Tijjaniyya youth social media

Tijjaniyya youth social media With remembrance of Allah our hearts 💕 feel calm ❤️

25/11/2023

Sallallahu alaihi Wa Alihi Wasallam 🥰❤️

Annabi Muhammad SallalLaHu alaiHi wa'AliHi wasallam yana amsa sallamar duk wanda yayi masa. Manzon Allah SAW yace : Babu...
25/11/2023

Annabi Muhammad SallalLaHu alaiHi wa'AliHi wasallam yana amsa sallamar duk wanda yayi masa.

Manzon Allah SAW yace : Babu wani mutum da zai yi mun sallama, face sai Allah ya mayar mun da ruhi na, na amsa masa sallamar sa.

Dan Uwa ya zakaji a lokacin da Manzon Allah SAW ya kira sunan ka wane sannan yace Wa'alaikas Salam.

Dan haka ka zama silar da wani zai san wannan sai ka rabauta da amsawar Manzon Allah SAW.

Assalamu alaika ya RasulalLaH.
SallalLaHu alaiKa wa'ala Alika wasallim.

FITATTUN SUFAYE FITOWA TA BIYAR (5).Suna: Sheikh Ahmad Sa'id Makari.Matsayi: Malami, Jagora, Uba.Gari: Zaria.  Ya kasanc...
22/11/2023

FITATTUN SUFAYE FITOWA TA BIYAR (5).

Suna: Sheikh Ahmad Sa'id Makari.
Matsayi: Malami, Jagora, Uba.
Gari: Zaria.

Ya kasance daya daga cikin manyan Malaman kasar Zazzau da ya fito daga tsatson gidan da magabata su kai jihadin yada addinin Musulunci, ya kasance wani abin misali tsakanin dubban mutane, ta fuskar sadaukar da komai na sa domin ganin ya tallafi matasa tashi neman ilmi, domin an ruwaito cikin himmarsa har yakan iya sayar da gidan da yake ciki, ya biyawa matasa kudi, suje kasashen waje dan yin karatu.

Duba ga sadaukarwarsa wajen ganin ya mayar da 'ya'yan al'ummar ANNABI (S.A.W) sun zamo mutane, ba abin mamaki ba ne, idan ALLAH ya azurta mutum irinsa da samun 'Da da ya zamo fitila mai haskakawa cikin milyoyin Al'umma, domin zakwakurin Shehin Malamin nan, Sheikh Prof. Ibrahim Maqari (H) ya kasance 'Da a gareshi.

Ba'a nan ya tsaya ba, ya bayar da gudummowa sosai wajen koyar da tarbiyar Musulunci tsakankn al'ummar Musulmi, ta hanyar wallafa litattafai, da kuma rubuta kasidu masu cike da zallar ilmi da zurfin hikima.

MUNA ROKON ALLAH, YA KARA MASA LAFIYA, TSAWON KWANA DA JINKIRI MAI AMFANI.

Sufi Media Connect ®2023.

HIMMA BATA GA RAGO: Ansha hidimar Addini tun daga kuruciya har zuwa manyanta, ansha gwagwarmaya kala-kala akan kare gask...
18/11/2023

HIMMA BATA GA RAGO: Ansha hidimar Addini tun daga kuruciya har zuwa manyanta, ansha gwagwarmaya kala-kala akan kare gaskiya, yau kuma da aka zo ta fannin tallafawa wasu yan uwa Musulmi dake chan wata Nahiya, tallafinku shine farko ga na kowa da adadi mai yawa.

ALLAH YA KARA DAUKAKA DARAJARKU FARIN DATTIJO JAKADAN MANZON ALLAH (S.A.W)

13/11/2023

kusan waye shehu Ibrahim tare da Mal Ibrahim mai ashafa

AN YI TA TA KARE...!  A karshe dai Khadimul Faidha Sheikh Alhaji Ibrahim Sheikh Dahir Usman Bauci (H) ya zauna da shugab...
08/11/2023

AN YI TA TA KARE...!

A karshe dai Khadimul Faidha Sheikh Alhaji Ibrahim Sheikh Dahir Usman Bauci (H) ya zauna da shugaban jami'ar BUK, kuma ya bashi tabbacin cewa babu abinda zai dakatar da Sufaye aiwatar da ayyukansu na Addini cikin wannan Makaranta.

Babu shakka wannan namijin kokarine da zallar jajircewa da sadaukarwa, muna rokon ALLAH ya saka masa da alkairinsa, albarkacin MANZON ALLAH (S.A.W).

ALHAMDULILLAH

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un 😭😭Allah yayiwa shugaban malamai na garin Gaya jihar Kano rasuwa jiya wato SHEIKH DR....
06/11/2023

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un 😭😭

Allah yayiwa shugaban malamai na garin Gaya jihar Kano rasuwa jiya wato SHEIKH DR.YUSUF ALI za'ayi jana'izar sa a yau
Allah gafarta masa ya sadashi da masoyi Annabi Muhammad s.a.w 🤲

Maulana Khalifa Ya Baiwa Palasd!nawa Gudummuwar Naira Miliyon Dari 100 Milion Naiara Domin Daukaka Addinin AllahDafatan ...
05/11/2023

Maulana Khalifa Ya Baiwa Palasd!nawa Gudummuwar Naira Miliyon Dari 100 Milion Naiara Domin Daukaka Addinin Allah

Dafatan Allah Yakara Masa Karama Duniya Da Lahira

FITATTUN SUFAYE FITOWA TA 3.SUNA: Sheikh Ishaq Rabi'u.MATSAYI: Halifan Tijjaniyya ta Jamhuriyar Nigeria, kafin rasuwarsa...
03/11/2023

FITATTUN SUFAYE FITOWA TA 3.

SUNA: Sheikh Ishaq Rabi'u.
MATSAYI: Halifan Tijjaniyya ta Jamhuriyar Nigeria, kafin rasuwarsa.

TAKAITACCEN TARIHINSA.

1- A shekarar 1928 aka haifi Halifa Sheikh Isiyaka Rabiu, sunan mahaifinsa, Sheikh Muhamamdu Rabiun Dan Tinki.

