Inside Katsina

  • Home
  • Inside Katsina

Inside  Katsina Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Inside Katsina, News & Media Website, .

Dan Majilasar Tarayya Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Kankara, Faskari Da Sabuwa Ya Samawa Al'ummar Motocin Dauka Marasa ...
26/01/2024

Dan Majilasar Tarayya Mai Wakiltar Kananan
Hukumomin Kankara, Faskari Da Sabuwa Ya Samawa Al'ummar Motocin Dauka Marasa Lafiya

A ranar Alhamis 25/1/2024 Dan Majilasar , ,, mai Kananan hukumomin Kankara, Faskari Da Sabu,,wa ac tarayya Hon. Jamilu Mohammed Lion ya samar da motocin Asibiti a Kananan hukumomin dayake wakilta.

Hon. Jamilu Mohammed Lion Yana daya daga Cikin Yan Majilasar Wakilai da s**a ionsamu nasarar akarkashin Jam'iyyar PDP ga Jihar Katsina azaben gama gari daya gudana a Shekarar 2023.

Dan Majilasar Wakilan ya fara Ƙaddamar da mika motar Asibitin ne da karamar Karamar Hukumar Kankara ayau m alokacin Gudanar bikin Hon. Lion ya kuma samar da motar daukar Marasa Lafiya kirar Golf sabuwa gadagal ga Al'ummar Mazabar Garagi ta Kankara.

Haka zalika ya samar da Fayib Fayib na rijiyar tuka tuka kimanin guda 250 domin gyaran wasu rijiyoyin burtsatsen da s**a Samu matsala gamida hannuwan buga rijiyoyin burtsatsen Guda Biyu.

Hon. Jamilu lion Baitsayana Nan ba ya Samar da Buhunnan Shinkafa guda 80 dukka ga al'umma Mazabar Garagin ta Karamar Hukumar Kankara Jihar Katsina.

Shugaban Jam'iyyar PDP a karamar hukumar Kankara Hon. Amadu Mai kanananzir yayiwa mahalarta taro barka da zuwa sannan yayi kira ga al'ummar Mazabar Garagi da kada su biye wani ya rudesu ayayin gudanar da Zaɓen Cika gurbin da za'a ayi nan GABA.

Comr. Nuraddeen Adam Tina Yayi kira da jan kunne ga al'umma yankin Garagi dasu tsaya tsaf su zabi Jam'iyyar PDP a Zaɓen mazabar domin cigaba da sharbar romon demokariya.

Shugaban Matasan Jam'iyyar PDP a Mazabar Garagi Alhaji Nura ya Tabbatarwa Dan Majilasar Wakilai da yardar Allah zasu Tabbatarwa duniya Mazabar Garagi ta PDP ce, yakuma godewa Waɗannan abubuwan Alheri da Hon. lion yasamar ayankin su.

Danmajilisar inda Zaku Iya tunawa bayan Zaɓen da ya gudana abonkin takararshi na Jam'iyyar APC Hon. Dalhatu Tafoki ya garzaya kutun sauraran kararraki zabe domin kalubalantar yanda aka gudanar da Zaɓen Saboda rashin yin zabw awasu rumfunan Zaɓe daga

SAMAR DA AYYUKAN YI GA AL'UMMA||An Gwangwaje Manomam Rani Da Kayan Aiki Na Zamani A Karamar Hukumar Kankara Jihar Katsin...
14/01/2024

SAMAR DA AYYUKAN YI GA AL'UMMA||
An Gwangwaje Manomam Rani Da Kayan Aiki Na Zamani A Karamar Hukumar Kankara Jihar Katsina.

Daga: Mannir Idris Kankara

K**ar yadda wakilin Jaridar Rana24 ya ruwaito Manoman rani ayankin Karamar hukumar Kankara dake jihar Katsina sun amfana da kayayyakin milyoyin Naira.

Shuagaban Kungiyar manoma rani yankin karamar hukumar Kankara Hon. Mansir ISHAQ Jery Yayiwa Jama'a jawabin maraba inda yayi godiya da nuna gamsuwa da yadda Gwamnan Jihar Katsina ke tafiayar da mulkin jihar Katsina.

Ajawabin shi shugabań karamar hukumar Kankara Hon. Anas Isah Kankara ya fara da godewa Gwamnan jihar Katsina akan samar da Waɗannan kayayyaki ga al'ummar Kankara.

Ya Kuma shaidama al'ummar wannan yankin cewa wannan Gwaji ne domin haka Waɗanda suke Gudanar da noman ranin ammàAllah baisa Suna cikin Waɗanda zasu amfanaba dasuyi hakuri.

Shuagaban Karamar hukumar na tsaka dayin Bayani sai ga Buhun Kabeji da kwandon timatir daga manuman rani na wannnan yanki domin nuna tabbatuwar su manoman ranin ne na zahiri.

Anas Isah yaji dadin yadda Waɗannan Jama'a s**a nuna godiyar su hadi da nunawa duniya Jin dadinsu, ya kuma kara kira da Suyi amfani da kayayyakin da s**a samu kamar yadda ya dace.

