14/08/2022
Expansion of The Universe (1):
_______________________________________
Sau da yawa zaka ji ana cewa wannan duniyar da muke ciki (Earth) tana 'kara fadi, girma da kuma yawa, Malaman Kimiyya Cosmologists, Astronomers da sauran masana sunce wannan duniyar da muke ciki ta faro ne tun shekaru Biliyan 13 da Miliyan 800 wato (13.8 Billion year Ago) da s**a wuce, tun bayan faruwar "Big Bang" wato Theory nan na "Big Bang Theory" na George Lematire.
Wannan Theory din tuntuni Al-Qur'ani ya gama bayanin sa fiye da shekaru 1,400 da s**a wuce, a Suratul Ambiyaa' (C-21 V-30).
Cewa asali sama da 'kasa a manne suke, a hade suke, sai Allah ya raba su, aka samu sama da 'kasa.
Amma yadda Malaman Musulunci s**a fassara Ayar tasha bam-bam da yadda Turawa s**a fahimci Big Bang Theory.
Tun daga lokacin da aka samu sama da 'kasa s**a ce duniyar tana 'kara fadi, tana 'kara girma da yawa ta kowane bangare, k**ar yadda "Baloon" ko "Balam Balan" yake 'kara fadi ta kowane Angle idan ana hura masa iska, haka ma duniya take Kara girma.
Duniya tana Kara girma, tana Kara fadi wannan gaskiya ne, toh sai dai akwai sabanin fahimta game da yadda fadin yake kasancewa, kafin 1920 Malaman Kimiyya suna cewa "The size of the universe was fixed and not changing", wato fadin wannan duniya tabbatacce ne, baya canzawa".
Sai dai a farkon shekarar 1912 wani Malamin Kimiyyar sararin samaniya "American astronomer" mai suna "Vesto Slipher" ya gano cewa wannan duniyar ba tsaye take waje guda ba ta wajen fadin ta, tana karuwa, yace:
"Slipher, noticed that the galaxies were moving away from earth at huge velocities", wato manyan Kwallon da duniyoyi suke ciki (Galaxies) suna 'kara nesanta kansu daga wannan duniyar tamu ta Earth, wannan yasa ya fahimci cewa duniyoyin suna yin nesa da Earth ne saboda ita Earth tana Kara girma, tana Kara fadi. Kamar ka ajiye Bokiti ne a kusa da kai, bayan minti biyu sai kaga yayi nesa da kai Nisan da sai kayi tafiyar Minti biyar kafin kaje inda yake.
Haka Galaxies suke Kara nisa da Earth.
Wannan shine Theory na farko da ya fara sauya tunanin masana Kimiyya daga Fixation of the universe sizes, wato the first turning point.
A wannan gabar zaka fahimci abu na farko shine fadin duniya shine Nisan da sauran duniyoyi suke Kara yi da Earth, suna baya baya da ita, wato kenan ba kasar da muke kanta ne take Kara fadi ba, tsakanin duniyar mu ta Earth da sauran duniyoyi ne nisan da fadin yake Kara karuwa.
A shekarar 1916 babban Masanin Kimiyya na duniya wato Albert Einstein, ya kawo babban Theory din nan nasa Mai cike da ban mamaki ga Turawa (kadai) wato "General Theory of Relativity Time and Space".
In 1916 Albert Einstein formulated his General Theory of Relativity that indicated that the universe must be either expanding or contracting.
A cikin Theory din, Albert Einstein yana fahimtar ko dai duniyar nan tana Kara fadi ko tana raguwa, dole za'a samu daya, da yace expanding or contracting ba yana shakka bane, saboda idan ka karanta Theory din zaka ga facts din da ya kawo na tabbatar da fadi duniya take karawa.
Amma tabbatuwar haka ga duniya bai samu ba sai a 1929 wani American Astronomer Mai suna "Edwin Hubble" ya tabbatar da haka, acikin theories dinsa da akai compiling ake kira da (Hubble's Law).