2- Mahaifin Halifa Sheikh Isiyaka Rabiu dan asalin garin Bichi ne kuma fitaccen Malamin addini ne

3- Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu yayi karatun Qur’ani da Ilimin Larabci a hannun mahaifinsa, daga shekarar 1936 zuwa 1942

4- Khalifa Sheikh Isiyaka Rabiu ya cigaba da yawon neman ilimi zuwa garin Maiduguri na jihar Borno.

5- A shekarar 1949 Malam Isiyaka Rabiu ya fara karantarwa a matsayinsa na cikakken Malamin Qur’ani da Larabci

ABINDA YA SHAHARA DA SHI.

1- Bayan kasancewarsa hamshakin Attajiri, kuma Halifan Tijjaniyya wata siffarsa bayyananniya itace hidimar Al-Kur'ani da kuma Makaranta Al-Kur'ani, ta wannan fuska yayi aiki tukuru na gina Makarantu, gidaje duk domin hidimar Al-Kur'ani, har takai Maulanmu Sheikh Ibrahim Inyass (R.T.A) ya kirashi da lakabin Khadimul Qur'an.

2- Ya gina Katafaran Masallatai, kamar Masallacin Sheikh Ahmad Tijjani da Masallacin Sheikh Ibrahim Inyass (R.Anhum) duk a cikin birnin Kano, bugu da kari ya tallafa wajen assasa abubuwa na addini masu dimbin yawa ciki kuwa harda gina Kafatariyar Jami'a a birnin Kano.

ALLAH yayi masa rasuwa a ranar Talata ta watan Mayu ta Shekarar 2018 bayan fama da doguwar ibada ta rashin Lafiya.

ALLAH YA JIKANSA, YA KARA KUSANCINSA DA MANZON ALLAH (S.A.W).

Sufi Media Connect ®2023

01/11/2023
GASKIYAR ABINDA YA FARU TSAKANIN WAHABIYAWA DA SUFAYE A BUK.  Ranar Asabar 29/10/2023, da Safe sai dalibai na Kungiyar S...
31/10/2023

GASKIYAR ABINDA YA FARU TSAKANIN WAHABIYAWA DA SUFAYE A BUK.

Ranar Asabar 29/10/2023, da Safe sai dalibai na Kungiyar Sufi Movement labari ya riske su cewa "Wahabiyawan M.S.S.N" sun gayyato wani bako daga America zai wa'azi a cikin "Umma Masjid" bayan sallar la'asar, shi kuma wannan lokaci ne dake cikin schedule Sufaye ke yin Wazifa, kuma sai ya zamo ba'a sanar da su ba, b***e su yi rescheduling.

Bayan idar da sallar la'asar, sai P.R.O M.S.S.N ya mike yana mai bayar da sanarwa akan zasuyi lacture a dai-dai wannan lokaci da 'Yan uwa Sufaye ke gudanar da Wazifa, sai wani cikin Dalibai Sufaye ya mike yace "Amma wannan lokaci fa lokaci ne da muke gudanar da Wazifa, me yasa baku sanar da mu ba?".

Take Dalibai Wahabiyawan M.S.S.N s**a mayar da wannan zance na shi zuwa rigima, wasu cikinsu s**a soma cewa rufe mana baki, a ayayin da wasunsu kuma suke cewa a fita da shi waje.

Haka dai su kai zantuka munana na tunzuri ga bangaren Sufaye, har da tsinka charbi, da kuma ture hulan wasu, amma jagororin Sufi Movement s**a umarci kada wanda ya tanka musu, ayi hakuri.!

Haka nan Dalibai Sufaye s**a zauna domin yin Wazifa, kan kace me sai Wakilan Wahabiyawa na M.S.S.N sun garzaya zuwa Student Affairs da kuma Ofishin Security suna ikirarin cewa ga Dalibai Sufaye sun je suna kokarin tayar da rigima da tarzoma a cikin Umma Masjid tare da shirya yarfe da sharri kala-kala.

Ko da aka kai labari zuwa ga Vice Chancellor ba tare da ya kira duka bangarori biyun yaji ta bakinsu ba, sai kawai ya yanke hukunci da abinda Wahabiyawa s**a kawo masa, yace ya haramta ayyukan Kungiyar Sufi Movement a cikin wannan Makaranta. Ayyukan da s**a hada da

1- Wazifa
2- Zikirin Juma'a.
3- Taron Mauludi
4- Da sauransu.

Tare kuma da kai sunayen wasu daga Dalibai gaban Senate da nufin za'a ladabtar da su, laifin su sunyi zikirin ALLAH.

KIRA.

Muna kira ga wannab Vice Chancellor ya sani, kafin shi ya hau kan wannan kujera akwai dayawa da s**a gabace shi, haka s**a tarar da Tijjanawa suna ambaton

KU TAMBAYE SHI, SHIN YA SHIRYA SOSAI KAFIN TUNKARAR YAKI DA BAYIN ALLAH..?.  Ita dai masarautar da aka karrama jami'ar d...
31/10/2023

KU TAMBAYE SHI, SHIN YA SHIRYA SOSAI KAFIN TUNKARAR YAKI DA BAYIN ALLAH..?.

Ita dai masarautar da aka karrama jami'ar da sunan magabacinta "BAYERO" ta kasance mai bin tafarkin Sufanci, kuma darikar masarautar itace "TIJJANIYYA", ashe kenan bai zamo cin fuska ba ga masarautar Kano, al'ummar Kano wani Bawahabiye yazo yace: Zai hana ambaton ALLAH da Dalibai Tijjanawa ke yi a Massallatan cikin Makarantar, tare da hana duka aikace-aikacensu, a gefe guda kuma ga nan Kristoci na Ibadarsu bai hanasu ba, ga Masu Addinin gargajiya na tsafe-tsafensu bai hanasu ba, ga Wahabiyawa na kafirtawa da Bidi'antarwa bai hanasu ba.

Kuma gashi babu wani sashe na kundin tsarin Mulki, ko wata doka da tahana Tijjanawa su aiwatar da ibadunsu.

