Kwankwasiyya Family

Kwankwasiyya Family aspiring influencer
Becoming a Journalist is my life's dream
🎤🎤🎤🎥

  Happy Birthday once again Bloodline
11/06/2024



Happy Birthday once again Bloodline

Touchdown Lagos🛬
15/05/2024

Touchdown Lagos🛬

Labari cikin hotuna: Gwamnatin jihar Katsina ta sauya wasu manyan Daraktoci na kowane bangare dake aiki a kananan hukumi...
17/04/2024

Labari cikin hotuna: Gwamnatin jihar Katsina ta sauya wasu manyan Daraktoci na kowane bangare dake aiki a kananan hukumin jihar Katsina 34 rankatakaf garin da zai koma da aiki

Najeriya ta shiga sahun wasu manyan ƙasashe yayin da Tinubu ya kaddamar da wani sabon tsarin aiki da zai ceto $4bn duk s...
17/04/2024

Najeriya ta shiga sahun wasu manyan ƙasashe yayin da Tinubu ya kaddamar da wani sabon tsarin aiki da zai ceto $4bn duk shekara - Duba a ƙasa.

📸: DOlusegun16/X
Full details in LLegit.ng Hausa

Ya kuke gani idan $100 ta koma dai-dai da ₦100.
17/04/2024

Ya kuke gani idan $100 ta koma dai-dai da ₦100.

Yanzu-Yanzu: Zanga-zangar nuna rashin amincewa da dakatar da Ganduje ta ɓarke.Rahotannin sun nuna cewa gungun magoya bay...
17/04/2024

Yanzu-Yanzu: Zanga-zangar nuna rashin amincewa da dakatar da Ganduje ta ɓarke.

Rahotannin sun nuna cewa gungun magoya bayan shugaban jam'iyyar APC, Dr Abdullahi Ganduje, sun fito zanga-zangar nuna rashin amincewa da dakatar da shi daga muƙaminsa, a mazabarsa da ke jihar Kano.

Jaridar Arewa ta gano cewa dubban Magoya bayan sun yi cincirindo ne a sakatariyar jam'iyar APC ta ƙasa da ke Abuja.

Sai dai shugaban Jam'iyyar Gwamna Umar Ganduje, ya yi wa magoya bayansa jawabi a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa, ya ce har yanzu yana kan karagar mulki.

Mai Girma Ɗan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Ƙaramar Hukumar Birni Hon. Engr. Sagir Ibrahim Koki ya hala taron kare kasa...
17/04/2024

Mai Girma Ɗan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Ƙaramar Hukumar Birni Hon. Engr. Sagir Ibrahim Koki ya hala taron kare kasafin kuɗi tareda Hukumar dake kulada sufurin jiragen Ruwa ta ƙasa wato Nigerian Maritime Administration and Safety Agency, (NIMASA) tareda daraktocin Hukumar ƙarkashin jagoranci Manajan Darakta na NIMASA.

Allah ya tabbatarda alkhairi
Kuma Allah ya kawarda dukkan abin ƙi.

KWANKWASIYYA FAMILY MEDIA TEAM

A yaune za a fara sauraron karar da hukumar yaki da rashawa ta Kano ta kai tsohon gwamna Dr. Abdullahi Umar ganduje  da ...
17/04/2024

A yaune za a fara sauraron karar da hukumar yaki da rashawa ta Kano ta kai tsohon gwamna Dr. Abdullahi Umar ganduje da wasu mutane biyar ciki har da matarsa da dansa bisa zargin cin hanci da rashawa da karkatar da dukiyar jama'a.

Muna tare da rahoto nan gaba.

Da dumi-dumi: Kotu ta dakatar da Dr. Abdullahi Ganduje daga bayyana kansa a Shugaban APC har zuwa lokacin kammala shari’...
17/04/2024

Da dumi-dumi: Kotu ta dakatar da Dr. Abdullahi Ganduje daga bayyana kansa a Shugaban APC har zuwa lokacin kammala shari’a tsakaninsa da Shugabannin Jam’iyya na mazabarsa.

Me za ku ce?

Babbar Kotun Jihar Kano me lamba 4 dake zaman ta akan titin Mila road, ta tabbatar da dakatarwar da wasu shugabannin Jam...
17/04/2024

Babbar Kotun Jihar Kano me lamba 4 dake zaman ta akan titin Mila road, ta tabbatar da dakatarwar da wasu shugabannin Jam'iyyar APC a mazaɓar Ganduje s**a yiwa Shugaban Jam'iyyar na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje daga Jam'iyyar.

