ATM Social Media Tudun Wada

ATM Social Media Tudun Wada Well come to Atm socia media team Tudun wada News organization and publicity channel.

Atm social media team founded by Ahmad Tijjani musah Executive chairman of Tudun wada local government kano state.

WASU ƁANGARORI DA MUKA TAƁA A BAYA.1. Mai girma chairman ya bada gudummawa mai karfi a bangaren ilimi a karamar hukumar ...
05/12/2022

WASU ƁANGARORI DA MUKA TAƁA A BAYA.

1. Mai girma chairman ya bada gudummawa mai karfi a bangaren ilimi a karamar hukumar Tudun-Wada. Idan muka duba yadda Mai girma shugaban ƙaramar hukumar Tudun-Wada yakeson ganin ƴaƴan talakawa sunyi karatu domin rayuwarsu ta inganta k**ar yadda ta sauran al'umma ta inganta, mai girma chairman ya shiga ya fita ya samowa matasa Admission a makarantu da dama dake fadin jihar Kano da sauran mak**antu dake makwabtaka da Kano.

2. Idan mukayi maganar raya Al'umma mai girma chairman ya Taimakawa al'ummarsa domin su dogara da kansu da abubuwa da dama k**ar Bada jari don ayi sana'a, samar musu da gurare na gwamnati domin suyi sana'a. chairman ya bawa matasa jari domin rage zaman banza da wannan yanayi da ake ciki na rashin aikin yi a kasa.

3. Mai chairman yayi namijin kokari wajen inganta bangaren lafiya a karamar hukumar Tudun Wada, zuku yadda dani idan kuka duba irin Alkhairan daya kawo asibititocin Tudun Wada lunguna da saƙuna, domin inganta lafiyar jama'ar Tudun Wada.

4.Mai girma chairman sai dai muyi Godiya ga Allah idan mukayi Maganar Cigaban kasuwanci ga jama'ar Tudunwada, abune mai tarin yawan gaske domin ya bawa wannan ɓangare gudunmawa mai karfin gaske, musamman yadda ya zamanantar da abubuwa da dama.

5. Idan mukayi maganar Inganta tsaro A Tudun-wada, Mai girma chairman ya samar da tsaro mai inganci a karamar hukumar Tudun-wada. Mai girma chairman ya samu hadin kan ɓangarorin dake kulawa da tsaro domin haɗin kansu ga al'umma tunda daga kan Ƴan sanda, Vigilant, Sojoji, Peace And Unity. Da sauran kungiyoyin da suke kula da al'umma, domin su jajirce kan kulawa da Al'ummar Tudun-Wada babu dare ba rana.

Allah Ubangiji Ya Kara Baka Damar Cigaba Da Taimakon Al'ummarka Akoda Yaushe, Allah yayi Jagoranci, Baba.

Aliyu El-Idrith Shu'aibu
Dan Autan Media.
SSA To The Executive Chairman of Tudun Wada LGA Kano State.

07/11/2022

Tudun wada short changed...!

06/11/2022

Tudun wada first...!

Kano2023
07/09/2022

Kano
2023

Mai girma zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Tudun-wada Hon. Ahmad Tijjani Musah (Matata), yana taya dukkanin al'ummar mu...
30/07/2022

Mai girma zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Tudun-wada Hon. Ahmad Tijjani Musah (Matata), yana taya dukkanin al'ummar musulmi murnar shiga Sabuwar Shekarar Musulunci ta (1444Ah) tare da addu'ar Allah ubangiji ya haɗa dukkanin musulmin duniya da alkhairin dake cikin wannan shekara.

Allah ya zaunar da ƙasarmu lafiya baki daya

Indai Taimakon Dalubai da Sashen ilimi ne A Karamar Hukumar Tudun wada Ko a da ko a Yanzu Banajin Akwai Dan siyasar da y...
27/06/2022

Indai Taimakon Dalubai da Sashen ilimi ne A Karamar Hukumar Tudun wada Ko a da ko a Yanzu Banajin Akwai Dan siyasar da ya k**a kafar Hon. Ahmad Tijjani Musah (MATATA) daga Hawansa Mulki a shekarar 2018 zuwa yanzu 2022 shekaru 4 zamu iya shaida kadan daga Cikin Abubuwan da zamu iya tunawa 👇👇👇 Rubutu da Hotuna 📸

1. Yayi schoolership ga dalubai yan asalin karamar hukumar Tudun wada sama da mutum 500 masu Phd #50'000 masters #20'000 Degree #10'000 Nce/Dip #50'00

2. Biyawa dalubai kudin registration na jarabawar JAMB 2018 da kuma 2019 tareda basu horo akan yadda zasu amsa jarabawar a CBT ,

