Fagen Labarai

  • Home
  • Fagen Labarai

Fagen Labarai Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Fagen Labarai, Media/News Company, .

Dalibin makaranta a Ogun ya kashe kansa bayan ya kashe kuɗin makarantarsa a wajen c**aWani dalibin Kwalejin Kimiyya da F...
25/05/2023

Dalibin makaranta a Ogun ya kashe kansa bayan ya kashe kuɗin makarantarsa a wajen c**a

Wani dalibin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Ilaro a Jihar Ogun, Samuel Adegoke, ya kashe kansa ta hanyar shan wani abu da ake zargin maganin kwari ne.

An ce marigayin ya kashe kansa ne bayan da ya yi kashe kudin makarantarsa ​​da na abokinsa a wata c**a ta yanar gizo.

rahotanni sun bayyana cewa Adegoke, wanda dalibin Difloma ne a fannin Electrical Electronic Engineering, ya kashe kansa ne a ranar Litinin a lokacin da abokan aikinsa ke shirin jarabawar kammala zango na farko.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa marigayin ya yi amfani da kudin makarantarsa ​​ne wajen yin c**a ta yanar gizo a ranar Juma’a kuma ya yi rashin nasara a car.

Ya kuma yaudari abokinsa don samun kalmar sirri, ya kuma shiga manhajar wayar abokin, sannan ya kwashe masa kudin asusu ya yi c**a da su sannan aka kuma cinye shi.

Mataimakin rijistara na makarantar, ɓangaren hulda da jama’a, Sola Abiala, ya tabbatar wa da jaridar faruwa lamarin.

Ƴansandan Ghana sun k**a ƴan Nijeriya 49 bisa zargin safarar mutaneƳansanda a Ghana sun k**a wasu 'yan Najeriya 49 bisa ...
25/05/2023

Ƴansandan Ghana sun k**a ƴan Nijeriya 49 bisa zargin safarar mutane

Ƴansanda a Ghana sun k**a wasu 'yan Najeriya 49 bisa zargin su da aikaita laifin safarar mutane da kuma laifukan da ake yi ta intanet.

BBC ta rawaito cewa wadanda ake zargin da s**a hada da maza 47 da mata biyu an damke su ne a birnin Accra sak**akon rahotonnin leken asiri da aka samu,

'Yan sanda sun yi bayanin cewa guda 45 daga cikinsu wadanda ke tsakanin shekara 18 zuwa 34 da haihuwa an yi safararsu ne zuwa Ghana bayan an yi masu alkawarin aiki kafin aka jefa su cikin aikata laifukan intanet.

Sun kara da cewa an riga an dawo da su Najeriya, ana kuma shirin gurfanar da sauran mutane hudun da ake zargin su ne shugabannin kungiyar a kotu.

Jami'an tsaro sun ce sun samu na'urorin kwamfuta guda 70, da motoci guda biyu, da wayoyin hannu guda 51 a lokacin da s**a kai samame gidan wadanda a ke zargin.

Hukumonmi a kudancin kasar sun kai samame irin wannan a wasu bangarorin kasar domin ceto 'yan kasashen waje da dama da ake tsare da su a gidaje daban daban.

Na yafe wa Buhari bisa maida Nijeriya baya da ya yiGwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu ...
25/05/2023

Na yafe wa Buhari bisa maida Nijeriya baya da ya yi

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta maida Najeriya daga sama zuwa kasa, amma ya yafewa shugaban kasar.

Ortom, wanda zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu a ranar 29 ga Mayu, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a jiya Laraba.

Da ya ke bada hujja daga littafin Bible, ya ce: “Idan ba kwa yafiya, to hakan yana nufin Allah ma ba zai gafarta muku ba. A matsayina na dalibin Littafi Mai Tsarki kuma a matsayina na Kirista na gari, na gafarta wa shugaban kasa Muhammadu Buhari.”

Ortom ya kuma bayyana fatansa na samun kyakkyawan shugabanci daga gwamnatin zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.

"Muna fatan gwamnati mai zuwa za ta ba da tallafi, taimako, tsaro, bunkasa tattalin arziki, da zaman lafiya ga jama'armu," in ji shi.

Sai dai ya shawarci Buhari da kada ya fice daga Najeriya, amma ya koma ya yi aiki da gwamnatin Tinubu domin daga likkafar kasar daga “kasa zuwa sama”.

