18/05/2024
Dan Tsokaci:
Manufar Da'awar Harkar Musulunci a karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shine yunkuri don dawo da ikon addini a wannan nahiyar da muke ciki.
Yunkurin dawo da addini din nan, ana yinsa ne ta hanyar sadaukarwa da tsayawa kyam wajen fuskantar zalunci da azzalumai har a kai ga nasara, nasarar zahiri ta tabbatar addini ko nasarar hakika ta komawa ga Allah cikin biyayyarsa ana masu neman uzuri a wajensa.
Kafin nasara, a kan sha wahala sosai, a kan samu Shahidai da s**a sadaukar da rayukansu saboda Allah. A kan samu masu rauni da aka raunata a wannan tafarkin saboda Allah. A kan kuma samu wadanda aka daure a kurkuku aka azabtar duk saboda Allah.
A irin wadannan wahalhalun da a kan fuskanta ne a ke samun wasu su daure duk runtsi su tsayu kyam a tafarki, a kuma samu wasu su zama masu raki har rakin nasu ya fara sa su fara shinshina wasu hanyoyin neman rangwame da sauki, wanda daga haka da yawa suke lalacewa su kauce daga tafarkin gaskiya. Allah Ya tsare mu.
Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya sha bayyanawa cewa bai yiwuwa a aiko wani Annabi don ya kawo gyara, ko wani mai Da'awa zuwa ga komawa tafarkin Allah, sai kuma ya zama ya shiga aikata irin abin da wadanda ake bukatar a kawar suke aikatawa wai da nufin ta hakan zai kawo gyara. Lallai gyare shi ake yi.
A kan hakan, lallai yan uwa ma'abota gwagwarmaya kar su sake su shiga rudu, mu yi kokarin fahimtar cewa lallai Jagora (H) ba zai taba sauya hadafi ba, kira yake zuwa ga komawa tafarkin Allah tun fiye da shekaru 40, kuma a kan wannan yake har gobe. A kan haka ya sadaukar da komai nasa. Babban burinsa shine wannan maguzancin da Bature ya kafa ya dankara mana da sunan Damukuradiyya a wannan kasar, ya zama miyagu, fasikai, fajirai, ashararan mutane suke jansa, ya zama an nannade shi an kawar da shi baki daya, an shimfida Musulunci na hakika.
Ya k**ata kuma mu iya lura da cewa akwai abin da ake kira 'principle', k**ar yadda Jagora (H) ya sha faɗa, shine manufa ko hadafi. Kuma hadafin nan na Harka shine yunkurin tabbatar addini. Sannan akwai abin da ake kira 'policy', wanda shine hanyar bi don cimma hadafi, shi yana iya canzawa daidai da canzawar yanayi. Wanda kuma hanyoyi suna da yawa, daga cikin hanyar da Jagora ya sha faɗa su yake bi don cimma manufarsa akwai amfani da Ilimi, da Hankali da Sahihin addini.
Ilimi shine, magana da mutane a irin sigar da suke fahimta, da bayyana musu dalilai a ilmance wanda wannan ke sa su amsa kiran. Hankali kuwa shine ke sa ya zama ba ana dira a kan mutane da duka ko zagi bane, bare kisa ko barnata dukiya, wanda wannan ke sa a gane mu ba barazana bane. Sannan kuma Sahihin addini na nufin bin irin tafarkin Manzon Allah (S) da Ahlulbaiti (AS) na nunawa azzalumai yatsa da kin yi musu sassauci ko da za su cire kai sai dai su ciren, ba tare da an rusuna ko an bi kazamin tafarkinsu ba.
Daukar makami a yi yaki, ko shiga siyasa, ko shirya karairayi da sharruka da sauransu duk suna daga 'Policies', hanyoyi ne da za a iya bi don kokarin cimma wata manufa, kuma duk wasu mutane ko Kungiyoyi daban-daban su kan tafi a kansu, amma matafiyar Jagora (H) sune wadannan abubuwan da ya saba faɗa, Ilimi, Hankali da Ingantaccen addini.
A kan wadannan ya k**ata mu doru. In har dan uwa na bibiyar jawaban Jagora (H) har na ziyarar karshe da aka yi, tun bayan fitowarsu, kullum yana nanata mana mafitarmu na a daukewa kyam ne a tafarkin addini, yana kuma nunawa mutane cewa mafitarsu ba shi a wannan rudadden tsarin da ke basu damar su zabi sabo ko tsohon macucinsu a matsayin maceci.
Na'am, kun tuna a baya can kafin Waki'a bayan da aka samu kyakkyawar alaka da fahimta da wasu Kiristoci, har Pasto ya roki Jagora (H) kan sun aminta, kuma suna rokon a samar musu da Dandalin Kiristoci a karkashin Harkar Musulunci, take Sayyid (H) ya amsa, aka kira su da 'Christian Forum under the Islamic Movement', ya zama su suna nan a Kiristocinsu, amma sun yarda da manufar Harka na a dawo da addinin Musulunci ya zama shi ke iko, a tsai da adalci a kasa ga kowa maimakon wannan tsarin da ke tafi da kasar a rikice.