Bayan Kammala jawabin shi Shugaban tsaron rayukan Al'umma da dukiyoyinsu yankin Kankara ya godewa Al'ummar Kankara ciki da wajenta ta yadda suke bada hadin Kai wajen samar da Tsaro.

Shima shugaban Hukumar tsaron CWC yayi gargadi da kakkausar murya akan wasu Bata gari da suke amfani da sunan shi domin karbar Wani abu daga Jama'a.
Yace kada Wanda ya bada wani abu ga wani da sunan wakilin wannan hukumar ne.

An fara da Kaddamar da rijiyar burtsatse wanda daga bisani aka raba kayayyakin noman ranin Waɗanda s**a hada da irin Kankana, Timatir, Albasa, kabeji, karas da Kuma tattasai ga dukkanin shiyyoyi 6 da aka tsara.

Waɗanda s**a samu halartar wannan rabon kayayyakin noman ranin sun hada Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina wanda yasamu wakilcin Kwaminshinan Ayyuka na Musanman

Kungiyoyi Sama Da 15 S**a Amfana Da Shirin FADAMA KATSINA NG-CARE A Karo Na 2 A Karamar Hukumar Kankara Jihar Katsina.Da...
05/01/2024

Kungiyoyi Sama Da 15 S**a Amfana Da Shirin FADAMA KATSINA NG-CARE A Karo Na 2 A Karamar Hukumar Kankara Jihar Katsina.

Daga : Mannir Idris Kankara.

A ranar 4/1/2024 aka rabawa Al'ummomi kayan dogaro dakai akaramar Hukumar Kankara Jihar Katsina Karkashin Maitaimakin Gwamnan Jihar Katsina Maigirma Malam Faruk Lawal Jobe,,(Sarkin Fulanin Joben Katsina) a shirin FADAMA KATSINA NG-CARE

Taron rabon kayan ya wakana ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mannir Halliru Jobe hadi da taimakon Malam Ishaq Bashir da wasu matasa Yan siyasa a cikin Kasuwar da ake kira Mordern Market dake kan hanyar zuwa garin Dutsinma a Kankara.

Ajawabin shi Alh Mannir Halliru Jobe wanda shine ya jagoran rabon kayayyakin yayi kira ga dukkanin Waɗanda s**a amfana da Suyi amfani da Waɗannan abubuwan Alheri kamar yadda ya dace, domin alfanon yan baya.

Mannir Halliru yakuma taya dukkanin Waɗanda s**a amfana murnar samun Waɗannan abubuwan Waɗanda kuma basu samu ba dasu kara hukuri zuwa nan gaba akwai wasu shirye shiryen makamanta irin Waɗannan dake tafe.

K**ar yadda Rana24 ta ruwaito wannan rabon abun arziki shine karo na 2 da al'ummar Karamar hukumar Kankara s**a amfana kamar sauran wasu Kananan hukumomin Jihar s**a amfana dashi.

A ruhoton da muka nakalto mako idan zaku iya tunawa ko a makon daya gabata a awaitar da rabon kayayyakin arziki Waɗanda s**a hada da Dabbobi jinsin kaji,Awaki,Injinan Markade,Injinan ban ruwa na miloyin nairori ga Al'umma garin na Kankara.

Haka zalika wakilin mu ya tabbatar ko awannan karon Kungiyoyi 15 ne masu dauke da 'ya'yan Kungiya kimanin 20 azuwa 40 da aka lalubo daga Ɓangarorin na Karamar hukumar Kankara maza da Mata s**a amfana da Injinan hudar gona na zamani 15, Injinan Markade 12, Injinan murzar tunkuza 2,kajin turawa 2000 daidai sauran kayayyakin dogaro dakai.

Jama'a da damane s**a nuna farin cikin su akan wannan Lamari na rabon kayayyakin arziki da Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina ke samarwa a Kankara.

Umar Bature Darda'u (BACHO) ya Tabbatar da godiyar shi, Mal

  ||                   SAKON TAYA MURNAGidauniyar KANKARA KE GABANMU ba taya Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Maigirma F...
27/11/2023

||
SAKON TAYA MURNA
Gidauniyar KANKARA KE GABANMU ba taya Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Maigirma Faruk Lawal Jobe Samun Sarautar Sarkin Fulanin Joben Katsina Wanda Masarautar Katsina Ta Bashi.

Allah Ubangiji Yasa Alheri.

WANNAN SAKONE DAGA
Secretary General

19/11/2023

RAHOTANNI RANA24 ||
A Karamar Hukumar Sabuwa Jihar Katsina Yadda 'Yan Bindiga Kecin Karensu Ba Babbaka.

18/11/2023

Jawabin Zababben Gwamnan Jihar Kano Engr Abba Kabir Bayan Hukuncin Kotu ajiya Juma'a

18/11/2023

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Malam Faruk Lawal Jobe Ya Halarci Hedikwatar Hukumar UNDP Ta Majalisar Dinkin Duniya Da ke Abuja.