A yau, Malaman Kimiyya suna cewa Galaxies are moving away from the Earth with almost 73 kilometers par second per megaparsec, kowane Megaparsec Kuma yafi One million light years.
Wadanda s**a iya buga wannan lissafin zasu fi kowa fahimtar wannan gabar. Abinda wannan yake nufi duk galaxy din da yake nesa da 'dan uwan sa a sararin sama da tazarar Over one million light years toh yana gudu daga dan uwa sa da abinda ya wuce 73 kilometers per second. So, zaka fahimci duniyar mu da sauran duniyoyi suna Kara nesa da juna sosai.
Hakan ya Kara tabbata daga hukumar NASA na kasar America suna cewa duk da cewa duniyar wata tana cikin Universe din su, Amma tazarar dake tsakanin zuwan farko da s**a yi yasha bam ban da kowane zuwa, a koda yaushe Nisan Kara yawa yake.
But, shin muna da wasu dalilai daga Al-Qur'ani da Sunnah da suke nuna duniyar mu ta Earth tana 'kara fadi da girma?
Amsa itace Eh, akwai.
Duk da cewa rubutun ya fara yawa, bari mu duba wasu abubuwa kadan daga Al-Qur'ani da Sunnah.
A cikin Suratuz Zaariyaat, Surah ta 51, Aya ta 47, Allah yana cewa:
والسماء بنيناها بأييد وإنا لموسعون
"Kuma sama (duniya) mun Gina ta da karfi, Kuma tabbas mu masu fadada ta ne".
Malamai da dama sunyi fassara daban daban ma wannan Ayar, zamu dauki daya kawai Wanda yake alaka da gundarin kalmar data zo a karshen Ayar, itace موسعون
Amma kafin mu fahimci Ayar sai mun fahimci wasu abubuwa biyu game da ita:
1. Farko, dole mu fahimci kalmar أييد data zo acikin Ayar, saboda kalmar ta Sha bamban da yadda aka Saba gani a galibin rubutu.
Duk Al-Qur'anin da kaga bugun sa a dai dai wannan Ayar an rubuta أيد da Ya'un kwaya daya ba Al-Qur'anin gaskiya bane.
Domin idan ka fassarar Ayar da Ya'un daya toh kana nufin "Mun halicci sama da hannu, block da block", which is totally wrong.
Ba kuskure bane kaga Ya'un biyu a dai dai kan Ayar, asalin Masdar din ta (Root Word dinta) shine (آد) ba daga يد na hannu bane, na karfi (Might).
2. Na biyu:
Arabic Language da aka yi amfani dashi acikin Ayar a zamanin da Ayar take sauka, kalmar "السماء" wato Sama, ana nufin (Duniya) ba wai sama sama dai da kake daga Ido ka kalla ba.
Duniya, k**ar yadda ake kiran Aljannah da "Heaven" madadin ace Paradise.
Kamar yadda aka cewa Mahaifiyar Annabi Isah (A.S) Nana Maryam "Kiyi Ruku'u tare da masu yin Ruku'u", ba zallan Ruku'u ake nufi ba, complete Sallah ake nufi.
So, idan mun fahimci wannan, sai muce ana nufin "Mun halicci duniyar da karfi, Kuma muna da ikon fadada ta (Expanding) ne". Al-Qur'ani yayi wannan bayanin tun 1400 years Ago, Turawa sun gano haka a 1929 wato shekaru 93 da s**a wuce rak.
Yayin da Manzon Allah ya gama sharhin wannan Theory din shekaru dubu 1,400 da s**a wuce.
Shiyasa "Michel Nestradamous" yace duk wani binciken da ake gani a wajen su suna samun link da leakages ne daga littafin Annabin Larabawan nan. Wannan fa babban researcher ne a duniya kaf an San dashi (Michel Nestradamous).