Sai ya zama Kiristoci ne su, amma suna taimakon Harkar Musulunci ta wata fuska na kusanto da mutanensu zuwa ga fahimtar fadin Imam Ali (AS) cewa "Mutum ko dai dan uwanka ne a addini ko kuma abokin gwaminka a halitta." Suna ta aikinsu na wanzar da zaman lafiya tsakanin Kiristoci da Musulmi, suna aikinsu na sanar da yan uwansu cewa Musulunci ba barazana bane, wannan barna da ake da sunan Musulunci ba Musulmi ke yi ba, kuma ko Musulmi ne mai yi, ba sunansa Musulunci ba. Suna ta kokarin fahimtar da su manufar Harkar Musulunci a irin yaren da suke ganewa.
To, babu mamaki, tattare da dagulewar lamuran kasar nan, da yadda siyasarta ke kazancewa, idan aka samu wasu kuma wadanda suke su yan Siyasar ne, kila suna cikinta da su ake damawa, kila sun san ta daga waje, sai s**a fahimci Harkar Musulunci, s**a ga cewa su tare da cewa yan Siyasa ne, amma sun gamsu da cewa za su iya ba Harkar Musulunci gudummawa a janibinsu a siyasance. Mai sauki ne su nemi a basu dama, Jagora (H) yace ku je an baku sunanku Dandalin Siyasa a karkashin Harkar Musulunci. Wannan kuma bai sabawa 'policy' din Harka ba, don ba bangaren hadafi bane.
Ka ga yadda Kiristoci a karkashin Harkar Musulunci suke hulda da yan uwansu suke ba da gudummawarsu ta wasu fuskoki, su ma wadannan 'yan siyasar sai su je tunda suna haduwa da yan uwansu suna kokarin wayar da kansu a kan manufa da hadafin Harka, ba tare da kyale miyagun Malamai da makusanta suna sanar da su ba.
Ko da yake aiki ne mai hadari, musamman ga ma'abocin addini da shiriya ya mai da kansa layin 'yan siyasar kasar nan, domin gaskiyar magana kazanta ce da in mutum ya fada mata yana wahalar wankuwa, dilmiyewa yake yi ya yi nitson da sai dai kuma wani rahamar Allah Ta'ala. K**ar yadda dangwalawa wani da nufin zuwansa karaga na nufin amincewarka da ayyukan da zai aikata a yayin da ya ci, kuma tunda Allah Yace, wanda ya aikata misalin zarra na Alkairi ko sharri zai gani a ma'auninsa ranar Alkiyama. Kuma ya bayyana taimakon azzalumi a matsayin tarayya da shi a zalunci, to fa makoma abin ji ne.
Don haka, ga dan uwa mai gwagwarmayar addini, shawara gareka, ka tsaya kyam a kan tafarkin gwagwarmayarka. Ka tsaya a matsayar Jagora (H) da ka santa yake ta jaddada maka ita. Babu wata rana da Jagora (H) zai ce ka je ka shiga wannan tsarin, ko ka je ka dangwala kuri'arka ga wani macuci don ya ceceka. Wallahi babu wannan ranar. Amma in ka ga wasu sun je ga Jagora sun ce za su ba da gudummawa ta fuska kaza, ya musu ijaza, wannan bai k**ata ya zama maka damuwa ko abu mai nauyi ba, tunda ba abu ne da ya shafi hadafi ko manufa ba, bangare ne da za su ba da gudummawa daidai da Layin da suke kawai.
Kai in ma aka ace Jagoran ne ya samar da su (alal misali), to babin 'Policy' ne, bai shafeka ba, kai ka tsaya kyam a bangarenka ka zura ido gare su yi aikinsu. Sai ka yi musu fatan Allah Ya basu ikon cika alkawarin nauyin da s**a dorawa kansu. Barsu su yi abinsu, ba ma sai ka yi magana a kansu ko zargi ko kushe ba.
Kai kila kana Dandalin Dalibai na Harkar Musulunci, ka ga wani kuma yana Dandalin Mawaka, wata rana Dandalin Kiwon Lafiya, wata na Dandalin Marubuta na Harka, wasu suna Lajanonin tsaro, wasu na Dandalin Ma'aikata ko na masu kudi, kuma duk na Harkar Musulunci. Shikenan, kila cigaba ya kawo an samu Dandalin 'yan siyasa. Duk sai kowa ya yi ta ba da gudummawarsa har zuwa lokacin da za a rusa tsarin da ke ba kazamai damar rike muk**an Siyasar kasar, a maye gurbin siyasar Mu'awiyyanci da irin ta Amirulmuminin (AS) wacce za ta zama bisa turbar Allah da Annabi yace, kuma ya zama Muminai masu tsoron Allah ne ke rike da muk**anta.
Allah Ya tabbatar da mu a kan tafarkinSa. Ya karawa Jagoranmu Sayyid Zakzaky (H) lafiya da kariya. Ya cika burinsa na ganin mun shiryu, mun tsayu kyam mun kau da wannan tsarin kafircin, addinin Musulunci ya yi iko da mu a doron kasa.