Ankin Cin Biri Anci Dila Munafukan Banza
AKWAI KUSKURE NA GANGANCI
Jiya mutane sun kalubalance ni akan cewa gurin bikin dinner da Babban Malamin Sunnah Sheikh Kabiru Gombe ya halarta ai babu kida, kuma babu cakuduwar mata da maza
Ku kalli wannan bidiyo, akwai kida da waka, sannan akwai haduwar mata da maza a ciki, zaku ga shi kansa Sheikh Kabiru Gombe bai ji dadin yanayin ba
An riga da an samu babban kuskure, jiya Sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo shima ya bayyana takaicinsa a kan zuwan su Malam Kabiru Gombe gurin nan a karshen karatunsa, yayi tsokaci da nasiha, kuma yace wani satin zai cigaba
Babu wani kwaskwarima da za'ayi wajen bawa su Malam Kabiru Gombe kariya anan, kuskure Malam sun yi, kuma kuskure ne na ganganci, domin duk abinda kasan zai saka maka shubuha to gudunsa wajibi ne
Sai dai wannan ba shine dalilin da zai sa a ci mutuncin Sheikh Kabiru Gombe ba, domin alherinsa ya rinjayi kuskurensa yawa bisa abinda ya bayyana garemu, amma hakan ba shine zai sa a ja baki ayi shiru ba, saboda kuskure ne da ya bayyana a zahiri ga kowa
Muna fatan Allah Ya yafe wa su Malam, Ya basu ikon gyara kuskurensu