01/12/2022
TSAKANIN SHUGABA BUHARI DA GWAMNONI WAYE MAI GASKIYA?
Maigirma Shugaban Kasar 'yan Nigeria masu sharholiya Muhammad Buhari ya zargi Gwamnonin Nigeria da jefa talakawan Nigeria cikin mawuyacin hali
Shugaba Buhari yace Gwamnonin suna sace kason dukiyar kananan hukumomin Nigeria inda mafi akasarin talakawa suke, hakan ya jefa rayukansu cikin mawuyacin hali, inji Baba Buhari
To sai mu duba mu gani👇👇
Ina tuna wani lokaci da Maigirma Shugaban Kasa ya gabatar da kuduri ga Majalisar dokoki na kasa akan abu guda biyu zuwa uku:-
Na farko: Tsame hannun Gwamnoni daga shiga lamarin Kotunan jiha
Na biyu: Samarwa Kananan hukumomi asusun banki daga tarayya, ta yadda daga Federal za'a ke tura musu kudin bajet
Na uku: Haramtawa Gwamnoni iko akan Shugabannin kananan hukumomi
Amma bana tunanin cikin wannan kuduri da Buhari ya kai gaban majalisa yayi tsayuwar daka wajen ganin sun tabbata, maciya amana sun sa shi ya shashantar da abin, wanda da ace yayi hakan shikenan ya samawa Kananan hukumomi 'yanci, talakawa zasu amfana, don haka anan zamuce laifin maciya amana ne ko laifin Baba Buhari
Abinda ya sake jefa rayukan talakawan Nigeria da suke rayuwa a kananan hukumomi cikin mawuyacin hali musamman a yankin Arewa maso yamma shine rashin tsaro, da fitinar garkuwa da mutane, an gaza wajen samar da tsaro, talaka baya iya noma sai ya biya 'yan ta'adda kudin haraji, wasu kauyukan noman ya gagara, tsakani da Allah Gwamnatin tarayya ita ke da alhakkin samar da tsaro da kawar da ta'addanci ba Gwamnoni ba, kowa ya san mai laifi anan
Daga cikin abinda ya jefa rayukan talakawan Arewa cikin tsananin yunwa da bakin talauci shine rufe boda da haramta shigo da abinci musamman Shinkafa daga Kasar waje, alhali an tsananta wa talaka kudin taki da maganin kashe ciyawa, noman ya gagara, wannan laifin Gwamnatin tarayya ne ba na jihohi ba
Don haka duk tsarin Gwamnatin APC na a cutar da talakawan Arewa ne ba komai ba, sun jefa rayukan talakawa cikin tsananin yunwa da talauci da fatara, tsoro da fargaba