26/10/2023
Atiku Abubakar Dan Kishin Dumokradiyya ne-Yasir Ramadan Gwale
Hukuncin kotun koli a ranar Alhamis ya nuna cewa duk wata Shariah da ta ke da alaka da zaben shigaban kasa na 2023 a Najeriya ta zo karshe, kuma shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu shi ne halastaccen shugaban Najeriya. Don haka babu wani batun sabon zaben shugaban kasa ko zuwa kotu har sai nan da shekarar zabe ta 2027. Nan da shekaru hudu masu zuwa, Alhaji Atiku Abubakar zai cika shekaru 81 a duniya, bana zaton a wannan lokacin idan Allah yasa yana nan zai iya samun damar tsayawa takarar shugabancin Najeriya a karo na biyar.
Babu mamaki Allah bai kaddarawa Alhaji Atiku Abubakar zama shugaban Najeriya ba, wannan kuma ba wata tawaya bace a gare shi, watakila nan gaba cikin zuri'arsa a samun wanda za su yi shugabanci har zuwa matakin shugaban kasa. Amma sanin kowa ne cewar Alhaji Atiku Abubakar yana daga cikin manya kuma fitattun 'yan siyasa a Najeriya da tarihi ba zai manta da su ba. Na taba jin dan Masanin Kano ya fada cewar mutum biyu a Arewa ba a yi 'yan siyasa k**arsu ba, idan ka cire Sa Ahamadu Bello to babu k**ar Shehu Musa YarAdua da kuma Atiku Abubakar. Kamar yadda yace a kudu idan ka cire Awolowo, babu wasu 'yan siyasa k**ar MKO Abiyola da Bola Ahmed Tinubu ba a cewarsa.
Ba shakka Alhaji Atiku Abubakar jajirtaccen dan siyasa ne maras tsoro kuma jarumi. A yanzu a Arewa babu wani dan siyasa da ya kai Atiku kashe kudi wajen yin hidima ga al'umma sarakuna da attajirai da talakawa, yana kashe kudi k**ar baya tsoron talauci, wadan da duk s**a yi mu'amala ta kurkusa da shi suna bayyana shi a matsayin mutum mai karamci da taakawa ga kuma tsoron Allah, mutum ne ance mai girmama mutane da son yi musu hidima da aljihunsa. Abu guda daya da ba zaka taba zargin Alhaji Atiku Abubakar da shi ba shi ne rashin kishin demokaradiyyar Najeriya. Zaka iya zarginsa da komai, amma ba zaka zarge shi da rashin kishin demokaradiyya a Najeriya ba.
Ko shakka babu Atiku Abubakar mutum ne da ya yadda kuma ya gamsu da samar da dunkulalliyar Najeriya da kowa zai yi alfahari da ita a matsayin dan kasarta, bugu da kari kuma gashi cikakken dan demokaradiyyar da ya yadda da hidimtawa alumma fama kasa baki daya a ko da yaushe. Shi ne dan siyasa guda daya tilo a wannan zamanin daga yankin Arewa da zai yi maka kyautar da baka taba tsammani ba, mutane su zage shi suci mutuncinsa gobe su dawo wajensa kuma ya dauki kudi ya basu yana murna yana fara'a, samun dan siyasa kwararre irinsa sai an tona kwarai da gaske muna yiwa Alhaji Atiku Abubakar fatan alheri da fatan Allah ya karbi kyawawan ayyukansa na alheri ya kuma yafe kurakuransa baki daya Amin.
Muna fatan alheri ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Allah yayi masa jagoranci ya tafiyar da kasarnan cikin Aminci da gaskiya da kuma rikon amana. Halin da ake ciki na tsanani da kuma tsada da hauhawar farashi, muna fatan Allah ya bashi basirar dawo da Najeriya cikin hayyacinta ta zama kasar da zamu dinga alfahari da ita a ko da yaushe. Muna kuma fatan shugaban a wannan lokacin zai rage nuna bambanci da kabilanci wajen rabon manyan muk**ai musamman wanda suke da maiko sosai.
Muna fatan ya mayar da hankali akan batun rashin tsaro musamman a yankin Arewa Maso yamma da kuma fatara da talauci da ta yi katutu a wannan yankin namu. Muna bukatar ayyukan cigaba da raya kasa ba tare da nuna mana bambanci ko wariya ba. Allah ya taimaki kasarmu Najeriya Amin.
Yasir Ramadan Gwale
26.10.2023