AMSAD MEDIA

AMSAD MEDIA Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from AMSAD MEDIA, Media/News Company, .

*MAJALISSAR DOKOKIN JIHAR KATSINA TA TANTANCHE ALH SHUAIBU ALIYU A MATSAYIN AUDITOR GENERAL LGA NA JIHAR KATSINA*Safiyar...
23/01/2024

*MAJALISSAR DOKOKIN JIHAR KATSINA TA TANTANCHE ALH SHUAIBU ALIYU A MATSAYIN AUDITOR GENERAL LGA NA JIHAR KATSINA*
Safiyar yau Talata 23/01/2023 majalisar dokokin jihar katsina kalkashin jagoranchin Rt. Hon Nasir Yahya Daura ta tantache Alh Shuaibu Aliyu, hakan ya biyo bayan gabatar da sunansa da mai girma gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umaru Radda yayi ga zauren majalissar.
Kafin tantacheshi an karanta tarihin aikace-aikacen da Shuaibu Aliyu yayi a matakai daban-daban a jihar Katsina.
Kadan daga ciki mai bincike kudi a fannoni da dama na gwamnati, Daraktan harkokin mulki a ma'aikatar kula da Tsare -Tsare da Tattalin arziki na jihar Katsina, Shugaban Shirin Gwamnatin tarayya na NG-Cares, sannan kuma shine zabbaben shugaban kungiyar akawun kudi ta kasa reshen jihar Katsina (ANAN).
Yan uwa da abokan arziki da dama s**ayi masa rakiya don tancewa.
Amsad Media Technologies.

Babban Executive Secretary na Scholarship Board Dr Aminu Salisu Tsauri ya Jagoranci Daliban da Gobnatin jahar katsina ta...
22/01/2024

Babban Executive Secretary na Scholarship Board Dr Aminu Salisu Tsauri ya Jagoranci Daliban da Gobnatin jahar katsina ta Malam Dikko Umar Radda ta Dauki Nauyin karatun su har su (41)zuwa jami'ar Alnahda Dake Cairo Egypt don karatun Aikin jinya(Medicine)Wanda zasu tashi Ranar laraba Mai zuwa insha Allahu.

Haka Kuma Dr Aminu Salisu Tsauri ya Gabatar da yaran wajen Maigirma Gobnan jahar katsina Malam Dikko Umar Radda don tabbatar mashi cewa sun Shirya zasu bar kasar kamar yadda ya Dauki Nauyin karatun su Allah ya sakamashi da Alkhairi Ameen.

🚨🗣️Xavi Hernandez: “Akan Wasan Madrid: Idan nayi magana akan wasan sai a dakatar da ni. Kowa yaga Abinda ya faru. Tun a ...
22/01/2024

🚨🗣️Xavi Hernandez: “Akan Wasan Madrid: Idan nayi magana akan wasan sai a dakatar da ni. Kowa yaga Abinda ya faru. Tun a wasanmu da Getafe, na fahimci abubuwa basa tafiya daidai. Abune mai mutukar wahala mu lashe League din.”

Domin “Inda ace Alkalan wasa nayin adalci, da a yanzu muna saman table da tazarar maki 6. Da tuni mun doke Getafe, fenareti mai kyau a karawarmu da Vallecano Amma babu wanda yace a duba, da kuma kwallon Joao Felix a karawarmu da Granada.. ba zamu iya yin komai ba, saidai mu cigaba da dagewa. In ji Kocin Barcelona Xavi,

Ya kuke Ganin Kalaman Xavi Anya Babu Kanshin Gaskiya a Ciki Kuwa...👀

The 72-year-old bookseller, Mohamed Aziz, located in Rabat, Morocco, spends 6 to 8 hours a day reading books. Having rea...
22/01/2024

The 72-year-old bookseller, Mohamed Aziz, located in Rabat, Morocco, spends 6 to 8 hours a day reading books. Having read over 5000 books in French, Arabic, and English, he remains the oldest bookseller in Rabat after more than 43 years in the same location. When asked about leaving his books unattended outside, where they could potentially be stolen, he responded that those who can't read don't steal books, and those who can, aren't thieves.

ZAMU INGANTTA HARKAR ILIMIN A JIHAR KATSINA..... GOV. DIKKO RADDA PHD.
22/01/2024

ZAMU INGANTTA HARKAR ILIMIN A JIHAR KATSINA.....
GOV. DIKKO RADDA PHD.

