26/06/2023
TARIHIN SHI'A DA AKIDOJINTA
KASHI NA 11
Daga Sheikh Saleh Sani Zariya
Cigaba daga inda malam yake magana akan ruwayoyin Tabari dangane da Ibn saba.
Majinginar at-Tabari a kan Kissar Ibin Saba’i
Idan kuwa muka bibiyi majinginar at-Tabari din – kan shi – a kan wannan kissa, wadda kusan duk wadanda s**a rubuta tarihin Ibn Saba’ da cewa Shi’a ta bayyana ne a lokacin Khalifancin Usman bin Affan, s**a dogara da ruwayarsa, zamu gan shi yana jingina ta ne a kan ruwayar da silsilarta ke farawa da wani mai suna Sarriyu (bincike a kan nasabarsa yana zuwa nan gaba), a karshe kuma yana karewa da wani mashbuhin mutum mai suna Saif bin Umar at-Tamimi – ko daga littafin shi Saif din - wanda ambatosa ke zuwa nan gaba. Idan muka koma tarihin at-Tabari mai suna Tarikh al-Umam Wal-Muluk, za mu ga, ba kawai ya takaita da jingina da Saif a isnadin wannan kissa ba ne, kissarsa ta Ibin Saba’ ma ta jingina ne - kacokan - a kan shi (Saif din)!! da cewa at-Tabari bai ruwaitota ta wata hanya sabanin hanyar wannan mutumin da aka jahilci hakikaninsa ba.
A wajen ambaton abubuwan da s**a faru a shekara ta talatin zuwa shekara ta talatin da biyar bayan hijra, at-Tabari ya fitar da hanyoyin da s**a shafi wannan kissa daidai da yadda ya zo a cikin littafin al-Riddah wal-Futuh Wa kitab al-Jamal Wa Masiiri A’isha wa Ali, wallafar Saif bin Umar at-Tamimi (bin diddigin Qasim as-Samarra’i, bugu na 2 na Dar Umayya dake Riyad, na shekarar hijra ta 1418, shafi na 57-58), daidai da yadda al-Allama al-Askari ya fitar a juz’in farko na littafinsa al-Ustuura as-Saba’iyya shafi na 33-38, inda ya jero ruwayoyi uku kamar haka:-
Ruwaya ta Daya: Sariyyu ya ba ni labari, ya ce: Shu’aibu ya ba mu labari, ya ce: Saif ya ba mu labari daga Atiyya, daga Yazid al-Saqa’asi, ya ce: [Abdullahi bin Saba’ – shi ne wannan dan bakar-mace – ya musulunta ne a lokacin mulkin Usman na da shekaru shida. Mutanen Sham sun kasance karkashin Haramomin nan biyu (na daular Umayyawa), don haka bai iya yaudararsu ba; wannan ya sa ya tafi Basara, ya sauka a wajen (’yan kabilar) Abdul-Qais, ya dogara da wadannan mutnen (na wannan kabila); labarinsa ya isa ga Ibin Aamir sai ya kore shi. Daga nan ya nufi Kufa a shekara ta takwas (na mulkin Usman), ya sauka a wajen (wannan kabila ta) Abdul-Qais, inda wasu mutane da s**a ballewa Sa’id s**a tafi gare shi, a tare da su akwai Ashtar da Abu Zainab da Abu Murawwa’u da (’yan) wannan dabaka; sai Sa’id ya aika masa da cewa: “Me ke isowa gare ni cewa kana fadin magangnu (marasa kyau) kuma kana karanta ayar da take cewa:
{Sai muka yi hukunci zuwa ga Bani Isra’ila a cikin littafi cewa lallai za ku yi fasadi a ban-kasa har sau biyu} (al-Isra’i: 4), alhali su (ba wasunsu ba) ne wadanda s**a yi fasadi a ban-kasa sau biyu”. Sai (Saif) ya amsa masa da cewa: “mu muka fi sanin zancen Banu Isra’ila fiye da ku”; sai wadannan (da suke tare dashi) s**a ce: “kwarai kuwa, ya yi gaskiya”. sai Sa’id ya ce: “karya yake yi, ku ma karya ku ke yi! wallahi in banda an umarce ni da kawar da kai daga gare ku da kun same ni da daci (wato da ya tsananta daukar mataki a kansu)”. A kan haka ya kore shi (Ibin Saba’) da mutanensa. Sai ya fita ya nufi Sham, bai samu abin ya yi nufi a can ba; sai ya tafi Masar, inda mabiyansa s**a yawaita, sai ya rubutawa ’yan’uwansa (wato masu ra’ayinsa) dake garuruwa; ya karfafe su a kan batan da suke kai.
Shi ne farkon wanda ya yada masu kiran mutane zuwa fito-na-fito” (duba Kitab al-Riddah wal-Futuh, na Saif bin Umar, shafi na 56-57, da al-Tamheed wal-Bayan fi Maqtali as-Shahid Uthman, na Muhammad bin Yahya al-Maliqi, bugun madaba’ar Darul-Kutub al-Ilmiyya dake Beirut, yadawar Muhammad Ali Baidun –mai yada littafan Ahlus-Sunnati wal-Jama’ah, shafi na 55 – kamar yadda ya zo a littafin al-Ustuura as-Saba’iyya, na al-Allama al-Askari, juz’i, na 1, shafi na 34).
Cigaba a kashi na (12)