08/04/2024
Ilimin Solar Eclipse gaskiya ne, wani lokaci idan masu ilimin abun sunyi hasashe yakan tabbata a zahiri, zazzabin rana da wata gaskiya ne yana faruwa (Khusufi).
~ Amma idan rana ta fadi a yau (Litinin) kubi umarnin Manzon Allah ku duba wata, babu wani karatu bayan wannan.
Kuskure ne kuma 'bata ne ace saboda hasashen masu ilimin Astronomy ba za'a duba Wata ba, dole a duba idan ba'a gani ba a cike Azumin ya zama 30 shike nan, dama ba mun dauka da Niyyar yin 29 bane.
Mun dauka ne da Niyyar sai lokacin Allah ya bayyana mana lokacin shan ruwan a bisa hasken ilimin Sunnah da Manzon Allah yazo da ita.
~ Ranar da 'dan Manzon Allah (S.A.W) Ibrahim (R.A) ya rasu, anyi zazzabin rana sai Manzon Allah yace "Lallai hakika rana da wata Ayoyi ne daga cikin Ayoyin Allah, basa kisfewa (ko basa yin zazzabi) saboda mutuwar wani ko saboda rayuwar wani (saboda an haifi wani)...".
~ Wannan yana nuna zazzabin rana ko wata gaskiya ne, mun yarda da abun ne saboda Annabi ya tabbatar mana is true yana faruwa.
Dan haka a duba Wata da zaran rana ta fadi, idan an gani ayi Sallah gobe Talata, idan ba'a gani ba a wuce sai Laraba, shike nan, ko Gwamnati ce kayi aikin da ya wuce working hours akwai special allowance da za'a 'kara maka, kuma hakan yana nuna kai me kokari ne.
~ Toh ina kuma ga Ibadar da muke yi wa kanmu saboda umarnin Ubangijin mu, da ace za'a nuna maka Allowance na 'karin kwana daya da za'a baka idan ka cike Azumi 30 (idan za'a yi 30 din kenan) da sai ka rike baki kana mamakin yawan Allowance din da Allah zai ce a zuba a Account dinka na Lada.
Allah ya amshi ibadun mu 🙏