IZZAH TV

IZZAH TV Izzah Tv our channel is on YouTube, please search,like, subscribe and share our videos for the benefit of other.

Aliko Dangote has reclaimed the title of the wealthiest person in Africa, as per Forbes Real-Time Billionaires. Previous...
11/01/2024

Aliko Dangote has reclaimed the title of the wealthiest person in Africa, as per Forbes Real-Time Billionaires. Previously, on January 4, The Nation reported that South African business magnate Johann Rupert had surpassed Nigerian Aliko Dangote as Africa's richest individual. However, according to the Forbes Daily billionaires ranking platform, Dangote's net worth increased by $10 million, reaching $10.1 billion as of January 8, 2024, allowing him to surpass Johann Rupert, whose net worth on the same date was $10 billion, down from $10.7 billion on January 30, 2023.

On the Forbes list, Dangote now holds the 191st position globally, while Rupert is ranked 197th. Additionally, Dangote maintains his status as Africa's richest person according to the Bloomberg Billionaire Index.

Bloomberg notes that a significant portion of Dangote's wealth is derived from his 86 percent stake in the publicly traded Dangote Cement. He owns these shares directly and through his conglomerate, Dangote Industries. Dangote also holds stakes in other publicly traded companies like Dangote Sugar, NASCON Allied Industries, and United Bank for Africa. Furthermore, Dangote Industries owns various closely held businesses in food manufacturing, fertilizer, oil, and other sectors. Among these holdings, a fertiliser plant with a capacity to produce up to 2.8 million tonnes of urea annually is highlighted as his most valuable closely held asset. The valuation is based on a discounted cash flow analysis by KPMG and confirmed by external analysts. Dangote's cash holdings are assessed through an analysis of dividends, taxes, insider transactions, and other expenditures.

Daga yau Litinin 01/10/2023 buhun Simintin BUA ya koma N3,500Shugaban kamfanin BUA ya cika alkawarin daya dauka akan rag...
02/10/2023

Daga yau Litinin 01/10/2023 buhun Simintin BUA ya koma N3,500

Shugaban kamfanin BUA ya cika alkawarin daya dauka akan rage farashin simintin kamfanin daga 5,500 zuwa 3,500 daga yau dokar zata fara aiki .

Allah ya tabbatar da alheri.

KABILANCI: AI BAKU GA KOMAI BAOfishin shugaban matasan jam'iyyar mu na APC ya fitar da sunayen matasan Nigeria daga aka ...
12/09/2022

KABILANCI: AI BAKU GA KOMAI BA

Ofishin shugaban matasan jam'iyyar mu na APC ya fitar da sunayen matasan Nigeria daga aka diba domin su yiwa Tinubu kamfen a media

To idan kuka tsaya kuka dubi sunayen list na matasan Nigeria da aka zaba, an yiwa yankin Arewacin Nigeria muguwar illa, an nuna zunzurutun kabilanci da wariya wa matasan Arewa da suke media, kusan Yarbawa ne zalla aka diba saboda aiki ne da za'a biya kudi makudai

To wannan ma kadan ne daga cikin abinda muke ankarar daku akan mulkin kabilanci da za'a mana idan muka yadda Tinubu ya kafa Gwamnati.

Allah Ya mana zabi mafi alheri

Daga datti assalafy 🙌

ABACHA BA BARAWO BA NE, GWARZON SHUGABA NE, KUMA JARUMI: Dr. BunkureDa yawa daga cikin Yan Nigeria an sanya musu a zuciy...
10/09/2022

ABACHA BA BARAWO BA NE, GWARZON SHUGABA NE, KUMA JARUMI:

Dr. Bunkure

Da yawa daga cikin Yan Nigeria an sanya musu a zuciyar su cewa Tsohon Shugaban Nigeria Marigayi Gen. Sani Abacha Barawo ne.

Wannan Tunani ne da wasu daga cikin Manyan Jagororin Nigeria tare da hadin Gwuiwar wasu Manyan Kasashen Gabas s**a kirkira domin cimma Bukatun su na Siyasa ko kuma Tattalin Arzuki.

Irin wadannan Jagorori da babu abunda suke a kullum banda kokarin kawo cikas ga cigaban Nigeria da zaman lafiyar Kasar sune kan gaba wajen kiran Abacha da sunan Barawa tare da taimakon wasu Kafafan Sadarwar da suke yada abun don Kabilanci.

Marigayi Gen. Sani Abacha yana daga cikin Shugabannin Nigeria wanda Kasar ba zata taba mantawa da Alkairan su ba.

Abacha Jagora ne wanda irinsa ne Kasar take bukata domin inganta lamuranta gida da waje domin shine shugaban da ya dora Nigeria akan Hanyar da Kasar zata Bunkasa.

Abacha ya inganta Tattalin Arzukin Nigeria wanda kusan babu ana iya cewa babu wani Shugaba da yayi irinsa a Tarihin Nigeria.