Jaridar Rana24 ta ruwaito makasudun taron an yi shi ne kan Yanayi, Zaman Lafiya da Tsarin samar Tsaro don Rigakafin Rikici.

Shidai wannan muhimminTaron ana yinshine shekara-shekara domin nufin tuntuɓar masu ruwa da tsaki masu mahimmanci.

Dafatan abubuwan da Mataimakin Gwamnan Jahar Katsina s**a Tattaunawa ayayin taron zasu zamo mana masu amfanie ta Fannin inganta zaman lafiya tsaro a Jahar mu ta hanyoyin zamani don rigakafin rikice-rikice.

03/10/2023

YADDA:
Akaron Farko Rukunin Makarantun Uncle 'D' Dake Kankara Reshen Sakandire Sun Gudanar Da Taron Bankwana Da Daliban Su.

Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Dake Goyon Bayan Maitaimakin Gwamnan Jihar Katsina  Ya Tallafawa Yara Marayu 50 Da Kayan Ma...
19/09/2023

Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Dake Goyon Bayan Maitaimakin Gwamnan Jihar Katsina Ya Tallafawa Yara Marayu 50 Da Kayan Makaranta Da Rubutu A Karamar Hukumar Kankara

A ranar 17/9/2023 ne shugabań gamayyar Kungiyoyin dake marawa mataimakin Gwamnan Jihar Katsina baya Malam Mansir Lawal Baure yayi bikin tallafawa Yara marayu Kayan Makaranta.

Taron da aka gudanar adakin taro na Hukumar Ilmin na karamar hukumar Kankara dake Kan hanyar Zuwa Funtua daura da Gidan man shema a garin Kankara.

Ayayin gudanar da wannan taron raba kayan Malam Mansir Lawal Baure ya Gudanar jawabi ga mahalarta taron inda ya baiyana sun yanke shawarar ba yara marayu da 'ya'yan marasa galihu Waɗannan kayan ne domin taya shuwaganin siyasa na jihar Katsina cika kwanaki 100 da hawa kujerun mulki.

Inda yacigaba da cewa amaimaikon su shirya wata liyafa ko wasa s**a ga yafi dacewa su yi wannan Tsarin ta yadda yadda yara marayu zasu amfana.

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Maigirma Faruk Lawal Jobe wanda yasamu Wakiltar Kwaminshinan Ayyuka Na Musanman Hon. Isah Mohammed Musa ya baiwa Al'umma hakuri akan rashin zuwan mataimakin Gwamnan duba da yanayin aiki baibashi damar zuwaba.

Ya kuma Tabbatar ma gishikin tsara wannan muhimmin taro dajin dadinshi hadi da goyon bayanshi dari bisa dari.

Shugaban Karamar Hukumar Kankara Hon. Anas Isa Kankara wanda Ksmsilan mazabar Pauwa A&B ya wakilta ya baiya na godiyar shi ga Mansir Lawal duba da wannan abun arziki Yana kuma goyon bayanshi.

Shugaban Hukumar Ilmin na karamar hukumar Kankara Alhaji Kabir Aliyu ya yabawa Shugaban gamayyar Kungiyoyin masu Marawa Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina akkan tsarin daya ba hukumar Ilmin na zabo Waɗanda s**a amfana da Tallafin.

Waɗanda s**a samu halartar wannan gagarumin taro sun hada da Sarkin Pauwan Katsina Hakimin Kankara Justice Adamu Bello wanda yasamu wakilcin Sabon Gari Mabai Alhaji Ahmed Rufa'i, Kanwan Katsina Hakimin Ketare Alhaji Usman Bello Kanwa wanda yasamu wakilcin wakilin Maigarin Katoge, Limamai, dasaura al'ummar gari.

28/07/2023
Yanzu Haka Ruwan Sama Nacigaba Da Sauka K**ar Da Bankin Kwarya A Garin Kankara Jihar Katsina
28/07/2023

Yanzu Haka Ruwan Sama Nacigaba Da Sauka K**ar Da Bankin Kwarya A Garin Kankara Jihar Katsina

Al'ummar Unguwar Dandutse Bayan Makarantar Kuka Na Rokon Sen. Yakubu Lado Dan-marke Yayi Masu Tituna.A ranar 26/7/2023 A...
28/07/2023

Al'ummar Unguwar Dandutse Bayan Makarantar Kuka Na Rokon Sen. Yakubu Lado Dan-marke Yayi Masu Tituna.

A ranar 26/7/2023 Al'ummar dake unguwar Dan Dutse mazauna bayan Makarantar Lawal Primary School Kankara wadda akafi sani Makarantar sun gudanar da taron tattaunawar cigaban Unguwar.

Anyi wannan taron Malam Aliyu Shehu Abdullahi wanda shine Mai Unguwar yankin yayi godiya ga Sen. Yakubu Lado Dan-marke duba yadda yake gudanar ayyukan titina acikin garin Kankara da sauran wurare afadin Jihar Katsina.