3. Biyawa dalubai kudin jarabawar (NECO /WAEC ) Yan Asalin karamar Hukumar Tudun wada 2018-2019

4. Biyawa Dalubai kudin jarabawar NECO PRIVATE (NOV/DEC) 2018 a kallah mutum 30 Yan Asalin T/wada @ GTC Dadinkowa

5. Samar gurbin karatu a makarantun kimiyya da fasaha na sakandire ( science and Technical schools) ga Dalubai a kallah 150 masu hazaka a matakin JSS a zuwa SS 2018/2019

6. Samarwa da daluban Tudun wada dake karatu a FCE/KANO POLY DA KUST wuraren kwana a WUDIL da kano , legal

7. Gyaran Blocks guda biyu na makarantar primary a gacha Burum Burum

8. Gyaran Blocks na primary a garin Ruwan Tabo

9. Gyaran Blocks 2 na makarantar primary a kamfar ma'aji Dalawa

10. Gyaran Blocks 2 a Dogon Kawo yaryasa

11. Daukar Nauyin Dalubai 15
a makarantar kimiyyar noma dake kano (FCAPT)

12. Gyaran ajujuwan karatu a makarantun primary da sakandire k**ar su:- Yammah primary, Arewa primary , GGSS-Rugu rugu GSSS -Faska , Burum burum etc

13. Saka matasa a harkar koyon sana'oin dogaro dakai k**arsu , da bankuna na zamani ,

14. Raba kayan koyo da koyarwa ga sashen ilimi a matakin farko na primary a karamar hukumar Tudun wada

15. Kaddamar da tsarin bada ilimi kyuta da uniform karkashin jagorancin maigirma gwamnan jihar kano

16. Bayarda offer ga daya daga cikin wanda s**a kammala karatun kiwon lafiya a garin jammaje

17. Samar da Admission a Sports School institute Dake karfi ga mutum 10 tareda biya musu Registration

18. Daukar Nauyin mutum ashirin 20 a kwalejin ilimi ta Sa'adatu Rimi Tareda biya musu Registration

19. Daukar nauyin Gyaran Gidan Dalubai Yan Asalin karamar Hukumar Tudun wada Dake Wailari Kumbotso

20. Samarwa Dalubai Dake karatu a makarantar Kimiyya da Fasaha ta Wudil (KUST) Gida

21. Jamb 2022 mutum 200

22. Neco 2022 Mutum 200+ 80

23. Tallafin kudi 500k ga Dalubai masu karatu a Nijar

24. Baiwa Kungiyar Dalubai Shago

25.Samar da Admission ga mutum 7 a FCE kano tareda Daukar Nauyin karatunsu

26.Samar da Admission ga mutum 5 a Kano poly tareda Daukar Nauyin karatunsu

27. Baiwa Kungiyar Dalubai Fili Domin Gina Office

28. Zagaye Makarantar mata GGASS T/wada

29. Daukar Nauyin Karatun HND na mutum biyu 2 a FCAPT har su gama

Banda tallafi da yake bayarwa jefi-jefi ga Dalubai na fannin Registration da jarabawa da sauran Abubuwan da shi kansa bazai iya Tunawa ba

Duk Wanda yakawo Mana 25% na irin wannan Aikin a Tudun wada daga wani Dan Siyasar yaci Kuri'a ta ko waye

Zamu zuba ido muga Shin Dalubai Zasu Rama Biki ko kuwa , Allah ya taimaki Maigirma chairman yayi masa Jagoranci a dukkan lamuransa Allah yabashi Damar da tafi wacce yake Kai

✍️✍️✍️
Abdulaziz Aliyu
SSA to the chairman

Maigirma zababben shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah Yakai Ziyarar duba wasu Muhinman Ayyuka da...
15/06/2022

Maigirma zababben shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah Yakai Ziyarar duba wasu Muhinman Ayyuka da Akeyi a karamar Hukumar Tudun wada karkashin Gwamnatinsa , 1 Aikin Yadda Kamfanin Hada Abincin kaji da Sauran Dabbobin Gida yake Gudana , 2 Sai Kuma Aikin Ginin Kamfanin Sarrafa Shinkafa Wanda Gidauniyar " Appeals project takeyi" Duk Wadannan wurare ne da zasu Samar da Cigaba da Kuma Hanyoyin Dogaro da Kai ga Matasa a karamar Hukumar Tudun wada , Fatan Allah yasa Agama Lafiya

Hukumar Sojojin Ruwa ta Najeriya (Navy) Reshen Portharcourt Dake jihar Rivers ta karrama Maigirma zababben shugaban kara...
11/06/2022

Hukumar Sojojin Ruwa ta Najeriya (Navy) Reshen Portharcourt Dake jihar Rivers ta karrama Maigirma zababben shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah (MATATA) a yau 11/06/2022 bisa irin Gudunmawar da yabasu a lokacin da yake Aiki a jihar ta Portharcourt , inda s**a zo kafa da kafa har gida s**a bashi wannan award bisa irin Jin Dadin Alkhairin da yayi musu da kyautatawa a zamanin Aikinsa a jihar ta Portharcourt , Kuma sunyi masa Fatan Alkhairi tareda fatan Nasara a dukkan Al'amuran Rayuwarsa

