Jibwis Social Media Gadabuke

Jibwis Social Media Gadabuke Da'awa

27/08/2023
12/08/2023
30/07/2023

Albayan Islamic Academy 1445/2023

28/06/2023

Sallan IDi 1444/2023

27/06/2023

Jibwis Gadabuke EID
Venue: GSS Gadabuke road
Time: 9:00am

Manzon Allah SAW yace Idan bawa ya yarda da laifinsa sannan yanemi gafarara Allah to Allah zaigafarta masa, Allahumma in...
21/06/2023

Manzon Allah SAW yace Idan bawa ya yarda da laifinsa sannan yanemi gafarara Allah to Allah zaigafarta masa, Allahumma inni zalamtu nafsi fagfirli fa innahu layagfiruzzunuba illa'anta

19/06/2023

DEAR JANNAH ASPIRANTS,
Fasting of the first ten days of DHUL - HIJJAH is highly recommended.

Manzon Allah (SAW) ya ba da labarin cewa: "An yi wani ɗan kasuwa da ya kasance yana bai wa mutane bashi. Duk lokacin da ...
04/06/2023

Manzon Allah (SAW) ya ba da labarin cewa: "An yi wani ɗan kasuwa da ya kasance yana bai wa mutane bashi. Duk lokacin da ya biyo sawun kuɗinsa in ya ci karo da wanda ke cikin ƙunci sai ya ce wa ma'aikatansa ku ɗaga wa wannan bawan Allah ƙafa da fatan mu ma Allah ya yi mana rangwame. Sakamakon haka Allah ya yafe masa"

Ka kiyayi cutar da rai wanda ba zata iya rama cutarwan da ka yi mata ba sai dai ta hanyan kuka da zata yi wanda babu mai...
28/05/2023

Ka kiyayi cutar da rai wanda ba zata iya rama cutarwan da ka yi mata ba sai dai ta hanyan kuka da zata yi wanda babu mai jin abun da take faɗa in banda Allah.

✍️ Umar Shehu Zaria
07 Dhul-Qa’dah, 1444
(27/05/2023).

Allah Sarki Rayuwa, Jiya ba yau ba.🤔Hotunan waɗanna malamai za ka iya ganewa a nan?Waɗanda s**a rasu Allah ya musu Raham...
26/05/2023

Allah Sarki Rayuwa, Jiya ba yau ba.🤔

Hotunan waɗanna malamai za ka iya ganewa a nan?

Waɗanda s**a rasu Allah ya musu Rahama, waɗanda suke Raye Allah ya ƙara wa Rayuwa Albarka 😍 🥰🤲


Duk ƴan Aljannah Matasa za su kasance babu tsufa kuma tufafinsu ma ba zai tsufa ba, in ji Manzon Allah, sallallahu alaih...
25/05/2023

Duk ƴan Aljannah Matasa za su kasance babu tsufa kuma tufafinsu ma ba zai tsufa ba, in ji Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama.

Yaa Allah ka sa muna daga cikin su.

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!! Shuwagabanni Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa'iqamatis-sunnah Reshen Jahar Nasarawa Al...
25/05/2023

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!
Shuwagabanni Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa'iqamatis-sunnah Reshen Jahar Nasarawa

Alh Abdullahi Muhammad Gindau Magayakin Lafia
(Shugaban Kungiyar JIBWIS Jahar Nasarawa)

Ustaz Imam Dawud Yahaya Abubakar Abu Faiza Magayakin Loko (Shugaban Majalisar Malamai Na Jahar Nasarawa)

Alh Ahmad Abdullahi Sani (Daraktan Agaji Na Jahar Nasarawa)

Suna Masu Farin Cikin Gayyatan Al-Ummar Musulamai Zuwa Ga Garumin Waazin Goron Sallah Wanda Insha Allah Zai Gudana Kamar Haka :

Ranar Asabar 27/5/2023
(7/11/1444)
A Cikin Garin Giza dake Karamar Hukumar Keana, A Jahar Nasarawa