Mai Unguwa Aliyu yaciga ba cewa domin haka ne shi da Al'ummar shi s**a yakamata dasu mika kokon baransu wannan aikin Alheri da Sen. Yakubu ke samarwar da yataimaka ma Wannan Yanki na Dandutse bayan Makarantar Kuka.

Malam Sule Katoge wanda na daya daga cikin mazauna yankin unguwa kuma jigo a Jam'iyyar PDP a Karamar hukumar Kankara ya kara da rokon Sen. Yakubu Lado Dan-marke da ya taimaka kamar yadda yakewa sauran yankuna Suma ayimasu tituna awasu layika biyu muhimmai na Unguwar.

Kuma yasha alwashin isar da wannan sakon roko na jama'ar bayan Makarantar Kuka ga Sen. Yakubu insha Allah.

Malam Dauda wanda yana daya daga cikin Limaman wannan unguwa ya fatan Sen. Yakubu Lado Dan-marke daya amshi wannan roko nasu da samar Masu wannan abubuwan Alheri.
Shima Malam Gambo Addu'a yayiwa mahaifan Sen. Yakubu Lado Dan-marke da Allah yajikansu da rahama.

Alhaji Shamsu Dan-yalo Mai kifi ya tofa albarkacin bakinshi inda yace Sen. Yakubu daman can yana tare da wannan unguwa kasantuwar yanzu haka Yanada kimanin gidaje biyu wanda Mutane ne cikin shi masu hijira.
Yakuma yayi fatan samuwar abunda ake nema

Daga karshedai angunar da Addu'ar fatan Alheri

NEMAN TAIMAKO:Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuhu.Wannan mutum da kuke gani sunanshi Abubakar Kafinta. Dake zaune...
28/07/2023

NEMAN TAIMAKO:
Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuhu.
Wannan mutum da kuke gani sunanshi Abubakar Kafinta. Dake zaune a unguwar Tudun Boka acikin garin Kankara Jihar Katsina, Mutum ne Mai Sana'ar Kafinta.

Bayan samun labarin halin da wannan mutum yake ciki KANƘARA COMMUNITY DEVELOPMENT INITIATIVE ta ziyarci wannan mutum inda muka zanta shi kuma abunda muka gano:

Malam Abubakar dan Asalin yankin kudancin Kasarnan wanda tun bayan daya Musulunta ne kimanin shekaru sama da Ashirin da s**a gaba 'yan uwanshi da basu musulunta s**a koma yankinsu s**a barshi anan garin Kankara saboda yazama musulmi.

Wanda ahalin dayake yanzu Jikin shi yayi taushi ££ manyanta baya iya Sana'ar Kafinta,ga rashin lafiya a'inda yake dazama wani mutum ne ya taimaka mashi da dakin kwana wanda yanzu haka ya lalace.

Ayayin Ziyarar KANKARA COMMUNITY DEVELOPMENT INITIATIVE ta Yi Kokarin sanin wani dan uwanshi amma mun binciko bashi da kowa amatsayin dan uwanshi ayankin nan na Arewa.

Haka zalika wani mutum ne daya ketaimaka mashi ta hanyar yimashi wanka,wanki,canza mashi sutura, bashi abunci domin Allah tare da Taimakon wani malamin Asibitin.

Wannan yasa muka ya dace musanar da 'yan uwa musumi irin halin da wannan Dan uwa namu yake domin tallafama addinin Musulunci aceto rayuwarshi.

Ga duk wanda yake bukatar ganin wannan mutum yananan a Karamar Asibitin Primary Health Care dake Garin Kankara.

Ko A Tuntubi Shugaban Gidauniyar
KANKARA COMMUNITY DEVELOPMENT INITIATIVE akan 07032340606.

Allah yabada ikon taimakawa Addinin Musulunci Amin.

Kasa Da Awanni 48 Dakai Ziyarar Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina An Fara Aikin Hanyar Ruwa A Gadar Kofar Kaura.An fara a...
07/07/2023

Kasa Da Awanni 48 Dakai Ziyarar Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina An Fara Aikin Hanyar Ruwa A Gadar Kofar Kaura.

An fara aikin fidda hanyar ruwa a Unguwar Kofar Kaura cikin birnin Katsina yankin da s**a fuskanci matsalar ambaliyar ruwa.

Idan zaku tunawa munkawo maku rahoton aranar 4/7/2023 Mai girma mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Faruk Lawal Jobe ya kai ziyara a Unguwar Kofar Kaura domin jajantawa ga Al'umma wannan Unguwa Waɗanda iftala'i ambaliyar ruwa ta shafa.
6

Haka zalika awancan lokacin mataimakin Gwamnan ya alkawaruntawa mazauna yankin da gwamnatin Jihar Katsina zatai kokarin ganin andauki matakin gudun afkuwar haka bada jimawaba.