MUNA FATA YA SHIRYA SOSAI DOMIN FITOWA WANNAN YAKI DA RUNDUNAR ALLAH DA BASU DA WANI MAKAMI DA YA FICE ADDU'A.

AN NEMI MALAMAI DA SUKE JIN TSORON ALLAH WAJEN SAUKE AMANA TA ILMI, GA BARIN SHIGO DA SIYASAR KUNGIYANCI YAYIN BAYAR DA ...
30/10/2023

AN NEMI MALAMAI DA SUKE JIN TSORON ALLAH WAJEN SAUKE AMANA TA ILMI, GA BARIN SHIGO DA SIYASAR KUNGIYANCI YAYIN BAYAR DA FATAWA.

Karshe dai an zakulo shafi da sunan littafin da yake dauke da bayanan da suke nuna cewa Imam Hassan Al Basari, da sauran tabi'ai sun tafi akan fahimtar babu laifi cikin shan rubutu sabanin abinda Sheikh Dr. Bashir Aliyu ya fadi kuma ya jingina musu.

Za'a samu bayanan a cikin littafin

كتاب كشف الظنون عن اسامى الكتب والفنون

Domin saukakawa ga nan shafin da bayanin ke ciki saboda daliban ilmi.

NASIHA.

Ya kamata Malamai su sani akwai amana mai girma akansu, wacce ALLAH zai tambaye su akanta, bai dace suke fadin abubuwa dan ya dace da ra'ayin kungiyarsu ba, ko matafiyarsu ko da ace ba haka jagororin Musulunci s**a tafi ba, ko da ba haka Musulunci ya koyar ba.

ALLAH YA BAIWA MALLAM IKON KARBAR GYARA, KO DOMIN KIYAYE AMANA TA ILMI.

A CIKIN SATI GUDA.YACE: Yana murna da abinda ke faruwa a Palasdine saboda Yan Shi'a ne, sai kuma gashi ya sake fito wa y...
22/10/2023

A CIKIN SATI GUDA.
YACE: Yana murna da abinda ke faruwa a Palasdine saboda Yan Shi'a ne, sai kuma gashi ya sake fito wa yana cewa: ALLAH tsine u*war wanda yace shi ya fadi hakan, ashe baza'a kai bawan ALLAHN nan Asibitti ba, kuma gashi sanyi ya soma sako kai, muna kira ga Gobnatin Bauchi ta dubi batunnan ta tausaya...!

IDAN KA FAHIMCI KANKA, KA GAMA DA KOWA. 1- Kai bawa ne na ALLAH, yadda babu wani cikin mutane da yake taimakon ka da bus...
14/10/2023

IDAN KA FAHIMCI KANKA, KA GAMA DA KOWA.

1- Kai bawa ne na ALLAH, yadda babu wani cikin mutane da yake taimakon ka da busawar numfashi guda, haka zalika babu wani da ya isa ya azabtar da kai a lahira, muddin aikin da ka rayu kai, aiki ne na neman yardar ALLAH.

2- Duk wanda zai zargeka, ya zageka, ko kuma ya jefe ka da wani mummuna suna, to ka sani babu wani da ya rayu akan wani tafarki na kirki da ba'a yi masa kwatankwacin hakan ba, domin mafificin halittu babu wani suna mafi muni da mutanen Makkah basu jefe shi da shi ba, amma shin muggan zantukansu yayi tasiri wajen da'afa sahihancin abinda ya rayu akai, lalllai ka kyautata riko da tafarkin da ka riski bayin ALLAH akai, ka toshe kunnuwa daga wargin dukkanin makiya.

3- Idan duk duniya zasu hadu, farkonsu da karshensu, Aljanunsu da mutanensu, babu guda da ya isa ya juyar da kyawawanka zuwa munana a wajen ALLAH, saboda haka ka zamo mai aikata kyakkyawa kana neman yardar zatin ALLAH, sam kada sunayen:- AHLI-SUNNAH, YAN BIDI'A, SALAF su dame ka, domin ba sunaye bane ke tasiri akan bawa face ababen da ya rayu yana aikatawa.

ALLAH KA BAMU IKON FAHIMTAR KAWUNANMU.

ALHAMDULILLAH.

13/10/2023

Ameen shehu 🤲

Sabon Masallacin Jumma’a Na Maulana Sheikh Dahiru Bauchi Dake Cikin Garin Bauchi
10/10/2023

Sabon Masallacin Jumma’a Na Maulana Sheikh Dahiru Bauchi Dake Cikin Garin Bauchi

Idan hujjojinmu basu iya gamsar da ku gane halaccin yin Mauludi ba, to haka zalika mu kuma bamu dauki inkarinku a matsay...
09/10/2023

Idan hujjojinmu basu iya gamsar da ku gane halaccin yin Mauludi ba, to haka zalika mu kuma bamu dauki inkarinku a matsayin abinda zai hanamu yi ba, idan har baku iya boye soyayyar da kuke ma 'ya'yanku wajen yi musu hidima, ba tare da neman dalili ba, to ba zamu taba gajiyawa da bayyana soyayyarmu ga MANZON ALLAH (S.A.W) ko da dalili ko babu ba..

TINA BAYA : NA FADI HAKA SHEKARU 8 DA S**A SHUDEYADDA MAKIYA ANNABI MUHAMMADU(Sallallahu Alaihi Wasallam) SUKE GANIN SAU...
09/10/2023

TINA BAYA : NA FADI HAKA SHEKARU 8 DA S**A SHUDE

YADDA MAKIYA ANNABI MUHAMMADU(Sallallahu Alaihi Wasallam) SUKE GANIN SAURAN MUSULMIN DUNIYA

Duk abin da s**a yi ko shirka ce, to shi ne tsantsar Sunnah.

Abin kuwa da duk wani Musulmi ya yi, ko da haka Alqur'ani da Hadithi s**a yi umarni, to wannan kuma shi: Bidi'a ne, Shirka ne, kuma tsantsar Kafirci ne. kuma wanda ya yi Dan Wuta ne, Allah ba zai gafarta masa ba, saboda su sun rufe kofar tuba tini.