MALAMAI MASU WA'AZI
Malamai masu wa'azi.
*Imam Dawud Yahaya Abubakar Abu Fa'iza
*Sheikh Abubakar Aliyu Musa Almorawee
*Mal. Shu'aib Yusuf Galadiman Wamba
*Sheikh Adam Ibrahim Ishaq (Almadniy)
*Mal.Kabiru Umar Bawa Keffi
*Mal. Hassan Isma'il Okinawiy Keana *Mal.Yusuf Haruna karu.
*Mal.zakariyya Abubakar Usman Nsarawa.
*Dr. Ali Jibirin ( Mal.Uba Doma)
*Mal.HARUNA NA KUDU NASARAWA EGGON,
*Mal. Jamilu Umar Akwanga,
*Mal. Aminu Muh'd Musa Lafia,
* Mal. Muh'd Kabir Adam Gudi,
* Mal. Shu'aib Muh'd Sabon Gida,
*Imam Isma'il Alhassan Dal Wamba,
*Mal. Abu-Fauzan Toto,
*Mal. Abubakar Salihu As-Sudaniy Awe.

ALARAMMOMI SUN HADA DA:

Alaramma Abdulkareem Akwanga
Alaramma Abdulmumin keana
Alaramma harith umar keffi
Alaramma Tamim sabon gida
Alaramma zakariya musa Tunga awe
Alaramma Abdulshakur s pada azara
Alaramma Suleiman Ibrahim
Alaramma Muhammad Gambo karu
Alaramma Shafi'u umar karu
Alaramma Ana's Muhammad karu
Alaramma Ilyasu Muhammad keana
Alarama ishaq mu'az Doma
Alarama Badamasi Aliyu Obi

Da sauran malamai dakuma alarammomi

Allah ya bada ikon Halarta Ameeen

Daraktan Media Na Jahar Nasarawa
Engr Hashim Muhammad Bello

FURSUNONI SUNYI KUKAN RABUWA DA MALAMLokacin da mushrikai da matsafan Bauchi s**a yi sanadin shigar Malam Idris Abdul-Az...
23/05/2023

FURSUNONI SUNYI KUKAN RABUWA DA MALAM

Lokacin da mushrikai da matsafan Bauchi s**a yi sanadin shigar Malam Idris Abdul-Aziz Jami'ar Annabi Yusuf wato gidan yari, lokacin da Malam zai fita daga gidan yarin fursunoni s**ayi ta kuka don basa son rabuwa dashi

Bayan Malam ya karantar da fursunoni a gidan yarin, ya dauki nauyin majinyata har da wanda ake masa chemotherapy na cutar kansa

Sannan Malam ya 'yanta fursunonin da aka dauresu saboda sun kasa biyan kudin tarar da Kotu ta musu, ya biya musu kudin daga aljihunsa s**a fita daga gidan yari

Dama mun fada muku, indai don Allah ne wannan daurin da aka yiwa Malam Idris alheri ne a gareshi da kuma karin daukakar daraja, gashi nan mun gani

Wannan shine banbancin Malamin Allah da Malaman bidi'ah mushrikai 'yan damfara

Yaa Allah Ka kara wa Malam daraja, Ka tsareshi daga dukkan sharri na waliyyan shaidan a doron Kasa

Allah ya mana tsari da riya
22/05/2023

Allah ya mana tsari da riya

Alhamdulillahi, an yi aiki lafiya An kammala, Muna roƙon Allah ya ƙara wa Malam Lafiya DA Nisan kwana me Albarka 😍 😍 😍 😍...
21/05/2023

Alhamdulillahi, an yi aiki lafiya An kammala, Muna roƙon Allah ya ƙara wa Malam Lafiya DA Nisan kwana me Albarka 😍 😍 😍 😍


Manzon Allah (SAW) ya ce: "Ba ya dacewa da mumini ya ƙasƙantar da kansa" Sai aka ce: "Yaya ne ƙasƙantar da kai?" Sai ya ...
20/05/2023

Manzon Allah (SAW) ya ce: "Ba ya dacewa da mumini ya ƙasƙantar da kansa" Sai aka ce: "Yaya ne ƙasƙantar da kai?" Sai ya ce: "Mutum ya ja wa kansa bala'in da ba zai iya jurewa ba"

"Ku auri budurwa, domin sun fi iya zance mai dadi, kuma sun fi haihuwa sosai, kuma suna yarda da kadan(abinci da sauran ...
18/05/2023

"Ku auri budurwa, domin sun fi iya zance mai dadi, kuma sun fi haihuwa sosai, kuma suna yarda da kadan(abinci da sauran abubuwan bukatun rayuwa da zaka basu).