Ayau ranar Alhamis 6/7/2023 akawayi gari da fara aikin samarwa ruwa hanyar dazai ringa bi duba da yanayin da ake ciki na damuna.

Ayayin da wakilin mu ya halarci wurin da ake gudanar da wannan aiki ya tarar da jama'a mazauna yankin na Yabawa da cika maganar da Gwamnatin Jihar tayi akan gudanar da aikin cikin lokaci kankane, Haka zalika sunkuma yi fatan akammala aikin lafiya kamar yadda akafara

07/07/2023

BODIYON:
Bayan Kai Ziyarar Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Faruk Lawal Jobe Da Kwana Daya.

Dubi Yadda Aka Fara Aikin Hanyar Ruwa A Gadar Kofar Kaura Under-Pass Bayan Matsalar Ambaliyar Ruwa Da Aka Fuskanta A Ranar 4/7/2023

Shugaba Tinubu Zai Sa Ranar Da Za'a Gudanar Da ƙidaya a Najeriya.Shugaban hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC), Nasir Kwarra, ya...
07/07/2023

Shugaba Tinubu Zai Sa Ranar Da Za'a Gudanar Da ƙidaya a Najeriya.

Shugaban hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC), Nasir Kwarra, ya jagoranci tawagarsa sun gana da Bola Tinubu a A*o Villa yau Alhamis.

Jim kaɗan bayan wannan gana wa, shugaban NPC ya ce wuƙa da nama sun koma hannun Tinubu game da sabon lokacin aikin ƙidaya.

Ya ce sun miƙa wa shugaban kasa rahoton inda aka kwana, zai duba sannan ya yanke lokacin da za'a yi kidaya.

📷: Buhari Sallau (Facebook)

Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina  Faruk Lawal Jobe Ya Ziyarci Unguwannin Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Cikin Bi...
05/07/2023

Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Faruk Lawal Jobe Ya Ziyarci Unguwannin Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Cikin Birnin Katsina.

Daga : Mannir Idris Kankara

Mai girma mataimakin Gwamnan na jihar Katsina Faruk Lawal Jobe yakai wannan ziyarar ne aranar Talata 4 ga watan Yuli na shekarar 2023 mintoci kadan bayan tsayarwar ruwan sama kamar da bakin kwaryar da Allah ya saukar a birnin Katsina wanda hakan yasa jawo wasu Unguwannin s**a fuskanci ambaliyar ruwan.

Mataimakin Gwamnan Faruk Jobe ya nuna alhinin shi gamida jajanta ma al'umma mazauna yankin hadi da yan Kasuwan dake gudanar da Kasuwancin su awurin da ambaliyar ruwan ta shafa.

Haka zalika maigirma Jobe yakuma tabbatar masu gwamnati zata dauki matakin ganin hakan bai kara faruwa domin zasu bi dukkanin hanyoyin dakile wanzuwar hakan da yardar Allah.

Unguwannin da mataimakin Gwamnan na jihar Katsina Faruk Lawal Jobe ta kaiwa ziyarar sun kunshi Kofar Kaura Under-Pass, Kofar Marusa da Tudun Katsira.

Gwamna Radda Yasa Hannu Kan Dokar Samar Da Asusun Bai-Daya Na TSAGwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda a ranar T...
03/07/2023

Gwamna Radda Yasa Hannu Kan Dokar Samar Da Asusun Bai-Daya Na TSA

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda a ranar Talata 3 ga watan 7, 2023, ya sa hannu kan dokar da za ta kafa asusun bai-daya da jihar za ta rika amfani da shi.

Gwamnan ya yi hakan ne bisa ikon da doka karkashin sashe na (5) karamin sashe na (2) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima da dukkanin sauran karfin doka da Gwamna ke da ita s**a bashi.

Kan haka ne, dukkanin wasu kudaden shiga da duk wasu hakkokin jihar, ciki hada daunin daga gwamnatin tarayya da duk wasu kudade da za a ba jihar a matsayin gudunmuwa, za a rika tura su ta wannan asusu na bai-daya, wanda ta nan ne kuma za a rika cire duk wasu kudaden da jihar za ta yi duk hidimar dake gabanta.

SSA Isah Miqdad
Ofishin Darktan yada Labarai.
3/6/2023.

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Shirya Daukar Matasa Aiki Tareda Basu Horo Daga Kananan Hukumomi 8 Da 'Yan Bindiga S**a Addab...
01/07/2023

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Shirya Daukar Matasa Aiki Tareda Basu Horo Daga Kananan Hukumomi 8 Da 'Yan Bindiga S**a Addaba Domin Magance Matsalar Rashin Tsaro

Daga: Mannir Idris Kankara

Rahoton da wakilin mu yacruwaito ya tabbatar da cewa Mataimakin gwamnan jihar Malam Farruk Lawal Jobe ne ya bayyana haka jim kadan bayan idar da Sallar Juma’a 30/6/2023 a babban masallacin JIBWIS na garin Kankara.

