Mikiya Reporters

Mikiya Reporters MIKIYA Reporter: Kafar yada labarai a online dake da gurin sanar daku abinda ke faruwa a fadin duniya

'Yan Nijeriya sun kone datar waya da ta kai giga miliyan 998.79 a cikin watan DIsamban 2024Karin bayani: https://is.gd/J...
01/02/2025

'Yan Nijeriya sun kone datar waya da ta kai giga miliyan 998.79 a cikin watan DIsamban 2024

Karin bayani: https://is.gd/JR0fGy

Shugaban EFCC ya caccaki ƴan Nijeriya kan kare shugabanni masu cin hanciShugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (E...
01/02/2025

Shugaban EFCC ya caccaki ƴan Nijeriya kan kare shugabanni masu cin hanci

Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Ola Olukoyede, ya ce ‘yan Najeriya na s**ar cin hanci da rashawa amma suna goyon bayan shugabanni masu laifi yayin da ake gurfanar da su a kotu.

Olukoyede ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a a Abuja yayin da jami’an Cibiyar Sadarwa da warware rikici ta (CCC), karkashin jagorancin Chris Olukolade, daraktan kwamitin amintattu na cibiyar, su ka kai masa ziyara.

Shugaban na EFCC ya ce idan kowa ya dauki rashawa a matsayin abokiyar gaba gaba, rashin ci gaba zai zama tarihi a kasar.

“Daya daga cikin manyan matsalolin da ke hana ci gaban Najeriya ita ce cin hanci da rashawa, kuma idan aka magance ta, rashin ci gaba zai zama tarihi,” in ji Olukoyede.

“Duk al’ummar da ke son ci gaba ba alhakin gwamnati kadai ba ne zai sa ta samu wannan ci gaba, har da na ‘yan kasa gaba daya," in ji shi

Namiji ba ɗan goyo ba ne! In ji wasu matanMace zuma ce sai da wuta" in ji wasu mazanA ganinku me ke sanyawa maza da mata...
01/02/2025

Namiji ba ɗan goyo ba ne! In ji wasu matan

Mace zuma ce sai da wuta" in ji wasu mazan

A ganinku me ke sanyawa maza da mata ke jifar juna da wadannan kalamai?

AlhamdulillahiAn tabbatar muna jama'a sun fara bada taimako, gwargwadon hali.Allah yasa muku da Alkhairi, sai dai bamu s...
01/02/2025

Alhamdulillahi

An tabbatar muna jama'a sun fara bada taimako, gwargwadon hali.

Allah yasa muku da Alkhairi, sai dai bamu sani ba ko yadade mu nemi da su tura mana alert na mutanen da s**a taimaka mu wallafa.

Kodai abarshi sunyi don Allah ba sai mun nemi alert message din ba ?

Seeking Help for Allah’s SakeAs mentioned, there has been a complaint regarding seeking help for this servant of Allah n...
01/02/2025

Seeking Help for Allah’s Sake

As mentioned, there has been a complaint regarding seeking help for this servant of Allah named Mutiyat Lateefa, who recently had surgery at Ola Hospital Jos.

Although she was supposed to be discharged, financial difficulties are preventing her from returning home. She is an orphan with no one to assist her except for those whom Allah may send to help her.

Mutiyat Lateefa has no food or medicine for her recovery. The total cost of the surgery was N156,600, but her family has only been able to pay N13,000, leaving a balance of N143,600.

Therefore, we are seeking help from you for the sake of Allah, to support this woman, by the grace of Allah and the mercy of His Prophet.

Account Number:
6317275259
Bank Name: Fidelity Bank

For those in Jos, you can call the following number for verification:
08094649679

May Allah accept this help and assist this servant of Allah, and bless us all. Ameen.

If possible, sharing this message will also be considered a form of charity (Sadaqah)!

Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum
🤲

Gwamna UBA SANI ya share hawayen ƙungiyar malamai ta NUT game da kuɗadensu na adashen gata na ENDWELL, inda ya amince da...
01/02/2025

Gwamna UBA SANI ya share hawayen ƙungiyar malamai ta NUT game da kuɗadensu na adashen gata na ENDWELL, inda ya amince da biyansu Naira Miliyan 548.

A wani muhimmin mataki da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya dauka, Gwamnan ya bayar da umarnin sakin Naira miliyan 548 ga kungiyar malamai ta Najeriya NUT, da nufin warware takaddamar da aka dade ana fama da ita a tsakanin Gwamnatin Jiha da ƙungiyar NUT Kan kudin sallamar malamai.

