta ilimin yaran Najeriya.

Ya ce yin haษ—in gwiwa da ษ“angarorin gwamnati da dama abu ne mai muhimmanci wajen ci gaban gwamnatinsu da kuma Najeriya.

A nasa ษ“angaren, shugaban Jam'iyyar APC, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da Tinubu cewa kwamitin gudanarwar jam'iyyar ya yi tsare-tsaren tabbatar da nasarar APC a zaษ“en cike gurbin da ke tafe a watan Fabarairun 2024.

๐— ๐˜‚๐˜๐—ฎ๐—ป๐—ฒ๐—ป ๐—ฑ๐—ฎ ๐˜€๐˜‚๐—ธ๐—ฎ ๐—บ๐˜‚๐˜๐˜‚ ๐—ฎ ๐—ต๐—ฎ๐—ฟ๐—ฒ-๐—ต๐—ฎ๐—ฟ๐—ฒ๐—ป ๐—™๐—ถ๐—น๐—ฎ๐˜๐—ผ ๐˜€๐˜‚๐—ป ๐—ธ๐—ฎ๐—ถ ๐Ÿญ๐Ÿต๐Ÿฑ'Shugaban ฦ™aramar hukumar Bokkos a Filato ya ce mutum 148 aka kashe ...
28/12/2023

๐— ๐˜‚๐˜๐—ฎ๐—ป๐—ฒ๐—ป ๐—ฑ๐—ฎ ๐˜€๐˜‚๐—ธ๐—ฎ ๐—บ๐˜‚๐˜๐˜‚ ๐—ฎ ๐—ต๐—ฎ๐—ฟ๐—ฒ-๐—ต๐—ฎ๐—ฟ๐—ฒ๐—ป ๐—™๐—ถ๐—น๐—ฎ๐˜๐—ผ ๐˜€๐˜‚๐—ป ๐—ธ๐—ฎ๐—ถ ๐Ÿญ๐Ÿต๐Ÿฑ'
Shugaban ฦ™aramar hukumar Bokkos a Filato ya ce mutum 148 aka kashe a hare-haren da ฦดan bindiga s**a kai a jajiberin kirsimeti a yankin.

Hakan na zuwa daidai lokacin da adadin mutanen da s**a mutu sanadin hare-haren a ฦ™ananan hukumomi uku na jihar ya kai 195.

Daga cikin adadin, an kashe mutum 148 a ฦ™aramar hukumar Bokkos dai 19 a ฦ™aramar hukumar Mangu da wasu 27 a Barkin Ladi.

An kuma ฦ™ona gidaje 1,290 a Bokkos sai gida ษ—aya a Mangu da shi ma aka ฦ™ona sai dai har yanzu ba a kai ga sanin yawan gidajen da aka ฦ™ona ba a Barkin Ladi.

Fiye da mutum 10,000 ne s**a ษ—aiษ—aita sak**akon hare-haren na ฦดan bindiga a yankunan Bokkos da Barkin Ladi.

๐—”๐—ป ๐˜†๐—ฎ๐—ป๐—ธ๐—ฒ ๐˜„๐—ฎ ฦด๐—ฎ๐—ป ๐—ณ๐—ฎ๐—ณ๐˜‚๐˜๐˜‚๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ ๐—›๐—ผ๐—ป๐—ด ๐—ž๐—ผ๐—ป๐—ด ๐˜€๐—ต๐—ฒ๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ๐—ฎ ๐˜€๐—ต๐—ถ๐—ฑ๐—ฎ ๐—ฎ ๐—ธ๐˜‚๐—ฟ๐—ธ๐˜‚๐—ธ๐˜‚ ๐—ธ๐—ฎ๐—ป ๐—ธ๐—ถ๐˜๐˜€๐—ฎ ๐—ต๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐—ป ๐˜๐—ฎ'๐—ฎ๐—ฑ๐—ฑ๐—ฎ๐—ป๐—ฐ๐—ถAn yanke wa wasu masu fafutuka uku...
28/12/2023

