![](https://img5.medioq.com/574/704/235138085747045.jpg)
02/04/2023
Kanal Abdul'aziz Musa Ƴar'adua Shi yafi Kyautuwa da zama Sanatan Katsina ta Tsakiya a shekarar 2023...
Daga Falalu Lawal Katsina
Lokaci Yayi Daya kamata Al'ummar shiyar Katsina ta Tsakiya Su mayar da biki Ga iyalai da Ƴan'uwan Marigayi Tsohon shugaban kasar Nigeria Marigayi Malam Umar Musa Ƴar'adua bisa alkhairin da yayiwa mutanen Jahar katsina da Najeriya baki ɗaya ta Hanyar zaɓar Ƙaninsa matsayin Sanatan Katsina Zone Ƙarƙashin Inuwar Jam'iyyar APC..
Idan Mukayi Duba ta Hanyar Cancanta to Matawallen Katsina Kanal Abdul'aziz Musa Ƴar'adua ya cancanta da a zaɓesa kasantuwarsa Mutumin kirki Kuma mai Ilmin Addini dana zamani, Mutum ne mai aiki da ilimin sa na addini dana zamani kuma sune kemasa jagoranci ya kuma kasance mutum dake sauraren al'umma komin girman ko karantar ka baya cikin jerin yan siyasar da ake shata shamaki wajen ganinsu ko yin magana dasu, Ya kasance kofar sa bude take ga kowa musamman inka taba ziyartar sa a gidan sa zaka tabbatar da hakan.
Tabbas irinsa ne muke bukatar su wakilce mu don duk lokacin da mukeson isar da korafin mu zuwa zauren majalissa bazamu sha wahala ba, Sabanin irin wadanda boys sukeyi tsakanin su da al'ummomin da s**a turasu su wakilce su.
Muna masu kira ga Ɗaukacin Al'ummar Katsina Zone da su fito Ranar zaɓe kwa nsu da Ƙwarkwata su kaɗa Ruwan ƙuri'u ga Mai Girma Matawallen Katsina Kanal Abdul'aziz Musa Ƴar'adua domin Tabbatar dashi matsayin Sanatan Katsina Zone...