Shi dama Haka Alkhairi yake komai daren dadewa indai ka Shuka shi sai ya biyoka duk inda kake , fatanmu Allah Yabamu iKon Aikata Alkhairi da dukkan Damar da muka samu a Rayuwa Congratulations Sir

✍️✍️✍️
Office of the executive chairman Tudun wada local government

Allah yasakawa chairman da Alkhairi bisa Wannan Aikin Alkhairi
04/06/2022

Allah yasakawa chairman da Alkhairi bisa Wannan Aikin Alkhairi

Maigirma zababben shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah yanayiwa daukacin Al'umar karamar Hukumar ...
03/06/2022

Maigirma zababben shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah yanayiwa daukacin Al'umar karamar Hukumar Tudun wada Barka da juma'ah, Allah yakarbi ibadunmu

Mai Girma Zaɓaɓɓen Shugaban Karamar Hukumar Tudun Wada Hon. Ahmad Tijjani Musah (Matata), Lokacin Daya Zauna Da Wasu Jaj...
30/05/2022

Mai Girma Zaɓaɓɓen Shugaban Karamar Hukumar Tudun Wada Hon. Ahmad Tijjani Musah (Matata), Lokacin Daya Zauna Da Wasu Jajirtattun Matasa Daga Unguwanni Daban-Daban Dake Mazaɓar Tsohon Gari, Bisa Jagorancin Matashi Na Matasa Abubakar Isco Twd

Wannan Matasa Sun Kawo Ziyarar Ban Girma Tare Da Jaddada Goyon Bayansu Ga Jam'iyyar Mu Ta APC Mai Albarka.

Allah Ubangiji Ya Bawa Jam'iyyar APC Nasara A Zaɓukanta Na Shekarar 2023.

Aliyu El-Idrith Shu'aibu
Dan Autan Media
Office of The Executive Chairman of Tudun Wada LGA.

To our students at Sa'adatu Rimi College of Education Kano, that;The executive Chairman of Tudun wada local government H...
19/05/2022

To our students at Sa'adatu Rimi College of Education Kano, that;

The executive Chairman of Tudun wada local government Hon. Ahmad Tijjani Musah (Matata ) in his efforts to provide a healthy environment(Accomodation) to our amiable students of Tudun wada LG studying at SRCOE Kumbotso , has APPROVED an immediate RENOVATION of Tudun Wada Local Government Students' owned house (ie. No. 98, Wailari/Basido) 'Yan Lemon Quarter, Kumbotso Local government area of Kano state And renovation will commence hopefully this week...

Maigirma zababben Shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah (matata) a yunkurinsa na tallafawa Harkar ilimin matasanmu na karamar Hukumar Tudun wada tareda Samar musu da muhali Mai kyau yadauki Nauyin Gyara Gidan Daliban Karamar Hukumar Tudun wada wanda yake A kumbotso Local Government (Wailari quaters) Zaafara gyara kowanne lokachi cikin Wannan satin, wannan dai ba sabon Abu bane wurin maigirma chairman domin ya sayi gidaje da dama daga hawansa Mulki zuwa yanzu ya mallakawa daluban makarantu irinsu KUST WUDIL da sauransu bayaga tallafin Schoolership , free registration , Jamb, Neco Free registration duk shekara , Allah yasaka masa da Alkhairi , Allah ya Azurtashi da kujerar da tafi wannan domin cigaban Karamar Hukumar Tudun wada

✍️✍️✍️
Abdulaziz Aliyu
Senior Special assistance

RABON KAYAN ABINCI GA MARAYU. Gidajen Marayu 200 Ne S**a Amfana Da Rabon Kayan Abinci, Na Mai Girma Zaɓaɓɓen Shugaban Ka...
29/04/2022

RABON KAYAN ABINCI GA MARAYU.

Gidajen Marayu 200 Ne S**a Amfana Da Rabon Kayan Abinci, Na Mai Girma Zaɓaɓɓen Shugaban Karamar Hukumar Tudun-wada Hon. Ahmad Tijjani Musah (Matata), Matatan Alkhairi, Matatan Taimakon Al'umma.

Cikin Hukuncin Allah Yau Mai Chairman Yayi Rabon Tallafi Ga Marayu Kamar Yadda Ya Saba Wannan Aiki A Duk Shakara A Irin Wannan Lokaci, Wannan Rabon Tallafi Anbawa Marayu Ne Dakuma Gajiyayyu Yau.

Mai Girma Chairman Yaja Hankulan Jama'a Akan Muhimmancin Taimakon Marayu Kamar Yadda Addininmu Ya Koyar Damu, Yana Fatan Kowa Zai Ƙara Himma Wajen Daukar Damara Ta Taimakawa Marayu Da Mabukata.