๐—”๐—ป ๐˜†๐—ฎ๐—ป๐—ธ๐—ฒ ๐˜„๐—ฎ ฦด๐—ฎ๐—ป ๐—ณ๐—ฎ๐—ณ๐˜‚๐˜๐˜‚๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ ๐—›๐—ผ๐—ป๐—ด ๐—ž๐—ผ๐—ป๐—ด ๐˜€๐—ต๐—ฒ๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ๐—ฎ ๐˜€๐—ต๐—ถ๐—ฑ๐—ฎ ๐—ฎ ๐—ธ๐˜‚๐—ฟ๐—ธ๐˜‚๐—ธ๐˜‚ ๐—ธ๐—ฎ๐—ป ๐—ธ๐—ถ๐˜๐˜€๐—ฎ ๐—ต๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐—ป ๐˜๐—ฎ'๐—ฎ๐—ฑ๐—ฑ๐—ฎ๐—ป๐—ฐ๐—ถ
An yanke wa wasu masu fafutuka uku ฦดan Hong Kong hukuncin shekara shida a gidan yari saboda samun su da hannu a kitsa wani hari da aka daฦ™ile kan gine-ginen gwamnati.

Mutanen uku tun da farko an tuhume su da "haษ—a baki wajen aikata ta'addanci" ฦ™arฦ™ashin dokar tsaro ta ฦ™asa.

Suna daga cikin ฦดan ฦ™ungiyar Returning Vailant da ta kitsa lamarin a 2021 bayan zanga-zangar neman rajin kafa dimokraษ—iyya.

An k**a su ne a Yulin 2021, kafin su aiwatar da ฦ™udirinsu.

Kotun ta samu bayanai cewa Ho Yu-wang da Kwok Man-hei da Cheung Ho-yeung sun tsara su haษ—a bama-bamai ta hanyar amfani da abin fashewa TATP tare da dasa su a gine-ginen gwamnati da dama har da ofisoshin gwamnati da ofisoshin ฦดan sanda da kotuna da kuma tashoshin jiragen ฦ™asa.

Sun yi niyyar wanzar da ฦ™udirinsu tsakanin 1 ga watan Afrilu da 5 ga watan Yulin 2021 amma aka k**a su kafin su haษ—a bama-baman, k**ar yadda kotun ta samu bayanai.

Masu gabatar da ฦ™ara sun ce Ho wanda yake shekara 17 lokacin da ya shiga hannu shi ne ke da "alhakin haษ—a abubuwan fashewar".

Ya amsa laifin tuhumar ta'addanci inda kuma aka yanke masa shekara shida a gidan yari sannan kuma kotu ta ayyana shi a matsayin jagoran ฦ™ungiyar.

Cheng mai shekara 23, shi ma an yanke masa shekara shida a kurkuku yayin da Kwok ษ—an shekara 21 aka ba shi hukuncin wata 30 a gidan yari. Dukkansu sun amsa laifin "haษ—a baki domin ta da abubuwan fashewa".

Alฦ™alin babbar kotu Alex Lee ya ce ya amince cewa yamutsin da aka samu yayin gangamin masu rajin a kafa dimokraษ—iyya na iya sauya ra'ayin nutsattsu su zama fitinannu", a cewar rahoton Reuters.

A watan Mayu aka yanke wa mutum huษ—u hukunci saboda hannun da suke da shi.

๐—ฌ๐—ฎ๐—ฑ๐—ฑ๐—ฎ ๐—บ๐—ฎ๐—บ๐—ฎ๐—ธ๐—ผ๐—ป ๐—ฟ๐˜‚๐˜„๐—ฎ๐—ป ๐˜€๐—ฎ๐—บ๐—ฎ ๐˜†๐—ฎ ๐—ต๐—ฎ๐—น๐—ฎ๐—ธ๐—ฎ ๐˜†๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐—ป๐˜†๐—ฎ ๐—ฑ๐—ฎ ๐˜„๐—ฎ๐˜€๐˜‚ ๐˜๐—ฎ๐—ฟ๐—ฎ ๐—ฎ ๐—”๐˜‚๐˜€๐˜๐—ฟ๐—ฎ๐—น๐—ถ๐˜†๐—ฎAฦ™alla mutum 10, ciki har da yarinya ฦดar shekara tar...
27/12/2023