10/04/2024

Barka da Sallah. I felicitate with the Muslim Ummah at home and beyond on this auspicious occasion. - RMK

27/07/2023
01/07/2023
01/07/2023

“Ina yiwa Kwankwaso addu'ar samun babban rabo, ina fatan Allah ya ƙara masa lafiya, ya kuma barmu tare."

© Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, yayin jawabinsa a taron barka da Sallah da aka gudanar yau a Gidan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso dake Kano.

01/07/2023

Barka da Sallah! - RMK

21/06/2023
21/06/2023

Batu na gaskiya game da kammala jami'ar Young Sheikh Zaria........

✍️ Comr Abba Sani Pantami

Yanzu daya daga cikin shugabannin jami'ar da ake cewa Young Sheikh Zaria ya kammala ya kirani, munyi doguwar tattaunawa dashi akan batun.

Da farko ya tabbatar mun da cewa Young Sheikh dalibine yanzu haka a jami'ar, kuma sun bashi Admission a shekarar 2021 bayan ya yi Apply ta internet da takaddun NECO da IJMB da kuma takaddar Declaration of Age mai dauke da shekaru 15 zuwa 16 a lokacin da yayi Applying din jami'ar.

Sunce basu san inda Young Sheikh ya samu T-shirt din da ya saka tare da wa 'yanda zasu kammala jami'ar a wannan shekarar ba. Sun tabbatar mun da cewa yanzu haka Young Sheikh yana aji daya ne zuwa biyu.

Batun karamar da ake yadawa yana da ita sudai a makarantar basu ganta ba, domin tun a satin da ya gabata aka kammala jarabawa a jami'ar, amma Young Sheikh ya tsaya yayi attending din "Summer Semester" domin ya gyara Carry Overs din da yake dasu masu yawa a makarantar, wanda a yanzu haka ya kammala rubutasu yana hanyar komawa gida.

Wannan shine zancen gaskiya da s**a fada mun kuma suke bukatan a isarwa Duniya cewa lallai Young Sheikh bai kammala jami'ar ba, domin an bata musu sunan jami'a a idon Duniya har wasu sun fara musu mummunar fahimta akan rashin ingancin karatun su.

Sannan suna bukatan lallai Young Sheikh da Gidajen jaridun mu na Arewa su fito duniya su karyata batun labarin da ake yadawa kamar yadda aka yada labarin kammalawarshi tun daga farko idan ba haka ba, zasu iya daukan matakin shari'a akan dalibin. Wallahi ko kadan banso na kara yin rubutu ko cewa wani abu ba akan Young Sheikh amma jin bayanin su da kuma hujjojinsu naga ya dace na isar muku da wannan sakon, saboda a yanzu haka Mutane da dama sun fara yiwa jami'ar su mummunan fahimta.

Ga sakon da s**a rubuta officially daga shugaban jami'ar;

Assalamu Alaikum,

Bayan gaisuwa ta musamman tare da jinjina ga malamai, dalibai, da duk wani maiyima wannan jami'a fatan alkhairi abayyane ko boye.

A ranar Alhamis 15th June, 2023 wannan makaranta ta wayi gari cike da abun al'ajabi da mamaki akan wasu hotuna da bayanai das**a kewaye kafafen watsa labarai akan daya daga cikin daliban mu mai suna Zakeer M.S Ali mai lakani da Young Sheck, cewa wannan dalibi ya kammala karatun shi na fannin Shariah da mafi karancin shekaru wato Shekara Shabiyu (12 years) a wannan jami'a tamu.

Domin cire wani kaikayi da rudani tsakanin dalibai, wannan makaranta na amfani da wannan dama tasanar da dalibai kadan daga cikin bayanai akan wannan dalibi kamar haka:-

1- Cewa wannan jami'a ta karbeshi amatsayin dalibi ne na din din din a watan November, 2021.

2- Haka kuma tun daga wancan lokaci shi wannan dalibi har yanzu yananan amatsayin shi na dalibi a wannan jami'a, ma'ana har yanzu bai kammala karatun sa ba.

