09/09/2023
Kotu Ta Tabbatar da Nasarar Zaben Shugaba Tinubu
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta tabbatar da nasarar zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kotun, Mai shari'a Haruna Tsammani ya ce matakin hukumar zaɓe na ayyana Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen 25 ga watan Fabrairu, ya dace.
Matakin na zuwa ne bayan kotun ta kori ƙarar ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam'iyyar adawar Najeriya, Atiku Abubakar da maryacen Laraba.
Shi, da Peter Obi na jam'iyyar Labour da kuma jam'iyyar APM, sun nemi kotun ta soke nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaɓen Fabrairu.
Sai dai, ba a ga 'yan adawa irinsu Atiku da Peter Obi a zaman kotun na ranar Laraba ba, yayin da manyan jami'an gwamnati ciki har da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje s**a shafe tsawon wuni suna sauraron hukuncin kotun.
Da farko, kotun ta yi watsi da ƙarar Peter Obi na jam'iyyar LP da ta jam'iyyar APM.
Ta kuma ce duk ƙararrakin, waɗanda aka shigar don neman a soke cancantar zaɓen Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, ba su da tushe.
Alƙalan kotun biyar wajen gabatar da hukuncin, wanda s**a shafe tsawon wunin ranar Laraba, suna gabatarwa.
Sun riƙa karɓa-karɓa wajen yin bita da karanta hujjoji, tare da tsefe bayanai, kafin bayyana matsayarsu a kan ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar.
Tuni fadar shugaban Najeriya ta fitar da sanarwa, inda ta ce Shugaba Tinubu ya yi maraba da hukuncin kotun cike da tsananin sanin nauyin da ke kansa, da kuma shirin hidimtawa dukkan al'ummar Najeriya.
Shugaban na Najeriya ya kuma bai wa al'ummar Najeriya tabbacin mayar da hankali wajen cika ƙudurinsa na samar da ƙasa mai haɗin kai da zaman lafiya da bunƙasar arziƙi.
Tinubu ya kuma ce ya yaba wa tsayin daka da jajircewar bin diddigin komai da kuma ƙwarewa daga alƙalan kotun biyar a ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Haruna Tsammani ga fashin baƙin doka.
Tinubu ya ce ya yi imani cewa 'yan takarar shugaban ƙasa da jam'iyyun siyasar da s**a yi amfani