Muna Addu'ar Allah Ubangiji Ya Kara Maka Jagoranci, Allah Ya Kara Baka Damar Cigaba Da Taimakon Al'ummarka Akoda Yaushe.

Aliyu El-Idrith Shu'aibu
Dan Autan Media
S.S.A To The Executive Chairman of Tudun Wada.

Maigirma zababben Shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah (matata) Ayinkurinsa Na Samarwa da Matasa ...
26/04/2022

Maigirma zababben Shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah (matata) Ayinkurinsa Na Samarwa da Matasa Aikinyi a karamar Hukumar Tudun Yasamar Da Aikin Wani Kamfani Karkashin Kano state Agro postal Development project (KSADP) da hadin gwiwar Islamic development Bank (IDB)
Aikin wannan Kamfani shine za adinga sarrafa Buntu, Harawa, Roba, da kwalaye Danyin Abinchin kaji,Da sauran Abincin Dabbobin gida , An saran daruruwan Al'uma yan Asalin karamar Hukumar Tudun wada zasu Sami Aikinyi sanadiyyar wannan kamfani da Ake Saka ran kanmala Aikinsa nan da watanni shida 6 masu zuwa

Maigirma shugaban karamar Hukumar Tudun wada yasamarwa Da wannan Kamfani wurin da za'a Gina Agarin Gimbawa Tsohon Kudif-difi Gefen Kwalta, wannan Kamfani zaaginasa Akan kudi Naira miliyan Tamanin Da biyar(85,000000) Ayanzu Haka Anbiya Dan kwangila Kudinsa zaafara Aiki kai tsaye Kuma anasa ran kanmalawa cikin abinda baiwuce watanni shida ba kacal,

wannan na zuwa ne bayan kamfanin sarrafa shinkafa da yakawo karkashin "Appeals project" zasu Gina Wanda yanzu haka Anfara Aiki duk sanadiyyar Jajircewar maigirma chairman na ganin yasamar da Hanyoyin dogaro da Kai ga matasanmu na karamar Hukumar Tudun wada

Duk Wanda yasan Karamar Hukumar Tudun wada ashekaru kadan baya kamin zuwan Hon. Ahmad Tijjani Musah to tabbas yasan an samu cigaba Kuma ana kan samu ta bangarori da dama Mussanman fannin kasuwanci da ingantuwar tattalin Arzuki , ya zamanantar da kasuwa ya karawa Yan kasuwa kwarin gwiwa, ya tallafawa masu karamin jari ta hanyar " Empowerment" yanzu kuma Yana yunkurin a Samar da kamfanunuwa da Matasa zasu Sami Abin yi , Wannan yasaka muke masa Addu'ar Allah yacigaba da bashi Damar da zai ciyar da karamar Hukumar Tudun wada Gaba fiyeda yadda yake kanyi Yanzu

✍️✍️✍️
Abdulaziz Aliyu
Senior Special assistance

Aikin Ginin Katafaren Masallacin (Kanmsu Salawat) Wanda Mai Girma Zaɓaɓɓen Shugaban karamar Hukumar Tudun-wada Hon. Ahma...
02/04/2022

Aikin Ginin Katafaren Masallacin (Kanmsu Salawat) Wanda Mai Girma Zaɓaɓɓen Shugaban karamar Hukumar Tudun-wada Hon. Ahmad Tijjani Musah (Matata), Yakeyi Ya Kusa Kammaluwa.

Mai Girma Chairman Ya Kusa Kammalla Aikin Da Yakeyi Na Masallaci a Unguwar Kuka Tsohon Gari, Wannan Aikin Ƙarashe Ya Rage, Daga Yanzu Zuwa Kowanne Lokaci Za'a Iya Kammala Wannan Aiki, Da Zarar An Kammala Mai Girma Chairman Ze Buɗe Wannan Masallaci Domin Gudanar Da Ibada A Wannan Wata Mai Albarka.

Muna Addu'ar Allah Ubangiji Ya Bada Ikon Kammala Wannan Aiki Lafiya, Allah Ubangiji Yasa A Mizani...

Aliyu El-Idrith Shu'aibu
Dan Autan Media
Office of The Executive Chairman of Tudun-wada LGA.

Maigirma zababben shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah Yana Mika Sakon bangajiyya ga daukacin yay...
19/02/2022

Maigirma zababben shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah Yana Mika Sakon bangajiyya ga daukacin yayan jam'iyyar APC da sauran Al'uma da s**a fito kwansu da kwarkwata domin tarbar sabon zababben shugaban jam'iyyar APC na Jihar Kano Alhj Abdullahi Abbas (Dan sarki) dafatan kowa ya koma Gida Lafiya , Allah ya taimaki jam'iyyarmu ta APC

Maigirma zababben shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah , Kullum Babu Abinda ke tsakaninka da Al'u...
17/01/2022

Maigirma zababben shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah , Kullum Babu Abinda ke tsakaninka da Al'umarka sai kyautatawa da Samar musu da cigaba , Muna Addu'ar Allah ubangiji yasa kagama da duniya lafiya 🙏

📷📸 Photo credit:
Dabo photography

Executive Chairman Office. Wannan Shine Ofishin Mai Girma Zaɓaɓɓen Shugaban Karamar Hukumar Tudun-wada Hon. Ahmad Tijjan...
10/01/2022

Executive Chairman Office.

