17/11/2023
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman a Abuja babban birnin Najeriya ta bai wa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna kuma dan takarar APC nasara a hukuncin da ta yanke game da zaben gwamnan jihar Kano.
A hukuncin da ta yanke, Kotun ta yi watsi da ƙarar da gwamnan jihar mai ci, Injiniya Abba Kabir Yusuf na jam'iyya NNPP ya ɗaukaka yana ƙalubalantar hukuncin kotun ta sauraron ƙorafin zaɓen ta jihar Kano.
A ranar 20 ga watan Satumba ne kotun sauraron ƙorafin zaɓe ta jihar Kano ta ce Gawuna ne ya lashe zaɓen wanda aka gudanar a watan Maris.
Kotun ta ce ba za a sanya ƙuri'u 165,663 da aka kaɗa wa Abba Kabir cikin lissafi ba kasancewar babu sa hannu ko tambarin kan sarki na hukumar zaɓe a jikinsu.
Hakan ne ya sanya aka zabge ƙuri'in Abba zuwa 853,939, yayin da shi kuma Gawuna ke da ƙuri'u 890,705.
Sai dai Abba Kabir ya yi watsi da hukuncin inda ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara.
Ya bayyana sakamakon kotun sauraron ƙorafin zaɓen a matsayin "kuskure" kuma maras "adalci."
Dama dai jam'iyyar APC ta roƙi kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar Gwamna Abba Kabir.
Takara tsakanin ɓangarorin biyu, na ɗaya daga cikin mafi zafi da aka gani kafin zaɓen 18 ga watan Maris a Najeriya, kuma ga alama har yanzu, yanayin siyasar bai daina tafarfasa ba, wata takwas bayan kammala zaɓe.
Hukumomin tsaro a Kano, tun farkon wannan mako sun ce sun tura ƙarin jami'ai da kayan aiki zuwa manyan fuskokin garin, don hana faruwar tashin hankali, da kuma kare rayuka da dukiyar al'umma, tun kafin sanar da hukuncin.
Dukkan 'yan takarar a zaɓen da ya wuce, suna da alaƙa da jiga-jigan 'yan siyasar Kano biyu, Rabi'u Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje, tsoffin gwamnonin jihar da ke kan ganiyarsu har yanzu, sannan tsoffin manyan aminan juna, kafin su ɓaɓe a tafiyar siyasa.
Tun farko a watan Maris, hukumar zaɓe ta ce ɗan takarar NNPP, Ab
ba Kabir Yusuf ya ci zaɓen gwamnan Kano, da ratar ƙuri'a 128,900.
Abba Kabir Yusuf, in ji INEC ya samu ƙuri'u mafi rinjaye har 1,019,602, inda Nasiru