22/04/2024
ME YA SA JAMI'AN TSARO SUKAI HARBI A KADUNA? (1)
Da yake su ƴan siyasa s**an yi shiru ne, ba su cewa komai, su ya k**ata su yi magana, ya k**ata duk lokacin da aka yi harbi (aka harba bindiga) ko ba a kashe mutum ba, to lallai za ka ga a wasu ƙasashen sai ministan cikin gida ko wani a cikin ministoci ya yi magana, to amma anan kasar za a kashe mutane za ka ji tsit, kuma an san cewa ba yadda za a yi a harba bindiga haka kawai, to amma tambaya ita ce me yasa a Kaduna? Tambaya kenan, dayake su ƴan sanda su s**an yi magana, an ce mai magana da yawun ƴan sanda ya yi magana, maganar tasa ta rashin kan-gado; na farko yace wannan kungiya an haramta ta a jihar Kaduna, na biyu kuma yace su basu kashe kowa ba, na uku kuma yace sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye ne, su ba su yi amfani da harsashi mai rai ba.
To in ka ga maganar tasa da karo, na farko doka ta hana Ƙungiya ne yace ko? Wannan kungiyar an haramta ta a jihar Kaduna, sai muce to idan aka haramta kungiya a jiha shi kenan kana iya kashe yan kungiyar kenan? Kana iya zuwa ka kashe su kenan? Mene ma'anar haramtawa ɗin in akwai doka? Ko ba a lura ba, ai dokar dole za ta ce in an haramta abu za ace wanda yake yi kila za a k**a shi ne a kai shi kotu ai masa hukunci, kotu ta ce ya yi kungiyar da aka haramta ko? Amma ba kashe shi za ka je ka yi ba ko?.
To sannan kuma muna bukatar mu ga dokar, wadda ta ce ainihin lallai wannan doka ta haramta maka kuma ka fito ka goyi bayan Falasdinu, ko ka yi Allah wadai da Isra'ila, don ya k**ata dokar ta fadi haka nan, don ya k**ata kuma dokar ta fadi mene ne aka hana wannan kungiyar, an hana su sallah ne? Ko An hana su azumi ne? An hana su daurin aure ne, ko juma'a ne? Da wannan fitowa a goyi bayan Falasdinu shi ma an hana su ne? Ko ba a lura ba? Sai dokar ta yi bayani.
Sannan kuma harwalayau wani abin mamaki jihar da ake ce mata Kaduna ba a Kaduna da Zariya kawai aka yi ba, an yi a Saminaka, da Birnin Gwari da Kafanchan, to tambaya, su kuma waɗannan ba jihar Kaduna bane? Aka yi na Saminaka lafiya lau? Birnin Gwari lafiya lau? Na Kafanchan lafiya lau? Me yasa to? Ai kaga ya k**ata suma aje, in wajibinku shi ne a harbi wayannan.
Sannan banda wayannan, hatta na Zariyan ma akwai wayanda aka yi a bangaren Zariya city, masu ibara suna cewa Zariya local government ko? Akwai wanda aka yi kuma aka dauko daga Sabon gari, Sabon gari local government kenan ko? To shi kuma shima ya halatta a yi a Zariya local government ne ya haramta ayi a Sabon gari local government? Saboda na Zariyan an yi an gama ba a yi harbi ba, sai na sabon gari aka yi harbi.
Wani bangare na jawabin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) a ganawarsa da wakilan yan'uwa a bikin karamar sallah ranar Talata (7/Shawwal/1445) a gidansa da ke Abuja.
Zan ci gaba Insha'Allahul Azeem.
Muhsin Shu'aibu Konkiyel
12/Shawwal/1445 (21/4/2024)