KARATUN SURATUL KAHFI SUNNAR ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALLAM A RANAR JUMA'AH.
12/05/2023

KARATUN SURATUL KAHFI SUNNAR ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALLAM A RANAR JUMA'AH.

"Duk wanda yake son abin dake cikin littafin shi na lahira ya burge shi to ya yawaita istigfari"In ji Manzon Allah (SAW)
11/05/2023

"Duk wanda yake son abin dake cikin littafin shi na lahira ya burge shi to ya yawaita istigfari"
In ji Manzon Allah (SAW)

Uƙbah Bn Âmir ya ce: "Na tambayi Manzon Allah (SAW) cewa mene ne abin da zai tseratar da ni?" Sai ya ce: "Ka kame harshe...
08/05/2023

Uƙbah Bn Âmir ya ce: "Na tambayi Manzon Allah (SAW) cewa mene ne abin da zai tseratar da ni?" Sai ya ce: "Ka kame harshenka. Sannan ka wadatu da zama a gidanka. Kuma ka yi kuka akan zunubanka"

Baka sanin an yi maka ni'ima sai idan baka a wurare uku:1. Asibiti. 2. Kurkuku. 3. Makabarta.In ji Sheikh Muhammad Aminu...
01/05/2023

Baka sanin an yi maka ni'ima sai idan baka a wurare uku:

1. Asibiti.

2. Kurkuku.

3. Makabarta.

In ji Sheikh Muhammad Aminu Ibrahim

Kar ka yi baƙin ciki alhalin al'amuranka suna hannun Allah, kar ka yanke ƙauna daga rahamar Allah alhalin dukkan burinka...
01/05/2023

Kar ka yi baƙin ciki alhalin al'amuranka suna hannun Allah, kar ka yanke ƙauna daga rahamar Allah alhalin dukkan burinka a cikin addinin Allah kake yin sa.

✍️ Umar Shehu Zaria
10 Shawwal, 1444
(30/04/2023).

"Kowane ɗan Adam yana da wani kaso na hassada a zuciyarsa, amma shi wanda ba shi da daraja shine yake bayyana ta, karimi...
30/04/2023

"Kowane ɗan Adam yana da wani kaso na hassada a zuciyarsa, amma shi wanda ba shi da daraja shine yake bayyana ta, karimi kuwa sai ya ɓoye ta" In ji Ibnu Taimiyah (RahimahulLah)

"Bawa ba zai yawaita ambaton mutuwa ba face  ya rage murna ya kuma rage hassada" In ji Abud-Darda'i (Allah ya ƙara masa ...
30/04/2023

"Bawa ba zai yawaita ambaton mutuwa ba face ya rage murna ya kuma rage hassada" In ji Abud-Darda'i (Allah ya ƙara masa yarda)

Ibnu Mas'ud (Allah ya ƙara masa yarda) yana cewa: "Ku daina adawa da ni'imar Allah" sai aka ce masa kamar ya kenan, Alla...
29/04/2023

Ibnu Mas'ud (Allah ya ƙara masa yarda) yana cewa: "Ku daina adawa da ni'imar Allah" sai aka ce masa kamar ya kenan, Allah shi gafarta malam? Sai ya ce: "Masu yi wa mutane hassada suna adawa ne da ni'imar Allah"

Asma'iy ya ce: "Na ga wani mutum ɗan shekara 120 a wani ƙauye, sai na gan shi lafiya lau ba alamar tsufa, sai na tambaye...
28/04/2023

