Mahmud Ishaq Rano

Mahmud Ishaq Rano Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Mahmud Ishaq Rano, Digital creator, Rano.

10/06/2024

Babbar sallah yau saura kwana 6, amma ko zancenta ma ba,a yi! Sabo da tsadar rayuwa, Allah ya kawo mana sauki.

JUMA,A TA UKU A CIKIN WATA MAI ALFARMA RAMADAN.  Kamar yau ne muka fara azumin watan Ramadan, yau gashi muna cikin juma,...
29/03/2024

JUMA,A TA UKU A CIKIN WATA MAI ALFARMA RAMADAN.

Kamar yau ne muka fara azumin watan Ramadan, yau gashi muna cikin juma,a ta uku a wannan wata mai alfarma, Ya ALLAH ka gafarta mana zunubanmu, ya Allah ka karbi dukkan ibadunmu, ya Allah ka sanyamu a cikin wadanda kakema gafara da rahama a cikin wannan wata Mai alfarma.

Yau gashi in mun kai azumine na 19 cif, kwanaki na wucewa, lokacinmu yana tafiya, muyi kokari Mu ribaci wannan damar da muka samu, Mai yiwuwane bama cikin wadanda zasuga azumin shekara Mai zuwa.

Ya Allah ka karba mana dukkan ibadunmu,

Yan,uwa Mu yawaita alkhairi da sadaka da kyauta da sada zumunci, da yawan salloli da karatun al,qur,ani.

Mu nace wajan rokon Allah musamman a lokacin da mukazo zamuyi buda baki, kafin musha Ruwa, ya tabbata Manzon Allah S .a.W yace ba,a juyar da addu,ar da Mai azumi yayita kafin Yayi buda baki,

Alla ka karba mana

Mahmud Ishaq Rano
Juma,a 19/Ramadan/1445.
29/march/2024.

CIYARWA A WATAN RAMADANHakika ciyar da dukiya ko abinci ga mabukata da talakawa ba karamin al,amari bane a wajan Allah a...
27/03/2024

CIYARWA A WATAN RAMADAN

Hakika ciyar da dukiya ko abinci ga mabukata da talakawa ba karamin al,amari bane a wajan Allah a kowanne wata, amma girmansa da falalarsa yafi a watan Allah watan falala da rahama watan Ramadan.

Hakika Annabi S.a.w ya Fada a Hadisi ingantacce yace: " Wanda ya ciyarda Mai azumi yana da lada kwatankwacin na Mai azumin, ba tareda an ragewa shi Mai azumin komai ba a ladansa".

Haka Manzon Allah S.a.W yace :" kuji tsoran wuta koda da tsagin dabino ne".

Ciyarwa musamman ta abinci ba Lallaine saika Tara bataliyar mutaneba, aa kayi iya Karfinka, wane mawadaci zai iya ciyar da mutum 100 misali, ko sama da haka, kai kuma bakada wadata iya mutum 2 ko 3 ko 1 zaka iya ciyar wa, to karka damu ka ciyar da iya Karfinka da iya wadatarka ka sanya ikhlasi, me yiwuwane in Allah ya karbi wannan sai kaga shine silar tafiyarka aljannah.

Ko da dabino ko kunu ko koko , ko wani lemo ko abin jikawa, ka fito dashi kaba mabukata, kayi da ikhlasi Dan Allah, in Allah ya karba shike nan ka gama dacewa.

Allah ya gafarta mana, Allah ya yassare mana, Allah ya sanya mana Karfi da jarumtar ciyarda dukiyarmu da abincinmu ga mabukata bisa ikhlasi, Allah ka karba mana ka yafe mana dukkan laifukanmu.