Saboda su ma'sumai ne ba wanda ya taba yin sabo a cikinsu?!

Ya Allah! Don matsayin Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallama) ka yi wa Musulmi maganin su, da gaggawa, Amin ya Rabb, Ya Rabb, Ya Rabb, ya Rabb, ya Rabb!

Gayyatar Taron Addu'a Na Bakin Ciki Da Farin Ciki....(Addu'ar Nemawa Mahaifiyarmu Gafara Da Addu'ar Radin Suna).Hakika G...
05/10/2023

Gayyatar Taron Addu'a Na Bakin Ciki Da Farin Ciki....

(Addu'ar Nemawa Mahaifiyarmu Gafara Da Addu'ar Radin Suna).

Hakika Gobe Juma'a Mahaifiyarmu (Sayyida Aminatu) Take Cika Kwana 7 Da Rasuwa Haka Kuma Yan'biyun Data Bari Randa Ta Haifesu Suma Goben Suke Cika kwana 7 da Haihuwa Don Haka Ina Amfani Da Wannan Damar Domin Gayyatar Jama'a Zuwa Wurin Taron Addu'ar.
Allah yaimata gafara yakarbi shahadarta sukuma jariran data bari muna rokon Allah yaimusu Tarbiya yakiyayesu ya Shiryasu kuma yaimusu Albarka, Mukuma sauran yayanta Allah Kazama Gatanmu Ubangiji kabamu kulawar da ko tana raye bazata iya bamuba,saboda Manzo S.A.W.

Za'a gabatar da taron Addu'an ne in Allah ya kaimu gobe Juma'a 6/oct/23 da Misalin karfe 8:00am na safe a kofar gidan maulana Sheikh Aliyu Maiyasin Sabon Layi Tudun Wada Zaria Allah yakaimu yabada ikon Zuwa Ameen.

Kasarmu Nigeria 🇳🇬 Allah kabamu Lafiya da zama lafiya da karuwar Arziki Amin.

Innalillahi wa inna Ilaihi Raji’un Muna Jajanta ma Iyayen Dalibai da aka dauka a makarantu dake Jahar Katsina da Zamfara...
05/10/2023

Innalillahi wa inna Ilaihi Raji’un

Muna Jajanta ma Iyayen Dalibai da aka dauka a makarantu dake Jahar Katsina da Zamfara dama sauran yan uwanmu da ake daukan iyalansu a fadin wannan kasa,
Allah ubangiji ya kubutar dasu.

Muna kira ga Shugabannin da abin ya shafa da suyi kokari wajen ceto wadannan bayin Allah, domin an Zabe su ne don su kare Rayuka da dukiyoyin Al’umma kuma sunyi Alkawarin hakan tare da rantsuwa da Qur’ani, to lalle su sani Allah zai tambayesu akan Alkawarin da s**a dauka.

Sannan Sauran Al’umma wajibinmu shine muyi ta Addu’a duk bayan Sallolinmu da niyyar Allah ya cecesu su koma ga iyayensu, Allah kuma ya kawo mana karshen wannan fitina a kasarmu Albarkan Manzon Allah S A W.

Sayyadi Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi

05/10/2023

Ina taya murna ga wanda Annabi Muhammad
S.A.W
yazama shine farincikinsa

Tsarabar maulid Girma Sai Annabi muhammad S.A.W!Duk girman ka baka kai Annabawa ba Amma Allah ce musu yayi da Annabin mu...
03/10/2023

Tsarabar maulid

Girma Sai Annabi muhammad S.A.W!

Duk girman ka baka kai Annabawa ba Amma Allah ce musu yayi da Annabin mu ze riske su toh su Ajiye Annabtar su su bishi wanda kuma ya bada baya ze zama fasiƙi.

وَإِذْ أَخَذَ اللَّهُ مِيثَاقَ النَّبِيِّينَ لَمَا آتَيْتُكُم مِّن كِتَابٍ وَحِكْمَةٍ ثُمَّ جَاءَكُمْ رَسُولٌ مُّصَدِّقٌ لِّمَا مَعَكُمْ لَتُؤْمِنُنَّ بِهِ وَلَتَنصُرُنَّهُ ۚ قَالَ أَأَقْرَرْتُمْ وَأَخَذْتُمْ عَلَىٰ ذَٰلِكُمْ إِصْرِي ۖ قَالُوا أَقْرَرْنَا ۚ قَالَ فَاشْهَدُوا وَأَنَا مَعَكُم مِّنَ الشَّاهِدِينَ فَمَن تَوَلَّىٰ بَعْدَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ.

Duk girman ka baka kai Sahabbai ba kuma Duk girman Sahabi bekai Sayyadina Abubakar da Umar ba, Amma Allah haka yace ze rusa Aikin su kawai saboda ɗaga murya a gaban Annabin mu S.A.W .

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَرْفَعُوٓاْ أَصْوَٰتَكُمْ فَوْقَ صَوْتِ ٱلنَّبِىِّ وَلَا تَجْهَرُواْ لَهُۥ بِٱلْقَوْلِ كَجَهْرِ بَعْضِكُمْ لِبَعْضٍ أَن تَحْبَطَ أَعْمَٰلُكُمْ وَأَنتُمْ لَا تَشْعُرُونَ.

Duk ƙasaitar ka baka kai Matan Annabi S.A.W a cikin su in ka cire Sayyida khdija babu kamar Aisha da Hafsa, amma Allah cewa yayi in s**a yiwa Annabi S.A.W tawaye da son Abunda yake ƙi, toh fa Allah shine me jiɓntar lamarin sa da Jibirilu da Sauran muminai, kuma ze canja mai wanda s**a fisu.

إِن تَتُوبَآ إِلَى ٱللَّهِ فَقَدْ صَغَتْ قُلُوبُكُمَا ۖ وَإِن تَظَٰهَرَا عَلَيْهِ فَإِنَّ ٱللَّهَ هُوَ مَوْلَىٰهُ وَجِبْرِيلُ وَصَٰلِحُ ٱلْمُؤْمِنِينَ ۖ وَٱلْمَلَٰٓئِكَةُ بَعْدَ ذَٰلِكَ ظَهِيرٌ.