๐—ฌ๐—ฎ๐—ฑ๐—ฑ๐—ฎ ๐—บ๐—ฎ๐—บ๐—ฎ๐—ธ๐—ผ๐—ป ๐—ฟ๐˜‚๐˜„๐—ฎ๐—ป ๐˜€๐—ฎ๐—บ๐—ฎ ๐˜†๐—ฎ ๐—ต๐—ฎ๐—น๐—ฎ๐—ธ๐—ฎ ๐˜†๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐—ป๐˜†๐—ฎ ๐—ฑ๐—ฎ ๐˜„๐—ฎ๐˜€๐˜‚ ๐˜๐—ฎ๐—ฟ๐—ฎ ๐—ฎ ๐—”๐˜‚๐˜€๐˜๐—ฟ๐—ฎ๐—น๐—ถ๐˜†๐—ฎ
Aฦ™alla mutum 10, ciki har da yarinya ฦดar shekara tara sun mutu a gabashin Australiya sak**akon mamakon ruwan saman da aka yi ranakun kirsimeti da kuma ranar raba kyautuka wato Boxing Day a turancin Ingilishi.

Akasarin mutanen da s**a mutu a jihar Queensland inda har yanzu dubban mutane ba su da hasken wutar lantarki.

An samu iska mai ฦ™arfin gaske da ambaliyar ruwa a Victoria da New South Wales.

Hukumomi sun yi hasashen samun ฦ™arin ruwan sama k**ar da bakin ฦ™warya amma sana tunanin yanayin zai inganta.

"Wannan ne karon farko da aka taษ“a samun iska mai ฦ™arfi ta lalata turakun wutar lantarki da aka dasa da daben siminti. Abu ne da ba mu yi hasashen sa ba." in ji Firimiyan Queensland Steven Miles.

Mazauna a yankunan New South Wales da South Australia sun shiga kaษ—uwa ganin yadda ฦ™anฦ™ara da dama da girmansu ya kai ฦ™wallon golf s**a mamaye ฦ™asa.

๐—™๐—ถ๐˜†๐—ฒ ๐—ฑ๐—ฎ ๐—บ๐˜‚๐˜๐˜‚๐—บ ๐Ÿฎ๐Ÿฌ ๐˜€๐˜‚๐—ป ๐—บ๐˜‚๐˜๐˜‚ ๐˜€๐—ฎ๐—ธ๐—ฎ๐—บ๐—ฎ๐—ธ๐—ผ๐—ป ๐—ณ๐—ฎ๐˜€๐—ต๐—ฒ๐˜„๐—ฎ๐—ฟ ๐—ฏ๐˜‚๐˜๐˜‚๐˜๐˜‚๐—ป ๐—บ๐—ฎ๐—ถ ๐—ฎ ๐—ฅ๐—ถ๐—ฏ๐—ฎ๐˜€Wata fashewa da ta faru bayan fasa wani bututun ษ—anyen m...
27/12/2023

๐—™๐—ถ๐˜†๐—ฒ ๐—ฑ๐—ฎ ๐—บ๐˜‚๐˜๐˜‚๐—บ ๐Ÿฎ๐Ÿฌ ๐˜€๐˜‚๐—ป ๐—บ๐˜‚๐˜๐˜‚ ๐˜€๐—ฎ๐—ธ๐—ฎ๐—บ๐—ฎ๐—ธ๐—ผ๐—ป ๐—ณ๐—ฎ๐˜€๐—ต๐—ฒ๐˜„๐—ฎ๐—ฟ ๐—ฏ๐˜‚๐˜๐˜‚๐˜๐˜‚๐—ป ๐—บ๐—ฎ๐—ถ ๐—ฎ ๐—ฅ๐—ถ๐—ฏ๐—ฎ๐˜€
Wata fashewa da ta faru bayan fasa wani bututun ษ—anyen mai da ke ฦ™arฦ™ashin ฦ™asa a ฦ™aramar hukumar Ogba/Egebema/Ndoni da ke jihar Ribas ta halaka aฦ™alla mutum 20.

Lamarin ya faru ne a ฦ™arshen makon daya gabata a ฦ™aramar hukumar da ke zama ษ—aya daga cikin cibiyoyi masu arzikin mai da iskar gas a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Rahotanni na cewa an kwantar da mutanen da s**a samu ฦ™una a asibitoci da dama a garin.