A Yanzu Kayan Lefe Na Naira Dubu 300 Da Sadaki Naira Dubu 70 Rainawa Iyaye Suke Yi, Amma Akan Naira Dubu Biyu Wani Zai Y...
01/12/2023

A Yanzu Kayan Lefe Na Naira Dubu 300 Da Sadaki Naira Dubu 70 Rainawa Iyaye Suke Yi, Amma Akan Naira Dubu Biyu Wani Zai Yi Zina Da Ɗiyarku. Don Haka Ruwa Cikin Cokali..., Cewar Hadiza Adamu Santuraki

Hakika ta fadi gaskiya.

TAYAYA ZAN ZAMA MIJI NA GARI?Zama Miji na gari wani abu ne da ya kamata mu fito da wadansu hanyoyi da za su taimaka mana...
26/11/2023

TAYAYA ZAN ZAMA MIJI NA GARI?

Zama Miji na gari wani abu ne da ya kamata mu fito da wadansu hanyoyi da za su taimaka mana, wajan zama miji na gari.
Kowa ne dan adam yana da bukatar abokin zama na gari, da zai nuna soyayya, kauna, daukar nauyi da kulawa. Domin samun zamantakewar aure mai aminci da inganci.

Ga yadda zaka gina zamantakewarka da matarka, domin zama miji nagari.

1. Ka zamo mai tattaunawa da abokinyar zamanka, tattauna matsalolinku tare da nemo mafita. Hakan zan kara muku fahimtar juna da tunkarar manufa iri daya ta samun dadin zamantakewar aure.

2. Nemi shawarar matarka akan wasu abubuwan rayuwarku, ko da kuwa baza kai aiki da ita ba. Manzon Allah SAW ya kasance yana neman shawara a wajen matansa, kuma har yai aiki da su.

3. Ku kiyayi karya da rashin gaskiya a cikin iyalanka, domin rashin gaskiya da karya yana kawo raini.

4. Taya matarka ayyukan cikin gida, idan kana gida kenan. Wannan zai kara mata kwarin gwiwar cewa ita kuwa ta samu miji na gari.
5. Wajibi ka kula da damuwarta, matukar kana son kaima ta damu da damuwarka.

6. Ka zamo mai yabo da kalmomi masu dadi ga uwar gidanka. Ka nisanci kyararta ko yi mata fada a gaban mutane.

7. Boye sirrin gidanka da zamantakewarka maras dadi a gidanka.

8. Nuna kauna da soyayya ga matarka, tare da furta gwalagwalan kalmomin raya zuciyar masoya.

9. Sumbatar iyalinka akai akai na kara dankon kauna a junanku.
10. Duk abin da take so, kai ma kaso shi dai dai gwargwadon iyawarka.
11. Kiransu da dadadan sunaye masu dadin gaske.
12. Ka zama kana biyawa matarka bukatarta ta kwanciyar jima'i, hakan zai kara muku nutsuwa da soyayya a zamantakewarku.
13. Ka yawaita addu'a ga matarka da zaman takewarku.
14. Ga kasance mai tunatar da matarka Allah, da kokarin bin tsarin addini domin gobenku ta yi kyau.

A karshe ku taya ni da addu'a, Allah ya bawa matata lafiya, ya sauketa lafiya dama sauran matan musulmi baki daya.

'YAR UWA TA ME ALBARKA!!! 🌷🌺ki kasance mace me tarbiya, da kuma nuna tarbiyan ki a ko ina. 🌷🌺ki kasance mace me hakuri d...
26/11/2023

'YAR UWA TA ME ALBARKA!!!

🌷🌺ki kasance mace me tarbiya, da kuma nuna tarbiyan ki a ko ina.

🌷🌺ki kasance mace me hakuri da halin yau da kullum, kada ki zama mace me tada hankalin mijinta akan halin babu data same shi ko yake Ciki.

🌷🌹ki kasance mace me godiya da dukkanin halin da Mijin ta yake ciki, ki din ga kwantar masa da hankali a kowane hali kuka tsinci kanku.