Asma'iy ya ce: "Na ga wani mutum ɗan shekara 120 a wani ƙauye, sai na gan shi lafiya lau ba alamar tsufa, sai na tambaye shi sirrin ƙwarin jikinsa, sai ya ce: "Hassada na guje wa, shine jikina ya wanzu da lafiya"

YAWAITA SALATI GA MANZON TSIRA:Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce: "Ku yawaita salati a gare ni a ranar J...
28/04/2023

YAWAITA SALATI GA MANZON TSIRA:

Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce: "Ku yawaita salati a gare ni a ranar Juma'a da daren Juma'a. Duk wanda ya yi mun salati sau ɗaya (1), Allah zai masa salati goma (10). Sahih al-Jami' 1209.

MASU KUDI SUN TAFI DA LADA!!!Wannan Shi ne Alhaji Yusuf Fantiya Attajirin da ya fi temakawa Sunnah da kudinsa a jihar Ka...
27/04/2023

MASU KUDI SUN TAFI DA LADA!!!

Wannan Shi ne Alhaji Yusuf Fantiya Attajirin da ya fi temakawa Sunnah da kudinsa a jihar Kano Shekaru masu yawa da su ka wuce

Alhaji Yusuf Fantiya shi ne ya Gina Masallacin Sunnah na kofar Wambai shi ya bayar da filin da aka Gina Masallacin Usman bin Affan da ke Gadon kaya

Shi ya bayar da filin da aka Gina Masallacin Al'muntada daka Dorayi shi ya bayar da filin da aka Gina Masallacin Malamin mu Dr Bashir Aliyu Umar (OON) na Alfurqan da ke Unguwar Nasarawa Kano a Lokacin an ta ya filin Masallacin Million Dari biyu (200) amma ya qi siyarwa ya bayar aka Gina Masallacin na Alfurqan

Shi ya Gina Masallacin kofar gidansa Wanda mutane da yawa suke tururuwar zuwa

Shi ne Attajirin da Lokacin da zai ta shi ya chanja gida makotansa s**a dinga zanga zangar basu yarda ya tashi ba Saboda yadda yake temaka musu

Shi ne Attajirin da in zai yi rabon ragon Laiya yana duba makotansa su arba'in (40) hagu da dama ya raba musu Ragon Laiya wadan nan kadan kenan daga cikin abubuwan alkhairinsa

Muna addu'ar Allah ya saka masa da alkhairi ya kara masa Lafiya da nisan kwana mai amfani.

✍️ Abbas Adamu - 27 - 4 - 2023 -


INNAA LILLAHI WA INNAA ILAIHI RAJI'UNAllah ya yi wa Sheikh Kabir Ahmad Azare rasuwa.Shehin Malamin ya rasu ne bayan fama...
27/04/2023

INNAA LILLAHI WA INNAA ILAIHI RAJI'UN

Allah ya yi wa Sheikh Kabir Ahmad Azare rasuwa.

Shehin Malamin ya rasu ne bayan fama da jinya a babban asibitin "Medical Center" dake garin Azare a jahar Bauchi.

Za'a gabatar masa da janaza gobe Juma'a da misalin karfe 10:00am na safe a kofar gidan marigayin dake unguwar Makara huta anan cikin garin Azare dake karamar hukumar Katagum a jahar Bauchin Naijeriya insha Allah.

Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, a madadin kungiyar wa'azin musulunci ta JIBWIS a tarayyar Naijeriyar na mika ta'aziyya ga 'yan uwa da iyalai, a'ummar garin Azare da ta karamar hukumar katagum, dama jihar Bauchi da kasa baki daya na alhini akan rasuwar wannan bujumin Malami wanda ya yiwa addini hidima tun yana matashi har zuwa lokacin rasuwar sa.

Allah ya jikansa da rahama, ya kyautata makwanci. Amin.

Jibwis Nigeria 🇳🇬
Hassan Idris Machina As-salafy

Address

Nasarawa

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jibwis Social Media Gadabuke posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share