16/10/2023
GARIN RANO: INA MUKA DOSA?
Bismillahir-Rahmanir-Rahim
Rano babban gari ne wanda Allah Ya a azurtamu da masu ilimi, malamai, ƴan kasuwa, ƴan siyasa ga kuma babbar masarauta. Gari ne wanda duk inda ka zagaya zaka tarar da labarin sa, amman shin ya garin yake a zahiri? Yaya mutanen garin suke rayuwa? Waɗannan wasu tambayoyi ne da amsoshin su za su bawa waɗanda ba ƴan Garin Rano ba mamaki.
Duk da Allah Ya azurtamu da waɗannan mutanen da na lissafo a baya, amman hakan bai sanya garin yana ɗauke da wasu abubuwa na more rayuwa ba (social amenities) wanda duk wanda yake jin sunan garin zai yi tunanin hakan a ransa.
Bari na fara da masu kuɗin garin irin su AA Rano, Saleh Baba (Salbas) da makamantan su waɗanda sune mutanen da suke matuƙar ƙoƙari wajen gina al'ummar garin (ta hanyar basu aikin yi), biya masu kuɗaɗen makaranta da wurin zama da kuma rage wa mutane raɗaɗi, waɗannan mutanen suna iya ƙoƙarinsu na ganin sun bayar da gudunmawar su wajen ganin garin nan ya cigaba. Allah Ya saka masu da Alkhairi Ameen.
Ƴan siyasar Rano (waɗanda ɗaya ne daga cikin matsalolin garin) sun ɗauki mutanen garin a matsayin waɗanda basu san me suke ba, suna cin karen su babu babbaka, suna amfani da rigar mulki suna tarawa kansu da iyalan su dukiya (wacce ba zata masu amfani ba).
A garin Rano, tunda na fara sanin kai na, banda aikin titu cikin unguwa da Ganduje yayi babu wani babban aiki (wanda zai amfani mutane da dama) da zaka ce an nemo wa al'ummar mu (daga matakin ƙasa ko jiha), rabon garin Rano da ruwan famfo yau shekaru goma sha biyu (2011-2023), magudanan ruwan garin duk babu gyara, gidajen mutane sai lalacewa suke. Babu wani tsari ga mata, ƙananan yara ko matasa, babu wani tsari da ake amfani da shi wurin ɗaukar aiki sannan babu wani tsari da za a ce yau ana ɗaukar nauyin karatun wasu. Menene amfanin ƴan siyasa idan ba su yi mana waɗannan abubuwan ba?
Manyan gari da dattawan gari ayi haƙuri, wani mai iya magana mai suna Emmanuel Kant yake cewa "Idan gaskiya zata kashe su (mutane) ka faɗa.
Nazifi Ibrahim Bako