🌷🌺ki kasance mace me tsaftar gida, tufafi da kuma jikinki, domin kazanta tana daga cikin abinda yake kore soyayya komai karkonta!! Ki kiyaye.

🌷🌺ki kasance mace me kyawun lafazi (furci) a koda yaushe koda kina cikin fushi ne, ki iya sarrafa fushin ki saboda kaurace aikin dana sani.

🌷🌺ki kasance mace me taimakon Mijinta akan addinin sa, mu'amalarsa, dukiyarsa da dukkan abin da ya shafe shi, da kinga zai kauce hanya kiyi kokarin dawo dashi kan hanyar gaskiya.

26/11/2023

"Ya Allah kasa Mutuwar mu ta riskemu cikin imani da biyayya ga Allah"

Send a message to learn more

Barkanmu Da Juma'a ....Ubangiji Allah Ka Sadamu Alkhairan Wannan Rana Ta Juma'a, Allah Kasa Muna Daga Cikin Ƴantattu, Al...
24/11/2023

Barkanmu Da Juma'a ....

Ubangiji Allah Ka Sadamu Alkhairan Wannan Rana Ta Juma'a, Allah Kasa Muna Daga Cikin Ƴantattu, Allah Ka Zaunar Da Kasarmu Da Jahar Kano Lafiya

WALLAHI KOMAI KUDINKA A DUNIYAKabarinka ba katifa, ba filo ko shimfida, ba window, ba silin, sai itace da za'a jera. Ba ...
23/11/2023

WALLAHI KOMAI KUDINKA A DUNIYA

Kabarinka ba katifa, ba filo ko shimfida, ba window, ba silin, sai itace da za'a jera.
Ba wuta, ba AC, ba fanka ba bargo.
Daga kai sai halinka sai Sallah.

Allah ka tsaremu daga azabar kabari.

Masu Matsalar Kaushi )Faso Anemi  Lemon Fata 1 Safa Man Kadanya Yadda Za a yi Idan ansamu mankadanya se a yanka lemon 2,...
22/11/2023

Masu Matsalar Kaushi )Faso

Anemi Lemon Fata 1

Safa

Man Kadanya

Yadda Za a yi

Idan ansamu mankadanya se a yanka lemon 2, a shanye Ruwan lemon , amma matsewa Ruwan za a yi ba taunewa ba , bayan an shanyen Ruwan , se a shafa mankadanyar aciki , se a sanyashi a dunduiniyar , asanya safa anaso Yakai awa 3 akafar mutum kafin a wanke.

Pls Share and Like

MUHIMMAN HANYOYIN KARFAFA LAFIYA CIKIN YANAYI NA SANYIDazaran ƙarshen shekara ya nufato, Sai a shiga yanayi na sanyi. Ha...
22/11/2023

MUHIMMAN HANYOYIN KARFAFA LAFIYA CIKIN YANAYI NA SANYI

Dazaran ƙarshen shekara ya nufato, Sai a shiga yanayi na sanyi. Hakan na iya zama kalubale ga lafiyar mutum ta hanya sauƙin kamuwa da mura, tari, bushewan labba, da sauransu.

A kula da waɗan nan shawarwari:

1. A yawaita shan ruwa sosai

2. A yawaita wanke idanu akai akai domin gujewa kamuwa da ciwon ido.

3. A yawaita amfani da abin rufe fuska da hanci (Facemask).

4. A takaita zirga-zirga a waje sai dai wanda ya zama dole, mai mahimmanci.

5. A yawaita sa kaya masu ɗan kauri, ko rigunan sanyi domin sanya dumi a jiki.

6. A yawaita rufe tagogi da kofofin domin takaita shigowar kura daki.

7. A yawaita shafa mai a jiki domin dandashe fata kar ta bushe.

8. A yawaita shafa mai a labba domin kare su daga farfashewa ko tsagewa.

ABIN LURA: Wannan yanayi na iya tayar ma da masu ciwon Sickler da Asthma ciwon su sosai. A kula.

