26/10/2022
Nakan yi mamakin wasu daga cikin mutanen mu da suke cikin lamarin crypto, kasancewar basu iya jure wahalhalun da ake yi a crypto, suyi ta korafi da surutu akan Coin kaza ya sauka, Coin kaza ya fadi, 'korafin da ake yi akan RENEC har yanzu fa RENEC bai Kai sati 'daya da budewa ba Amma mutane sai magana suke yi, RENEC yana sauka fa, yaya za muyi?
~ Idan naga haka nakan dauka sababbin 'yan crypto ne, wallahi wallahi coins da na saya shekaru kusan uku da s**a har yanzu faduwa suke ban, ban samu Uwar kudina ba b***e riba, a 2019 na saya Pundix, kafin ayi Redonomination dinsa, har yau Ina rike dashi.
~ A farkon 2021 na sayi Free Coin akan Probit Exchange har yau ban samu Riba akai ba, Wink (WIN) yau shekara daya da rabi bata dawo da kudin ba b***e riba, a 2020 na Saya Dent a Binance, har yanzu a kasa yake, a April 2021 na saya Safemoon muna neman Shekara daya da rabi yanzu ba riba, wadannan duk basu dame ni ba wallahi, saboda Ina da tabbacin za'a lokacin da zasu 'daga sosai.
~ Mutanen mu suna son yin kudi da gaggawa ne kawai, ba haka sunnar rayuwa take ba, dole kayi hakuri ka cigaba da jajircewa.
~ B***e RENEC din da duk bai wuce kwana biyar ba, Kuma har yanzu basu zuba masa Liquidity din da s**a ce zasu zuba masa ba, idan kaje ka dauki Supply na liquidity din da aka ce za'a saka ka lissafa shi da circulating supply RENEC sai ya haura Dala dari biyu 70 ($270), Remitano basu zuba komai wa RENEC ba, mutane ne suke zuba masa Liquidity yanzu haka a tsarin AMM (Automated Market Maker).
~ Kasan Dala Miliyan nawa s**a kashe s**a yi Coin din, nawa s**a kashe s**a yi Blockchain din? duk yadda kake so ka samu kudi da RENEC wallahi sun fika, aiki suke yi dare da rana akan network dinsu.
~ Network ake ta kaiwa Exchangers din da za suyi listing RENEC, wallahi idan aka Kai RENEC Coin Base kawai da wahala ka iya Sayan sa Kai talakan Nigeria, haba Jama'a mu dinga hakuri mana.
Yanzu idan kaji Shirin da ake yi masa zaka ce gara ya Kara yin kasa domin ka kwasa da yawa.