Daga Shekarar 1993 zuwa Tsakiyar 1997 Abacha ya daga Asusun ajiyar Nigeria na Ketare daga Dalar Amurka Miliyan 494 zuwa Dala Biliyan 9.6, ya rubanya shi da kusan kaso 90%.

Har ila yau Abacha ne shugaban da ya rage yawan Bas**an da Kasashen Waje ke bin Nigeria daga Dalar Amurka Biliyan 36 zuwa Dala Biliyan 27 abunda ya kara tayar da hankulan Kasashen Gabas domin ganin cewa Abacha ya hau layin Yantar da Nigeria ne daga Mulkin Malakarsu.

Abacha ya rage yawan hauhawar Farashi a Nigeria daga kaso 54% da ya gada daga Tsohon Shugaba Ernest Shonekan zwa 8.5% tsakanin 1993 - 1998.

Baya ga haka, Abacha ya samar da Tituna masu tsahon 25-109 KM a mafiyawancin Biranan Nigeria irin su Zaria, Kano, Enugu, Benin, Gusau, Funtua, Kaduna, Port Harcourt, Lagos, Lakoja da sauran su.

Abacha ne ya samar da Hukumar PTF wacce ta samar da manyan ayyukan cigaba a fadin Nigeria Lungu da Sako na Kasar wanda har ya zuwa yanzu Yan Nigeria na amfana da ayyukan wannan Hukuma wacce Abacha ya nada Shugaban Nigeria Muhammad Buhari domin ya Jagoranta.

Irin wannan ayyuka da Abacha ya kewa Nigeria ne ya sanya Kasashen Gabas yin gaba da shi tare da kokarin ganin bayansa ta hanyoyi daban-daban wanda ya hada da taimakon wasu marasa kishin Nigeria.

Anyi amfani da wasu Jaridu masu kokarin yada Kabilanci domin bata sunan Abacha wanda wasu lalatattun Shugabanin Nigeria ke daukar nauyi.

Hakik rashin karanta tarishi na daya daga cikin babban matsalar mu a yau.

Allah ya jiqan Abacha yayi Rahma gare shi, Amin.

:
Major Hamza Almustapha Network

AN TSINCI GAWAR MUTUMIN DAYA SHEKARA HUDU A DAKINSA KULLE A  IBADANMazauna unguwar Apete dake Ibadan na cikin zullumi tu...
09/09/2022

AN TSINCI GAWAR MUTUMIN DAYA SHEKARA HUDU A DAKINSA KULLE A IBADAN

Mazauna unguwar Apete dake Ibadan na cikin zullumi tun bayan da aka samu kwarangwal din wani mutum, bayan ya shafe shekaru hudu kulle a Dakinsa batareda sanin kowa ba.

Ana tunanin cewa kwarangwal din gawar (wanda ba a bayyana sunansa ba) An samu rahoton tane daga makwabta bayan shafe shekaru hudu batareda sunga anshiga ko an fito daga gidan ba.

Mutumin wanda yake mazaunin jihohi biyu ne wato Rivers da Oyo yakan zo garin na Ibadan ne lokaci zuwa lokaci inda ya ke sauka a gidan sa wanda shi kadai ne ke cikin.

Har a lokacin hada wannan rahoton ba a samu wani bayani game da abunda ya haddasa wannan kwarangwal din gawar ba.

Amma Mazauna unguwar sun shaida wa manema labarai cewa,babu wani dan unguwar daya san da faruwar lamarin har sai wannan satin,a lokacin da jama'a s**a yanke shawarar shiga gidan domin cire ganyayyaki da ciyawun da s**ayi yawa har sun fara haddasa macizai a layin.

Bayan an gama jinga ko ciniki da mutanen da zasuyi aikin cire ciyawar gidan,inda s**a haura ta katanga tunda gate din gidan kulle yake.

Bayan sun haurane s**aga Ashe motar maigidan tana nan har ganyayyaki da ciyawu sun lullubeta.

A cewar wadanda s**a gani da ido, bayan anyi kokarin cire ganyayyakin ne aka leka ta taga inda s**aga kwarangwal din mutum kwance bisa gado rike da waya a hannunsa.

Jami'an yan sanda na jihar oyo suna cigaba da bincike akan lamarin.

19/06/2022

YANDA ZAKA HARDACE ALQUR'ANI CIKIN SAUƘI || SHAIKH OKASHA KAMENY.

Kada ku manta kuyi mana subscribe (IZZAH TV) KU danna ƙararrawa domin samun sabbin bidiyoyi, sannan kuyi share domin Wasu su amfana.

18/06/2022

Mushaƙata da Alqur'ani mai Girma || Alaramma Kabir Abdurrashid Kuringafa

Address


Telephone

+2349022848638

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when IZZAH TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share