Amfanin namijin goro, ga lafiyar Dan Adam Amfanin sa, Guda goma sha shidda (16)(1) Namijin goro yana maganin tari idan A...
22/11/2023

Amfanin namijin goro, ga lafiyar Dan Adam

Amfanin sa,

Guda goma sha shidda (16)
(1) Namijin goro yana maganin tari idan Aka hada da (Tom Tom) Ana chi.
(2) Namijin Goro yana maganin matsalar ciwon sanyi, idan Aka hada da kanunfari A tasafa Asha Ruwan.

(3) Namijin Goro Yana maganin ulcer idan Ahada dabino Adaka, Asa Zuma A sha cokali biyu.

(4) Namijin Goro Yana maganin matsalar tsutsar ciki idan Aka jajjaga A matse Ruwan A Zuma Asha .

(5) Namijin Goro Yana Qara kuzari da nisan tafiya ga Mai iyali idan Anaci da dabino daya namijin goro A tauna.
A Cinye kullun kaci sau uku.

(6) Namijin Goro Yana gayra maniyyi Idan Aka jajjagashi A samu garin Hulba Tafasa dashi Asaka madaran Ruwa Asha.

(7) Namijin goro Yana kawar da majinar kirji idan kana cin shi.

(8) Namijin Goro yana hana shan Taba idan Aka hada da furan tumfafiya Ayi garin su Asamu Karan sigarin da mutum yake Sha da madaran shanu wanda babu Hadi, Ajika yakwana da safe kafin Aci Komi A ba maishan Taban ya shanye duka zaiyi Amai.

(9) Namijin goro yana maganin hawan jini, Idan Aka hada ganyan cediya A tafasa Asa Zuma Asha.

(10) Namijin Goro Yana maganin ciwon Kai, idan kayi garin shi Ana hayaki Koda mace Mai yawan ciwon Kai tayi.

(11) Namijin goro yana gyara murya idan kahada da danyar citta da Zuma kana dafawa da Lipton kasha kafin kaci Komai.

(12) Namijin Goro Yana maganin kuraje Idan kasamu garin namijin goro ka kwaba da Man zaitun.
Idan Kuma kazuwa ce ko bakon dauro ka kwaba da manja kashafa.

(13) Namijin Goro Yana maganin sanyin Mara idan kahada da kanunfari da lemon tsami da Citta da garin Albabunaj.ka tafasa kasha da Zuma.

(14) Namijin Goro yana maganin wuta- idan kahada da sassaken itacen Qirya kadaka kasa gurin da wuta taci.

(15) Namijin Goro Yana tsayar dajini idan Kika hada da tsamiya ki tafasa Kisha zai tsaya.

(16) Yawan cin namijin Goro Yana kawar da wasu cututtukan da suke cikin mutum.

Allah kara mana lafiya da Imani Amin.

Kalubale  gareku samari      Mai yasa indai zakaga saukar Alqur,ani mai girma saidai kaga mata zallah ko mata 50 maza 3T...
22/11/2023

Kalubale gareku samari

Mai yasa indai zakaga saukar Alqur,ani mai girma saidai kaga mata zallah ko mata 50 maza 3
Tambayar anan shin mu maza Allah bai wajabta mana naiman ilimi bane ko kuma sakaci ne da ni man duniya
Amma in kaga bikkin kammala jami,a zakagga maza sunfu kowa yawa aciki
Saboda na naiman duniya ne gashi duniyar bata samuwa ka gama karatu ka koma yaron wanda ko primary baije ba
Gara ma ka karanci Alkur,ani ko bakomai ya ceceka aranar tashin ALQIYAMA
ALLAH YASAMU DACE

29/10/2023

Ahamdulilllah! This is officiall page for MAHMUD ISHAQ RANO

Address

Rano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mahmud Ishaq Rano posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share