Malam faruk Lawal Jobe ya ziyarci garin na kankara inda nan ne mahaifarshi domin gabatar da gaisuwar Sallah ga abokan ’yan uwa da abokan arziki.

Mataimakin Gwamnan ya bayyana cewa, magance matsalolin tsaro nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, don haka akwai bukatar hadin kan al’umma don kawo karshen matsalar.

Daga nan sai ya yi kira ga shuwaganin gargajiya da su taimaka a cikin wannan tsari don tabbatar da cewa matasan da za a dauka suna da kyawawan halaye.

Malam faruk Lawal Jobe ya jaddada cewa Malaman addinin Musulunci Hadi da Sarakunan gargajiya suna da mutuntawa a cikin al'umma wanda hakan ya sa ya zama dole su shiga harkar zabar matasan da za a dauka.

Ya yi kira gare su da su ji tsoron Allah a cikin aikin da aka ba su.

Mataimakin gwamnan ya jaddada cewa gwamnati ta damu matuka da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar baki daya.

Ya kuma tabbatar ba maganar zancen yin sulhu atsakanin Gwamnatin jihar ta Katsina da'yan bindiga, saidai wanda ya ajiye makamin amatsayin mikawuya.

Hon. Jobe ya bayyana Gwamnan Jihar Malam Dikko na daya da wannan Ta'addanci yashafa domin su s**a Kashe yayanshi, haka zalika shima sanin kowane Yan Ta'addar sun sace mashi shanun dayake kiwo agarin na kankara.

Mannir Idris Kankara

Wani Shugaban Makarantar Firamare (HEAD MASTER) Ya Baiwa Daliban Makaratun Karamar Hukumar Kankara Horo Akan Yadda Zasu ...
27/06/2023

Wani Shugaban Makarantar Firamare (HEAD MASTER) Ya Baiwa Daliban Makaratun Karamar Hukumar Kankara Horo Akan Yadda Zasu Rubuta Jarabawar Makarantun Kimiyya da fasaha A Kankara.

Malamin Mai Suna Mal. Damaliki na daya daga cikin shugabanun makarantun hukumar ilmi ta bai daya(SUBEB) reshen Karamar Hukumar jihar Katsina amakarantar PILOT SCIENCE PRIMARY SCHOOL KANKARA.


Kasancewar shi tsoho kuma kwararre a fannin malunta yasa kasance zakaran gwajin dafi acikin tsarakunshi sauran shuwaganin makaratun firamare kaf karamar hukumar Kankara.

Wannan yasa awannan shekarar Hukumar Habaka ilmin kimiyya da fasaha ta Jihar Katsina wato Katsina State Science And Technical Education Board na fara sayar da tikitin nuna Sha'awar shiga Makarantun ta Mal. Danmaliki yayi kokarin fadakar da saura shuwaganin makaratun firamare harma da kananan sakadaren Yankin domin su sayawa dalibansu dake da bukata.

Bayan aikin fadakarwar tare da samun tallafawar wasu zakakuran Matasan biyu Mal. Danmaliki yayi gudanar da bayar da horo ga dukkanin daliban da s**a sayi fom din shiga Makarantun dake Karkashin wannan hukumar.

Ayayin da wakilin mu ya samu zantanwa da Malam Abdulganiyu Musa Shehu wanda dayane daga Waɗanda s**a tama Mal. Danmaliki bayar da horon yace sun dauki akalla makonni biyu suna bayar da horon ga daliban ta yadda zasu amsa tambayoyi.

Haka zalika Malam Abidina Idris Ketere ya wanda shine cikon malamin daya s**a taimaka wa Shugaban Makarantar Firamare yace Sun samu dalibai ne daga dukkanin Makarantun da s**a sayi tikitin rubuta jarabawar daga kowace Makaranta dalibi ya ke batare da nuna wani banbanci ba.

Bugu da kari Mai gayya mai aiki Mal. Danmaliki ya kara dacewa kimanin dalibai 60 ne s**a rubuta jarabawar abangaren firamare sannan akwai 20 Waɗanda suke a matakin karamar Sakataren.

Bayanan yace sune s**a raka daliban har makarantar Sakandiren kimiyya ta.'Yan Mata dake garin Malumfashi.

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Hon Faruk Lawal Jobe Ya Gwangwaje Al'ummar Karamar Hukumar Kankara Da Abun Alheri.Kasa ...
27/06/2023

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Hon Faruk Lawal Jobe Ya Gwangwaje Al'ummar Karamar Hukumar Kankara Da Abun Alheri.

Kasa da makonni bakwai da karbar madakon mulki Hon. Faruk Lawal Jobe wanda shine mataimakin Gwamnan jihar Katsina Dr Dikko Umar Radda, ya gwagwaje daruruwan mutanen karamar hukumar shi ta kankara da dubunnan nairori.

Hon. Jobe ya rabawa Al'ummomin kankara wannan abun arzikin nea ranar Litinin 26/6/2022 agarin Kankara inda nan garin mahaifarshi.