Zuwa yanzu, babu tabbacin abin da ya jawo fashewar da ta haddasa gobara da kuma adadin mutanen da s**a mutu.

Shugaban matasan yankin ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da matasan suke raba ษ—anyen man da aka sato a jarkoki.

Wani ษ—an jarida ya tabbatar cewa gobarar ta tashi lokacin da matasan suke rige-rigen kwasar ษ—anyen man daga wani bututu da ke ฦ™arฦ™ashin ฦ™asa a lokacin da gobarar ta tashi.

Join Us Tomorrow 8:00am Ghana Time as we discuss and learn from Sarki Musah Mahmoud Yamboni (Sarki Nii Boi Town)Itโ€™s all...
26/12/2023

Join Us Tomorrow 8:00am Ghana Time as we discuss and learn from Sarki Musah Mahmoud Yamboni (Sarki Nii Boi Town)

Itโ€™s all about commitment and dedication.

Like, Comment, Share & Follow




ฦ˜๐—ฎ๐˜‡๐—ฎ๐—ณ๐—ถ ๐—ฎ๐—ธ๐—ฒ ๐—บ๐—ถ๐—ป, ๐—ฏ๐—ฎ๐—ป ๐—ฏ๐˜‚ษ—๐—ฒ ๐—ฎ๐˜€๐˜‚๐˜€๐˜‚๐—ป ๐—ฏ๐—ฎ๐—ป๐—ธ๐—ถ ๐Ÿฑ๐Ÿต๐Ÿฏ ๐—ฎ ฦ™๐—ฎ๐˜€๐—ฎ๐˜€๐—ต๐—ฒ๐—ป ๐˜„๐—ฎ๐—ท๐—ฒ ๐—ฏ๐—ฎ - ๐—š๐—ผ๐—ฑ๐˜„๐—ถ๐—ป ๐—˜๐—บ๐—ฒ๐—ณ๐—ถ๐—ฒ๐—น๐—ฒTsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, God...
25/12/2023

ฦ˜๐—ฎ๐˜‡๐—ฎ๐—ณ๐—ถ ๐—ฎ๐—ธ๐—ฒ ๐—บ๐—ถ๐—ป, ๐—ฏ๐—ฎ๐—ป ๐—ฏ๐˜‚ษ—๐—ฒ ๐—ฎ๐˜€๐˜‚๐˜€๐˜‚๐—ป ๐—ฏ๐—ฎ๐—ป๐—ธ๐—ถ ๐Ÿฑ๐Ÿต๐Ÿฏ ๐—ฎ ฦ™๐—ฎ๐˜€๐—ฎ๐˜€๐—ต๐—ฒ๐—ป ๐˜„๐—ฎ๐—ท๐—ฒ ๐—ฏ๐—ฎ - ๐—š๐—ผ๐—ฑ๐˜„๐—ถ๐—ป ๐—˜๐—บ๐—ฒ๐—ณ๐—ถ๐—ฒ๐—น๐—ฒ
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya musanta zarge-zargen satar dukiyar ฦ™asa da ake yi masa a wani rahoton Mai Bincike na Musamman kan harkokin bankin CBN da aka fitar a baya-bayan nan.

Ya bayyana matsayin nasa ne a cikin wata sanarwa mai taken, โ€˜Re: Emefiele, others stole billions, illegally kept Nigeriaโ€™s funds in foreign banksโ€™ da ya fitar ranar Lahadi.

Idan za ku iya tunawa a cikin makon jiya ne, Mai Bincike na Musamman kan harkokin Babban Bankin Najeriya, Jim Obaze, ya bankaษ—o cewa tsohon gwamnan bankin ya jibge fam miliyan 543, 482,213 ba tare da izini ba a bankunan Birtaniya kawai.

Wani ษ“angare na rahoton Jim Obaze a cewar jaridar Daily Post ta intanet, โ€œTsohon gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ya jibge kuษ—aษ—en Najeriya ba tare da izini ba a asusun ajiya 593 na bankunan ฦ™asashen waje a Amurka da China da Birtaniya, lokacin da yake mulki.

