
28/09/2022
STILL ON THE MATTER OF LAYIN ZOMO
JARIDAR AMANA
Home
About Us
Contact Us
Home Labarai
Ya kamata a tuna damu cewar matasan Layin Zomo
Jaridar Amana September 23, 2022
Daga Umar Idris Kaduna
Da safiyar ranar Talata ne kungiyar ci gaban Layin zomo dake karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna s**a koka akan yadda garin nasu ya zama abin kyama ga yan siyasa bayan sun basu kuru'unsu a lokutan zabe.
Wakiliyarmu ta ziyarci Anguwar yayin da yan anguwar s**a baiwa manema labarai goron gayyatar gani da ido a wannan yankin
Yayan kungiyan ta bakin shugaban su malam Danjuma Bawa sun bayyana cewa ya zuwa yanzu babu wani abin da zasu iya nunawa a matsayin romon Kamakuradiyya a halin yanzu.
Shugaban yace duk wani aikin da aka gani a yanzu to aikine da gwamnatin PDP a lokacin baya.
Tuni yayan kungiyar s**a koka bisa irin kokarin da s**ayi a wannan gwamnatin ta APC kafin hawanta karagar mulki.
Yayan kungiyar wanda galibinsu matasane masu jini ajika sun baiyana cewa yanzu haka akwai hanyoyi da s**a lalace a tsakiyar garin Layin Zomon amma babu wani dan siyasa da ya taba zuwa domin kawo masu tallfin gyarawa.
Haka zalika matasa sunce yanzu haka kadar da ta hada garin Falladan da Layin Zomo itama ta lalace gaba daya.
Yayan kungiyar sun bayar da misali da makarantar UPE na Layin Zomon cewa yanzu haka Awaki ne ke kwana a ciki sakamakon yadda ta lalace.
Sun kawo maganar Asibitin su dake anguwar tasu shima sun koka da cewa ba kayan aiki ba magani da sauran abubuwan da asibiti ke bukata.
Karshe matasan sun nemi alfarma ga dukkan masu fada aji na karamar hukumar ta Sabon gari da suyi wa Allah da Annabinsa su sa hannu akan halin da garin yake ciki a halin yanzu.
Kuma sunyi kira ga Dan majalisar taraiya Honorabul Garba Datti Babawo da ya waiwayi matasan yankin Layin Zomo a shirinsa daya saba gudanarwa lokaci bayan lokaci kamar yadda yake waiwayan sauran takwarorinsu dake fadin karamar hukumar ta Sabon Garin baki daya.
Malam Muhammad Mudassir shene sakataren kungiyar ta ci gaban Layin Zomon shima cewa yayi ya kamata yan siyasan karama hukumar Sabon Gari su gane cewa Layin Zomo ba abin yardawa bace domin sunada kuri'u masu yawa da yawansu na taka rawar gani sosai lokacin zabe bisa haka ne yace suna sane da duk wanda ya taimaki yankin su
Suma idan lokaci yayi suma zasu taimaka mashi da ikon Allah
Malam Zakari Sani tsohon shugaban Yan bangan Layin Zomo shiko cewa yayi gaskiya bai kamata ace sai dai jama'ar Layin Zomo suga ana yin wasu aiyuka a wasu yanki su kuma suna gani.
Bisa haka yayi kira ga shugaban karamar hukuma da yan majalisarsu da suyi abin da ya kamata a wannan anguwa don haka ne zai karawa jambiyar APC farin jini tare da samun nasara a nan gaban.
Karshe suyin fatan Allah ya kawo wanda zai share masu hawayensu ba tare da wani matsalaba.
Created By Blog | Distributed By Jaridar Amana