Indiyawa a Zamfara? 👩‍❤️‍👨 Ma’auratan da s**a karaɗe shafukan sada zumunta saboda bikin Indiyawa da s**a yi a jihar Zamf...
22/01/2024

Indiyawa a Zamfara? 👩‍❤️‍👨

Ma’auratan da s**a karaɗe shafukan sada zumunta saboda bikin Indiyawa da s**a yi a jihar Zamfara sun bayyana wa BBC dalilinsu na yin hakan.

Dangote prepares young Nigerian engineers to take over management of refinery at completion.
22/01/2024

Dangote prepares young Nigerian engineers to take over management of refinery at completion.

APC Fingers Kwankwasiyya As Groups Call For Ganduje’s Sack.
22/01/2024

APC Fingers Kwankwasiyya As Groups Call For Ganduje’s Sack.

Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya kaddamar sabon jirgin saman Rano Air wanda zai rika jigilar al’umma daga Katsina zuwa ...
21/01/2024

Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya kaddamar sabon jirgin saman Rano Air wanda
zai rika jigilar al’umma daga Katsina zuwa Abuja

Cikin matukar farin ciki, Gwamna Radda ya kaddamar da jirgin kai tsaye a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina da yammacin ranar Lahadi, 21 ga watan Janairu 2024, inda ya jaddada kudirinsa na bude hanyoyin zuba jari da kuma inganta kasuwanci a Jihar Katsina.

A jawabinsa yayin kaddamar da jirgin, gwamnan ya bukaci mazauna jihar Katsina da masu sha’awar zuwa jihar da su yi amfani da wannan sabon tsarin sufuri, wanda a cewar shi wannan wani gagarumin ci gaba ne a harkar sufurin jihar.

Gwamnatin jihar Katsina za ta hada kai da gidauniyar Qatar Foundation domin gudanar da wasu muhimmin ayyukan gina al’umm...
19/01/2024

Gwamnatin jihar Katsina za ta hada kai da gidauniyar Qatar Foundation domin gudanar da wasu muhimmin ayyukan gina al’umma a Katsina

A wata ziyarar aiki a ofishin Qatar Charity Foundation da ke Abuja, Maigirma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya samu kyakkyawar tarba daga Daraktan Kasa, Hamdi El-Sayid Abdou a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu 2024.

Qatar Charity shahararriyar kungiyar agaji ce ta kasa da kasa wacce ke gudanar da ayyukanta a kasashe daban-daban ciki har da Najeriya. Ayyukan nasu sun maida hankali ne kan muhimman fannoni kamar ilimi, kiwon lafiya, ruwa da tsaftar muhalli, kawar da fatara, da ba da agajin gaggawa.

A yayin ziyarar, Gwamna Radda ya bayyana matukar jin dadinsa da wannan gagarumin taimako da jin kai da gidauniyar Qatar Charity Foundation ta ke yi a jihar Katsina. Ya kuma yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya wajen sabunta yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu.

Bugu da kari, Gwamna Radda ya bayyana bukatar gidauniyar Qatar ta ci gaba da tallafa wa jihar Katsina, musamman a kan aikin samar da gidaje ga yan gudun hijira wanda lamarin yan ta’adda ya sa dubban mutane s**a rasa gidajensu.

Gwamna Radda ya bada tabbacin jajircewar sa da tallafawa ayyukan gidauniyar a duk lokacin da ake bukata.

Maimartaba Sarkin Zamfaran Anka ya Aminta da baiwa Gwamna Dauda Lawal na Zamfara Sarautar (Gamjin Zamfara)....
19/01/2024

Maimartaba Sarkin Zamfaran Anka ya Aminta da baiwa Gwamna Dauda Lawal na Zamfara Sarautar (Gamjin Zamfara)....

RASHIN TSARO: GWAMNAN ZAMFARA YA HANA SARAKUNA BAYAR DA TAKARDAR IZINI DON HAƘAR MA'ADINAIGwamnan jihar Zamfara, Dauda L...
19/01/2024

RASHIN TSARO: GWAMNAN ZAMFARA YA HANA SARAKUNA BAYAR DA TAKARDAR IZINI DON HAƘAR MA'ADINAI

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanya hannu kan wata doka da ta haramta wa sarakunan gargajiya bayar da takardar amincewa don hakar ma’adanai a fadin jihar.