Wannan Shine Ofishin Mai Girma Zaɓaɓɓen Shugaban Karamar Hukumar Tudun-wada Hon. Ahmad Tijjani Musah (Matata), Dake Sabuwar Sakateriyar Karamar Hukumar Tudun Wada Wacce Mai Girma Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Islam Ya Ginata A Farkon Mulkinsa.

Baba Ganduje Gandun Aiki💪

Aliyu El-Idrith Shu'aibu
Dan Autan Media
S.S.A To The Executive Chairman of Tudun Wada LGA Kano State.

ABU NAMU.....!A madadin Maigirma zababben shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah Muna farin cikin G...
02/01/2022

ABU NAMU.....!

A madadin Maigirma zababben shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah Muna farin cikin Gayyatar Yan uwa da Abokan Arzuki zuwa Wurin daurin Auren Abokin Aikinmu kuma Daya daga cikin masu Taimakawa Shugaban karamar Hukumar Tudun wada Rchp Zhrddn Ya'u Yaryasa Wanda zai gudana Kamar yadda yake a Rubuce a jikin katin gayyata , Wadanda Basu Sami zuwa ba Muna bukatar Addu'oinku

Allah yasanya Alkhairi

GWARZON DAN SIYASA NA SHEKARAR 2021 A KARAMAR HUKUMAR TUDUN WADAHon. Ahmad Tijjani Musah Shugaban karamar Hukumar Tudun ...
31/12/2021

GWARZON DAN SIYASA NA SHEKARAR 2021 A KARAMAR HUKUMAR TUDUN WADA

Hon. Ahmad Tijjani Musah Shugaban karamar Hukumar Tudun wada Shine Gwarzon Dan siyasata na shekarar da muke bankwana da ita ta 2021 sannan kuma shine Gwarzon Dan siyasa a kaf fadin Karamar Hukumar Tudun wada, Haka zalika Daya daga cikin Jajirtattun Shuwagabannin Kannan hukumomi da ya taka muhinmiyyar rawa wajen kawo sauye sauye na cigaba a cikin Al'umarsa , Muna Addu'ar Allah ubangiji yacigaba da dafa masa da yimasa jagoranci a dukkan lamuransa

On behalf of the executive chairman of Tudun wada local government Hon Ahmad Tijjani Musah (MATATA) I would like to use ...
29/12/2021

On behalf of the executive chairman of Tudun wada local government Hon Ahmad Tijjani Musah (MATATA) I would like to use this medium to congratulate the newly elected president of Tudun wada local government student Association (TUWALSA) in person of Comr Nura Babani Musa and his crew , the election which held today 29/12/2021 at Islamic centre Tudun wada was indeed free and fair election , I salute the electoral committee (ielcom) for dedicating their time and knowledge in making it possible and awesome , i urge the newly elected Caretakers to be altruistic ,truthworthy and vibrant in serving the needs of our able Student of Tudun wada Local Government Congratulations once Again ✅

✍️✍️✍️
Abdulaziz Aliyu
SSA Media to the executive chairman
Tudun wada local government

Matata murtala media team 💥A madadin Maigirma zababben shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah ( MAT...
27/12/2021

Matata murtala media team 💥

A madadin Maigirma zababben shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah ( MATATA) dan Amanar Kwamanda yaki na baba Ganduje Alhj Murtala Sule Garo (Galadiman garo) Muna yiwa daukacin Yayan jam'iyyar APC Na jihar Kano karkashin jagoranci Shugaban jam'iyyar APC na Jihar Kano Dan sarki jikan sarki Alhj Abdullahi Abbas fatan Alkhairi , Allah yacigaba da bamu Nasara

✍️✍️✍️
Abdulaziz Aliyu
SSA Media to the
Executive chairman

Muhinman Sako 💥Muna Mika sakon Godiya ta Mussanman ga Maigirma Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar ganduje OFR (Khadimu...
24/12/2021

Muhinman Sako 💥

Muna Mika sakon Godiya ta Mussanman ga Maigirma Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar ganduje OFR (Khadimul Islam) da Maigirma Kwamishinan kananan hukumomin jihar Kano Alhj Murtala Sule Garo bisa sahalewa karamar Hukumar Tudun wada Damar nada masu taimakawa na Mussanman da masu bada shawara a matakai daban daban har mutum 145 karkashin jagoranci Zababben Shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah (MATATA )

Jan Hankali ga SSA/SA 145

Shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah Yana Jan hankalin dukkanin Wadanda s**a rabauta da wadannan muk**an da su kasance masu jajircewa da bada Gudunmawa da Aiki tukuru domin ciyar da Gwamnatin Karamar Hukumar Tudun wada da wannan Al'uma gaba