Sai dai Godwin Emefiele a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi ya ce, bayan sakin sa a matakin beli daga gidan yarin Kuje, hankalinsa ya kai kan wasu labarai masu alaฦ™a da rahoton Jim Obaze.

โ€œNa karanta labaran, kuma da ฦ™arfin murya ina cewa abin da s**a ฦ™unsa, ฦ™arairayi ne da karkatar da hankali da kuma maฦ™arฦ™ashiya don a ษ“ata min suna, a ci mini zarafi sannan da biyan muradin mai binciken.โ€

Ya kuma ce ba shi da hannu a buษ—e asusun ajiya 593 a sassan duniya, kuma bai ma san an buษ—e su ba.

Sai dai ya ce akwai sashe-sashe na babban bankin da ke da iko su aiwatar da irin waษ—annan harkoki k**ar yadda doka ta amince musu bisa tanade-tanaden aikin CBN.

Don haka, a cewar Emefiele "Ni ma k**ar sauran 'yan Najeriya masu kyakkyawar niyya da s**a yi magana kan wannan batu, ina neman a gudanar da cikakken bincike kuma a fayyace komai a faifai game da waษ—annan zarge-zarge na almundahana".

Ya kuma ce ya umarci lauyoyinsa, su hanzarta ษ—aukan matakan shari'a don wanke sunansa daga kalaman ษ“ata-suna da ke ฦ™unshe a cikin rahoton da kuma labaran da s**a wallafa shi.

๐—™๐—ฎ๐—น๐—ฎ๐˜€ษ—๐—ถ๐—ป๐—ฎ๐˜„๐—ฎ ๐˜‡๐—ฎ ๐˜€๐˜‚ ๐—ณ๐˜‚๐˜€๐—ธ๐—ฎ๐—ป๐—ฐ๐—ถ ๐—บ๐—ฎ๐˜๐˜€๐—ฎ๐—น๐—ฎ๐—ฟ ๐˜†๐˜‚๐—ป๐˜„๐—ฎ ๐—ถ๐—ฑ๐—ฎ๐—ป ๐—ฎ๐—ธ๐—ฎ ๐—ฐ๐—ถ ๐—ด๐—ฎ๐—ฏ๐—ฎ ๐—ฑ๐—ฎ ๐˜†๐—ฎฦ™๐—ถ โ€“ ๐— ๐——๐——Al'ummar Falasษ—inu kusan 500,000 na fuskantar mu...
22/12/2023

๐—™๐—ฎ๐—น๐—ฎ๐˜€ษ—๐—ถ๐—ป๐—ฎ๐˜„๐—ฎ ๐˜‡๐—ฎ ๐˜€๐˜‚ ๐—ณ๐˜‚๐˜€๐—ธ๐—ฎ๐—ป๐—ฐ๐—ถ ๐—บ๐—ฎ๐˜๐˜€๐—ฎ๐—น๐—ฎ๐—ฟ ๐˜†๐˜‚๐—ป๐˜„๐—ฎ ๐—ถ๐—ฑ๐—ฎ๐—ป ๐—ฎ๐—ธ๐—ฎ ๐—ฐ๐—ถ ๐—ด๐—ฎ๐—ฏ๐—ฎ ๐—ฑ๐—ฎ ๐˜†๐—ฎฦ™๐—ถ โ€“ ๐— ๐——๐——
Al'ummar Falasษ—inu kusan 500,000 na fuskantar mummunan yanayi k**ar yadda hukumart samar da abinci ta Majalisar ฦŠinkin Duniya ta bayyana.

Ta ce Falasษ—inawa za su ci gaba da fuskantar haษ—arin yunwa idan aka ci gaba da yaฦ™i tsakanin Isra'ila da Hamas.

Hukumar ta ce galibin al'ummar yankin da s**a kai miliyan 2.2 na fama da ฦ™arancin abinci.

"Babu wani da ya tsira daga yunwa a Gaza," in ji Cindy McCain daga hukumar samar da abinci ta MDD.