Musuluncin gaba ɗaya in ka cire tauhidi toh fa bashi da wata Ajanda inba ka girmama Annabi S.A.W ba ka kanbama shi.

إِنَّآ أَرْسَلْنَٰكَ شَٰهِدًا وَمُبَشِّرًا وَنَذِيرًا لتُؤْمِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَتُعَزِّرُوهُ وَتُوَقِّرُوهُ وَتُسَبِّحُوهُ بُكْرَةً وَأَصِيلًا

Jifa yayi da hannunsa kowa yana gani Allah yace bafa shine yayi ba Allah ne yayi, Caffa akayi mai gashi shi aka yiwa Amma Allah yace bashi aka yiwa ba Allah aka yiwa.

وَمَا رَمَيْتَ إِذْ رَمَيْتَ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ رَمَىٰ
إِنَّ ٱلَّذِينَ يُبَايِعُونَ

JAHILIDE YAJI DADINSA Bari mu biya maka karatu , idan kuma ka sani ka boye don ka halaka wasu to ka qara sani cewa ta Al...
02/10/2023

JAHILIDE YAJI DADINSA

Bari mu biya maka karatu , idan kuma ka sani ka boye don ka halaka wasu to ka qara sani cewa ta Allah ba taka ba :-

Shi Ahlari da sauran littafan da ka ambata littafai ne na Fiqhu , don haka mai Neman bayanan tsarki da sallah sai ya nemesu ya karanta .

Amma shi Maulidi ba a littafan tsarki da sallah ake samun batunshi ba, a'a a littafan Hadisi da Sira ake samun bayaninsa .

Ka duba Littafai kamar Haka :-

البداية والنهاية
سير أعلام النبلاء
شذرات الذهب في أخبار من ذهب
لطآئف المعارف فيما لمواسم العام من الوظآئف

Wadannan duk littafan malamanku kune kuma kowanne akwai fasali da babi da Bayanin maulidi.

Fasalin maulidi har guda biyu a Jere Ibn Rajab Alhambali ya kawo a cikin
لطائف المعارف فيما لمواسم العام من الوظآئف
Kuma Da lafazin Maulidi ya kawosu ba can za masa nayi ba .

Don haka tambayarka da kace :- ka taba ganin .......

Amsa itace:- E na taba gani kuma ga a inda na gani , Kaima ka bude ka gani.

MAKIYA MAULUDI KASHI BIYU NE.1- Masu kin Mauludi Saboda kiyayyar MANZON ALLAH (S.A.W), wadannan Misalinsu cikin Musulmin...
30/09/2023

MAKIYA MAULUDI KASHI BIYU NE.

1- Masu kin Mauludi Saboda kiyayyar MANZON ALLAH (S.A.W), wadannan Misalinsu cikin Musulmin yau, kamar Misalin su Abdullahi Dan Salul ne a cikin Musulmin karnin farko. Sune wadanda Dan Abdulwahab ya ribata a kokarinsa na kaskanta ambaton MANZON ALLAH (S.A.W), bayan ya yaki Sharifai Alawiyyawa dake mulkar yankin Hijaz, wadannan su ne gaskiyar Sahabban Zhulhuwaisara da basu son MANZON ALLAH (S.A.W). su ne Almajiran Dan Abdul-wahab din da ya sanya aka cire kan ladanin da bayan kiran Sallah yayi Salati ga MANZON ALLAH (S.A.W).

2- Su ne wanda aka yaudara da Bidi'ah, su wadannan dayawansu Jahilai ne, da basu da ilmin Addini b***e su iya rarrabe tsakanin Ijma'i ko Ijtihadin Malamai, b***e Istinbadi, sun baiwa Malamansu yarda, a lokacin da su kuma s**a kasance masu ha'intarsu akan fakewa da Bidi'ah suna kin MANZON ALLAH (S.A.W).

Saboda haka lallai kaso na farko ANNABI (S.A.W) suke ki, a yayin da kaso na biyu kuma aka ribace su da kalmar Bidi'ah alhali a cikintaa suke tsamo-tsamo.

ALLAH YA SHIRYE SU YA GANAR DA SU.

Muhammad Usman Gashua ✍️

INNANILLAHI WA'INNA ILAHIR RAJI'UN mahaifiyar Young Sheikh ta rasu.Cikin jimami da alhini muke sanar da ku rasuwar mahai...
29/09/2023

INNANILLAHI WA'INNA ILAHIR RAJI'UN mahaifiyar Young Sheikh ta rasu.

Cikin jimami da alhini muke sanar da ku rasuwar mahaifiyar Matashin Malamin nan wato Young Sheikh Zaria Zakeer M.S Ali Malama Aminatu Muhammad.

“Malama Aminatu ta rasu a Sanadiyyar haihuwa inda ta haifo 'yan biyu mace dana miji, ta rasu ta bar 'ya'ya goma Rigis.

“Za'a yi jana'izar ta da misalin ƙarfe 4:30pm na yamma yau Juma'a a Zawiyyar Sheikh Aliyu Mai Yasin Sabon Layi Tudun Wadan Zariya.

“Muna addu'ar Allah (SWA) yajiƙanta da rahama yasa ta huta.

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un 😢Yanzu nake ganin mummunan labarin rasuwar manyan ƴaƴan Sharif Rabi'u Usman Baba, Sha...
28/09/2023

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un 😢
Yanzu nake ganin mummunan labarin rasuwar manyan ƴaƴan Sharif Rabi'u Usman Baba, Sharif Muhammad Fatihu da Sharif Hassanu. Allah tabaraka wata ala, ya haskaka qabarinsu Allah yasada su da Annabi Muhammadu SalLalLahu Alaihi WasalLam ♥️❤️

Intamu tazo Allah kasa mu cika da Imani Albakacin Annabi SalLalLahu Alaihi WasalLam ♥️♥️

JIHAR KADUNACIKIN HOTUNA: Taron Mauludin Annabi Muhammadu (SAW) Wanda Ya Gudana a Jihar Kaduna, Nigeria. Allah Ya Kara M...
28/09/2023

JIHAR KADUNA

CIKIN HOTUNA: Taron Mauludin Annabi Muhammadu (SAW) Wanda Ya Gudana a Jihar Kaduna, Nigeria.