Wannan taƙaddama da ta ɗauki lokaci ta jefa dubban malamai a jihar cikin halin ƙiƙi-ƙaƙa inda mai girma Gwamna ya kawo karshen wannan rikici. Wannan na nuna yadda Sanata Uba Sani ke fifita buƙatun malamai da kuma tabbatar da an yi musu adalci biyo bayan wannan babban mataki da ya ɗauka.

Yarjejeniyar da ɓangarorin biyu s**a sanyawa hannu a ranar 30 ga watan Janairu, 2025, na da nufin yauƙaƙa dangantaka tsakanin hukumar ilimin bai ɗaya ta jihar Kaduna(KADSUBEB ) da kuma kungiyar malaman ta NUT. Wannan mataki shi ya ƙara jaddada kudirin Mai Girman Gwamna na fifita ɓangaren ilimi da kula da buƙatun malamai da shimfida tsarin shugabanci na gari.

Gwamnatin Gwamna Uba Sani ta ba da fifiko kan harkokin ilimi da ci gaban al'umma. Tun daga lokacin da ya hau karagar mulki, Gwamnan ya inganta damar samun ilimi, samun karin yaran dake zuwa makaranta da kuma tabbatar da wadanda ke zuwan sun kammala.

Gudunmuwar da Gwamna ke bayar kan harkar ilimi ya bayyana kan yawan makarantun da ya gina cikin kanƙanin lokaci da kuma samar da kayayyakin koyo da horaswa domin inganta kwarewar malamai.

Bisa wannan cigaba da aka samu, yanzu malamai za su iya samun hakkokinsu, kuma gwamnatin jihar Kaduna a karkashin jagorancin Mai Girma gwamna, Sanata Uba Sani ta himmatu wurin samar da kyakkyawan tsarin samun nagartaccen ilimi da kula da jin dadin malamai, san nan da shugabanci na gari.

RUSHE RUSHE GIDAJE DA GOMNATIN BORNO SUKEYI!! ; SHIN WAYE YAFI GASKIYA NE? Sometimes Bakomai bane Lawyer zaiyyi magana m...
01/02/2025

RUSHE RUSHE GIDAJE DA GOMNATIN BORNO SUKEYI!! ; SHIN WAYE YAFI GASKIYA NE?

Sometimes Bakomai bane Lawyer zaiyyi magana mussamman idan akwai Karancin Hujja!

Wato Ana ta kirana da tura min messages akan na fito nayi magana akan abunda Gomnati takeyi.

Nasamu munyi magana da wasu waenda abun ya shafa wajen rusa musu gida kuma na samu nayi Magana da Babban Jami’ain Gwamnati Borno wanda shine Babbansu masu kula da Harka Filaye da Gidaje na Borno wato “ Engnr Bababe” kuma Yayi min Bayani dana Gamsu dashi.

A matsayina na Lawyer zan Gina kaina ne akan Hujja da kuma shaida mai inganci.

Na Farko ina mai bada Hakuri da jimami ga duk waenda abunan ya faru dashi. Gaskiya abun babu dadi. Naji takaici wannan abun yayi matukar tayar min da hankalina .

Mutum ya gina gidanshi anma azo a rushe mishi a rana daya. Abun babu dadin gani ko ji.
Allah ya baku ikon juriya da kuma samun fiye da wanda kuka rasa.

Anma ni Abunda yasaka ban saka baki na ba shine Har yanzu babu wanda yake da wata takarda na gomnati tabashi akan Gidansa da aka rusa.

Idan kuma akwai mai wata takarda ta gwamnati ya kawo min ko yayi min magana ta private messenger insha Allah zan tsaya masa kyauta kuma insha Allah zan kwato masa Hakkinsa har diyya sai an biyashi anma banda takardar Bulama “ Mai Unguwa”

Abun dai Babu dadi!

Amma idan zakayi fada yak**ata kana da kayan yaki. Bazaiyyi mu shiga harka na shariah ko fadawa gomnati Gaskiya ba babu abunda zamuyi dogoro dashi ba.

Nima Abun Bai mun dadi ba amma Kamar GOMNATI TA FIMU GASKIYA !