3- Cewa kafin wannan jami'a taba wannan dalibi damar fara karatu wato (admission) wannan dalibi ya gabatar da takardun sa kamar haka:-

a- Takardar National Examination Counsil (NECO).

b- Takardar Interim Joint Matriculation Board (IJMB).

c- Takardar shaidar shekarun haihuwa wato (Declation of age) wadda alokacin da aka bashi admission dalibin yana tsakanin Shekara Shabiyar zuwa Shashida. Haka dai dasauran wasu sharuddan da doka ta tanada kafin ba dalibi damar fara karatu a makaranta irin wannan.

4- Wannan jami'a batada masaniyar yanda wannan dalibi ya mallaki wadancan kayan, tareda yin hotuna domin nuna ma duniya cewa ya kammala karatun sa. Kuma wannan jami'a na kyautata zato cewa ba manufar dalibin kenan ba. Sai dai tareda haka, atsarin wannan makaranta takarda ce kadai ke nuna tabbacin kammala karatu ba hoto ko kwalliya ba.

Dalili haka wannan jami'a batada hakki ko wajabta ma dalibi yin bayani akan yadda yamallaki kayan domin kowa ma zai iya sanya kayan domin taya saura yan' uwa ko abokan karatu murna.

Bisaga wadancan dalilai da aka ambata asama, wannan jami'a tana so tayi kira ga dukkan dalibanta dasusan wadancan labarai dake yawo a kafafen yada labarai cewa KARYA NE! KARYA NE!! KARYA NE!!!. Labarai ne wadanda basuda tushe balantana asali. Saboda haka duk lokacin da wani dalibi yaci karo dasu to yasan matsayin su a idon jami'a.

Daga karshe muna kara godiya ga dukkanin malamai, dalibai da masu fatan alkhairi wajen kokarin kariyar martaba da mutuncin wannan jami'a.

Muna godiya sosai

Muohammad Abuobakar Lawwali.
DVC
Abuobakar Ibrahim International University Maradi, Niger.

21/06/2023
Yau Juma'a 16 june 2023 Mataimakin gwamnan Kano Comrd Aminu Abdussalam ya karbi bakuncin Jakadiyar kasar Faransa A Niger...
17/06/2023

Yau Juma'a 16 june 2023 Mataimakin gwamnan Kano Comrd Aminu Abdussalam ya karbi bakuncin Jakadiyar kasar Faransa A Nigeria da tawagar ta.

Anyi batutuwa ciki harda batun bashin da Ganduje ya karbo a Kasar Paris shekara uku data gabata na Euro Milion 64, Kudin sunkai Naira Biliyan 45, Ya karbi kudin da sunan zai magance matsalar ruwan sha a jihar Kano. Masana sun bayyana cewa kudin ya isa a gina sabbin Gidajen ruwa na zamani wadanda zasu iya magance dukkanin matsalar ruwan sha a jihar Kano, Amma ya kasa bayyana abunda yayi da Kudin domin ko cikin bashikan daya bayyana ya karba cikin kundin karbar mulki baisa da bayanin suba.

Kana daga karshe Jakadiyar ta gana da Kwankwasiyya scholars wadanda s**ai Karatu a kasar Paris. Dukkanin zaman ya gudana ne a gidan gwamnatin Kano a dakin Taro na Africa House.

Daga Khatimu Kulkul.
Adamu Lawan Imam

17/06/2023

AKWAI RIKIDARWA: A shekarar 2021 anyi hira da Young Sheikh Zaria yace yana Primary aji na 4, kwatsam ko shekara biyu ba'a cika ba, gashi ya kammala jami'a ya karanci bangaren shari'a.

A kwanakin baya na yi wani rubutu game dashi tare da kafa wasu hujjojin wani malami da ya fada har na bawa iyayenshi shawara mai kyau.

Bai kamata iyayen Young Sheikh su bari a dinga fitar da irin wa 'yan nan abubuwan da hankali ma bazai dauka ba akanshi, domin ana kara cirewa Mutane yarda dashi da kuma abunda yake yi da kadan-kadan ta yadda nan gaba ko sauraron wa'azinsa ma ba za'a dinga yi ba. Idan don neman suna da daukaka yasa ake fitar da irin wa 'yan nan abubuwan ya kamata su chanja salo.

Bazan manta ba a shekarar da ta gabata 2022 wani matashi ya kirani wai shine Director Media na Young Sheikh yana son zasu dinga turo mana da fatawowi da karatun da Young Sheikh yake yi da sauran abubuwan shi domin mu dinga saka mishi a jaridunmu na Arewa.