Kamar yadda yake kunshe a jikin Takardar k**a Aiki da aka baiwa dukkanin SSA/SA cewar ;

* Zakai Aiki kafada da kafada da karamar Hukumarka da jiha a duk lokacin da bukatar hakan ta taso

* Zaka/ki kasance Mai Samar da hanyoyin ciyar da Karamar Hukumar ka Gaba da jiharka Baki daya

* Zaka/ki kasance Mai amana da ruke sirrikan karamar Hukuma a kowanne mataki

* Zaka kasance Mai biyayya ga dokokin Gwamnati da kuma bata shawarwari nagari domin cigaban karamar Hukuma

* Sannan Gwamnati zata dauki mataki akanka idan ta sameka da karya wadannan sharuda na Aiki

Wannan shine rubutun da ke kunshe a jikin Appointment letter din kowa Dan haka maigirma chairman Yana Kara Jan hankalin dukka SSA/SA bisa wannan nauyi da yake kansu Babu Wanda aka nada domin a ringa biyansa albashi da kudin Gwamnati batareda Yana aikin da ya rataya a wuyansa ba sabanin Hakan kuma ko karya Doka mutum zai fuskanci hukunci daga karamar Hukuma

" Domin mu bunkasa hanyoyin cigaba a karamar Hukumar Tudun wada yasaka muka nada masu bada shawara da taimakawa na Mussanman har mutum 145 - cewar maigirma chairman Ahmad Tijjani Musah

Allah ya taimaka karamar Hukumar Tudun wada da Gwamnatin Maigirma gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje

✍️✍️✍️
Abdulaziz Aliyu Ahmad
SSA MEDIA

ZIYARAR JINJINA💪Mai Girma Zaɓaɓɓen Shugaban Karamar Hukumar Tudun Wada Hon. Ahmad Tijjani Musah (Matata), Ya Ziyarci Sab...
22/12/2021

ZIYARAR JINJINA💪

Mai Girma Zaɓaɓɓen Shugaban Karamar Hukumar Tudun Wada Hon. Ahmad Tijjani Musah (Matata), Ya Ziyarci Sabon Ofishin KAROTA Na Ƙaramar Hukumar Tudun-wada Wanda Ya Basu Domin Gudanar Da Aikin Al'umma.

Mai Girma Chairman Yayi Jinjina Garesu Ta Yadda Suke Gudanar Da Aikinsu Cikin Tsari Mai Kyau Duk Domin Kare Al'ummar Ƙaramar Hukumar Tudun Wada.

Muna Addu'ar Allah Ubangiji Ya Kara Jagoranci Cikin Wannan Aiki Naku.

Aliyu El-Idrith Shu'aibu
Dan Autan Media
S.S.A To The Executive Chairman of Tudun Wada LGA Kano State.

SHEKARA GUDA A ZANGO NA BIYU ✌️Alhmdulillah Yayin da muke bankwana da shekarar 2021 zuwa 2022 Muna iya hango kadan daga ...
21/12/2021

SHEKARA GUDA A ZANGO NA BIYU ✌️

Alhmdulillah Yayin da muke bankwana da shekarar 2021 zuwa 2022 Muna iya hango kadan daga cikin wasu Muhinman Ayyukan Alkhairin da Maigirma zababben shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah ( MATATA) ya gabatar cikin shekara Daya tak a sabon zangon mulkinsa Karo na biyu

1- Samar da sabon tsarin kasuwar zamani a karamar Hukumar Tudun wada domin bunkasa harkar kasuwanci (Matata central market)

2- Gyaran makarantu (Renovation) a garuruwan kamfar ma'aji , Gacha , ruwan tabo , faska , dogon kawo

3- Samar da kayan koyo da koyarwa ga makarantu Primary a karamar Hukumar Tudun wada domin inganta harkar ilimi

4- Samar da Ginin masallaci a Unguwar kuka Tsohon Gari ( Ana akan Aiki)

5- Zagayewa tareda tsaftace wasu daga cikin makabartu

5- Samar da Ginin masallaci a Nata'ala Hayin Gada

6- Gyaran burtsatse a fadin karamar Hukumar Tudun wada domin samun wadatar ruwa

8- Samar da Solar Mai Aiki da hasken Rana a asibitin Buga duniya domin inganta harkar kiwon lafiya

9- Kaddamar da yan shara , domin tsaftace titunan karamar Hukumar Tudun wada

10- Baiwa kungiyar Kanikawa NATA ta karamar Hukumar Tudun wada guraben koyon sana'a

11- Empowerment na 20k ga Matasa 100 domin dogaro da kai

12- Kaddamar da dokar Hana cin zarafi a Kafar sadarwa ta social media a fadin karamar Hukumar Tudun

