
30/05/2025
Sanata mai wakiltar babban birnin tarayya, Ireti Kingibe, ta caccaki minista Nyesom Wike a kan kudin hayar kasa a babban birnin tarayya Abuja.
Kingibe ta ce ba ka'ida ba ne a kwace wa mutum fili ko gida saboda bai biya kudin hayar fili ba maimakon a kwace sai dai a yi mishi tara kuma a bashi lokaci ya biya.