02/03/2024
FIFIKON ILIMIN JAGORA (H) AKAN RIJIYAR LEMO.
Yin magana da larabci yana zamowa ma'auni na gane Wanda yafi ilimin addini?
Wasu wayanda basu fahimci meye ilimin addini ba Sai s**a dauka gwanancewa a Iya sarrafa kalmomin larabci a yayin magana a gaban jama'a shine ma'auni.
Bana Jin ko a ilimin boko idan kafi Iya turanci a yayin magana to ma'anar sa shine kafi kowa ilimi a fannin da ka Karanta.
Mun San akwai dayawan masu digirin digirgi a Iya komai na larabci Amma a fagen addini Sai Kaga basu da masaniya.
Shin rubuta littafi shi kadai ne hanyar da za'a Iya Gane mai ilimi?
Abinda masu hankali zasu Iya yarda dashi shine:
Lallai rubutun littafi daya ne daga hanyoyi na gane mai ilimi Amma ba dole bane Wanda ya rubuta littafi ya zamo mai ilimi, b***e yafi wasu ilimin.
Amma hanyar da sayed zakzaky (H) yakebi to itace tsantsar hanyar ilimi.
A hanyar isar da sakon addini da yakeyi munga yanda yayi nasara wajan canja Al'ummah ta fuskoki da dama.
Daga cikin canjin akwai kasancewar inkaga mahaifiyarka ko matar wani malamin ka a najeriya tana Sanya hijabi na shar'ia to daga sayed zakzaky H) ne.
Wannan canjin Bai kebanci Iya Yan Shi'a ba.
Idan sayed zakzaky H) yana magana to akan doron ilimi yake Dora duk wata magana tashi.
Kamar maganar kananun bullet 38 a cikin kansa wannan duk masu ilimin "Balagha" da masu ilimin "Mandiqi da Falsafa" da masu ilimin "Usulul fikih" dama wasu ilmummukan zasu fahimci maganar.
Amma duk Wanda yayi inkarin maganar sayed zakzaky (H) to lallai Indai a asasin ilimi ne to zamu Iya fahimtar mutum Bashi da alaka da ilimi (ko gaba daya ko wani bangare).
Kuma duk Wanda yake bibiyar lamarin sayed zakzaky (H) to yasan lallai karama ko mu'ujiza a tafiyar sa to ta zamo ruwan dare da rana!
Mabiyansa suna fahimtar sa da dukkan ma'anar fahimta.
Domin kuwa shine kadai Wanda yake da almajiran da suke karatu a fannonin ilimin addini da Falsafa da Mandiqi Wanda in kace zaka shugaban ce Su ba tare da ilimi ba to hankali bazai karba ba.
Daga cikin abinda yake t