Saboda yawanci mutane sun saya Filaye a wajen Bulama “ Mai Unguwa” batare da wani Bincike ba “ Search” kuma batare da sun tuntunbi Maaikatar Kula da filaye ba ko kuma Hukumar Bunkasa Gari ba.

Sai dai ina Rokon Gomnati ta shiga Lamarin wanenan mutanen. Ta taimamusu tunda duk jama’anta ne. Kuma Gomnati na Jama’ane. Ba’q gyara Kuskure da Kuskure. Ayi Hakuri Don Allah Gomnatin ki dubi Al’amarin mutanenki.

NEMAN TAIMAKO DON ALLAH.Kamar yadda mukayi bayani sun samu koke akan mu nemawa wannan boyar Allah taimako kwanan nan.Ita...
01/02/2025

NEMAN TAIMAKO DON ALLAH.

Kamar yadda mukayi bayani sun samu koke akan mu nemawa wannan boyar Allah taimako kwanan nan.

Ita dai wannan baiwar Allah mai suna Mutiyat Lateefa anyi mata aiki a asibitin Ola Hospital Jos yau sati daya kenan.

Ya k**ata a sallame ta amma matsalar kudi ya hana su tafıya gida, ga ta marainiyar Allah bata da kowa sai wanda yaga Allah ya taimaki ta.

Abincin da zataci da magungunan da zata rika sha ma bata dashi.

Kudin aiki N156,600 iya abinda yan uwanta s**a iya biya shine N13,000 saura N143,600.

Dan haka muke naiman taimako fissabililahi a taimaka musu domin girman Allah da manzon rahama.

Ga account number account wadda ke jinyar ta nan ga wanda Allah yaba dama da iko mai 100 200 500 1000 har abinda ya sawaka.

Account Number
6317275259.
Bank Name:
Fidelity Bank

Ga wadanda ke garin Jos zasu iya kiran wannan number domin tabbatarwa.
08094649679.

Allah ubangiji yasa adace Ameeen ya hayyu ya qayyum 🤲

Sannan idan da daama kayi mana share, itama sadaqah ce !!!

Gwamnonin jam'iyyar PDP sun buƙaci shugaban riƙo na jam'iyyar, Amb. Iliya Damagum ya shirya babban taron ƙoli na jam'iyy...
01/02/2025

Gwamnonin jam'iyyar PDP sun buƙaci shugaban riƙo na jam'iyyar, Amb. Iliya Damagum ya shirya babban taron ƙoli na jam'iyyar na ƙasa ranar 13 ga watan Maris na wannan shekarar.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar, Sanata Bala Mohammed - wanda shi ne gwmann Bauchi ya fitar bayan taron gwamnonin a jihar Delta.

Haka kuma gwamnonin sun tabbatar da Sunday Ude-Okoye a matsayin halastaccen sakataren jam'iyyar na ƙasa, bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da shi.

RIKICI YA ƁARKE A JAM'IYYAR APC TA ƘASAJam'iyyar APC ta ƙasa ta faɗa cikin mummunan rikici wanda zai iya jefata cikin ya...
31/01/2025

RIKICI YA ƁARKE A JAM'IYYAR APC TA ƘASA

Jam'iyyar APC ta ƙasa ta faɗa cikin mummunan rikici wanda zai iya jefata cikin yanayin da zata rasa kujerar shugaban ƙasa da gwamnonin jihohi, ƴan-majalissar tarayya da sanatoci a zaɓe mai zuwa 2027

Jam’iyyar APC na shirin dakatar da manyan membobinta, ciki har da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai; tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi; tsohon ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola; tsohon Ministan shari'a Abubakar Malami SAN; da kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi.

Ana zargin cewa wasu daga cikin waɗannan manyan ‘yan siyasar sun nuna rashin amincewa da shugabancin jam’iyyar, inda s**a yi kakkausar s**a ga yadda ake gudanar da harkokin jam’iyyar da kuma yadda ake gudanar da mulki a ƙasar Wannan ya haifar da cece-kuce da tashe-tashen hankula a tsakanin membobin jam’iyyar, wanda hakan ya sa shugabannin APC s**a yi la’akari da daukar matakin dakatar dasu.

Hausawa sunce alhaki kuikuyo ne maishi yake bi, sabo da irin zalincin danniya da babakeren da gwamnatin APC keyi a ƙasar nan tsawon shekaru goma (10) Allah(S.W.A) bazai barsu su zauna lafiya ba.