๐—”๐—ป ๐—ธ๐—ฎ๐—ณ๐—ฎ ๐—ธ๐˜„๐—ฎ๐—บ๐—ฎ๐˜๐—ผ๐—ฐ๐—ถ๐—ป ๐˜†๐—ฎฦ™๐—ฎ๐—ฟ ๐˜€๐—ฎ๐˜๐—ฎ๐—ฟ ษ—๐—ฎ๐—ป๐˜†๐—ฒ๐—ป ๐—บ๐—ฎ๐—ถ ๐—ฑ๐—ฎ ๐—ถ๐—ป๐—ด๐—ฎ๐—ป๐˜๐—ฎ ๐˜๐—ฎ๐˜๐˜๐—ฎ๐—น๐—ถ๐—ป ๐—ฎ๐—ฟ๐˜‡๐—ถ๐—ธ๐—ถ๐—ป ๐—ก๐—ฎ๐—ท๐—ฒ๐—ฟ๐—ถ๐˜†๐—ฎMataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shett...
22/12/2023

๐—”๐—ป ๐—ธ๐—ฎ๐—ณ๐—ฎ ๐—ธ๐˜„๐—ฎ๐—บ๐—ฎ๐˜๐—ผ๐—ฐ๐—ถ๐—ป ๐˜†๐—ฎฦ™๐—ฎ๐—ฟ ๐˜€๐—ฎ๐˜๐—ฎ๐—ฟ ษ—๐—ฎ๐—ป๐˜†๐—ฒ๐—ป ๐—บ๐—ฎ๐—ถ ๐—ฑ๐—ฎ ๐—ถ๐—ป๐—ด๐—ฎ๐—ป๐˜๐—ฎ ๐˜๐—ฎ๐˜๐˜๐—ฎ๐—น๐—ถ๐—ป ๐—ฎ๐—ฟ๐˜‡๐—ถ๐—ธ๐—ถ๐—ป ๐—ก๐—ฎ๐—ท๐—ฒ๐—ฟ๐—ถ๐˜†๐—ฎ
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima da gwamnonin ฦ™asar sun kafa kwamatoci kan satar ษ—anyen mai da kuma na harkokin tattalin arziki.

An ษ—auki matakin ne a taron majalisar tattalin arziki ta Najeriya karo na 138 wanda aka yi ta intanet ranar Alhamis.

A cewar sanarwar da mai taimaka wa mataimakin shugaban Najeriyar kan harkokin yaษ—a labarai, Stanley Nkwocha ya fitar, kwamatocin za su kasance ฦ™arฦ™ashin shugabancin gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdurrazak da takwaransa na jihar Imo, Hope Uzodinma.

Ya ce an yi taron ne bayan tattaunawar da aka yi game da matsalolin da s**a shafi tattalin arziki da kuma nazari kan tsare-tsaren magance matsin tattalin arziki na gajere da dogon zango.

Kwamitin inganta tattalin arzikin yana da alhakin samar da tsarin kula da batun cire tallafin mai da bijiro da tsarin kare tattaunawar albashin ma'aikata da batun hauhawar farashin kayayyaki da sauran lamuran da s**a danganci tattalin arziki.

Mambobin kwamitin sun haษ—a da gwamnan jihar Gombe mai wakiltar arewa maso gabas da gwamnan Legas mai wakiltar kudu maso yamma sai gwamnan Akwa Ibom mai wakiltar kudu maso kudu da gwamnan Anambra mai wakiltar kudu masu gabas da gwamnan Neja mai wakiltar arewa ta tsakiya da gwamnan Kaduna mai wakiltar arewa maso yamma.

22/12/2023

EDUCATION ENDOWMENT FUND
Host: Shafatu Billah Ango
Guest: Sarki Nii Boi Town

๐—”๐—บ๐˜‚๐—ฟ๐—ธ๐—ฎ ๐—ป๐—ฎ ๐˜๐˜‚๐—ป๐—ฎ๐—ป๐—ถ๐—ป ๐—ฎ๐˜†๐˜†๐—ฎ๐—ป๐—ฎ ฦด๐—ฎ๐—ป ๐—›๐—ผ๐˜‚๐˜๐—ต๐—ถ ๐—ฎ ๐—บ๐—ฎ๐˜๐˜€๐—ฎ๐˜†๐—ถ๐—ป ฦด๐—ฎ๐—ป ๐˜๐—ฎ'๐—ฎ๐—ฑ๐—ฑ๐—ฎAmurka na duba yiwuwar ayyana ฦดan tawayen Houthi da ke Yemen a...
20/12/2023