Allah Ya Kara Mana Kauna Da Soyayyan Annabi Muhammadu ﷺ. Amiiiin Yaa ALLAH

SANARWAR GAGGAWAAna sanar da dukkanin `Yan uwa `Yan FAIDHA cewa `YAN IZALAH a Kano sun kai karar MALAM NURA ARZAI wajen ...
27/09/2023

SANARWAR GAGGAWA

Ana sanar da dukkanin `Yan uwa `Yan FAIDHA cewa `YAN IZALAH a Kano sun kai karar MALAM NURA ARZAI wajen `YANSANDA da nufin kai shi KOTU wai zai haddasa fitina da tayar da hankalin jama`a don ya zagi JA`AFAR.

Don haka `YANSANDA suke neman ya kai kansa Shalkwatar su da take a BOMPAI ran Alhamis 28/09/2023 da karfe 10:00am na safe.

Ana bukatar gudunmowar `Yan uwa da su ba shi goyon baya wajen halartar sauraren karar a wajen `Yansanda da kuma Kotu.

Haba jama`a ! yanzu in ba raini da wulakanci ba, a ce a Kano zagin SHEHU TIJJANI da SHEHU IBRAHIM ba laifi ba ne sai zagin Ja`afar?

Muyi Kishin Dan Uwammu Sheikh Nura Arzai.

MAULUD : " Ya kamata Musulmai su yi bakin ƙoƙarinsu wajen bin koyarwar Annabi Muhammad saq. Akwai manyan darussa na sada...
27/09/2023

MAULUD : " Ya kamata Musulmai su yi bakin ƙoƙarinsu wajen bin koyarwar Annabi Muhammad saq. Akwai manyan darussa na sadaukarwa da jajircewa da juriya da sauƙin kai da kuma sadaukarwa da dukkanmu za mu iya koya daga rayuwar Annabin,” in ji shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu.

26/09/2023

Daren da Aka haifi Annabi Yafi Daren lailatul Qadari Daraja
Yau Daren Babbar SALLAH ❤️
Haihuwar Manzon ALLAH
(S.A.W)
EID-MAULUD

KAFIN HAIHUWAR KA BA'A HAIFI KAMAR KABAAN HAIFE KA BAKAI ZAMANI DA IRIN KABA BAYAN WAFATIN KA BAZA'A HAIFI KALAR KABAمحم...
23/09/2023

KAFIN HAIHUWAR KA BA'A HAIFI KAMAR KABA
AN HAIFE KA BAKAI ZAMANI DA IRIN KABA
BAYAN WAFATIN KA BAZA'A HAIFI KALAR KABA

محمدرسولﷲ

KADA KA RUDU, KUMA KADA KA BARI A YAUDARE KA.Mala'ikun dake tare da kai (Atid da Rakib), suke rubuta ayyukanka, babu ruw...
22/09/2023

KADA KA RUDU, KUMA KADA KA BARI A YAUDARE KA.

Mala'ikun dake tare da kai (Atid da Rakib), suke rubuta ayyukanka, babu ruwansu da me mutane s**a ce akanka, suna lurane da me ka aikata, shin abinda kake aikatawa na da'a ga ALLAH ne ko kuma sabawa ALLAH.

Misali;-

Ka wuni kana salati, hailala da istigfari, matsayin ka dan Bidi'a wajen wasu daga mutane, amma shin aikin da kayi Mala'ikan rubuta zunubi ne yake rubutawa ko kuma mai rubuta kyawawa shin aikin sabon ALLAH ne ko kuma da'a gareshi?

Shi kuma mai kiranka da wannan suna ya wuni yana cin naman mutane, yana kallon matan mutane, yana zagi da aibata mutane shin Mala'ikan dake rubuta kyakkyawa ne zai rubuta aikinsa ko kuma mai daukar munana..?

Shin da kaje wajen Mauludi, ka saurari karatun Kur'ani, ka saurari kasidun yabon MANZON ALLAH (S.A.W) ka saurari zikirin ALLAH, shin Mala'ikan kiyaye kyawawa ne zai rubuta ko mai kiyaye munana?

Shi mai ikirarin shi Ahli Sunnah da yaje wajen Kamfen na Siyasa, ya fadi karya, yayi zagi, ya chakudu maza da mata, ya ja aya ba a Mahallinta ba, ya kasuwantar da Addini shin Mala'ikan kiyaye kyakkyawane zai rubuta ko mai kiyaye mummuna?

IDAN KA FAHIMCI CEWA "HUKUNCIN WANI DAGA MUTANE, BAI DA WANI TASIRI CIKIN CHANJA MAKOMARKA WAJEN ALLAH (S.W.T) TO A WANNAN LOKACI KA SAMU YANCIN TUNANI, TARE DA TSIRA DAGA WAHAMIN SHAIDAN DA JAMA'ARSA".

ALLAH KA AZURTAMU DA IKHLASI DA ISTIQAMA.

ALHAMDULILLAH

Muhammad Usman Gashua

SHEHU IBRAHIM  YACEDaidai da Taku Daya Ban Isa na Kaucewa Annabi ,ﷺ 🤍 ba. Inji Maulana Shehul islam wasa adatul anam alh...
22/09/2023

SHEHU IBRAHIM YACE

Daidai da Taku Daya Ban Isa na Kaucewa Annabi ,ﷺ 🤍 ba.
Inji Maulana Shehul islam wasa adatul anam alhaji Ibrahim Niasse. RTA

💌فَإِنْ حَادَ عَنْ نَهْجِ الرَّسُولِ فَإِنَّنِي 💌

💌عَلَى نَهْجِهِ مَا عِشْتُ فَهْوَ حَمِيـــدُ💌

Idan Wani ya Kaucewa Hanyar Al Aminu (Annabi)ﷺ 🤍 ; to ni Iyakar rayuwa ta ina kan hanyar sa, domin hanya ce abun yabo.