A ranar Alhamis ne aka rattaba hannu kan dokar zartarwa a zauren majalisar, gidan gwamnati, Gusau.

A wata sanarwa da kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, an sanya hannu kan dokar zartaswar ne domin dakatar da daya daga cikin munanan halaye na yaki da ‘yan fashi.

A cewarsa, odar ta haramta duk wasu wasiƙun neman izinin hakar ma'adinai. "Wannan ya haɗa da wasiƙun yarda ga mutane, kamfanoni, ko ƙungiyoyi don ayyukan hakar ma'adinai."

A nasa jawabin, yayin da yake sanya hannu a kan wannan umarni, Gwamna Lawal ya sake nanata cewa an yanke wannan shawarar ne saboda munanan hadurran da ke tattare da yawaitar fitar da wasikun amincewa.

Ya ce: “A yau, a kudurin gwamnatina na magance matsalar rashin tsaro, na sanya hannu kan wata doka da ta haramta wa sarakunan gargajiya bayar da wasikun neman hako ma’adanai a fadin kananan hukumomi 14 na jihar Zamfara.

“Kamar yadda kwamishinan shari’a ya bayyana, an gano ayyukan hakar ma’adanai a Zamfara a matsayin wani muhimmin al’amari da ke kawo tabarbarewar tsaro a jihar, musamman matsalar ‘yan fashi.

“A matsayinmu na gwamnati mai alhaki, yana da matukar muhimmanci mu dauki kwakkwaran matakai don magance matsalar hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba da ke haifar da rikicin. Shi ya sa na rattaba hannu kan dokar zartarwa. Muna ɗaukar duk matakan da s**a dace don gyara matsalolin da ke tattare da ba da wasiƙun amincewa da hakar ma'adinai a fadin jihar mu.

"Muna rokon Allah madaukakin sarki da ya yimuna jagora a cikin wannan aiki na kare rayuka da dukiyoyin al'umma."

BA ZAN  LAMUNCI RASHAWA BA, GWAMNAN ZAMFARA YA GARGAƊI JAMI'AN GWAMNATINSAGwamna Dauda Lawal ya ce gwamnatinsa ba za ta ...
19/01/2024

BA ZAN LAMUNCI RASHAWA BA, GWAMNAN ZAMFARA YA GARGAƊI JAMI'AN GWAMNATINSA

Gwamna Dauda Lawal ya ce gwamnatinsa ba za ta aminta da duk wani nau'i na cin hanci da rashawa ko rashin tausayi daga mambobin majalisarsa ko ma'aikatan gwamnati a jihar Zamfara ba.

A ranar Alhamis ne gwamnan ya jagoranci zaman majalisar zartarwa na musamman a zauren majalisar da ke gidan gwamnati a Gusau babban birnin jiha.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce zaman majalisar na yau shine taron majalisar na farko na gwamnatin Zamfara a shekarar 2024.

Ya kara da cewa Gwamna Dauda Lawal ya bukaci dukkan masu manyan mukamai, kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman da su fahimci manufar sa tare da yin gyare-gyaren da s**a dace.

A cewar sa: Zuwa ga Kwamishinoninmu, Shugabannin Hukumomi da Ma'aikatunmu, ku ne Manyan Jami'an Gudanarwa a cikin ma'aikatun ku. Ba ku kaɗai ba ne masu gudanarwa. An nada ku don samar da ingantaccen jagoranci, ba don bayar da kwangila ko raba kayan aiki, sai don ci gaban jama'a da al'ummominmu.

“Ku ba ’yan kwangila ba ne ko masu kawo kayan aiki, ku bayin mutane ne. Dole ne ku cire tunanin ku na daidaiku, ku tabbatar da cewa an nada ku ne don hidimtawa jama'a ta hanyar samar da abubuwan more rayuwa da za su tallafa wa rayuwarsu.

“Dole ne mu kawo chanjin da ake bukata domin ciyar da jihar a gaba.

“Mutanen jihar nan ba sun zabe mu bane don kawai mu maye gurbin fuskoki da halayen wadanda s**a gabace mu. An zabe mu ne don mu chanza yadda ake gudanar da harkokin gwamnati, ta hanyar kawo sauye sauye da zasu chanza jihar zuwa matsayi na ci gaba.”