“Ba ya bukatar ya je Jamhuriyar Nijar. Ya zauna a nan (a Najeriya) tare da mu. Mu yi aiki da gwamnati mai zuwa kuma da yardar Allah za mu tashi daga kasa zuwa sama,” inji gwamnan.

HOTUNA: Yadda ɗaliban jam'a mallakar jihar Taraba (Taraba State University) s**a gudanar da shagalin 'ranar tsumma' wato...
25/05/2023

HOTUNA: Yadda ɗaliban jam'a mallakar jihar Taraba (Taraba State University) s**a gudanar da shagalin 'ranar tsumma' wato Rag Day.

Me zaku ce akan wannan shagali?

Daga Abba Ibrahim

DA DUMI-DUMIN SU!Ku gaggauta kawo karshen y@n ta'add@ ko kuma in sauke ku--Gargadin shugaban kasa Muhammad Buhari ga huk...
25/07/2022

DA DUMI-DUMIN SU!

Ku gaggauta kawo karshen y@n ta'add@ ko kuma in sauke ku--Gargadin shugaban kasa Muhammad Buhari ga hukumomin tsaron Najeriya

Shugaban kasa Muhammad Buhari ta bakin Malam Garba Shehu ya gargadi shugabannin tsaro na kasa da su gaggauta kawo karshen yan ta'add@ ko kuma su yi murabus.

Buhari ya yi wannan kira ne a lokacin da ya yi wa tsohon shugaban jam'iyyar PDP Adamu Mu'azu ta'aziyya kan kisan dan uwan sa tare da sace yar uwar sa.

Shin ya kuke kallon wannan kira na shugaban kasa ne ga hukumomin tsaro?

Menene ra'ayoyinku

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kamfanin mai na kasar wanda aka sauya wa fasali, inda a yanzu ka...
19/07/2022

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kamfanin mai na kasar wanda aka sauya wa fasali, inda a yanzu kamfanin na NNPC ya koma wani kamfanin kasuwanci mai zaman kansa

An yi kaddamarwar ne a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar a Abuja babban birnin kasar ranar Talata.

Shugaba Buhari ya fara ne da gode wa mahartar taron, wanda ya kira shi da ''mai dimbin tarihi''.

A jawabin da ya gabatar a wurin taron, Shugaba Buhari ya ce an mayar da ikon gudanar da kamfanin ga 'yan kasuwa ne, saboda inganta shi, don samar wa kasar makashin da take bukata.

Ya kuma kara da cewa ''daga yanzu kamfanin NNPC ya koma karkashin gudanarwar 'yan kasuwa, zai kasance kamfani mai zaman kansa ta yadda zai yi gogayya da takwarorinsa a fadin duniya, domin ci gaba da bunkasa hannayen jari sama da miliyan 200 tare da habaka fannin makashi a fadin duniya''.

''A yanzu doka ta dora wa kamfanin alhakin tabbatar da samar wa Najeriya wadataccen makashin da take bukata domin samun habakar tattalin arzikin ta hanyar farfado da wasu fannonin da ke bukatar makashin," in ji Shugaban na Najeriya.

ABIN JINDADI ABIN SHA,AWA: Alh. Ahmad Idris tsohon Akanta Janar na Najeriya tare da matasan ƴan jihar Kano da ya samawa ...
17/07/2022

ABIN JINDADI ABIN SHA,AWA:
Alh. Ahmad Idris tsohon Akanta Janar na Najeriya tare da matasan ƴan jihar Kano da ya samawa aikin ɗamara, Kuma an ce dukkanin su ba dangin iya ba na Baba.

Tabbas ya yi ƙoƙarin sosai domin irin su aka rasa a cikin al'umma, Allah Ta'ala ya saka masa da alkairi ya ƙaro mana irin su.

Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Ademola Adeleke ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.Adeleke ya samu ...
17/07/2022

Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Ademola Adeleke ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.

Adeleke ya samu kuri’u 403, 371 wajen lallasa babban abokin hamayyarsa Gboyega Oyetola na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 375,027.

Labari da dumi dumi!Sanata Ademola Adeleke na Jam'iyyar PDP na lashe zaben Gwamnan Jihar Osun da aka gudanar ranar asaba...
17/07/2022

Labari da dumi dumi!

Sanata Ademola Adeleke na Jam'iyyar PDP na lashe zaben Gwamnan Jihar Osun da aka gudanar ranar asabar 16/07/2022.

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fagen Labarai posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share