💟أَسِيـــــرُ غَــــرَامٍ لاَ أَزَالُ مُتَيَّمًــــا💟

💟وَعَنْ نَهْجِ خَيْرِ الْخَلْقِ لَسْتُ أَحِيدُ💟

Ni ribatacce ne na Soyayyar Annabi,ﷺ 🤍 Ba zan gushe ba ina 'dimautaccen son Annabi, sannan ba zan taba iya kaucewa Hanyar Fiyayyen Halitta ba

❤️إِذَا سَارَ خَيْرُ النَّاسِ سِرْتُ وَرَاءَهُ❤️

❤️وَإِنْ حَلَّ يَوْمًا فَالْمَسِيـــــرُ بَعِيـــدُ❤️

Duk inda Fiyayyen Halitta ya tafi, to zan bi bayan sa, Amma yana tsayawa to ni ma tafiyar ta yi min Nisa(dole na tsaya) .

MUNGODOWA ALLAH DA MUKA SAMU KANMU A TAFARKIN SHEHU

YA KU AHLI-SUNNAH NA GASKIYA DA GASKIYA, KU ZAMO NA DABAN A KOYIN KU DA MANZON ALLAH (S.A.W) A AIKACE...!Idan wani ya cu...
20/09/2023

YA KU AHLI-SUNNAH NA GASKIYA DA GASKIYA, KU ZAMO NA DABAN A KOYIN KU DA MANZON ALLAH (S.A.W) A AIKACE...!

Idan wani ya cuce ka, to ka tuna da yadda mutanen Da'ifa s**a cutar da MANZON ALLAH (S.A.W) yayi hakuri, kai ma sai kayi koyi da shi ka yi hakuri.

Idan aka zageka, ka tuna da zagin da Matar Aba Lahab ta dinga yiwa MANZON ALLAH (S.A.W) yayi hakuri, kai ma sai kayi hakuri.

Idan kaga mabukaci, ka tuna da yadda ANNABI (S.A.W) yake tallafawa mabukata, kai ma sai kayi koyi dashi wajen tallafi.

Idan zaka fadi magana, ka tuna da yadda ANNABI (S.A.W) yake fadin gaskiya, kai ma sai kayi koyi da shi ka fadi gaskiya akan masoyi da makiyi.

Idan zaka yi wa'azi ko nasiha, ka tuna da yadda ANNABI (S.A.W) yake kamewa daga zagi ko cin fuskar abin kira, kai ma sai kayi koyi da shi ka tausasa lafazi.

Idan zakayi ko wacce irin mu'amala da kowa, ka tuna da irin gaskiya da amanar MANZON ALLAH (S.A.W) cikin mu'amala, sai ka kwatanta koyi da shi.

Idan kaga wani na aikata aiki mummuna, kada ka la'ance shi ko ka aibatashi, kayi kokari wajen jawo shi zuwa dai-dai cikin hikima ta hanyar koyi da MANZON ALLAH (S.A.W)

Idan zakayi zumunci, ka tuna da yadda ANNABI (S.A.W) ke sadar da zumunci da kowa, kai ma sai kayi koyi da shi.

YA DAN UWA MAI KARAMCI, SUNNAH A DABI'A DA AIKI TAKE, BA A IKIRARI DA SIFFA TA ZAHIRI KO BAJO BA, ALLAH KUMA ZAI MANA HISABI NE AKAN AYYUKA BA'A KAN IKIRARI KO BAJO BA.

ALLAH YA BAMU IKON KYAUTATA KOYI DA MANZON ALLAH (S.A.W).

Muhammad Usman Gashua ✍️

 'ANARSAﺍَﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺻَﻞِّ ﻋَﻠﻰ ﺳَﻴِّﺪِﻧَﺎ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ ﺍَﻟﻔَﺎﺗِﺢِ ﻟِﻤَﺎ ﺃُﻏْﻠِﻖَ ﻭَﺍﻟْﺨَﺎﺗِﻢِﻟِﻤَﺎ ﺳَﺒَﻖَ ﻧَﺎﺻِﺮِ ﺍﻟﺤَﻖِّﺑِ...
16/09/2023

'ANARSA

ﺍَﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺻَﻞِّ ﻋَﻠﻰ ﺳَﻴِّﺪِﻧَﺎ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ ﺍَﻟﻔَﺎﺗِﺢِ ﻟِﻤَﺎ ﺃُﻏْﻠِﻖَ ﻭَﺍﻟْﺨَﺎﺗِﻢِ
ﻟِﻤَﺎ ﺳَﺒَﻖَ ﻧَﺎﺻِﺮِ ﺍﻟﺤَﻖِّﺑِﺎﻟْﺤَﻖَّ ﻭَ ﺍﻟﻬَﺎﺩِﻱ ﺇﻟﻰ ﺻِﺮَﺍﻃِﻚَ
ﺍﻟﻤُﺴْﺘَﻘِﻴﻢِ ﻭ ﻋَﻠَﻰ ﺁﻟِﻪِ ﺣَﻖَّ ﻗَﺪْﺭِﻩِ ﻭ ﻣِﻘْﺪَﺍﺭِﻩِ ﺍﻟﻌَﻈِﻴﻢِ
FASSARA
ﺍَﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺻَﻞِّ ﻋَﻠﻰ ﺳَﻴِّﺪِﻧَﺎ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ
ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDNA
MUHAMMAD,
“Ya ALLAH! Kayi Salati Ga Shugabanmu
Annabi MUHAMMADU”

ﺍَﻟﻔَﺎﺗِﺢِ ﻟِﻤَﺎ ﺃُﻏْﻠِﻖَ
AL FATIHI LIMA UGLIQA,
“Wanda Ya Bude Abinda Yake Rufe(Kafin
Manzon ALLAH Ya Bayyana Komai Yana Cikin
Taskar ALLAH Sai Da Ya Zo Ya Bude)”

ﻭَﺍﻟﺨَﺎﺗِﻢِ ﻟِﻤَﺎ ﺳَﺒَﻖَ
WAL KHATIMI LIMA SABAQA
“Wanda Ya Zama Cikamakin Dukkan Abinda ya rigaya
"(Annabawa Da S**a Gaba Ce Shi)”