Bayan munyi waya sai daya daga cikin abokanan aikina ya kirani yake fada mun Director Media na Young Sheikh ya kirashi ga aikin da suke son mu dinga mishi suna son Duniya tasanshi, sai nace mishi nima sun kirani, amma kaje ku dai-daita dasu, daga baya ya sake kirana an tsaida matsaya akan kudin da zasu dinga bayarwa akan kowane rubutu da zasu dinga turowa, muka fara gudanar da aikin sama-sama.

A kwanakin da ya gabata na rubutun da nayi na bawa iyayenshi shawara saida Director Media dinshi ya sake kirana ina dagawa ya fara mun rashin kunya akan wai na zagi Young Sheikh, a take nace mishi kaje ka sake karanta abunda na rubuta idan har kaga inda na zagi Young Sheikh to ka mini Screenshot ka turo min sannan sai in saurareka mu fahimci juna, amma babu yadda za'a yi ka mini kage kuma ka kirani kana son ka zageni, na kashe wayan har yau dai basu sake kirana ba.

Na kawo muku wannan labarin ne domin nidai a fahimtana dasu shine; suna son Young Sheikh ya yi kaurin suna a Duniya ko'ina a sanshi kamar yadda aka san sauran manyan malamai.

Ya kamata su sani kaurin sunan da suke nema mishi bai kamata su dinga yin shi ta sigar hanyoyin da za'a zubar mishi da kima da Daraja ba, domin irin wannan labarin nasu duk mai hankali yasan karya ce kawai aka kirkiro. Allah ya tsarkake mana zukatanmu, yasa mu dace.

✍️
Comr Abba Sani Pantami,
CEO Hausa Daily Newspapers NIG LTD,
Marubuci, Mai Fashin Baki, Dan Jarida Mai Yada Labarai A Kafofin Sada Zumunta.

13/06/2023

DARIYAN MADUGU IS GOLDEN!

13/06/2023
12/06/2023

Yadda aka hadu a filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikwe dake babban Birnin tarayya Abuja, tsakanin Sanata Ibrahim Shekarau da amininsa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

📷 Hon Saifullahi Hassan

09/06/2023

Baiwar Iya Sarrafa Harshen Hausa.

Tunda nake ban taɓa ganin wanda Allah ya yiwa baiwa iya baiwa ta iya sarrafa harshen Hausa cikin hikima da jan hankali da kalmomi masu rikitar da tunanin mai ƙaramin kai ba, kamar Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo.

Na karanta litattafan Hausa masu yawa, kuma nima na rubuta littafi aƙalla ya kai 15 zuwa sama, na zauna da manyan Daktoci a fannin Hausa kuma wasu daga cikin litattafai na kafin a buga sai na kaisu wajen gogaggun Marubuta domin su tantance kalmomin da ya kamata nayi amfani dasu.

Amma duk da haka Duk lokacin da nake sauraron jawabin Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, babu abinda nake tunani sai cewa " Anya Kwamared ba Farfesan Farfesoshi bane a ɓangaren Yaren Hausa ?".

Saboda idan kaji yana faɗar wasu kalmomi na Hausa sai ka rantse da wani Yaren yake faɗarasu wanda ba Hausa ba, sai bayan kayi bincike mai zurfi ka gane kalmar Hausa ce.

Misali guda ɗaya da zan bamu akwai wata kalma wacce Kwamard yake faɗa "CIN DIRIRIN DINTSI", wannan kalma na ɗauki tsawon lokaci kafin Zuciyata ta nutsu cewa kalmar Hausa ce.

Na tabbata da Kwamared ya kasance Marubucin Littafin Hausa, to babu shakka sai ya zama Zakaran Gwajin dafin da babu kamarsa a Nahiyar Afrika ta fannin tasarifi da kalmomin Hausa.

Ina roƙon Allah ya ƙarawa Kwamared Aminu Abdulsalam Lafiya da ƙarfin Imani Amin.

Ukashatu Abubakar.
Kwankwasiyya Reporters Zamfara State.

Address

Rano

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00

Telephone

+2347043801244

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kwankwasiyya Family posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kwankwasiyya Family:

Videos

Share


Other Rano media companies

Show All

You may also like