Ya Allah ka kawo mana ƙarshen gwamnatin Apc a nigeria 2027 ka sauya mana su da shugabanni masu kishin cigaban ƙasa da taimakon talakawa.

Aliyu Sale K.o Turmi
Masoyin Jigawa da Nigeria

An ruwaito kashe Salwan Momika mai shekara 38 ne a yammacin ranar Laraba a wani gida a birnin Stockholm.Karin bayani - h...
30/01/2025

An ruwaito kashe Salwan Momika mai shekara 38 ne a yammacin ranar Laraba a wani gida a birnin Stockholm.

Karin bayani - https://bbc.in/4hBceu7

30/01/2025

AKWAI BOYAR ALLAH
Data aiko mana ta sako a DM tana neman al'ummah su taimaka mata.

Wakilin mu zaije gobe yaganta da kanshi, muka ta inda zamu taimaka ta hanyar nema mata taimako ga yan uwa musulmi.

Amma sai in mun tabbatar da gaskiya abinda ta gaya muna.

HATSARIN MOTA:Kyauta dillaliyi sunyi hadarin mota ta samu raunuka a fuska. Ku saka ta cikin addu'a ?
30/01/2025

HATSARIN MOTA:

Kyauta dillaliyi sunyi hadarin mota ta samu raunuka a fuska.

Ku saka ta cikin addu'a ?

Da dumi'dumi Kotun a Abuja ta bayar da Belin Sowore kan ₦ 10million beli tare da umarnin mika Passport ta  ba da awa 24 ...
30/01/2025

Da dumi'dumi Kotun a Abuja ta bayar da Belin Sowore kan ₦ 10million beli tare da umarnin mika Passport ta ba da awa 24 don Cika sharudan belin.

Kamfanin Meta mamallakin Facebook da Instagram zai ba wa Donald Trump kudin shafe hawaye dala miliyan 25.A shekarar 2021...
30/01/2025

Kamfanin Meta mamallakin Facebook da Instagram zai ba wa Donald Trump kudin shafe hawaye dala miliyan 25.

A shekarar 2021 kamfanin ya toshe shafukan Shugaba Trump na Facebook da Instagram bayan harin da 'yan jagalisarsa s**a kai a harabar majalisar dokokin Amurka.

Shugaba Trump ya shigar da kara a kotu yana mai kalubalantar matakin Meta.

Da Dumi-DumiJami‘an tsaro sun k**a Farfesa Usman Yusuf a yammacin wannan Laraba a gidansa da ke Abuja.Majiyoyi daga iyal...
29/01/2025

Da Dumi-Dumi

Jami‘an tsaro sun k**a Farfesa Usman Yusuf a yammacin wannan Laraba a gidansa da ke Abuja.

Majiyoyi daga iyalansa sun shaida wa DCL Hausa cewa jami‘an tsaron ba su bayyana dalilin k**a tsohon shugaban hukumar inshorar lafiyar Nijeriyar ba. Amma dai ya yi kaurin suna wajen s**ar manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta Nijeriya

Jam'iyyar APC Ba Ta Da Ƙarfin Da Za Ta Iya Warware Matsalolin Nijeriya, Inji Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-rufa...
29/01/2025

Jam'iyyar APC Ba Ta Da Ƙarfin Da Za Ta Iya Warware Matsalolin Nijeriya, Inji Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-rufa'i

Me za ku ce?

Alhamdulillah Yan Hisba a Jihar Gombe hadi da 'yan sanda sunyi Nasarar k**a wannan yarinya tareda mai mata video wannan ...
29/01/2025

Alhamdulillah Yan Hisba a Jihar Gombe hadi da 'yan sanda sunyi Nasarar k**a wannan yarinya tareda mai mata video wannan yaro dan daudu

Tana hannun yan hisbah shikuma ankai sa komar yan sanda a yanzu

Yarinyar marainiya ce mahaifinta yarasu tun tana karama mahaifiyar ta kuma tayi aure

Mutane da dama sunnuna son taimaka mata dan gyara rayuwar ta wannan yake nuna mana Jihar Gombe garin addini ne ba garin yan daudu da kawalai ba

Allah ka shirya mana Amin Amin.

✍️ Ismail Abubakar Maisalati

Address

No. 45 Tudun Wada Kaduna
Sokoto
58973

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mikiya Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Mikiya Reporters:

Videos

Share