13- Samar da office's ga Yan vigilante , fire service , NCDSC da karota

14- Samar da gidan zama ga daluban jami'ar kimiyya da fasaha Dake Wudil (KUST)

15- Yunkurin Samar da wuri na dindin din ga masu sana'ar Saida waya

16- Samar da wuri da magani ga masu lalurar Mai da Gudawa a Asibitin Hayin yawa

18- Tallafawa mabukata da kayan Abinci da sutura

19- Bayarda tallafin Kayan koyon sana'a da s**a hada da wellbarow , shovel , sprayer da sauransu

20- Diban matasa domin koya musu Gyaran Waya hadin gwiwa da kamfanin Huzzy global communication

21- Inganta harkar tsaro

22- Inganta harkar ruwa

23 Kawo tsarin Aikin Gyaran ido kyauta a asibitin Hayin yawq

24 - Baya ga Nadi na masu bashi shawara na Mussanman (SSA) da Masu taimakawa ( SA)a kallah mutum 150 Wanda Hakan duk na cikin yunkurin Rike Al'uma da kyautata musu domin Samar da cigaba Mai dorewa tareda hanyar samun shawarwari domin ciyar da Tudun wada Gaba

✍️✍️✍️
Abdulaziz Aliyu
Senior Special Assistance
Tudun wada local government

Muna taya Musa Dankaka murnar nasarar rabauta   da wannan matsayi a Jami'ar kimiyya da fasaha ta Wudil KUST WUDIL a mats...
14/12/2021

Muna taya Musa Dankaka murnar nasarar rabauta da wannan matsayi a Jami'ar kimiyya da fasaha ta Wudil KUST WUDIL a matsayin Assistant lecturer Allah ya taya ruko Hakika wannan narasa ce ga al'ummar karamar Hukumar Tudun wada baki Daya.

A koda yaushe al'amari na ciki gaba ya same ka kakan tuna wadanda s**a baka Gudunmawa bayan godiya ga Allah..!Mal Musa,a kwai bukatar ka isar da Godiya ta Mussanman ga jagorancin Rt Hon Alhassan Ado Doguwa domin shine yayi amfani da office dinsa Mai alfarma ya bada takardar farko zuwa ga hukumar wannan Makaranta ta Wudil ..
bisa wannan foundation duk wani mai bada gudun mawa baya ya bada har zuwa nasarar da aka samu..!Dangane da haka muna Mika godiya ta musan man ga Rt Hon Alhassan Ado bisa tasa gudunmawa,da duk sauran wadanna ma S**a taimaka Koda a matakin adua ne.Once again
Congratulations!!!

✍️✍️✍️
Abdulaziz Aliyu
office of the executive chairman
Tudun wada

Akokarinsa na inganta rayuwar Al'ummarsa shugaban karamar huk**ar T/wada Hon Ahmad Tijjani Musah MATATA. Yatura ma'aikat...
05/12/2021

Akokarinsa na inganta rayuwar Al'ummarsa shugaban karamar huk**ar T/wada Hon Ahmad Tijjani Musah MATATA. Yatura ma'aikatar wutar lantarki KEDCO domin duba aikin gyaran wutar B/BURUM -BABURI-DALAWA.

Allah yasa Agama lafiya

Hon. Ahmad Tijjani Musah 💥Jagoran Masoya Kwamanda na Gaskiya na karamar Hukumar Tudun wada  !
01/12/2021

Hon. Ahmad Tijjani Musah 💥

Jagoran Masoya Kwamanda na Gaskiya na karamar Hukumar Tudun wada !

29/11/2021
Sakon ta'aziyya Amadadin Maigirma zababben shugaban karamar Hukuma Tudun wada Hon Ahmad Tijjani musah da daukacin Al'uma...
29/11/2021

Sakon ta'aziyya

Amadadin Maigirma zababben shugaban karamar Hukuma Tudun wada Hon Ahmad Tijjani musah da daukacin Al'umar karamar Hukumar Tudun wada

,muna Mika sakon ta'aziyya na Mussanman ga Maigirma Kwamishinan Kannan hukumomin da masarautu na jihar Kano Hon. Alhj Murtala Sule Garo bisa rasuwar gwagwonsa da yayi ,Muna addu'ar Allah yajikan hajiya da Rahama , Allah yasa Aljannace makoma

✍️✍️✍️
Abdulaziz Aliyu
Senior special assistance
Tudun wada local government
29/11/2021

Sule Garo: forever evergreen By Aminu Dahiru;~Hon. Murtala Sule Garo, the Kano State commissioner for Local Government a...
28/11/2021

Sule Garo: forever evergreen

By Aminu Dahiru;~

Hon. Murtala Sule Garo, the Kano State commissioner for Local Government and Chieftaincy Affairs, is not just a politician or a grassroots mobilizer, but a myrtle that breathes its fragrance into space.

As myrtle stands out among plants for its ability to retain its leaves throughout the year, so the commander stands tall among his peers.

He invests in women, youth and children and he has formed a habit out of it.