Yakuma raba Waɗannan Kuɗi ne bisa tsarin kungiyoyin siyasa da Waɗanda bana siyasa ba iri daban - daban dake yankin, Ayayin rabawar kongiyoyi da s**a shafi siyasa kimanin 50 amatakin kanana da kuma manya s**a amfana.

A rahoton da muke samu ya tabbatar da Kananan kungiyoyin siyasa sun amfana da naira dubu Hamsin -Hamsin N50,000 kowanen su Waɗanda s**a hada Kungiyar Yada labarun Jam'iyyar APC a Karamar hukumar Kankara,Kungiyar siyasar matasan Dandutse, Sabon gari,kunyangizo dadai sauran su.Inda su kuma manyan kongiyoyin s**a amfana da N100,000:00 kowace Kungiya.

Abangaren kungiyoyin daba na siyasa Akwai irin su Kungiyar Derebobi reshen Karamar Hukumar Kankara da dai sauransu.

Hon. Faruk Lawal abangaren Addini nanma yarabawa Dukkanin Limaman Darika da JIBWIS dake yankin, Haka zalika ya rabawa daidaikun mutane gari N5000wasu kuma N10,0000 kowane.

Atabakin daya daga cikin hadiman Mataimakin Gwamnan ya bayyana mana cewa wannan abun Alheri Hon. Jobe yayi ne domin mutane su samu gudanar da shagulgulan Sallah lafiya cikin farin ciki.

Daga karshe ta roki Al'umma na Karamar hukumar ta Kankara,jihar Katsina da Kasa baki muyi amfani da wannan lokaci wurin yin Addu'a samu zaman lafiya akasa baki daya

Shugaban Karamar Hukumar Kankara Ya Dauki Nauyin Rubuta Jarabawar Shiga Makaratun Kimiyya Da Fasaha Na Jihar Katsina.(KS...
25/06/2023

Shugaban Karamar Hukumar Kankara Ya Dauki Nauyin Rubuta Jarabawar Shiga Makaratun Kimiyya Da Fasaha Na Jihar Katsina.(KSTEB) Ga Daliban Kankara.

Aranar Asabar 24/6/2023 Hon. Anas Isah Kankara wanda shine shugaban karamar hukumar Kankara Jihar Katsina ya daukin nauyin biyan rubuta jarabawar dalibai 'yan asalin Karamar hukumar.

Daliban daga karamar hukumar Kankara su kimanin 63 s**a rubuta jarabawar ajiya Asabar karkashin tallafawar shugaban karamar hukumar.

Sakataren Karamar hukumar Hon. Ibrahim Yakubu Kasko wanda aka gudabar da tafiyar da wannan aiki akarkashi, ya baiyana cewa karamar hukumar Kankara ce ta yanke hukuncin tallafawa dalibai yara kanana Waɗanda s**a kunshi Waɗanda ke aji 6 a matakain makaratun firamare.

Haka zalika kuma akwai dalibai amatakin karamar sakandire Waɗanda dukkanin su aka tattaro daga Makarantun lungu da sakon karamar hukumar ta Kankara batare da nuna wani banbanci Siyasa,yamki ko na addini ba.

Hon. Kasko yace makasudin yin hakan shine domin Kara farfado da martabar ilmi ga yara masu tasowa musanman ayankin karamar hukumar Kankara Jihar Katsina.

Kamsilan nadi mai kula da fannin ilmi Hon. Ibrahim Badamasi Pauwa ya kara dacewa karamar hukumar Kankara ta zartar da wannan tallafine duba targaden da akaiwa ilmi musanman afannonin kimmiya abaya asakamakon abinda ya faru a Sakandiren GSSS Kankara wanda ayanzu komi ya wuce abangaren Tsaro.

Hon. Pauwa yakuma bayyana tundaga sayen tikitin, hotuna,abinci,sha Kuɗin mota zuwa da dawowa kyauta ne.

Idan zakutuna karamar Hukumar Kankara dake yankin Katsina ta kudu dai na daya daga cikin manyan kananan hukumomin Jihar wanda inka cire karamar hukumar Katsina babu wadda takai yawan Al'umma.

Kana akyawon gari inbanda Funtua, Malumfashi,Daura da Dutsinma babu wadda tafita.

Tanada ishasshen filin kasar noma gami da dabbobi hadi da 'ya'ya masu kaifin basira, wanda asakamakon hakane ashekarar 1999 Gwamnatin jihar Katsina karkashin mulkin marigayi Malam Umar Musa 'Yar'adua ya Kafa makarantar Sakandiren kimiyya ta GSSS Kankara,wadda take taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaratan dalibai na kimiyya amatakin Jiha da Najeriya baki daya.

Har yazuwa Yanzu wannan makarata na cigaba da yaye dalibai dakeda hazaka duk da wata matsalar da akasamu asheru biyu da s**a gabata, wanda ayanzu Allah cikin ikonshi asamu nasarar samar da zaman lafiya, wanda ake saran cigaba ayyukan koyo da koyarwa a makarantar dake da mazaunin a garin na kankara kamar yadda akasaba.