Imamul Bukhaariy ya ruwaito Hadisi, Manzon Allah (S.A.W) ya bada labarin wani mutum da ya kashe mutane 100, sai ya Tuba, sai Malamin da ya bashi Fatawar ya tuba din yace masa, ya bar garin, ya koma wani gari dake can nesa, yaje ya zauna ya cigaba da Ibada wa Allah acan.
Manzon Allah yace yana cikin tafiya sai mutuwa taje masa, bayan ya mutu sai Mala'ikun Rahama dana Azaba suke je daukan ransa. Mala'ikun Azaba suna cewa "Mu zamu dauki ransa mu kaishi Azaba, saboda 'dan ta'adda ne, ya kashe mutane 100, bai taba yin aikin alkhairi ba tun da yake".
Mala'ikun Rahama suna cewa:
"A'a, to ai ya tuba, yazo yana Mai tuba zuwa ga Allah".
Mala'ikun Rahama dana Azaba suna ta jayayya, Manzon Allah yace sai Allah ya turo wani Mala'ika yazo da abin gwaji, ya zama mai alkalanci a tsakanin su, yace a auna idan aka ga yawan Nisan kilometers din da mutumin yaci yafi kusa da garin su, garin da ya kashe mutane 100 toh Mala'ikun Azaba su dauke shi, idan kuma aka ga yafi kusa da garin mutanen kirki da ya nufa to Mala'ikun Rahama su dauke shi.
Sai aka gwada aka ga yafi kusa da garin mutanen kirki da yayi nufin zai je, sai aka ce Mala'ikun Rahama su dauke shi.
A Ruwayar Imamul Bukhaariy, Manzon Allah yace:
"Sai Allah yayi wahayi wa wancan kasar cewa ta bude, wannan kuma ta tsuke ta matsa, sai s**a yi hakan, sai aka ga hatta kirjin sa ma ya fuskanci garin da yayi nufin zai je".
Karanta Sahihul Bukhaariy, Hadisi na 3,470.
Kasar ce ta Buda, ta Kara fadi, dama hakan na yiwuwa ne? ta Yaya aka yi haka?
Akwai Ayoyin da zasu duba nan gaba, a rubutu na biyu, in Sha Allah.
Wannan Hadisin kenan, sharhin sa Scientifically yana da ya yawa, bari mu tsaya a nan kawai.
Kafin mu tsaya da rubutun, wani zai ce shin dama bayan wannan duniyar akwai wasu duniyoyin ne, akwai wani wajen da akwai sama, akwai kasa, akwai taurari akwai duwatsu, rana da wata irin wannan duniyar tamu Kuma babu kowa a ciki yanzu haka?
Kwarai kuwa akwai, suna da yawa ma, amma kafin muje rubutu na biyu bari na bamu hint, muje mu fara research kafin rubutu na gaba, duba Suratu Yaseen, shafin karshe na Surar da Allah yace:
أوليس الذي خلق السماوات والأرض بقادر على أن يخلق مثلهم
Abin nufi:
"Yanzu (Allah) Wanda ya halicci (wannan duniyar) wadannan samman da kasa, Kuna ganin ba zai iya halitta wasu irin su ba?".
Tambaya Allah yayi, kuna ganin ba zai iya halitta wasu duniyoyin ba?
Allah da kansa ya bada amsa yace tabbatas zai iya, Karanta Suratu Yaseen shafin karshen.
Allah yasa mu dace.
Zamu tsaya a nan, a rubutu na biyu akan Expansion of the universe zamu kawo Hadisan Manzon Allah (S.A.W) da sauran Ayoyin Al-Qur'ani akai, tunda Aya daya kawai muka kawo yanzu, itace ta Suratuz Zaariyaat (C-51 V-47).
Akwai Hadisai da s**a tabbatar da wadannan facts din da ake ganin k**ar wai dama Turawa ne s**a binciko s**a kawowa duniya. No, ko kadan, it was in our scriptures since.
Allah yasa mu dace.
Copied
✍️
Abdul-Hadi Isah Ibrahim.
AIO Tv