We cannot just speak of the battle-ready commander as a politician, but a Good Samaritan that never gets tired of giving.

You can easily trace his good characters - integrity, honesty, courage, loyalty, fortitude - to his father of blessed memory that many see him as a reincarnation of Alhaji Garo.

Murtala Sule Garo’s political dexterity, focus and burning ambition to turn Kano population into an asset are lessons he has learnt from Governor Ganduje and he is always proud to say so.

Not only this; the commander has been loyal that he is to Governor Ganduje what Man-Friday was to Robinson Crusoe; or simply his most trusted servant.

Blessed is this giver that he is young, old, men and women’s favourite.

Maigirma Zababben Shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah ( MATATA) ya nada Sabon Shugabancin  kungi...
21/11/2021

Maigirma Zababben Shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah ( MATATA) ya nada Sabon Shugabancin kungiyar masu sarrafa shinkafa na karamar Hukumar Tudun wada biyo bayan rashin fahinmtar juna da aka samu tsakanin bangarorin biyu sannan ya soke rajistar dukkanin kungiyoyin biyu Dake ja'in ja tareda kaddamar da sabon Shugabanci karkashin jagorancin kwamiti Wanda ya kunshi mutum goma Sha biyu 12 da s**a hada da :

1-Hon. Ismail Yusuf yaryasa
2- Isah wada sulaiman
3- Alhaji Babangida Gadara
4- Alhji Saminu Hussaini gidan dogari
5-Alhaji Nafi'u yalwa
6-Alhaji Bala mudan jandutse
7-Alhaji Musa over
8-Suwidi Hafizu Bako
9-Faisal Saminu
10- Bala Tukuda
11-Alhaji Sani dan'uma
12- Alhji Jume khalid

Sannan yayi kira ga dukkanin bangarorin biyu da sauran Al'uma suyi biyayya ga wannan sabon Shugabancin domin samun cigaba da dorewar zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki a wannan yankin , k**ar yadda aka Sani dai maigirma chairman bashida wani buri face ganin habakar kasuwanci a yankin karamar Hukumar Tudun wada , Allah yayi musu jagoranci ya tayasu ruko

✍️✍️✍️

Abdulaziz Aliyu
Senior Special Assistance
to the executive chairman
Tudun wada local government 21/11/2021

💥💥💥Commander na Matata
21/11/2021

💥💥💥

Commander na Matata

Gida kenan da Maigirma zababben shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah (MATATA) ya samarwa da dalub...
20/11/2021

Gida kenan da Maigirma zababben shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon Ahmad Tijjani Musah (MATATA) ya samarwa da dalubai Yan asalin karamar Hukumar Tudun wada masu karatu a jami'ar kimiyya da fasaha ta WUDIL (KUST WUDIL)

Maigirma Shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon. Ahmad Tijjani Musah zai Gina katafaren massallacin juma'ah a Garin Yar...
18/11/2021

Maigirma Shugaban karamar Hukumar Tudun wada Hon. Ahmad Tijjani Musah zai Gina katafaren massallacin juma'ah a Garin Yar maraya Dake mazabar yaryasa bisa sahalewar maigirma Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar ganduje ofr ) (Khadimul Islam) karkashin gudanarwar ma'aikatar kananan hukumomin jihar Kano wacce Hon. Alhj Murtala Sule Garo ke jagoranta

Wannan Aiki zai gudana akan kudi kimananin ,amadadin Al'umar karamar Hukumar Tudun wada Muna Mika sakon godiya ga maigirma Gwamnan da Kwamishina Alhj Murtala Sule Garo bisa kula da Sha'anin Addini a jihar Kano

Zuwan maigirma chairman Ahmad Tijjani Musah Shugabancin karamar hukumarmu ta Tudun wada tabbas Alkhairi ne domin sanadiyarsa ne ake ta samun tagomashin Alkhairi a wannan gari , Allah yasaka masa da Alkhairi

✍️✍️✍️
Abdulaziz Aliyu
Tudun wada Local government
18/11/2021

Matata Administration Tabbas fannin ilimi yasami gagarumin gata a karamar Hukumar Tudun Wada zuwan Hon. Ahmad Tijjani Mu...
18/11/2021

Matata Administration

Tabbas fannin ilimi yasami gagarumin gata a karamar Hukumar Tudun Wada zuwan Hon. Ahmad Tijjani Musah Shugabancin wannan gari bayaga schoolership har karo biyu ga kuma gyaran makarantu a lungun da Sako na karamar Hukumar Tudun wada

Muna addu'ar Allah yakai matsayi Gaba
Domin cigaba da kawo Ayyukan raya kasa da Al'uma Tudun wada

Address

Abdulazizaliyuahmad @Gmail. Com
Tudun Wada
ATMSOCIALMEDIA

Telephone

08105573068

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ATM Social Media Tudun Wada posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share


Other News & Media Websites in Tudun Wada

Show All