Gwamnan ya kara jaddadawa majalisar cewa ba yazo wannan mulki don neman kudi ba.

“Game da haka, ina gaya muku wannan a yau: Ba zan yarda da duk wani aiki na cin hanci da rashawa da rashin tausayi daga kowane mukami ko ma’aikacin gwamnati ba. Na sha cewa ban zo nan don neman kudi ba, kuma duk wanda ke da burin arzuta kansa gara ya chanza shawara ko kuma yayi murabus daga aiki

A yau, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda PhD, ya samu bakuncin Darakta Janar/ Shugaban Hukumar Bunkasa Kana...
18/01/2024

A yau, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda PhD, ya samu bakuncin Darakta Janar/ Shugaban Hukumar Bunkasa Kanana da Matsakaitan Masana’antu ta Najeriya, SMEDAN, Charles Odii, a Katsina Governors Lodge da ke Abuja.

Tattaunawar da aka yi a tsakanin su ta ta’allaka ne kan hanyoyi daban-daban na inganta da kuma taimaka wa kanana da matsakaitan masana’antu a jihar Katsina. Gwamna Radda ya bayyana aniyar sa na samar da yanayi mai kyau tare da ci gaba da bayar da gudunmawar ga kananan masana’antu wajen ci gaban tattalin arzikin jihar.

Darakta Janar Odii ya yaba wa kokarin gwamnan, ya kuma sha alwashin bayar da hadin kai ga gwamnatin jihar wajen aiwatar da tsare-tsare masu inganci don bunkasa harkokin kanana da matsakaitan masana’antu.
AMSAD MEDIA
18/01/2024

But the fact in our favour is that nothing was done under the veil of secrecy. We were as transparent and accountable as...
18/01/2024

But the fact in our favour is that nothing was done under the veil of secrecy. We were as transparent and accountable as possible, being aware of the fact that posterity was the ultimate judge. We kept records of our stewardship, knowing that we would always be required to account for the trust entrusted to us.

"But the fact in our favour is that nothing was done under the veil of secrecy. We were as transparent and accountable as possible, being aware of the fact that posterity was the ultimate judge."

Gayyata daga Dr. Tukur Hassan Tigilin MD Water Board Katsina State.
17/01/2024

Gayyata daga Dr. Tukur Hassan Tigilin MD Water Board Katsina State.

KATSACA 2024 PROJECT KATSACA under the Leadership or it"s Executive Secretary Dr Bala Nuhu (Sadaukin Kankia) in Collabor...
17/01/2024

KATSACA 2024 PROJECT

KATSACA under the Leadership or it"s Executive Secretary Dr Bala Nuhu (Sadaukin Kankia) in Collaboration with SPHCA and UNICEF trained 34 Mentor Mothers, 34 LGA Health Educators, 12 UNICEF LGAFs and 235 Village Word Supervisors (VWS) on HIV Awareness, Benefits of Antinatal Care, HIV Counselling & Testing to Pregnant Womem as well as Communication for Development (CD4) in the Context of HIV/AIDS in order to Scale Up PMTCT Services across the State.

The training was conducted in the three Senatorial Zones of Katsina State (Katsina, Daura and Funtua Zones) and sponsored by UNICEF. In attendance are State Health Promotion Officer (SHPO) from SPHCA, UNICEF Consultants and Directors from KATSACA that serves as Facilitators.

Dandazon Al-Umma Magoya bayan Sabon Director General(DG)na ma'aikatar Katsina State Erosion and watershed management Age...
17/01/2024

Dandazon Al-Umma Magoya bayan Sabon Director General(DG)na ma'aikatar Katsina State Erosion and watershed management Agency(KEWMA)Hon Alh Mannir Ayuba Sullubawa sun raka shi zuwa office bisa mukamin da Maigirma Gobnan jahar katsina Dr Dikko Umar Radda ya bashi inda s**a yi ta Adua da fatan Alkhairi Allah ya taya shi Riko Ameen.

Reported:
AMSAD MEDIA TECHNOLOGIES.

Yau saura kwanaki 3 a rantsar da zauren majalissa ta 9 a Najeriya, wane fata kuke dashi ga wannan zauren majalissar?
10/06/2023

Yau saura kwanaki 3 a rantsar da zauren majalissa ta 9 a Najeriya, wane fata kuke dashi ga wannan zauren majalissar?

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AMSAD MEDIA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share