13/01/2025
πππππππππππ π¨π'ππππ ππππππ π£πππ'π¦π
Gaskiya muna fuskantar matsalar rashin kyakkyawan shugabanchi da adalci a Arewa.
Shugabanni sun yi biris da matsalar :-
Tsaro,
Kiwon Lafiya,
Ilmi,
Kimiya da Fasahar Zamani,
Matasa,
Masana'antu,
Noma da sauransu.
Hakika, sai an bunkasa wadannan fannonin ne, har za'ayi tunanin fita daga cikin matsalolin.
Babban abin ban haushi shine, babu wata alamar da ke nuna chewa manyan Arewa suna da kudurin kawo karshen wannan dambawar dake addabar Arewa.
Ya kamata Talakawa su yiwa kawunan su mafita, ta hanyar dawowa daga rakiyar azzalumman shugabanni. Maimakon haka, su jajirche wajen ganin suna zaben shugabannin da ke da adalci da son ci gaban yankin mu na Arewa.
Allah Ya yi mana mafita ta alkhairi. Amin
Sokoto Solidarity Group