![IDAN AN JARRABEKA DA WANI ZUNUBIN DA KA KASA DAINAWA,Sadaka Zatai Maka Maganin Shi.NA FARRKO-MANZON ALLAH (SAW) YACE:الص...](https://img4.medioq.com/809/567/441966668095679.jpg)
21/11/2022
IDAN AN JARRABEKA DA WANI ZUNUBIN DA KA KASA DAINAWA,
Sadaka Zatai Maka Maganin Shi.
NA FARRKO-
MANZON ALLAH (SAW) YACE:
الصدقة تطفئ الخطيئة كما يطفئ الماء النار، رواه الترمذي
Sadaka Tana Kashe Zunubi Kamar yadda Ruwa Yake Kashe Wuta.
فإن للصدقة تأثيرا عجبا في دفع البلاء حتى ولو كانت من الفاجر أو الظالم بل من كافر، فإن الله يدفع بها أنواعا من البلاء
Ibnul Qayyim Rahimahullah Yace:
Lallai Acikin yin Sadaka Akwai Tasiri Mai Ban Mamaki Cikin Tunkude Bala'o'i, Koda Kuwa Wanda Yayi Sadakar Fajiri ne, Ko Azzalumi, Kai Koda Kafiri ne, Allah Yana Tunkude Nau'ikan Bala'o'i da Ita.
YAQARA DA CEWA:..….
إعلم أن حاجتك لأجر الصدقة أشد من حاجة من تتصدق عليه بتلك الصدقة
Kasani Buqatuwarka ga Ladan Sadaka, Yafi Tsananin Buqatuwar Wanda ka bawa Sadaka ga Sadakar
ALLAH (SWT) YACE:
فأما من أعطى واتقى، وصدق بالحسنى فسنيسره لليسرى
Duk Wanda ya Bayar da Sadaka Yaji Tsoran Allah, Kuma ya Gazgata Allah da Manzonsa, Tabbas Zamu Sauqaqe Masa izuwa ga Sauqi,
Ibni Abbas Yace (Aljannah)
DAYA DAGA CIKIN SALIHAI YACE:
Idan Aka Jarrabeka da Wani Zunubin da Kake Son ka Daina Aikata Shi Ka Kasa Daina wa,
Ka Yawaita Yin Sadaka da Niyyar Allah ya Yaye maka Shi,
Allah Zai Rabaka da Zunubin, Kuma Zunubin da ka Aikata a Baya Za'a Mayar Maka dashi Lada a Mizaninka.
BAHAUSHE YAYI GASKIYA CEWA:
Sadaka Maganin Bala'i da Musibah.
IDAN KAYI SADAKA DON ALLAH RIBA BIYAR ZAKA CI.....
1- Za'a Tunkude Maka Bala'i
2- Za'a Kankare Maka Zunubi
3- Za'a Rubuta Maka Lada
4- Za'a Nunka Maka Abin da ka bayar,
5- Za'a Sanya ka Cikin Masu Shiga Inuwar Allah Aranar Alqiyamah.
ALLAH (SWT) YACE:
وما أنفقتم من شيء فهو يخلفه، وهو خير الرازقين،
Duk Abinda Kuka Bayar na Wani abu Allah Zai Mayar Muku da Gurbinsa, Shine Mafi Alkairin Masu Arziki,
ABUBAKAR AMINU ALI