11/01/2024
Jiya Laraba babban bankin Najeriya CBN ya dakatar da Management da kuma Board of Directors na Bankin Union Bank, Polaris Bank da Keystone Bank, sannan a jiya din CBN ya sake nada sabbin Board of Directors da Management na bankunan.
~ CBN yace an dakatar dasu ne saboda rashin cika ka'idar lasisin da aka basu da kuma aikata laifukan da s**a sabawa dokokin Bankuna da na kasa gaba, tare kuma da wasu laifuka.
Sai dai, a hakikanin abinda ya faru shine, a watan July na 2023 data gabata shugaba Tinubu ya nada Dr. Jim Obazee a matsayin wanda zai binciki badakalar da tsohon shugaban Babban Bankin kasa Godwin Emefiele ya aikata.
~ Sati Uku da s**a wuce Dr. Jim Obazee ya mika rahoton sa wa shugaban kasa Tinubu, a cikin rahoton ya bayyana cewa binciken sa ya gano cewa Godwin Emefiele ya mallaki Bankuna uku ta bayan gida, cikin sirri ta hannun wasu mutane shida. Bankuna ukun sune Keystone, Polaris da Union.
Sannan yayi amfani da Kudin sata ya kafa wani Banki me suna Titan Trust Bank (TTB).
~ Dr. Jim Obazee ya sake bayyanawa a cikin rahoton sa cewa sun gano cewa Godwin Emefiele ya mallaki Keystone da Union ne, yayin da yake jibge kudaden satan a Polaris Bank ta hannun wasu Kamfanonin 'kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE, ko (United Arab Emirates) guda biyu.
Jim Obazee ya nemi EFCC, DSS, wasu tsofaffi 'yan sanda, Lauyoyi, tsofaffin Sojoji wajen taya shi wannan aiki.
Bayan Dr. Jim Obazee ya kammala aiki ya aike su ga shugaba Tinubu sati Uku da s**a wuce, shi kuma ya karanta report din sannan aka bayar da umarni wa CBN ya dakatar da shugabannin gudanarwar Keystone, Polaris da Union Banks.