๐—”๐—บ๐˜‚๐—ฟ๐—ธ๐—ฎ ๐—ป๐—ฎ ๐˜๐˜‚๐—ป๐—ฎ๐—ป๐—ถ๐—ป ๐—ฎ๐˜†๐˜†๐—ฎ๐—ป๐—ฎ ฦด๐—ฎ๐—ป ๐—›๐—ผ๐˜‚๐˜๐—ต๐—ถ ๐—ฎ ๐—บ๐—ฎ๐˜๐˜€๐—ฎ๐˜†๐—ถ๐—ป ฦด๐—ฎ๐—ป ๐˜๐—ฎ'๐—ฎ๐—ฑ๐—ฑ๐—ฎ
Amurka na duba yiwuwar ayyana ฦดan tawayen Houthi da ke Yemen a matsayin ฦดan ta'adda.

ฦณan tawayen waษ—anda ke samun goyon bayan Iran na ฦ™addamar da hare hare kan jiragen ruwan kasuwanci a tekun maliya a matsayin martani ga yaฦ™in da Isra'lla ke yi a Gaza.

Amurka ta ce za ta jagoranci wani ฦ™awance na ฦ™asa da ฦ™asa domin samar da tsaro ga harkokin sufurin jiragen ruwa a tekun.

Wakilin ya ce ฦดan Houthin sun ce ฦ™awancen da za a samar don kare harkokin jiragen ruwa a tekun maliyan mataki ne na ci gaba da ฦ™untata wa Falasdinawa.

๐—”๐—ป ๐˜€๐—ฎ๐—ฐ๐—ฒ ๐˜€๐—ฎ๐—ฟ๐—ธ๐—ถ ๐—ฑ๐—ฎ ฦ™๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐—ป ๐—บ๐˜‚๐˜๐˜‚๐—บ ๐Ÿฎ๐Ÿญ ๐—ฎ ๐—ง๐—ฎ๐—ฟ๐—ฎ๐—ฏ๐—ฎBayanai daga Taraba a Najeriya na cewa an sace mutum 21 har da sarki mai daraja ...
19/12/2023

๐—”๐—ป ๐˜€๐—ฎ๐—ฐ๐—ฒ ๐˜€๐—ฎ๐—ฟ๐—ธ๐—ถ ๐—ฑ๐—ฎ ฦ™๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐—ป ๐—บ๐˜‚๐˜๐˜‚๐—บ ๐Ÿฎ๐Ÿญ ๐—ฎ ๐—ง๐—ฎ๐—ฟ๐—ฎ๐—ฏ๐—ฎ
Bayanai daga Taraba a Najeriya na cewa an sace mutum 21 har da sarki mai daraja ta uku na al'ummar Pupule, Alhaji Umaru Nyala a ฦ™aramar hukumar Yorro da ke jihar.

Wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne s**a yi awon gaba da su bayan da s**a mamaye ฦ™auyen cikin dare inda s**a riฦ™a harbin kan mai uwa da wabi a sassa daban-daban na ฦ™auyen.

Wani shaida da ya yi hira da gidan Talabijin na Channels ya ce cikin mutum 22 da aka sace, har da wata mai juna biyu, da wasu ฦดan gida ษ—aya da kuma ษ—an sarkin da dogarin sarkin.

Wannan ne karo na uku da ake sace mutane don neman kuษ—in fansa a ฦ™auyen cikin ฦ™asa da wata shida kuma ba a taษ“a cafke waษ—anda ake zargi ba.

Shaidu sun kuma ce a yanzu, mutanen ฦ™auyen na zama cikin zullumi yayin da wasu kuma ke tserewa.

Har yanzu ฦดan sanda ba su tabbatar da faruwar lamarin ba inda s**a ce sun aike tawagar jami'ansu zuwa wajen domin gudanar da bincike.

Address


Telephone

+2348148131927

Website

https://www.instagram.com/hijrahtvghana/

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hijrah Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hijrah Tv:

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Videos
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share