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Ya Cika Alkawarin Babur Dayiwa Wani Masoyin shi mai Suna GarbaAranar Juma'a 23/6/2023 m...
23/06/2023

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Ya Cika Alkawarin Babur Dayiwa Wani Masoyin shi mai Suna Garba

Aranar Juma'a 23/6/2023 mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Hon. Faruk Lawal Jobe ya damkawa wani masoyin shi babur na hawa sabo dal.

Malam Garba Ma'azu wanda dan asalin garin 'yartsamiya Sarkine dake Karkashin mulkin Karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina,ya kasance masoyi ga Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina ne wato Hon. Faruk Lawal Jobe ne.

Awata zantawa da wakilin mu yayi da Malam Garba Ma'azu ya bayyana cewa soyayyar Hon. Faruk Lawal Jobe abune dadadde wanda Allah ya dasa acikin zuciyar shi tun Lokacin da yayi takarar kujerar Sanatan Katsina ta kudu,har yazuwa lokacin daya tsaya takarar Gwamnan Jihar Katsina har zuwa wannan lokaci.

Garba Ma'azu yakara dacewa soyayyar ce tasa bayan kammala zaben gwamnoni inda Dr. Dikko Umar Radda ya lashe yayi alkawarin yin tattaki tun daga Garin 'Yar tsamiyar Sarki dake Karkashin mulkin Karamar hukumar Kankara Zuwa birnin Katsina aranar Karbar Mulki daga tsohon Gwamnan Masari zuwa Dr. Dikko,Inda Allah cikin ikonshi ya cika wannan Alkawari.

Bayan kimanin mokonni buyu wata kungiya Mai Suna Kankara Unity Forum ta gudanar da taron karramawa ga Mataimakin Gwamnan Hon. Faruk bikin daya gudana afarfajiyar Sakatariyar mulkin Karamar Hukumar Kankara a ranar 10/6/2023 wanda Malam Garba yakara takowa daga Garin'Yar tsamiyar Sarki zuwa garin domin ganawa da Masoyinshi Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina.

Malam Garba yasamu ganawa da mataimakin Gwamnan inda Nan take Hon. Faruk Lawal Jobe ya alkawaruntawa Garba sabon babur domin sauwaka mashi tafiya kasa.

Kasantuwar dan adam ajazine, Duba da yawan ayyukan da mataimakin Gwamnan suke ciki shida Gwamnan Jihar sai ayau ne Hon. Faruk ya damkawa Malam Garba Ma'azu wannan sabon babur kamar yadda kuke Kallon awadanan hotuna.

Duk dacewa lokacin da aka dauka sun fara jawo Cece kuce gawasu a kafar sada zumunta ta Zamani.

07/06/2023

Kungiyar Kankara Unity Forum Ta Karrama Daya Daga Cikin 'Ya'yanta Sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Hon Faruk Lawal Jobe

KANKARA UNITY FORUM KUF (KUFHadaddiyar Kugiyar Hadin Kan Al'ummar Karamar Hukumar Kankara Kankara Unity Forum.Na Farin C...
04/06/2023

KANKARA UNITY FORUM KUF (KUF
Hadaddiyar Kugiyar Hadin Kan Al'ummar Karamar Hukumar Kankara Kankara Unity Forum.

Na Farin Cikin Gayyatar Dukkanin Daukacin Jama'a Maza Da Mata Dake Jihar Katsina Da Makwabta Zuwa Wurin Taron Karrama Sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Hon Faruk Lawal Jobe.

Wanda Za'ayi K**ar Haka:
RANA:4/6/2023
WURI:Dakin Taron Karamar Hukumar Kankara Chamber.
LOKACI:10:00am

Allah yabada ikon Zuwa amin

SPONSORED: 07032350606

An K**a Ɓarawon Dake Shiga Maƙabarta Yana Sace Allunan Alama Dake Jikin Ƙabubura A Jihar Kano
25/05/2023

An K**a Ɓarawon Dake Shiga Maƙabarta Yana Sace Allunan Alama Dake Jikin Ƙabubura A Jihar Kano

1st KANKARA FACEBOOK CONNECT Wannan Kwamiti Suke Da Alhakin Wallafawa Da Yada Ayyuka Da Shirye Shiryen 1st Kankara Faceb...
24/05/2023

1st KANKARA FACEBOOK CONNECT
Wannan Kwamiti Suke Da Alhakin Wallafawa Da Yada Ayyuka Da Shirye Shiryen 1st Kankara Facebook Connect.

Dafatan Zamu Basu Hadin Kai Idan Kaga Sunanka Kayi Magana Da Lambar Ka Zuwaga Lambobin Dake Kasa Domin Sakaka Zaure (Group)

Kwamiti Nagaba Bayan Awa 12 Insha Allah Mungode

Signed
Mannir I. Kankara
Media And Publicity Kankara Facebook Connect✅

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Inside Katsina posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share