ﻧَﺎﺻِﺮِ ﺍﻟﺤَﻖِّﺑِﺎﻟْﺤَﻖَّ
NASIRIL HAQQI BIL HAQQI,
“Wato Shi Manzon ALLAH(S.A.W), Mai
Taimakon Gaskiya Da Gaskiya Ne,

Qur’ani Yana Cewa:’WA AMINU BIMA NUZZILA ALA
MUHAMMADIN WAHUWAL HAQQU”
ﻭَ ﺍﻟﻬَﺎﺩِﻱ ﺇﻟﻰ ﺻِﺮَﺍﻃِﻚَ ﺍﻟﻤُﺴْﺘَﻘِﻴﻢِ
WAL HADI ILA SIRADIKAL MUSTAQIM’
“Mai Shiryarwa Zuwa Hanyarka (Hanyar Allah) Madaidaiciya,
Haka ALLAH(S.W.T) Ya Fada Masa:’WA
INNAKA LA TAHDI ILA SIRADIL MUSTAQIM”

ﻭ ﻋَﻠَﻰ ﺁﻟِﻪِ ﺣَﻖَّ ﻗَﺪْﺭِﻩِ ﻭ ﻣِﻘْﺪَﺍﺭِﻩِ ﺍﻟﻌَﻈِﻴﻢِ
WA ALA ALIHI HQQA QADRIHI
WAMIQDARIHIL AZIM,
“Ya ALLAH Idan Zaka Masa Salatin Ka Sanya
Hadda Mutanen Gidansa, Kuma Ka Masa
Salatin Gwargwadon Girmansa a Wajenka,
Dama Kai Kasan Shi, Ka Kuma San
Girmansa Wanda Ya Kai Matuqa”

faɗakarwa:-

Wannan Ita Ce SALATUL FATIH Da Wasu Suke Zagi, Dukkan Lafuzan Cikinta suna Daukaka Darajar SAYYIDUL-WUJUDI (S.A.W) Ba Qasqantar dashib,

Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah
✍️ ✍️

Gaskiya ne ya Sheikh, Allah bamu ikon gyarawa 🤲
16/09/2023

Gaskiya ne ya Sheikh, Allah bamu ikon gyarawa 🤲

Ahlan Bi Shahril Mauludi 🤸🏼‍♀️ Shahril Ulaa Was Su'udadi 💓Shahrin Nabiyyin Ahmadi ✨Shahri Rabi'il Auwali 🌙Ina Mika sakon...
16/09/2023

Ahlan Bi Shahril Mauludi 🤸🏼‍♀️
Shahril Ulaa Was Su'udadi 💓
Shahrin Nabiyyin Ahmadi ✨
Shahri Rabi'il Auwali 🌙

Ina Mika sakon Barka da shigowa Watan Rabi'ul Auwal wa Daukacin Musulmi Masoya Manzon Allah S.A.W na Duniya baki daya.

Watan da aka bayyanar da Hasken Duniya da Lahira.

Watan da aka Kore Karya, aka bayyana Gaskiya.

Watan da aka Aiko Shugaban Duniya da Lahira.

Watan da Duniya ta cika da Haske.

Watan da Albarka ta cika duniya.
Watan da ta rushe Katangan Kisra.

Watan da Duk wani Musulmi ke Farin ciki dashi.

Watan da dukkan Halitta ke cin Albarkacinta. Da........

Watan Mauludi

Ya Allah muna tawasulli da wannan Watan da ka kara mana Lafiya da Zaman Lafiya a kasarmu Nigeria baki daya.

Allah albarkacin wannan wata ka kara mana Arziki da wadata, don Albarkan Annabi Muhammad S. A. W.

HAPPY MAULUD... 1445/2023.

YAN NIGERIA  BASU KYAUTATA AMFANI DA ARZIKIN DA ALLAH YA HUWACE MUSU.Lura mana...!  ALLAH ya huwacewa Nigeria arziki mai...
10/09/2023

YAN NIGERIA BASU KYAUTATA AMFANI DA ARZIKIN DA ALLAH YA HUWACE MUSU.

Lura mana...!

ALLAH ya huwacewa Nigeria arziki mai tarin yawa, amma Arzikin ya zamo abin amfanarwa ne ga wasu kasashen Duniya da kuma wasu 'yan tsirarun Shugabanni, ayayin da kaso 80% na al'ummar kasar ke fama da talauci matsananci.

Haka abin yake ta bangaren Addini, ALLAH ya huwacewa NIGERIA Malaman da Duniyace baki dayanta ke amfana da ilminsu da dimbin litattafan da s**a rubuta na fatawowi a fannoni mabambanta, amma abin mamaki sai kaga wani da jiya ya koyi farfaru da babbagu yau yazo ya tara mutane a cikin Masallaci yana nuna shine ya fahinci addini, yana zagi da la'antar wadancan da Duniyar Ilmi ta risinawa, wanda hakan yasa dayawa yau ana talaucin Ilmin Addini tsakanin talakawa fiye da kashi 70%, gwargwadon Jahilcin Malami da iya tsara zancensa, gwargwadon yawan mabiyan da zai tara.

WALLAHI ABINDA ALLAH YA HUWACEWA MAULANA SHEIKH SHARIFF IBRAHIM SALEH ALHUSSAINI (R.T.A) NA ILMI, ABIN WADATARWA GA NAHIYAR AFRICA DA DUNIYA BAKI DAYANTA, AMMA BABU MAI IYA FAHIMTAR HAKA, SAI WANDA YA BIBIYI LITATTAFANSA.

FATAN MU ALLAH YA KARA MASA LAFIYA DA TSAWON KWANA ALBARKACIN MANZON ALLAH (S.A.W).

Muhammad Usman Gashua ✍️

Today's Best Photo ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️        's Best            •      
05/09/2023

Today's Best Photo ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️








's Best














Address

Zawiyyar Harazimiyya
Tsangaya

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tijjaniyya youth social media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share